Showing 90001 words to 93000 words out of 279257 words

Chapter 31 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34677

ba shi da abokin hira sai ita, komai zai yi sai ya fada mata tufafi ma ita take bashi shawarar wadanda zai saka, a gidanta yake zaune. Sai dai yana haduwa ya Afrah sai ya fara canja mata, bayan kuma ya guji matar da ta so ya aura da farko, har ta kai ya kasa zama a gidan kamar yadda ta bukata saboda Afrah ta nuna masa ta fi sha'awar zama a gidanta ita kadai ba dole sai a gidan mahaifinsa ba kamar yadda Hajiya Fatee take so, shi ma kuma da yayi tunani sai ya yarda da shawararta, yana yin auren sai rayuwarsa ta koma gaba daya a gidan matarsa, zabin tufafinbda zai saka wasa da dariya ko wani abun na rayuwa da matarsa yake ba da ita ba, idan ma zai nemi shawararta sai idan wani abun ne da ya shafeta ko kuma yake da muhimmanci sosai, idan zai siya mata tufafi zai dauki Afrah su tafi tare Afrah ta zaba mata tufafi mai kyau mai tsada su kawo mata, sai dai hakan baya kara komai sai wutar kiyayyar Afrah a zuciyarta, duk kuwa da kasancewar tana kyautata mata. Wannan ya saka ta fara zagon kasa tana son ya saki matarsa shi kuma ya nuna mata yana sonta sosai, kuma idan ya rabu da ita ba shi da mai rike masa yaransa.


Cikin matukar damuwa Fadeel ya isa gidansa, ya samu kansa da zama a cikin motar ya kasa budewa ya fita, shi dai a ra'ayin kansa ba shi da burin aure mace fiye da daya saboda baya son tashin hankali kuma yana son matarsa tana sonsa, ya yanzu ma yana cikin tashin hankalin rashin jituwar da suke samu da Hajiyarsa ina ga ya kara aure, and all this love da biyayya da Afrah take masa ya rasa da me zai saka mata sai kishiya. Jin yayi ana kwankwasa kofar motar yana daga kai sai yayi arba da annurin zuciyarsa tana aiko masa da murmushi. Ta tsaba ado kamar Sequence Wax din da ya siya mata a gurin Khadeeja Candy ta karbi jikinta sai kyali take kamar an wantsa mata gold. Ya sauke gilashin motar

 Madam

 Yallabai yau lafiya kake kuwa

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya bude motar ya fito ya rufe.

 Habibina fada min me yake damunka daman ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tun jiya na lura da haka, me ke damunka?

Sai da ya kasa bakinsa sau biyu sannan ya iya aje numfashi a muhallinsa.

 Afrah yau na ga Hajiya a cikin wani hali da ban taba ganinta ba, ban san wata rana da Hajiya ta zubar da hawaye saboda da ni ba, sai na ranar da aka daura aurena shi amman na farinciki ne yau kuma akasinsa ne

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, me ka aikata haka wanda ya bata mata rai Abban Aiman?

Yayi shiru yana kallonta ba tare da ya amsa mata ba, tana ganin haka ta san inda matsalar take kuma bata bukatar karin bayani, a take zuciyarta ta fara bugawa.

 Cewa ta yi ka rabu da ni? Hajiya ta ce ka sake ni ne? Dan Allah karka kara minti daya a gidan nan baka aikata abun da mahaifiyarka ta bukata ba, akwai pen da takarda a cikin motar nan dan girman Allah ka dauko ka rubuta min matukar haka ne silar zubar hawayenta

 Ba saboda haka ba ne

Ya amsata still yana kallonta.

 To minene?

 Aure take son na kara....

Bugun zuciyar da ta ji a yanzu da ya fada mata bukatar Hajiya ya dara wanda ta ji a lokacin da take zargin sakinta Hajiya ta ce yayi. Sai dai ko kadan bata yarda ta nuna masa ba, sai ma dariya data fara yi dariya sosai har sai da mai gadinsu ya juyo ya kalli gurin da suke tsaye.

 Shi ne kawai? Oh Ya Rabbi ai Hajiya ta yi min da sauki, ni a yanzu ba ni da tashin hankali kamar na rabuwa da kai, ko da raina Hajiya zata ce ka cire ka kawo mata duk mai sauki ne matukar bata ce na rayu babu kai ba

Ta mamaki yake kallonta babu alamar tashin hankali a tare da ita sai ma farinciki.

 Afrah you're joking?

Ta ware hannayenta ta rika hannunsa suka nufi cikin gidan, sai da ta raka shi har dakinsa ta taimaka masa ya fara cire tufafinsa sannan ta ce.

