Showing 261001 words to 264000 words out of 279257 words

Chapter 88 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34706

idonki zai bude Babyna kuma saboda shi Muka zabi yin aikin a wannan asibitin da yake karatu gashi kuma an yi nasara Alhamdulillah

Hurriya ta kalli Captain tana murmushi kamin ta maida dubanta gurin kofar da Dr Nyala ta bude. Wani matashin yaro ne ya shigo sanye da lab coat fuskarsa da idonsa sun yi ja sosai kana ganinsa ka san ba karamin kuka ya sha ba, domin har a yanzu ma hawaye zuba suke a idonsa. A take murmushin dake fuskar Hurriya ya gushe ta kalli Captain da sauri ta sake duba yaron dake tsaye gabanta sai jikinta ya fara rawa kamar zata kamkame guri daya ta rufe ido da sauri tana shisshika da karfi....



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
Captain yayi saurin rike matarsa da sauri yana leka fuskarta.

 Hurriya...

Ta kama rigarshi da karfi ta rike har lokacin idonta a rufe yake jikinta kuma rawa yake. Ta kasa yarda ba mafarki take ba, kamar yadda take jin kamar tsananin son rayuwa da an uwanta yana neman haukata a yanzu da yake mata gizo, to amman kuma kalaman da Captain ya furta fa? Wani hannun ta ji a jikinki wanda ya banbanta da na mijinta, dumin hannun ya fahimtarta da alakar jininta da jinin mai taba ta, shi ma dai sunanta yake kira kamar yadda Mijinta ma yake kiranta, wata kila ta yi dagon zango ne ko kuma kokarin farkawa take da daddadan mafarki. Hakan ya kara mata kuzarin bude idonsa sai ta sake arba da wani mai irin fuskar dan'uwanta mai irin hanci da idonta mai hasken fata kamar nata, sai dai ya girmi Hamad fuskarsa ya sauya sosai. Hannayenta sake rawa ta dago zata murza idonta Captain yayi karaf ya rike

 Karki murza ido

 Gizo suke min

Ta amsa a cikin wani sauti mai kokarin gauraya da kukanta.

 Ba gizo ba ne, da gaske ne wannan ma...

Ta sake bude idon a karo na uku ta kalli matashin yaron dake a yanzu yake dukushe gaban gadon da take zaune yana kuka har lokacin hannunsa ya kan hannunta ya rike ta gam. Ta kalli Captain hawaye na sauko mata.

 To waye wannan?

Captain be ce komai ba sai da yayi magana da Doctors din suka fada masa dokokin abubuwan da zata kiyaye da kuma abun da da zata ci sannan yayi musu godiya suka fita.

 Hurriya...

 Na'am

Ta amsa da sauri domin amsarsa kawai take jira.

 Ba kin ke kika fada mim dan'uwanki yana raye ba? Shim ba ke kika kasa yarda cewar Hamad ya tafi ya barku ba? Kowa ya karbi mutuwar Hamad amman ban da ke haka ne?

Ta daga kai tana kuka ta kalli Hamad din da shi ma kuka yake sosai.

 Saboda jikinki yana baki dan'uwanki wadda ya fi kowa kusanci da ke yana raye, jikinki be fada miki karya ba tabbas Hamad yana raye, kuma shi ne a gabanki yanzu

 Taya wannan karyar zata zama gaskiya? Ji yanayin yau nake kamar ba ni ba, tsoro nake kar na farka daga wannan bachi na ga komai ba gaske ba

Hamad ya kalli Captain cikin wani yanayi marar misaltuwa da wata murya ta samari masu tashen balaga ya ce.

 Me yasa ka yi min karya? Why? Ka ce min kowa ya mutu bana da kowa a yanzu why? Ko kuma kowa ya mutu Hurriya ce kadai a raye?

Cikin tashin hankali da ba a sakawa rana Hurriya ta dubi dan'uwanta muryarsa ta sauya kamar yadda siffarsa ma ta sauya, ko a can baya daman wasu shi suke dauka yayanta ita kanwa saboda girman jikinsa.

 Dan Allah ya zan yarda Hamad ne...? Ya zan yarda? Ki kira Amma.. Kira min Mama Rukayya... Dan Allah

Ta rike Captain da karfi kamar zai tsere mata, taya idanuwanta za su bude a yau kuma ta yi arba da wani mai kama da Hamad yace mata Hamad din ne.

 Amma tana raye? Daman Amma tana raye?

Hurriya ta kalleshi kamar yadda yake kallonta da tsananin mamaki da al'ajabi.

