Showing 72001 words to 75000 words out of 279257 words

Chapter 25 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34632



 Okay to muje ki zauna

Ta kalleshi kamin ta kalli gurin da ya nuna mata. Sannan ta fara takawa da kansa yaja mata kujera ta zauna ta dan jin kunya abun ka da wanda be saba ba, not like bata saba zuwa birthday ba she used to amman ba irin wannan ba, kuma wani namiji be taba ja mata kujera ta zauna ba.

 Thank you

 You're welcome kyakkyawa, kina son shan wani abu?

 Aa na gode

Ta dauke kai tana kallon yadda kawayen Khairi suke ta takawa MC sai zuba mata kirari yake kamar wata amarya.

 Me yasa kika saka Abaya baki san birthday za'ayi ba?

Ta juyo ta kalli abayarta.

 Na sani

 To why do you wear abaya?

Ta yi masa shiru kamar bata gurin, idonsa na kan wuyanta zuwa kirjinta domin wuyan abayar mai yankan V ne dake bayyana kasan wuyan mutum, wani abokinsa ne ya kai masa duka yana dariya.

 Shegen kaya ashe nan ka boye who's this?

Gayen ya kalleshi yana murmushi.

 My new friend i think kawar Khary ce

 Her Blood Sister

Hurriya ta amsa masa da kanta sannan ta tashi ta bar taburin ta nufi wanda babu kowa a kai ta zauna tana bawa idonta abinci. Bata ankara ba ta ji ana mata magana dama da ita.

 Sai kuma kika gudu? Tsoron mutane kike ne? Na ga kin kasa sakewa ma what's wrong

Ta kalleshi ta dauke kai ba tare da tace komai ba, hannunsa ta ji a fuskarta yana kokarin juyowa da ita, da sauri ta buge hannu ta mike tsaye.

 Miye haka? Akan me zaka taba min fuska?

Ya daga kafadunsa.

 Fuska ce fa kawai

Kwafa ta yi ta juya zata bar gurin sai yayi dariya ya mike tsaye da gangan ya riko hannunta, shi dai kam ta masa kyau and as she know friend dinsa Khairy ba zai yarda duk wanda ya zo party ta a yau yace ba a saba rika hannunsa ba, domin kusan rabin yan bikin duka suna rike da hannayen juna ne, saboda wasu are in relationships wasu a dating wasu kuma a new friends to them hugging ko rike hannu is nothing in their team.

 Ya kike yanga yan mata saboda kina da kyau ne?

Jin ta yi kamar ta tsinka masa mari sai kuma ta ji bata da wannan kuzarin.

 Karka sake taba ni, ni ba irin sauran matan da suke nan ba ne

 Miya banbanta ki da su? Saboda kina da kyau?

Ta masa banza, a abu mai muhimmanci ma Hurriya bata cika son amsawa ba balle na banza. Ya dan cize baki yayi murmushi.

 Shikenan zauna ba zan sake ba

Bata zauna ba ta bar masa gurin tana rabon ido ko zata hango wanda ta sani ta zauna a kusa da shi.

 Wani kike nema?

Wani ne kuma dabam yayi mata magana har kara wacan gayen da wannan domin wannan kansa ma wani kalar aski ne na yan iska. Shi ma dai bata ce masa na ta nufi gaba gaba ta inda Khairi zata hangota ko zata samu su daga mata kafa. Wani gurin ta nufa ta zauna tana kallon yadda yar'uwarta take rangaji kamar ta sha kwaya, gayen da ya fara yi mata iso ta hango ya isa gurin Khairi yana mata magana a kunne, kamin ya nuna gurin da take zaune har Khairiya ta kalleta ita ma ta mayar masa da maganar a kunne. Sannan ya sauko daga gurin ya nufi gurin MC, before she know sunanta ya cika gaba daya hall din.

