Showing 213001 words to 216000 words out of 279257 words

Chapter 72 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34695

ba na san a cikin zuciyarka haka ne, Appa ko kare ka aura min a matsayin miji, Wallahi zan karbe shi na zauna da shi, balle kuma mutumen da kake kyautatawa zato, na gode da zabin da ka yi min. Ya Allah mahaifina na ciyar da ni da halak, Allah ka ciyar da shi da abinci da ya fi ko wane abinci dadi a aljanna, mahaifina ya shayar da ni da halak, Ya Allah ka shayar da shi da ruwan alkausara, ruwan da bayan su babu sauran ?ishi bayan shansu, Mahaifina ya tufatar da ni da ni da Halak, Ya Allah ya tufatar da shi da mafi kololuwar darajar tufafi a aljanna, Mahaifina ya sama min muhalli, Ya Allah ka yi masa muhalli kusa da Annabi Muhammad S A W, Ya Allah ka shaida a yau mahaifina ya sauke nauyi na zaba min mutumen da yake ganin ya dace da ni, Ya Allah ka sauke masa nauyin zunubai, a saka a aljanna a saukake

 Ameen, Allah ya miki albarka Hurriya

Appa ya amsa yana kuka, sannan ya kalli Amma ya ce.

 Iyami na gode da kika haifa min ?a mai tarbiya da sanin ya kamata a kananan shekarunta, wannan ma kadai abun alfahari ne a gurin, ku yafe min a inda na yi ba daidai ba, na barku lafiya

Ya mike tsaye ya saka talkaminsa ya nufi kofar fita daga tsakar gidan, sai ga yaransa yan tawaye sun shigo sanye da uniform din makaranta rike da lunch box, suna ganinsa sai suka yi gurinsa suna murna kamar sun saba da shi.

 Appa...Appa.... Appa...

Durkusawa yayi yana shafa kansu a madadin ya amsa sai ya fashe da kuka kamar ba shi ba. Yasir mai ya sauke kansa kasa yana hawaye, Gwaggo ma hawayen take ita da Hindu, Rukayya kuma ta koma kusa da Hurriya ta zauna ta rungume suna kuka. Cikin karfin hali Appa ya mike tsaye ya kama hannun yaransa ya fice daga gidan, Yasir ya share hawayensa ya kalli Amma.

 Amma...

Sai ta daga mishi hannu tana hawaye.

 Dan Allah tashi ka bi mahaifinka

Ya mike tsaye ya kalli kakarsa.

 Hajiya tashi mu tafi

Hajiya ta yi murmushi.

 Zan tafi Iyami amman zan dawo idan kin huce

Sannan ta mike tsaye suka fice tare da Yasir. Amma ta share hawayenta ta kalli Hurriya dake kuka ta ce.

 Shikenan abun da zaki fadawa mahaifinki? Kin goyi bayan auren da yayi miki? Kin san wacece Nafisa, kin kuwa san irin zabin da Alhaji yayi miki?

Hurriya ta dago daga jikin Rukayya ta ce.

 Amma, mata da yawa iri na ba su san ubansu ba, saboda uban ya mutu a lokacin da suke ciki ko suke da kurciya, da yawa iyayensu ba su ga ranar aurensu ba saboda mutuwa ta yi katanga, suna da yawa wadanda iyayensu ba su samu damar zaba musu miji ba, wasu kuma an fasa aurensu, saboda ba a san ubansu.... Shim ni a gareni, wannan na gata ba ne?

Amma ta kasa amsawa. Cikin kuka Hurriya ta cigaba.

 Amma..., baka sanin?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? muhimmanci uba sai ranar da ka rasa shi, uba yana da ?ima, shi uban bango ne majingina ko wace ?a. Idan kana son ka san darajar uba tambaye maraya, idan kana son sanin tsadar uba da halin da ?a mace take shiga idan bata da shi, tambayi ?ar da aka haifa ta hanyar zina...

Ta saka hannunta tana share hawayen da suka ki tsaya mata

 Ni dai kam na sani, dukan abun da zai zo daga gurin Ubangijina mai kyau ne, dan haka zan tara hannu biyu na karba, ko da ba zai min dadi a yanzu ba, zai zama daraja ce da nasara a gaba, shi dan'adam ba ya kauce kaddara, kaddara bata wuce bawa, wannan ma daga gurin Allah ne....

Amma ta girgiza kai tana kuka.