 Yallabai ko da ka auro ni fa, mahaifina mace uku yake aure, na bude ido a gidan mu na ga mahaifiyata da abokan zama ba ita kadai ba

 I know amman na san kina hakan ne just to support me amman ku mata baku son kishiya ai

 Abban Aiman idan ban taimaka maka ka yi ma Hajiya biyayya ba ni da kai duk a wuta zamu tashi, karka manta ni fa yar gidan Malamai ce, an karantar da ni ni ma na karantar, na san hakki uwa akan yaya ta ina zan yarda Hajiya ta sake zubar da hawaye saboda mu? Dan Allah karka fara tunanin wani abu ko ka damu, kuma wanda Hajiya take so zaka aura

Ta fada tana lakatar hancinsa tana dariya as normal yadda ta saba kamar be fada mata komai ba.

 Shiga ka yi wanka ka fito bari na shirya abinci, kuma sauran idan ka fito ka manta baka yaba kwalliyar da na yi maka ba

Ta bukata sannan ta fice tana dariya, shi dai mamakin karfin halinta ya hana shi motsawa daga inda yake ma. Tana fita dakin ta nufi kitchen dinta kofar kitchen din ta fara rikewa ta kai hannu ta dafa zuciyarta dayan hannun kuma ta rike kofar kitchen din kamin ta saki ta nufi sink ta dora hannayenta hawaye suka fara floating.



HURRIYA POV.

Sai da aka fara kiran Magariba sannan ta fito daga Garden din ta dawo cikin falon, dakinta ta shiga ta yi alwala ta yi sallah sannan ta sauko Namra na yi mata magana.

 Na tura miki kudin

Ta dauri ta nufi gurin da take zaune ta rumgume ta.

 Na gode sosai Yaya Namra

 Never mind yar kanwata

Namra ta amsa mata tana dariya, Hurriya ta zauna kusa da ita tana matsar yatsun hannunta.

 Yaya Namra

Ta dago ta dubeta.

 Ina son na tafi gidansu Husna dan Allah

 Yanzu?

 Eh ba zan dade ba

 Okay sai kin dawo

 Amman Momy bata sani ba, kar ta zo duba ni, kuma kin san bata son a shiga dakinta balle na fada mata

 tafi zan fada mata

Ta tashi cikin jindadi da murmushi a fuskarta ta sake haurawa sama ta shiga dakinta, jakarta ta bude ta dauko ATM dinta ta boye a cikin rigarta sannan ta dauko hijab ta saka ta sake saukowa ta fice. Tafiya take kamar ana dagata sama saboda sauri tsoronta kar wani ya fito daga yaran Hajiya Kaltume su hanata fita ko kuma Appa ya dawo a daidai lokacin ta san shi ma ba zai barta ta fita ba. Kamar an korota haka ta rika knocking gate din gidansu kawarta kuma Neighbor dinsu a house four ne tsakaninsu. Mai gadin na bude gate din ta fada da sauri.

 Ina wuni Baba

 Lafiya Kalau Hurriya ce

 Ni ce Baba sannu da aiki

 Yauwa

Ta nufi main door din tana tafiya a hankali saboda ta shigo cikin gidan. A falo ta samu kawarta da sisters dinta suna hira, Husna na ganinta ta tashi da sauri ta rumgume ta

 Oyoyo Hurry

Hurriya ta yi dariya, sai da ta gaishesu gaba daya sannan suka shiga dakin Husna. ATM dinta ne first abun da ta fara danka mata.

 Me zan yi da Atm

 Ba ke na bawa ba, dan Allah taimako na ke son ki yi min Husna kin ga ke ana barinki fita, dan Allah ki kaiwa Amma akwai kudi a ciki 20k dazun Yaya Namra ta saka min, kin ga ni ba school nake zuwa ba yanzu balle na biya, kuma idan na ce zan je Hajiya ba zata bari ba, Appa ma fada yake yi

 In Shaa Allah zan kai mata, Hurriya wai ya zancen makarantar ki, an kusa rufe siyar da form fa, kin ga da kina zuwa makaranta irin wannan duk ba zai gagara ba sai ki yi satar hanyar kawai ki tafi

 Ban sani ba Husna, ba ni zan saka kaina makaranta ba Appa kuma be yi wani motsi ba, sun kyale ni haka nan zama kawai nake, gidan ma babu dadi

Ta sauke kanta kasa hawaye suka fara sauko mata.

 Husna I'm lonely, komai baya min dadi yanzu i miss those old days da zan zauna na yi hira da Appana yana dariya, na yi marmari jin muryar Amma, na yi marmarin ganinmu a inuwa daya, na yi marmarin Hamad fadan da muke ma na yi marmarinsa, Husna kowa yana da uwa a gidan yana da abokin hira ni kuma ba ni da shi, idan suna bukatar abu kowa zai je gurin mahaifiyarsa ta yi masa ko Appa ni kuma ba ni da uwa a gidan, idan kuma na kusanci gurin da Appa yake sai ya rufe ni da fada, baya ma son ganina

Husna ta dafa kafarta tana jin tausayinta.