 Ina Gimbiyar take, Hurriya ki fito kin yi farar tafiya daya daga cikin kananan matasan mu masu ji da kudi dan gidan Alhaji Buba Sarauta yana nemanki ya ce a kira masa kanwar Hajiyar ta mu wato Khairy domin ta taya yayarta murnar wannan birthday da take da kuma na graduation dinta

Kowa sai ya fara rabon ido ana ta ga wayw Hurriya wacece Hurriya, Khairi kuma ta kasa boye mamakin dake fuskarsa, tambayarta sunan kanwarta da yayi ta fada masa bayan ya nuna mata ita bata dauka abun da zai yi kenan nan ba. Gaban Hurriya kamar zai fado tsabar bugawar da yake domin bata saba ba, irin haka ma be taba faruwa da ita ba. Kasa tashi ta yi ta rasa me zata yi ba zata iya zuwa gurin da aka bukace ba, bata san ma'anarsa na yin haka ba, so she decided to hide herself, tana kokarin janye kujerar ta boya karkashin teburin, gayen ya nufo inda take MC na biye da shi, hakan ya hanata boya sai kallonsa take ta cikin gilashinta tana jin ta ga abun da zai mata, gaba daya sai hankali ya dawo gurinta ita kanta Khairy sai ta sakar musu ido tana son ganin me ke shirin faruwa. Tun kamin ta karaso gurin da Hurriya take zaune ya cire rapper dollars ya fara bararwar har ya isa gurin da take ya tsaya akanta yana ta zuba mata dollars, idan suka kare sai ya dauko wata a aljihunsa ya cigaba da zuba mata, a take gurin ya dauki ihu aka fara daukarsu da manyan wayoyi wasu yan matan da suke crushing akansa kuma suka kasa boye kishinsu. Gaba daya mantawa aka yi da wani birthday party sai ihu ake ana daukar Hurriya, da gayen dake zuba mata kudin kamar be san zafinsu ba. Hurriya ta mike tsaye da sauri tana kallon Namra da sai a lokacin suka ga juna, bata tsaya komai ba ya nufi kofar fita ta fice daga gurin da gudunta, abun da ta yi ya bawa kowa a gurin mamaki domin at first wasu sun dauka ko budurwarsa ce, sai dai guduwar da tayi ya saka shakku a zukatan mutane. Khairy kan ta cika har tana kusan fashewa domin ta san saboda ita ya zo birthday even though ba saurayinta ba ne he's just her friend amman ta san kudin da ya zo da su ita ya kamata yayi ma kari da su gashi be yi ba ya karar da su gurin kanwarta.

Hurriya ta fito da sauri ta biyo hanya tsoro duk ya gama cika ta gaba daya ma a firgice take, hankalinta be kara tashi ba sai da ta iso titi, ko'ina tsit yake kamar babu mutane, arzikinta daya rana ce ba dare ba, wannan ya saka ta dan ji sauki. Juyawa ta yi kamar zata koma sai kuma ta ga ba mafita ba ce, tafiya ta fara yi tana rumgume da hannayenta sai ta ji an mata horn, juyowa ta yi ta kalli motar da bakin gilashi ya hana a ga wanda ke ciki. Ta juya ta cigaba da tafiya kamin ta tsake tsayawa kamakon fakawar da mai motar yayi gefenta ya sauke gilashin motar.

 Saboda na miki karin kudi zaki gudu? Idan ni ne ki koma ba zan sake ba

Ta kalleta ta dauke kai ta cigaba da tafiya, shi ma tafiyar yake slowly cikin motar yana kallonta..

 Idan kuma gida kike son zuwa shigo na kai ki, you're not safe hare

Kalmarsa ta karshe ta saka tsoron dake cikinta ya karu, ta dan karkato kadan ta kalleshi sai ya kai hannu ya bude mata front seat. Tsayawa ta yi kamar mai tunani shi ma sai ya tsaya daidai ita.

 Gida zan kai ki, shigo

Ta kalli abun da ke aje a kasan inda mutum zai dora kafafuwansa idan ya shiga, sai yayi saurin kai hannu ya dauke ya jefata baya.

 Shisha ce please shigo

Ita dai tun da take bata taba ganin tukunyar shisha a fili ba sai yau, tana dai ganinta a fina fina kuma ta san abun da ake yi da ita domin wadanda ake nunawa rike da ita sha suke suna fitar da hayaki.

 I'm Adam by name, please ki shigo mana Hurriya

 Na gode zan kira yayana ya zo ya kai ni gida

 So you get phone please saka min number ki a nan

Yayi picking latest IPhone dinsa dake cikin motar ya cire key ya mika mata. Ta kalli wayar ta sake kallo sannan ta kai hannu ta karba without saying anything ta saka number yayanta daman daga numbersa sai ta Appa da Ammanta ta haddace a kai. Kara wayar ta yi a kunne

 Hello Yayana.. Ka zo ka dauke ni please ina jin tsoro kuma ina bakin titin gurin Event din ba kowa

 Me ya fito dake to?