 Aa Hurriya ban yarda da wannan auren ba, ba zaki je ki sha wahalar da na sha a gidan ubanki ba, na yi irin wannan wautar na ki a lokacin da nake da kurciya kamar ke, amman yanzu me ya haifar min?

 Nasara....

Gwaggo ta amsa mata a tsawace.

 Nasara ya haifar miki Iyami, haihuwar da kika da Alhaji Haruna nasara ce..! Zaman auren da kika yi a gidansa nasara ce...! Samun soyayyarsa da ta mahaifiyarsa nasara ce....! Abun da kuma ya same ki yanzu jarabawa ce ni ma na gane...

Amma ta runtse ido ta jingina da bangon gidan.

 Abun da ya gudana a yau din nan ma Nasara ce Gwaggo...

Cewar Hindu tana murmushi. Gwaggo bata sake cewa komai ba ta mike tsaye ta shige falonta, Hindu kuma ta dafa kafadar Amma tana bata magana, Rukkaya ta kama Hurriya ta kwantar da ita a jikinta.


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
44

 Ni kaina ban yi farinciki da wannan auren ba, sai dai ba zaka iya nunawa Yaya ba ya fada maka ba daidai ba ko ma yace ba ka yi tunani ba, amman yarinyar sam bata dace da matar Jamal ba sam, sam sam

Cewar Momy Ikilima a madadin ta kwantar da hankalin Ammy sai zugata take, Hajiyar Maru ce ta kawar da maganar Momy Ikilima ta hanyar nunawa Ammy ta karbi wannan kaddara ta so abun da danta yake so.

 Ba zan iya kallon yarinyar a matsayin surukata ba Hajiyar Maru, shi kansa zafin soyayya ne da rashin tunani yake dawainiya da shi, amman da zarar ya dawo hayyacin zai gane kuskure suka aikata shi da mahaifinsa

 Kamin su gane hakan, sai ki zuba musu ido ki ga yadda abubuwan za su yi, kin san dai ba zaki iya ja da mijinki ba ko?

 Ba zan iya ja da shi ba Hajiya amman ba zan karbi yarinyar nan a matsayin sukura ba

Hajiyar Maru ta mike tsaye ganin ta yi iya nata ta fice ta bar ma Ammy dakin. Hajiya Turai ta dafe kanta tana kiran kukan da baya kusa da idonta.

 Sallamu Alaikum, daman ni na san ba da saninki Yaya ya aikata wannan abun ba, abun bakinciki abub takaici abun Allah wadai

Momy ce take fadar hakan daga shigowarta dakin, Hajiya Turai ta dago ta dube.

 Ta ina zan yarda Captain ya auro yarinyar nan, Engr be yi shawara da ni ba, be fada min ba kawai yaje ya aiwatar da abun da zuciyarsa take so

 To wai haka kika hade hannaye suka zuba ido ba tare da daukar mataki ba?

 Matakin me zan dauka Hajiya Nafisa? An riga an daura aure me zan yi? Kin san dai Engr ba zai bari na cilastawa Captain sakin yarinyar a yanzu ba

Momy ta zauna tana karkasa yadda bakincikin ya rabu mata gida gida. Har La'asar Hajiya Turai da Momy suna cikin dakin suna ta juya zancen, bayan saukowa daga sallah La'asar ne Daddy ya shigo dakin, Hajiya Turai ta dauke kai ta juya fuska sai dai hakan be hana shi zama kusa da ita ba, sai ma dariya da yayi yana tsokanarta a gaban Momy.

 Haba Turaita yar Baturiya yau kuma da Engr ake fushi?

Momy ta kalli dan'uwanta cikin bacin rai ta ce.

 Dole Hajiya Turai ta yi fushi, abin nan ya wuce duk inda kake tunani Yaya, kuma ba a kyauta mata ba, ni ma kuma ba a kyauta min ba, na aikata abu ba tare da tunanin halin da zamu shiga ba, yanzu haka ko da na fito na bar Namra tana kuka saboda bakin auren nan da aka daura a yau da bakar yarinyar can, Namra da Captain suna kaunar junansu amman yanzu wannan auren da daura masa a yau ya lalata komai

Da kamar mamaki Daddy yake kallon fitinanniyar kanwar tasa.

 Amman Jamal be taba gabatar min da wata magana makamancin haka ba a game da Namra, kuma ni na aikata abun da na aikata ne a yau saboda na gama karantar abun da Jamal yake so ne, sannan abun da kuke ta kushe yarinyar nan da shi koraren ne a gurin wanda ya san gaskiya, ni dai na ga video kuma yanzu haka shigowar da na yi a nan na zo ne da maganar Bashir Sarauta yana falo yana jirana yanzu haka

 Ai dansa ne ma ya dace ya auri yarinyar tun da yar'uwar badalarce, amman be nema nemawa dansa ba sai mu, kamar dai masu bakin uwa

Daddy yayi murmushi yana kallon fuskar kyakkyawar matarsa take magana cikin kuka da fushi.