 Magana kake kamar ka san kowa...

 Na san kowa mana Hurriya, Hamad ne Hamad dinki mai yawan dukanki mai yawam fada dake mai saka ki kuka, Hamad yaron Amma da Appa ni ne Hurriya

Hurriya ta rike baki tana kallonsa hawaye na sauko mata sharrr. Captain ya zauna kusa da ita ya rumgumeta.

 Abu ne mai wahala dukanku ku yarda da wannan

Ya dago hannun Hurriya ya nunawa Hamad.

 Awarwaron da ka taba bani as a gift ka ce na bawa budurwata, shi ne nan, Hurriya kin tuna lokacin da na baki kyautar wannan na ce miki wani ne wanda ya dauke ki d
?ar'uwanki ya baki?

Ta daga kai fuskarta na kirjin Captain tana kuka kamar ba gobe.

 Shi ne ya ba ni

 Me yasa ka bar ni na yi rayuwa a cikin duhu? Why? Me yasa ka ce min kowa ya mutu?

Hamad ya tambaya da karfi yana wani nishi sai kallon Captain yake cike da bakinciki yana jin kamar ya shake shi.

 Na rayu da wasu mutanen da ba jinina ba, a kasar da ba tawa ba, na rayu akan cewar kowa nawa baya raye, recently nan Salim take yake fada min cewar akwai gaskiyar da kake boye min ashe da gaske kake

 Shiyasa na saka aka canja maka gida ai, wata kila da ban maka wannan karyar ba da baka samu lafiya ba, da ban maka wannan karyar ba da baka rayu ka kawo yau ba, da ban maka wannan karyar ba da baka natsu ka yi wannan karatun ba, gashi kuma saboda shi ka cika burinka tare da kai aka yi aikin idon da ka taba fada min cewar ka yi yar'uwarka alkawari


Hurriya ta dago ga kalli Hamad ta mika masa hannayenta so take ya taba ta a karo na biyu ta ji idan da gaske dan'uwanta ne. Hamad ya kama hannun yar'uwarsa da ya fi Marmari fiye da kowa ya rike. Sai ta fashe da sabon kuka.

 Ni dai ina so ko da waninka ne aka kawo min a matsayin kai, zan karba kai ne kadai ka rage min farincikina ya cika, ni kadai ce na yarda baka mutu ba Hamad, amman duk haka ganinsa nake kamar ba gaske ba

 Tun a ranar da da Captain yace min za'ayi wani aiki da yake son ayi tare da ni amman ba zai kawo aikin ba sai a lokacin da zan fara koyon aikin a wannan asibitin sai na kagara na ga haka, da na zo na ga fuskarki sai na ji kamar wata rayuwa ce ta same ni da ba zahiri ba, kuma ya hana ni magana a ranar har sai yau... Kuka nake Captain ya cutar da ni

 Ban cutar da kowa ba a nan, ni kawai taimako na yi, kuma ba zan amsawa kowa tambaya ba sai a gaban iyaye

Captain ya fadawa Hamad a tsawace, kamin ya rika fuskar Hurriya ya share mata hawayenta.

 Ya isa haka, yau aka bude idonki i thought hakan zai saka farinciki ba kuka ba, karki janyo min wata matsala please

Ya rumgumeta a kirjinsa, ita kuma kamar ya karawa kukanta fetir haka ta ji sai ta kara fashewa da kukan sosai.

 Ina son na tafi gida ina son na ga iyayena idan suna raye...

 Hakan ba zai yiyu ba, sai an dauki permission daga makarantarka hakan kuma ba zai yiyu ba sai da hujja, dole ka kwantar da hankali kamin mu yi tunanin abun da zai fi

 Ba zan kwantar da hankali ba, 8na bukatar ganin Amma, babu ruwanka da rayuwata you lie to me azzalumi kawai, ka kira min Amma zan yi magana da ita

Captain ya daka masa tsawa a karo na biyu.

 Ba zaka bar garin nan ba sai da izini, kuma ba zan kirata ba...! And control yourself Hamad na hadeye ka a zuciya Wallahi

Yadda Hamad din yake ta fada ya kara tabbatarwa da Hurriya lallai dan'uwanta sai dai akwai abun da ita da shi ba su sani ba, waya kawo shi a garin nan? Meya saka ce ya mutu? Ta ya ya hadu da Captain? Kuma me yasa Captain ya boye mata gskiyar har zuwa yau? Ta dago kai ta kalleshi tana jin idonta yana wani dauri kamar zai like.

 Kira min Amma...

