Showing 84001 words to 87000 words out of 279257 words

Chapter 29 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34700

aka bude motar wani matashin saurayi ya fito sanye da black T-shirt da wandon soja haka ma kafarsa na sanye da black shoes. Murmushin da suka gani a fuskarsa ne ya dan sanyaya musu zuciya domin alama da yanayin jikinsa be yi kama da masu aikata mummunan aiki ba. Ya iso gurinta ya duko yana kallon fuskokinsu ko wannensu da tsoro a idonsa.

 Nice race

Namra ta dan yi murmushin karfin yana kallonsa, daga fuskarsa har hasken fatarsa be yi kama da dan nigeria ba rigar soja dake jikinsa da kuma wandon. Sai dai kafarta na kan burki jiran kawai take ta ga wani abu ba daidai ba ta taka burkin da karfi.

 Na zo na bi ku har gida sai kuma na yi gudun kar na tsorata ku

 Yanzu ma a tsorace muke

Yayi murmushi sosai ya shafa kansa.

 Na gani ai a idon wannan

Ya nuna Hurriya.

 But i like it, tun da kuka fito Mall nake binku shiyasa na so na bi ku har gida in case of na yi mussing race sai na biyo na kwankwasa muku

Namra ta yi murmushi, Hurriya kam har lokacin a tsorace take. Hannu ya saka Aljihu ya ciro karamin kati ya aje mata.

 Here is my cart duk lokacin da kika yi marmarin race just give me a call I'm Salim Sarauta aka Ethiopian nice to meet you All

Still idonsa ya kan Hurriya da tsoro ya gama bayyana a fuskarta, ya juya ta nufi gurin motarsa ya shiga ya yi reverse ya hau titi, sai da ya kawo saiti mn gurin da Hurriya take sannan ya danna horn sau biyu. Namra ta danna ta masa sau daya murmushi yayi ya dauke kai yaja motarsa, Namra ta bi motar da kallo ta mirror ta kai hannu ta dauki katin tana dubawa kamin ta kai babban yatsanta ta shafa. It take her some minutes tana kallon katin sannan ta ja motar suka cigaba da tafiya, bata yarda baya binsu ba sai da suka isa ta faka motarta.

 Yaya Namra na fada miki account din a yanzu

 Bari sai mun shiga ciki na huta

 Toh

Ta bude motar ta fita tare da ledar da suka yi siyayya, har ta isa bakin kofar falon ta tura ta shiga Namra na zaune a motar bata zare key ba sai kallon katin take, har yanzu zuciyarta bata gama yarda mutumen kwarai ne ko na banza ba, and ta kasa zaba mata tsakanin jefar da katin da kuma barinsa...



" " " " "
" " " " "
" " " " "

khairi ta tashi zaune da sauri tana kallon Hajiya Kaltume dake yakar hakora tana murmushi.

 Haba Hajiya ni dai gaskiya

Sai kuma ta yi shiru.

 Ke dai gaskiya me? Kin san dai tarenmu da Hajiya Fatee ko wani dabam ta dauko ta ce ki aura ba zaki ce aa ba balle kuma danta, yaro kuma yana da nasa rufin asiri daidai gwargwado

 Amman yana da mata fa Hajiya

 Ina ruwanki da matarsa? Matar da uwarsa ma ba sonta take ba, kuma saboda ita ne ake son hada aurenku

 Ni gaskiya ba zan auri mai mata ba da kurciyata haka nan, kuma yana da yara fa, Hajiya kin fa san sha'anin kishiya yadda yake

 Ko rabuwa suka yi ba hannunki yaran zasu zauna ba, kuma muna fatar kamin ki shiga ma ita ta fita kin ga shi kenan an huta

Ta bata fuska sosai kamar zata yi kuka.

 Gaskiya Hajiya ina da sauran time yanzu fa na gama makaranta kuma nake rayuwa

 Matsalata dake wani lokacin baki da wayo Wallahi gaba Khairi

Ran Hajiya ya fara baci ganin tana kokarin taro yarta tana kaucewa.

 Tashi dauko min wayata tana ringing

Ta tashi yana turo baki gaba domin ta ko'ina bata ganin ta dace da aure a yanzu da take cikin cin lokacinta.

 Maama ce

Ta fada tana juyowa tare da picking din call din.