 Ki yi hakuri Hurriya, wata rana komai zai wuce ya zama tarihi

Hurriya ta kalleta hawaye na mata sallama.

 Hakan na nufin Appa ba zai sake so na kamar da ba kenan? Hamad ba zai dawo ba?

 Ba haka nake nufi ba, ina nufin wata rana rayuwar farinciki zata dawo komai zai wuce, dazun ma sai da muka yi hirarki da Umma ita ma take tambayata maganar karatunki, tace kina bata tausayi sosai saboda halin da kike ciki

 Husna ina cikin kunci ina jin rashin sakewa sai na ji kamar a wani guri nake rabe ba a gidan mahaifina ba

 Komai zai wuce Hurriya, ki yi hakuri, me Amma zata yi da wannan kudin?

Ta share hawayenta.

 Gwaggo ta fada min an kai Amma gurin magani kuma mutumen yace sai an bashi 150k shi ne dazun da Yaya Namra zata siya min abu na ce bana so ta ba ni kudin kawai zan bawa Amma, saboda Gwaggo ta ce basu da kudi yanzu duk sun kashe kudin da ya rage musu gidan da suke ciki za a siyar ni kuma bana son a siyar da gidan, kuma ban isa na tunkari Appa na ce ina son kudi ba, sai ya fara min fada ni tsoron ganinsa ma nake yanzu

 Innalillahi Abun har ya kai haka? Wallahi duk wanda ya raba ki da mahaifinki ya ci amanarki Hurriya, da a baya ne ko miliyan kika ce kina so Appa zai baki. Ya Allah ka dubi Amma ka bata lafiya, zan fadawa Umma in Shaa Allah zata cika kudin

Hurriya ta rumgume ta da sauri.

 Na gode Husna, na gode Allah ya saka miki da alheri

 Ba komai, Allah ya kawo miki sauki

 Ameen, zan tafi kar a fara nema bana kusa

 Okay muje ki gaishe da Umma sai na raka ki

Sun tashi a tare Husna ta saka Hijab dinta suka fito daga dakin, Husna ce ta yi mata jagora zuwa dakin Ummanta not because of gidan yana bakonta sai dan zata fi sakewa idan Husna ta shiga gaba. Mahaifiyar Husna ta amsa da far'a tana sakawa Hurriya Albarka sannan ta kara ja mata kunne akan addu'a da kuma hakuri.

 Karki yi wasa da addu'a kina ganin yadda aka maida mahaifiyarki bayan an cireta a gidan ubanki, ke ma kuma an shata muku layi, ki yi ta fadawa Allah matsalarki, sannan ki kara hakuri ki yi da hakuri Hurriya komai zai wuce

 In Shaa Allahu Umma na gode

Ta tashi ta fito, suka jero da Husna a harabar gidan suna tafi suna hira, sam bata lura da Yayan Husna dake tsaye can gefe dare da Abokinsa yana hira ba har sai da abokin ya kirata.

 Hey Young Lady...

A tare suka juya suna hada ido sai ya sakar mata mata murmushi ita ma ta dan yi masa murmushinta mai tsada kadan ta gaishe su.

 Ina wuninku

Mutumen ya tako ta karaso gurin da suke tsaye tare da Yayan Husna, still tufafin da ta fara ganinshi da su ne sanye a jikinsa wato wando sojoji da bakar rigarsu T-shirt.

 Kin gane ni

Ta daga kai kadan sai yayi murmushi.

 Ina kawarki?

 Yayata ce

 Amma fa ta iya driving, kun ba ni wahala dazun fa, but still i enjoyed it, it was fantastic

Bata ce masa komai ba har ya sake wata tambayar.

 Nan unguwar kuke

Nan ma bata amsa masa ba, Yayan Husna ya tambaye shi.

 Ka santa ne Ethiopian?

 Yeah i meet them today at Sarauta's Mall

Ta juya zata fara tafiya.

 Please ki kirata mu gaisa idan kusa ne, or invite me na je na gaishe da Yayarmu

 Zan fada mata

Ta fada ba tare da ta juyo ba.

 Okay ina nan ina jira

As always bata ce masa uffan ba, sai kallon juna da suka yi da Husna, sannan ta shiga fadawa Husna yadda suka hadu...

5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5?? 08036126660


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 1?? 4??