 Toh zan kirata, amman yanzu ki min hakuri mu tafi masaukinmu kim ga Mama Rukayya da Momy Ikilima ma suna waje suna jiranmu! Sai mu magana a masauki zai fi kin ji

Magana yake mata ta siffar rarashi yana shafa gashinta, sai ta girgiza masa kai ta lake kafadarta daya.

 Aa dan Allah ka kira Amma

 Okay

Ya ciro wayarsa ya danna number surukarsa ya aikata mata da kira. Wayar bata dade tana ringing ba Amma ta dauka tana sallama sai da ya amsa sallamar ya gaisa da ita sannan ya mikawa Hurriya wayar. Hurriya ta karba tana kuka

 Hello Amma...

Hamad yayi saurin kara kunnensa a jikin wayar yana sauraren muryar mahaifiyarsa sai ya fashe da kuka.

 Lafiya Hurriya idon be bude bane?

 Amma wata gaskiya zan fada miki mai kama da karya, Amma Hamad ne yana raye yana tsaye a gefena yanzu na yi magana da shi kuka ma yake yi Amma Hamad dinki yana raye...

Amma ta yi shiru for some seconds sannan ta amsa.

 To ba Jamal wayar...

 Amma baki yarda da ni ba?

 Na yarda ba shi wayar..

Hurriya ta mikawa Captain wayar sai Hamad yayi karaf ya karbe ya kara a kunnensa.

 Amma... Amma.. Amma...

Nan ma Amma bata ce komai ba, domin ba muryar Captain ta ji ba, kuma ba muryar wanda ta sani ba ne, sai dai hankalinta ya tashi sosai tana jin kamar yarta ta samu matsala ne.

 Amma ki ce wani abu dan Allah Hamad ne...

 Ba Hamad ba dai.... Ko waye kai dan Allah ka bawa Jamal wayar...

Hamad ya dauke wayar a kunnesa ya mikawa Captain sannan ya nufi kofa zai fice hawaye na sauko masa, Hurriya ta yi saurin sakowa daga kan gadon tana kiranshi.

 Dan Allah karka tafi, dan Allah karka tafi Hamad inda da gaske kai din ne karka tafi dan Allah...

 Jamal matarka bata da lafiya ne?

Amma ta tambaya Captain ya sauke ajiyar zuciya.

 Lafiyarta kalau, kuma an yi aikin idon ya bude Alhamdulillah an yi nasara

 To me yasa take min zan cen Hamad? Ko idonta ya fara ganin fatalwa ne yanzu kuma...

 Da gaske ne Amma Hamad yana raye, akwai abun da baku sani ba, akwai abun da na boye muku sai a yanxu nake jin lokaci yayi da ya kamata ku san komai...

 Kai ma baka da hankali ko Jamal? Dana Hamad ya dade da rasuwa...

 Be rasu ba Amma Hamad yana raye....

Ta katse wayar ji take kamar wasa suke son yi da hankalinta ko kuma dukansu ba su da lafiya ko kuma dai yana biyewa matarsa ne wata kila ta tabu.

 Ka ga abun da ka janyo ko? Ka kashe kowa a gurina kuma ka kashe a gurinsu...

 Ban kasheka a gurinsu ba, ba ni na yi wannan ba step mother dinka ce ka tuna wannan? Ban fadawa kowa kana raye ko a mace ba, amman kai na fada maka suna a mace ne saboda ka rayu...

Captain na kai aya kiran Appa ya shigo wayar Captain cikin girmamawa da mutuntawa ya amsa kiran.

 Lafiya kalau ya matarka?

 Alhamdulillah an yi aiki cikin nasara Appa ido ya bude...

 Alhamdulillah maa sha Allah ina take bata wayar..

A madadin ta karba sai Hamad ya sake karbewa.

 Appa...

Appa yayi shiru kamin ya amsa.

 Na'am waye wannan...

 Hamad ne Appa Hamad ne...

 Hamad na mu?

 Eh Wallahi ni ne Appa wallahi ni ne ba fatalwa ba ne ban mutu ba

 Me ka fada min na yarda kai ne? A ina ka hadu da Hurriya? Ina ka san Captain...

 Ina karkashin kulawarsa ne Appa, ina tare da Captain kusan ko da yaushe, amman ku ya fada min kun mutu...

 To ba shi wayar zan yi magana da shi....

Hamad ya aje wayar akan gado domin bakin cikin abun da Captain yayi masa ba zai barshi ya sake hada hannu da shi ba. Captain ya kalli wayar sannan ya danne zuciyarsa domin ya san babba baya zama kamar yaro, kuma dole zai yi ma Hamad uzuri na halin da yake ciki a yanzu.