 Ni na gaji ne bana son zama ciki gida nake so, kuma su ba su gama bikin ba babu wanda zai kawo ni

 Okay ki koma ciki gani nan zuwa

 Toh Yayana ka yi sauri ance I'm not safe here

 Waya ce haka?

Ta kalli mutumen dake jiran ta ba shi wayarta.

 Adam

 Wane Adam

 Ni ma ban san shi ba, yanzu na hadu da shi

 Okay ina kusa da gurin koma ciki zan zo na dauke ki

 Toh

Ya kashe ya mika masa wayarsa.

 Thank You

Ta juya ta cigaba da tafiyarta har ta koma ciki, wannan karon masu gadin ba su hanata ba domin sun gane ita ce ta dazun. Ciki ta koma ta samu gurin inda ba za a ganta ba ta zauna ta zubawa kofar shigowa ido Yayanta kawai take son gani. Tana hango Adam ya shigo ta kara boya kamar ta san ita zai fara nema, sai ko ya hau rabon ido yana neman inda zai ganta, gaba daya ta tafi da shi, a gurinsa duk abun da take tana masa yanga ne saboda ta ga tana da kyau. Ta yi rabin awa a gurin sannan ta tashi ta nufi kofa kamar mai shirin sata ta fice tana duddubawa ko Yayanta ya zo, aikuwa ta yi sa'a tana fitowa motarsa na shigowa harabar da sauri ta nufi shi yana fakawa ta bude front seat ta shiga.

 A tsorace kike Hurriya me ya faru?

Ya tambaya yana kokarin kashe motar.

 Ba komai ni gida nake so

 Ina Khairi ita da waye a gurin cikin yan gida?

 Yaya Namra kawai na gani, sauran duk kawayenta ne ban sansu ba

Ya duba agogo hannunsa.

 Su ma ai ya kamata ace kowa ya tafi gida yanzu, Je ki kirata

 Yaya ba zata fito ba, kuma zata ce na bata mata birthday fa

Ta saka mishi kuka domin ta san halin Khairy ko a banza ta dora mata laifi balle kuma da dalili.

 Karki ce ni nake kiranta, ki ce wani ne yake kiranta, idan ba haka ke ma sai na bata miki rai

Ta fita motar ba dan ta so ba sai dan Yasir yayi mata dole, ciki ta koma ta isa har gurin da Khairi take tana rawa ana zuba mata kudi ta rikota ta kai bakinta kunneta.

 Wani yana kiranki a waje

 Waye?

 Ban san shi ba

 Je ki ce masa ya shigo ciki

Hurriya ta juyo, ita dai bata san yadda aka yi masu gadin suka bar Yasir ya shigo ba, sai hangon shi ta yi ya kankance ido yana kallon mutanen dake ta kai da kawo a gurin. Ta nufi shi ma ya nufo gurin Khairy da bata san me ke faruwa ba sai rawarta take ana zuba mata kudi. Galala Hurriya ta yi tana kallonsa ganin ya wuce ta ya nufi gurin Yayarta, yana isa be tsaya komai ba ya dauke Khairy da mari ya fara dukanta kamar an zugoshi.

 Wannan iskacin ne birthday? Kin mai da kanki kamar yar kafirai? Babu mutum daya mai mutumci a nan kim hada maza da mata ana shashanci ki cw birthday? Daman sai na hana Hajiya ta ce sai an yi saboda kawai ku ja mana zagi

Dukanta yake ta ko'ina wadanda suka san yayanta suka fara ficewa da sauri, wasu suka suka fara kai mata dauki ciki har da ma'aikatan gurin.





HAJIYA KALTUME.

 Hello

Hajiya Fatee ta amsa daga dayan bangaren.

 Hajiya ina ta kira baki daga ba

 Yanzu na shigo dakin, kin gan ni garin sauri har faduwa na yi kamar an turo ni

 Subhanallahi, sannu daman ina ta kira na ce miki Fadeel zai zo

 Ya ma zo har ya tafi, ya ce wai kin ce ya zo ya kai Khairi bata samu mota ba

 Eh haka na ce masa saboda na samu ya zo, wato Hajiya akwai abun da nake tunani sai dai gan gama yanke shawara ba sai kin zo, shiyasa da kika fada min zata birthday na fara da wannan

Hajiya Kaltume ta yi murmushi tana murza kafarta dake zogi.