 Sheri ne aka yi mata Turai bata aikata ba, kuma ko da ta aikata tun da har danki yaji zai iya zama da ita a haka mu miye na mu a ciki?

 Ni dai ba zan karbeta a matsayin suruka ba, kuma ba zan bari ayi bikin komai ba domin ba za a yada hotunanta a matsayin matar Captain ba

 Daman daura aure dai shi ne wajib, kuma an yi, wadanna abubuwa ne da al'ada ta tana da, shi ma kuma idan bangaren yarinyar suka nuna sha'awar yin haka ba zamu hana su ba, ke dai a bangarenki ne ba zaki yi haka ba, ni ba tsegumi ya kawo ni nan ba, Bashir Sarauta ne ya zo tare da yan'uwansa da iyalinsa akan maganar yarinyar, da yi tunanin ko zaki so saurare a matsayinki na mahaifiyar Captain ko ba komai haka zai share zargi da rashin ganin kimar yarinyar nan da kike yi, amman yanzu na fahimci baki bukatar hakan

Ya kalli agogon dake daure a wuyan hannunsa.

 Ki shirya na fada miki jirgina zai tashi 5pm na yamma

 Babu inda zan tafi na tafi na bar yarona a nan da wannan yarinyar nan, idan na bar garin nan sai idan tare da amaryar ne

Daddy yayi murmushi.

 Amaryar da kika ce baki so? Ayi haka?

 An dai riga an daura aure yanzu a ba mu amaryarmu mu tafi da ita Kaduna?

 Ina aka taba haka? Daga daura aure yau babu kintsawa babu komai sai mu tafi karbar Amarya kuma mu wuce da ita Kaduna? A kaduna ina zata zauna ma? Ai dole? mu ma muna bukatar lokaci ba yanzu yanzu ba

 Duk gidanjen da suke garin Kaduna ace ba a san wanda zata zauna ba? Kai kace wata yar zinari?

 Tarin gidaje ba shi ne mafitar ba, sai wanda mijinta yake sha'awar su zauna tukuna, wannan ma na aikin mu ba ne, ta ina ma za a dauki amarya akai a Kd bayan mijinta yana nan garin Gusau yana aiki, tare da mu zata zauna ni ba zan iya bari saboda Captain yayi aure ya zauna a gida daban, shi kadai Allah ya ba ni ba zan bari wata ta kwace min shi ba

Daddy yayi murmushi ya dauke kai ya fice daga dakin, shi dai duk a tunaninsa Hajiya Turai take tana yi ne saboda ranta a bace, idan aka bata kwana biyu zata sauko ta.

 Wallahi ba zan taba bari ayi zaman auren nan ba, ba zan bar garin nan ba sai da yarinyar nan

Bayan Daddy ya fice Ammy take fadar haka, Momy ta mata kallon rashin fahimta.

 To ai idan kika yi haka kin nuna kina sonta kenan, ai kamata yayi ki banza ajiyarta ki share yar banza ta fahimci familyn nan ba gidan aurenta ba ne

 Shiyasa zan yi haka ai, idan na barta a nan cikin satin nan zata iya tarewa, idan kuma ta haihu da ana ai zance ya kare, ina nan garin idan kuma ta tare sai dai ta tare a gidana

 Wannan ba mafita ba ne lokacin da zai saci kafa ya tafi mai nawa ko gani be yi ba, ki dai canja shawara

Ammy ta juyo ta kalli Momy kamar zata fasa kuka. Momy ta yi shiru domin ita ma bata san abin yi ba a yanzu kanta a rufe yake.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un wannan abu da me yayi kama? Wane irin rayuwa ne wannan? Ni na rasa ma me ye abun yi, babu abun da yafi min bakinciki kamar neman auren yarinyar nan da aka yo a cikin falona kuma aka yo sadakinta da sinari

 Zinarin ma mai tsada, yarinyar ko gani bata yi. Amman ni na san abun yi ni na sani, ta yaro ai kyau take bata karko

Ammy na maganar zuciyarta na kuna, kamin ta mike tsaye ta nufi bangaren da mijinta yake sauka idan ya zo gidan.
Daddy yana fitowa daga dakin ya hau sama ya shiga dakin Captain kicibus suka yi da Daddy shi zai fito Daddy kuma zai shiga dakin.