 Hello Appa..

Iyami ce ta kirani tana kuka tana fada min wata magana da bata kama hankalinta ba, ni ma kuma bata kama nawa hankalin ba, shiyasa na kiraka sai kuma na ji makamancin abun da take fada min me yake faruwa.

 Labari ne mai tsawo Appa ba zai yiyu a waya ba, dole sai an zauna hakan kuma ba zai yiyu ba sai an dauki permission daga makarantarsu Hamad gudun lalacewar karatunsa

 Hamad kake kira fa Captain...

 Hamad Appa Hamad yana raye... Amman yanzu kamin uzuri zan tafi masaukinmu idan Hurriya ta natsu zamu yi magana... Zan kiraka na fada maka yadda komai zai gudana.

Hankali namiji be taba zama iri daya da na mace ba hakan ya saka Appa ya saurare shi.

 Toh ina jira..

Captain ya kashe wayar ya kalli Hurriya dake kallon Hamad kamar zata cinye shi tana hawaye.

 Kukan nan ya isa haka, ni da na san haka abun zai zama ba zan bayyana miki shi ba

 Ni kuma sai na yi ta zama har zuwa lokacin da zaka bayyana ni bayan na ga yar'uwarta?

Hamad ya fada a tsawace, Captain ko gefe da yake be kalla ba ya kama matarsa.

 Mu tafi Mama Rukayya suna reception suna jiranmu, daga can zan yi clearing kudin asibitin sai mu tafi masauki mu yi magana hakan yayi miki...

Ta daga mishi kai.

 Hamad zai tafi tare da mu ko?

Ya daga mata kai yana shafa fuskarta hawayen dake zubar mata yake jinsu har a ransa.

 Toh...

Ya dauki mayafinta ya rufe mata kai sannan ya kama hannunta suka fito daga dakin.



NIGERIA....

Appa ya saka hularsa yana amsawa Yasir.

 Eh can zan tafi gurin Iyami na yi magana da ita, saboda na ji tana ta kuka abun ne da daure kai na rasa gane kan gadon labarin..

 Ni ma na ji abun wani iri, maybe akwai abun da Captain din yake boyewa ko kuma Hurriya ta samu matsala ne? Yake biye mata...

Yasir ya fada with confused.

 Amman na ji wata murya yake cewa Appa ni ne Hamad ne har da rantsuwa ni abun ya daure min kai... Shiyasa nake son na tafi gurin mahaifiyarta

 Okay Aappa Allah ya tsare

 Amin sai na dawo...


A tare suka fito bangaren Appa ya shiga motarsa, Yasir kuma na nufi bangaren Hajiya Kaltume domin labarta musu halin da ake ciki. Shigarsa bangaren ta yi daidai ta cire mayafin da Hajiya Kaltume take tana sauke gajiya. Tana kallon fuskar danta ta san ba kalau ba, domin mamaki ne da daure kai a fuskarsa sai dai bata ce masa komai ba har sai da ya zauna.

 Lafiya.?

 Wani abu ne mai daure kai Hajiya... Yanzu muna tare da Appa a gida muna duba kasafin kudin da suka shiga da fita na wannan watan bangaren Motocin Appa, sai Amma ta kira tana kuka wai Hurriya ta kirata da number Captain tana mata zancen Hamad, Appa ma be gane kan maganar ba sai da ya kira Captain din da kanshi sai wani ya karba yana cewa shi ne Hamad, Appa dai yayi magana da yaron kamin Captain ya karba ya ce idan sun koma masauki zai kira Appa su yi magana kuma shi Captain din ya fada ma Appa cewar Hamad ne, but labari mai dadi dai idon Hurriya ya bude

 Hamad......!

Hajiya Kaltume ta fada da karfi kamar zata rusa dakin.

 Karya ne ba dai Hamad ba, Hamad din da ya mutu? Hamad din da aka kashe? Yaushe zai rayu? Wane irin Hamad kuma? Wannan karya ne, an riga da an kashe Hamad ba zai dawo ba, wannan wai duk na minene Yasir? Duk na ganin bayana ne? Duk na son a ga karshena ne? An hana ni zaman lafiya da mijina, an fitine ni har sai da Alhaji ya sake ni, yanzu kuma zai maida Iyami, idon Hurriya ya bude, ta yi aure ta auri babban mutum, sannan n fasa auren tawa yar, mahaifinku

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login