 Innalillahi

Ta yi saurin mikawa Hajiya Kaltume jin yayarta tana kuka. Hajiya Kaltume ta karba ta kai a kunne gabanta na faduwa.

 Subhanallahi Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, abun har ya kai haka? Wai anya Rilwan yana da hankali kuwa? Be san waye ubanki ba a garin nan da zai saka hannu ya dake ki

 Duka...!

Khairi ta amsa da karfi tana kai hannu a gaba da mugun mamaki.

 Shi kenan gani nan zuwa, ki fada masa sai ya san ya saka miki hannu, ni da nake uwarki ban doke ki ba sai shi da ya ganki da hakoranki talatin da 2

Ta sauke wayar tana masifa

 Ni da na san haka yaron nan yake Wallahi ba za'ayi auren nan ba, tun da aka yi auren nan kullum cikin tashin hankali nake, shiyasa idan na ga kiranta gabana har faduwa yake, yanzu abun ya kai har da duka da zagin iyaye

Khairi ta tabe baki.

 Wannan mijin nata fa dan shaye shaye ne Wallahi komai zai iya aikatawa

 Wane irin shaye shaye halinsa ne, tun tana amarya yake mata wannan iskanci yanzu kuma abun ya fara wuce gona da iri, yau shekara uku da aure nan amman kullum cikin fitina ake ita ba kishiya ba balle ace asiri ake mata

 Amman dai ai yana neman mata kuma yana shaye shaye

 Ta ina kika sani kin jiki da zancen banza, ke ba zako iya shaidar mutane da abun kirki ba sai na banza

 Ni Wallahi na san abun da yake nan Hajiya ke ce baki wayanci duniya ba

Hajiya Kaltume ta mike tsaye daker tana latsa kafarta dake ciwon tun faduwar da tayi.

 Ina jin ciwon kafar nan haka dole zan tafi, wannan wane irin tashin hankali ne, ga mu cikin makiya yaro yana son kwance mana zane a kasuwa

Ta nufi gurin da tufafinta suke ta shirya ta dauki jakarta tana tafiya kamar zata yi gurmanta saboda zugin da kafar take mata duk kuwa da zuwan da ta yi asibiti jiya ta kai kafar. Rai a bace ta shiga mota direba ya ja motar suka fice. Shekara uku kenan da auren babbar yarta da ke bin Yasir wato Maama amman ta kasa samun kwanciyar hankali irin na uwayen da suka aurar da yaransa, kusan duk wani kira da Maama zata mata daya gaisuwa daya kuma na karar mijinta ne ko kuma shi ya zo har gidansu ya kawo kararta.



__________

A gafarce ni please Wallahi uzuri ya rike ni. Amman In Shaa Allah ba zan sake post late ba, idan na sake ku ce min Hajiya Kaltume ?z?

14Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?

5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


5??5??5? ?5?? 1?? 2??



Tun daga falo Hajiya Kaltume take jin kukan Maama, hankalinta be kara tashi ba sai da ta shiga cikin dakin ta ga halin da yarta take ciki.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Maama? Haka Rilwan yayi miki da jiki?

Maama ta kara narkewa da kuka tana daga idonta da yayi ja ta kalli Hajiya.

 Hajiya Rilwan kashe ni zai yi, Hajiya makure ni yayi Wallahi, yau babu kalar zagin da be yi min ba

 Saboda me? Me kika masa? Wai me ya dauki kansa ne? Ko an fada masa baiwa aka kawo a gidan?

Maama ta rike kafar Hajiya da sauri tana kuka.

 Hajiya ki kai ni asibiti kar idona ya siyaye

 Haba idon yayi? Wai me kika masa ne?

Kasa magana ta yi sai kuka take sosai tana taba jikinta, kana ganinta zaka san an doketa amman ba irin dukan dake bayyana jini ko fatar mutum a waje ba, ma'ana be fasa mata fata ba amman yayi nasarar kumbura mata jiki, idon kuma yayi ja sosai saboda kuka da kuma dukan idon da yayi. Cikin takaici da bacin rai Hajiya ta daga wayarta ta kira Yasir ta fada masa halin da ake ciki, sannan ta rika Maama suka fita daga gidan suka nufi asibiti.
Duk wata kulawa da ya kamata a bata likitocin sun bata, bayan an yi mata allura suka rubuta mata magani, a asibitin Yasir ya same su shi ya karbi takardar maganin ya siyo sannan suka dawo gida. Zama kawai ta yi Yasir be jira ta huta ba ya fara tambayar ta abun da ya hadata da mijinta.