Har bakin gate din gidansu Husna ta rakota sannan suka yi sallama ta shigo ciki Husna kuma ta juya ta koma. Hanayenta nade cikin hijab ta shiga falon Momy, Namra na zaune a gurin da ta barta tana operating wayarta, Momy kuma na zaune gefenta a dayar kujerar tana cin abinci. Hurriya ta fara isa gurin Momy ta risina ta gaisheta.

 Momy sannu da gida

 Ina kika fito

Namra ta yi karaf ta ce

 Ta fada min da zata fita

Momy ta dauke kai ba tare da ta saks cewa komai ba. Hurriya ta tashi ta nufi gurin da Namra take zaune ta kai bakinta saitin kunnenta.

 Yaya Namra wannan mutumen da muka gani dazun yayi tsere da ke har kika karbi katinsa, na ganshi yanzu a gidansu Husna tare da Yayanta kuma ya ce a kira ki ku gaisa

Namra ta wara ido tana kallonta da dan mamaki. Like really. Hurriya ta daga mata kai.

 Yace ba zai tafi yana can yana jiranki sai kin zo

 Ya akayi ya ganeki?

Namra ta tambaya kadan kadan tana dan murmushi, Hurriya ta daga kafadunta alamar bata sani ba.

 Okay zan je

Hurriya ta yi murmushi tana amsa mata da kai sannan ta daga ta nufi dakinta. After ta maida kofar ta rufe ta cire hijab dinta ta zauna bakin gadonta ta dauko Qur'anen ta bude tana karatu, bata daga ba sai da aka kira sallah Isha'i sannan ta aje ta dauki hijab din ta saka ta gabatar da Sallah Isha'i. Tana sallamewa Namra ta turo kofar dakin ta shigo tana murmushi.

 Na je mun gaisa, amman ya tambaya wai ko ni na hana mi dawowa

Hurriya ta yi murmushi tana karanta addu'o'in sallame sallah. Namra ta zauna bakin gadon Hurriya.

 Yana da ban dariya, he's nice na yi mamaki yadda ya gane ki

Hurriya ta shafa addu'ar da take ta mike tsaye tana kallon Namra irin duban nan na tuhuma (Zargi)

 Yaya Namra.... 

 What? Nonono please daga haduwa da mutum? Don't please

Ta tashi da sauri ta fice tana dariya, Namra ma dariyar ta yi ta hau saman gadonta ta kwanta, zuciyarta cike da farinciki alkwarin da Husna ta yi mata domin ta san zata cika. Washe gari da yamma Husna ta dawo mata da martanin cewar ta fadawa Ummarta kuma ta cika kudin and the most beautiful thing is ta tafi ta kaiwa Gwaggo kudin har suna saka mata albarka suna godewa Umma. Hurriya ta rumgume ta da sauri tana murna.

 Na gode sosai Husna

 Ba komai tarenmu y wuce haka, and Umma ma na ji tana magana akan makarantarki domin ta nuna damuwarta sosai akai gaskiya

 Ni ma abun yana damuna, ina son na yi ma Yayana magana shi zai iya magana da Appa ko Allah zai saka ya tuna da ni ya saka ni

 Hurriya da neman magana waya ce miki Appa ya manta da ke?

Ta yi dariya.

 Haka dai nake gani

 kin ga bari na tashi ke ma haka kike da kin zo gidanmu baki wani dadewa sai ki fara cewa zaki tafi

 Laaaa ai to ni kin san yadda gidanmu yake ba ni da freedom ne, amman ke ba a miki tsananin da ake min, dan Allah ki zauna Husna na jidadin zuwanki

 Ba zan zauna ba, muje ki rakani

 Idan naje zan sake dadewa

 Naki wayon zan tafi idan ba zaki rakani ba

Hurriya ta tashi da sauri ta dauki Hijab dinta ta saka, sannan ta bi bayan kawarta da tuni ta fice daga dakin, a tare suka daga kai suna kallon Ruma dake isar da sakon Hajiya Kaltume ga Hurriya.

 Ni kuma? Me na yi to Hajiya take nema na?

 Sako aka kawo miki

Gaban Hurriya ya fadi ita da Husna suka kalli juna kamin su kalli Ruma da tuni ta wuce abunta ta barsu a stairs din tsaye.

 Kin yi da wani za'a kawo miki sako?

 Aa Wallahi ni wa nake da shi da zai kawo min sako? Kuma idan za a kawo sako da sanina ai ba za a kai bangaren Hajiya ba sai dai nan da nake zaune ko?

 Haka ne kuma, to sakon miye

 Ban sani ba

 Allah yasa ba wani sherin aka kulla miki ba

 Amin, bari na tafi kar na dade na yi laifi

Husna ta dafata.

 Na rakaki?

 Aa dan Allah ki tafi, idan Hajiya ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login