 Daddy

Captain ya fada yana sauke idonsa saka haka nan dai yake jin kunyar Daddy a yau.

 Kai ba mace ba miye na rufe kai a daki? Ko Ammy kake yi ma boyo?

Captain yayi murmushi yana sosa bayan kansa. Daddy ya ce.

 Mahaifin yaron nan ne Adam ya zo tare da Iyalinsa, ya fara koro min bayana na takatarda shi saboda ina ganin kai da mahaifin yarinyar ne kuka dace da yin shawara ko yanke hukunci

A take bacin rai ya mamaye zuciyar Captain da tsananin fushi ya ce.

 Me suka zo yi Daddy?

 Kamata yayi ka sauko mu ji, bana son bata lokaci 5pm zan wuce Kaduna

Daddy ya karasa yana duba agogo hannunsa, a tare da Captain suka sauko, a tunaninsa iyayen Adam din za su sake bukatar ya basu dansu ne ko kuma wani abun da ya shafi karar da ya shiga a DSS. Captain be ji zai iya gaisawa da ko daya a cikin family ba domin dan su ya janyo musu kallon marasa mutunci yake musu. Salim be kalli gurin da Captain yake zaune ba domin kowa baya marmarin ganin abokinsa a yanzu.
Sai da Daddy ya kalli Captain da fuskarsa take a gintse sannan ya ce.

 Ina tunanin kun san Captain, ko da iyalanka ba su sani ba kai dai ka san da cewar Jamal ana ne, Salim zai iya fadar hakan, dalilin da ya saka na dakatar da kai daga bayani saboda na kira shi ne, domin shi da mahaifinta suke masu hakkin akanta yanzu, kasancewarsa mijinta an daura Aurenta da Jamal a yau...!

Da matukar firgici Salim ya kalli Captain da goshinsa ke kyalli kana arba da shi zaka san ango ne latest. Kallo kallo suke da Salim kowa ya kasa dauke idonsa.

 Maa Shaa Allah, abu yayi kyau Allah ya saka maka da alheri a wannan jihadin da ka yi, kuma ya baka wuyan dauka

Cewar Bashir Sarauta yana jinjina kokarin Captain na toshe kunnuwansa a wannan mawuyancin yanayin da ba kowa zai iya ba. Salim ya dauke idonsa da mugun karfi ya mike tsaye fuuu ya fice daga falon

 Zaka iya cigaba ko kuma ka fara daga farko saboda ya fahimci me ke tafe da ku

Alhaji Bashir ya kalli Captain cikin yanayin damuwa ya ce

 Daman mun zo nan ne akan maganar abun da ya faru da ne yi ma kowa dadi ba, DSS sun sanar mana su suka dauki Adam sakamakon karar da Captain ya shigar, sun ce sun dauke shi ne saboda bincike yanzu haka dai sun dawo da shi yana asibiti domin sun masa duka sosai daurin da aka yi masa ma likita yace sai an sake daura shi... Dalilin da ya saka muka zo nan shi ne mun bincike Adam akan abun da ya faru daman kuma tun farko an yi masa fada kuma mun tambaye shi taya hotunan suka fita, sai yace mana be sani ba, kuma ya fada mana cewar tabbas yana tare da yarinyar ne...

A wannan gabar ne Captain ya kasa jurewa ya kalli Daddynsa cikin yanayin bacin rai domin baya bukatar a nanata masa abun da ya riga da haddasace.

 Daddy na dauka magana ce mai muhimmanci za su yi, amman wannan yana maida hannun agogo ne baya

Daddy ya kalli Captain with serious face domin ko da Alhaji Bashir Sarauta ba abokin kasuwancin Daddy ba ne ta wata fuskar ya kai ya haifi Captain and duk wani abu na nuna rashin mutunci ko rashin girmama na gaba Daddy baya lamuntar dansa Jamal ya aikatawa kowa.

 Respect yourself ka saurare shi ka ji abun da yake tafe da shi

Captain ya maida hankalinsa gurin Alhaji Bashir Sarauta ba dan ransa yana so ba, dai dan bin umarnin Daddynsa.

 A yanzu maganar da nake da ku, yanzu haka Adam ya fada mana gaskiyar cewar kazafi aka yi ma yarinyar nan!.. 

Yadda ya fadawa Captain gaskiyar abun da ya faru haka iyayensa suka fada. Daddy ya girgiza

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login