 Maama me ya hada ku?

Kasa kallonshi ta yi balle har ta amsa mata, ko kadan bata son bude dalilin fadansu, domin ta san yadda ransu zai bace idan ta fada, gashi mijin nata ba shi fa hakuri bata san iya inda yamutsin zai kai ba.

 Ba magana yake miki ba?

Hajiya ta saka bakinta.

 Hajiya tsabani ne kawai irin na mata da miji

 Tsabani dai amman sai yayi miki wannan dukan? Kullum da kalar matsalar da ake fama yanzu kuma abun ya kai ga duka

 Ai har da zagin iyaye dazun da ta kira wayata ce min ta yi ya doke ta ya zageta, amman yanzu ta kasa fadar komai, idan mu baki fada mana ba ai dole shi mahaifinki ki fada masa

Ta sauko kan kujerar da take zaune da sauri.

 Hajiya dan Allah karki fadawa Appa, dan Allah wannan abun ya tsaya iya nan?

Yasir yayi mata kallon mamaki, Hajiya Kaltume ta rike baki.

 Yau na ga abu, Maama wane iri son kike yi ma bawan Allah nan ne? Mutum ya cutar da kai ka kasa fada saboda a daukar masa mataki kuma yanzu zaki ce kar a fadawa mahaifinki? To idan ya ganki me zaki ce?

 Zan koma anjima Hajiya bana son Appa ya sani please bana son kowa ma ya sani, laifina na duk abun da ya faru amman na miki alkawari daga wannan ba za a sake ba

Cikin kuka sosai take maganar tana hade hannayenta.

 Kin sha fadar haka, amman babu wani canji gashi nan duk ki bi kin rame saboda tashin hankali, lokacin da kike gida ma kin fi kiba, an yi aure dan huta amman hutun ya gagara

Yasir ya mike tsaye.

 Hajiya tana da gaskiya, akwai abubuwa da yawa ba be zama dole iyaye su ji ba, kuma tun da har ta fadi cewar laifinta ne sai a barta ta gyara

Hajiya Kaltume ta dube shi.

 Yasir ba yau aka saba irin tashin hankalin nan ba, kuma yanzu tun da ya fara gwada mata da duka ba raga mata zai yi ba, musamman ma idan ya ga an kyaleshi

 Toh ya zamu yi Hajiya, kina jin abun da take fada da bakinta fa, kuma daman ko wane gidan aure da kalar tashi jarrabawar maybe tata ke nan, kuma tun da har bata son mu ji sai mu daga mata kafa

Maama ta lumshe ido hawaye na sauko mata ita kadai ta san yadda take ji a zuciyarta haka zalika ita kadai ta san kalar zaman auren da take da mijinta, abubuwa da yawa ta kan rufewa iyayenta da kawayenta saboda kar ran mijinta ya bace, ta wani bangaren kuma tana gudun haka ya zama silar lalacewar aurenta da mutumen da take jin idan baya tare da ita zata iya mutuwa.

 Shi ke nan, Allah ya kyauta idan ya san wata ai be san wata ba, zan tashi tsaye da rokon Allah ya kawo miki kwanciyar hankali a gidan mijinki, kuma za'ayi nasara

Hajiya ta fada ita kanta Maama ta san Hajiya na fada ne kawai saboda Yasir yana zaune a gurin, amman ba rokon Allah take nufi ba. Yasir ya nufi dakinsa be dade ba ya sauko ya fice daga gidan gaba daya, Hajiya Kaltume ta mikawa Maama hannu alamar ta dawo kusa da ita, haka kuwa aka ayi Maama ta bar kujerar da take ta dawo ta zauna ta kusa da Hajiya Kaltume.

 Sha kuruminki, ko yanzu zamu sake Zub kudi da yardar Allah sai mun mallake shi, sai na saka an yi masa aikin da sai ya dawo karkashin kafarki yana tsoronki, yadda nake iya juya mijina a yanzu yadda nake so ke ma haka zaki juya naki mijin, ki kwantar da hankalinki komai zai wuce

Ta share hawayenta, ba dan ta gamsu ba, domin sun sha gwada yi amman shiru ko abun yayi kamar zai kama shi sai ya kuma ya watse. Ta daga kai ta kalli Khairi wanda ta shigo rai a bace hannunta rike da waya. Ta nufi yar'uwarta da sauri hankali a tashe.