 Toh Hajiya Fatee kenan wato idan hagu ta ki a koma dama

 Kwarai kuwa, idan ba zai iya rabuwa da wacan bakar karyar ba da ta dafa ta ba shi ya shanye, to ya karo wata idan ya auro wanda nake so ko da bakinciki ai sai ta bar gidan

 Wato Hajiya Fatee magana nan ba ta waya ba ce, bari dai sai na zo kawai ko kuma idan kin shigo

 Toh shikenan Hajiya sai mun hadu

Ta sauke wayar tana murmushin jindadi, domin an yi tsara akan gaba Khairy ta kamalla karatu daman kuma can tana sha'awar hada jini da aminiyarta ko dan karfafa zumuncinsu.


**** **** ****

Hajiya Fatee ma da murmushi ta sauke wayar, sannan ta fito falo ta zauna tana ta sake saken yadda zata kara bullowa lamarin. Domin ta san ba karamar wahala zata sha ba kamin ta samu kan danta Fadeel ya yarda zai aure, a ganinta mallakar da Afrah ta yi masa ba karama ba ce ta yadda ta hana idonaa ganin ko wace mace sai ita kadai.

 Sallamu Alaikum

Ta dago tana amsa masa.

 Wa'alaikassalam har ka dawo?

 Eh ko da na je Already ta wuce ma

Ta yi tusar baki tana jin rashin dadin bw tarardar Khairy ba.

 Aikin banza, zuwan kawai ka yi kenan

Ya yi dariya yana saka keys din hannunsa ya taba kunnensa.

 No na sauke kanwarta yar farar nan ita ce bata samu mota ba, sai na kaita

 Oh yar makauniya? Ko yar wajen Hajiya Nafisa?

 Tana gani Hajiya fa

 Amman sai da gilashi ai, ita da makafi duk daya, Allah yasa dai ka shiga ciki

Ya yi fuskar mamaki.

 No why would i?

 To wish her happy birthday mana, kuma Allah yasa dai baka je mata hannu sake ba

Ya zauna yana dariya.

 Hajiya Khairi kanwata ce fa, kuma ban ma san tana birthday ba, sai da kika kira ni kika fada min naje na daukota, ban shirya komai ba

 Toh sai ka shirya wani abun ka kai nata daga baya, ko tana kanwarka ai tana sin kyautatawa

 Yanzu kuma ai ya wuce, sai da mu hari gaba kuma

Ya mike tsaye yana cigaba da wasa da keys din hannunsa.

 Bari na tafi na bar aiki a office

 Wane irin aiki yanzu da yamma, wai shike nan ba dama na zauna na yi hira da kai sai ka ji kamar kama kan kaya, yar hirar ma sai a hana ka?

 Waye zai hana ni hira dake duk duniyar nan Hajiya?

Ta tabe baki ta dauke kai.

 Dan Allah karki ce Afrah bata ma san na zo nan ba, ki daina dora mata laifi kina daukar alhakinta ne kawai

 Kullum ai ni mai daukar alhakinta ce, daman ta ina Afrah zata yi laifi a gurinka? Yar zinari, ina dai son ka sani ni uwarka ce ko kana so ko baka so, matarka bata fi ni matsayi ba

 Ai ba za a ma hada ba, babu mai matsayin uwa a duk duniyar nan Hajiya, amman duk da haka tana da nata iyaka mata ma tana da muhallinta, ban san miyasa kika tsani mutanen Afrah ba, yarinyar nan tana mutuntatako daidai gwargwado tana miki biyayya

 Na ji dan Allah kama hanya ka tafi Allah ya bada sa'ar aiki

Rokonsa take har da hade hannaye. Ya sauke ajiyar zuciya cikin yanayi na damuwa ya koma ya zauna domin ba zai iya barin gidan ran mahaifiyarsa a bace ba.


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
Page 9

 Ka tashi ka yi tafiyarka bana bukatar zaman ka daman ai bana da muhimmanci a gurinka, da ina da muhimmanci ba zaka wulakanta ni ba

Maganarta ta sake sukarsa gaba daya sai mood dinsa ya sake sauyawa. Sometime baya ganewa rikicin Hajiya Fatee gashi bata yi tsufan da zai ce ya kai ace bata gane wasu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login