 Innalillahi Maama ji fuskarki

Wani hawaye ya sakd taruwa a idon Maama.

 Wai ke ba zaki iya rabuwa da wannan azzalumin mutunen ba? Ba haihu kika yi da shi ba balle ko ace saboda Yaya

Maama ta rike hannunta sosai ta jimke.

 Khairy ba zaki gane ba, duk wani abun da kike ganin zaki iya yi ko kin iya a waje ne, da zarar an yi aure labari ya sauya, kuma ki roki Allah kar ya dora miki jarabawar son namiji fiye da yadda yake sonki

Daga Hajiya har Khairi tausaya mata suka yi, domin su duk yan kallo ne babu wanda ya san abun da take going though sai idan ta fada ko kuma shi ya fada. Khairi bata tada balli ba sai da dare yayi ta ga Maama ta shirya Yasir zai maida ita gida, a lokacin ta fara fada tana ganin be dace abar Maama ta koma ba bayan duk abun da yayi mata, ba a kira shi an masa gargadi ba.

 Ni ma dai haka na gani, abun ya fara kaiwa ga duka ya kamata ai iyaye su shigo ciki, ko da baki fadi abun da ya hada ku ba sai ayi masa gargadi

Ta girgiza ma Hajiya Kaltume kai tana fashewa da kuka.

 Aa Hajiya dan Allah, bana son kowa ya ji, kuma abun be kai ace za a saka iyayensa ba, duk abun da ya faru laifina na na fada muku

 Toh Allah ya kyauta gaba, tashi ku tafi

Khairi ta bita da kallo baki sake tana ayyana idan ita ce ba zata iya daukar wannan iskancin ba. A mota babu kalar nasiha da jan kunnen da Yasir be mata ba, bayan ya yaba mata na boye sirrinta da ta yi.

 Sai dai ba komai yake bukatar boya ba, wani abun idan yayi yawa yana da kyau iyaye su ji saboda a dauki mataki

 Na gode Yaya kuma In sha Allah zan dauki shawarka

 Allah ya sauwake kuma ya kawo kwanciyar hankali a tsakaninku

 Ameen

Ta bude motar ta fita kamar ba ita ba, aure mai saka ladabo in ji hausawa. Tsayawa ta yi a gurin har sai da yayi reverse mai gadi ya bude masa gate ya fice sannan ta juyo ta shigo ciki.




HURRIYA POV.

Hurriya ta shiga dakinta ta aje mata siyayyar da suka yi sannan fito ta shige dakinta. Namra kam ta dade a motar tana sannan ta fito ta rufe ta shiga cikin gidan. Ko'ina na falon kamshi yake alamar an sauke abincin dare tun kamin magariba, tun kamin ta haura sama ta cire mayafinta ta shiga dakinta, saman gadonta ta aje mayafin kuma a saman dai ta zauna tana duba kayan shower gel ne da perfume. Bandaki ta nufa ta fara jera gel din sannan ta fito ta jera turaren ta dauki daya ta nufi dakin Hurriya, ko da ta shiga Hurriya na tsaye jikin windows rumgume da hannayenta tana kallon waje.

 Hurriya

Ta juyo ta kalleta

 Ga turare daya ki yi amfani da shi, kuma ki tura min account din sai na saka miki kudin, amman dan Allah me zaki yi da su?

 Wani abu ne na sirrina Yaya Namra karki takura please

 Shikenan i trust you na san ba zaki yi wani abu marar kyau da har za ace waya baki kudin ba? You're not a bad girl

Namra na magana tana kai hannu ta ja naman fuskarta cikin salon wasa. Hurriya ta yi murmushi ta sauke kanta kasa. Namra ta aje mata turaren saman gado ta fice zuwa dakin Momy. Ta tura kofar dakin tana sosa kanta.

 Momy wai ni kam Sarauta nan suna da Family da yawa ne?

Momy dake kokarin cire sarkar zinarin dake wuyanta ta kalleta.

 Sarauta sunan kakansu sai ya zama yaya da jikoki suna

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login