Showing 57001 words to 60000 words out of 279257 words

Chapter 20 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34672

nuna Hajiya Kaltume da yatsa.

 Ke Kaltume ke kin sani ko ban haife ki ba, na yi kanwa da ke, dan haka na cancanci girmamawa a gareki ko dan Iyami

Hajiya Kaltume ta yi murmushi da ya fi kama da yar siririyar dariya.

 Wannan kuma ai da ne Gwaggo, yanzu babu wannan alakar, kuma da kuke neman daga mana hankali ni ma fa tawa yar tana can tare da Hamad aka sace su, ko kuma ita ba mutum ba ce?

Gwaggo ta mike tsaye.

 Kwarai kuwa mutum ce, shiyasa ai na ganki kin sha wanka kina ta far'a da jindadi an sace miki auta, gashi nan ai ya nuna a fuskarki

 Gwaggo karki gayan magana, to faduwa zan yi na yi birgima? Ko kuma an fada miki ni din kamar yarki ce Iyami da bata yarda da kaddara ba? Ai ma dai da kunya Wallahi ku tako gidan nan da sunan ganin Alhaji shi be nemu ba ku za su neme sa, abu dai kamar ba Fulani ba

 Ba rokonsa muka zo akan ya ba mu wani abu ba, kuma ba zuwa muka yi akan ya maida Iyami ba, shi ne abun kunya, mun zo ne saboda Hamad, ai kin san ko an rabu idan akwai yaya kamar ba a rabu ba ne, sai hakuri Hajiya Kaltume Iyami dai ta zama murucin kan dutse, ta zama kadangaren bakin tulu, kuma ta zama ?ashin wuya bata haWuwa bata amayuwa

Maama ta juyo tare da tasowa daga dinning din zata fadawa Gwaggo magana Hajiya Kaltume ta yi saurin daga mata hannu.

 Babu ruwanki Maama je ki cigaba da cin abincinki, Allah dai baya baci zalinci da kuka min sai ya saka min macuta kawai masu abun kunya

Hankali kwance Gwaggo ta ce.

 Ba mu da abun kunya, da muna da abun kunya mijinki ba zan lallaba ya nemi hada iri da mu ba, kuma Alhamdulillah ko yanzu kasuwa ta watse Wan koli mai rabo ya ci riba, tun da ga ?a?a nan Allah ha raya su ya saka musu albarka

Gwaggo na kaiwa nan ta kabe Hijabinta ta fice daga falon ta bar Hajiya Kaltume da ciwon rai. Ko da Gwaggo ta iso gurin Bappa na nasa masifar Yasir na bashi hakuri.

 Bappa ka yi hakuri Wata kila ransa ne a bace

 Idan ransa ne a bace be san waye ni ba da zai fada min maganar banza?

Gwaggo ta dubi Yasir ta dubi Bappa.

 Malam lafiya?

 Yasir ya shiga ya kira min Alhaji Haruna, daker mutumen ya fito, kuma abun da yake fada min shi be da miliyan dari biyu da zai bada yanzu, kuma ina damunsa da kira ban san damuwarsa ba, ai ba Hamad kadai aka dauka ba har da yarsa amman mun daga masa hankali kamar Hamad ne kadai a, idan muna da kudin mu ba su mu karbo Hamad din har da rubuto min number mutanen ya turo min, wai shi ba zai bada kudi ba police sun ce za su karbo su

 Hmmm Allah ya kyauta, tun da ya baka Number mu tafi Malam

Yasir ya nufi Gwaggo cikin rashin jindadin abun da ya faru yana bata hakuri

 Gwaggo dan Allah ku yi hakuri, maybe damuwa ce ta yi ma Appa yawa, dan Allah ku yi hakuri ba halinsa ba ne Wallahi

 Karka damu Yasir babu komai

Gwaggo ta fada sannan ta bude motar ta shiga, Bappa yaja motar sai masifa yake ta yi domin yau Alhaji Haruna yayi masa abun da be taba masa ba.

 Har yana cewa muje mu biya kudin ganin yake kamar ba zamu iya ba ko? Har yaushe za a bata lokaci gurin jiran abun da baka san faruwarsa ba? Ko bayan haka ni bana je akan ya bada kudi ba, naje ne mu yi magana ta fahimta da shi na ji halin da ake ciki, amman mutumen ko kallona baya son yi, sai fada yake kamar shi ne uban ni ne dan, na fada masa ni ba zan dauki wannan rainin wayon ba, kuma ni da gidansa har abada, wato saboda ya saki Iyami shiyasa yanzu baya ganin kimarmu ko?

 Allah kadai ya san abun da yake nan Malam, Allah dai ya isarwa Iyami da yaranta Allah ya saka mata da gaggawa

Gwaggo tana addu'a tana kuka daman idan ranta ya bace bata da wuyar kuka.



_________________

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


5??5??5? ?5?? 4??

 Gaba daya an juye kan Alhaji Haruna, kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, ba zai wuce Kaltume ba, domin bata hada hanya da imani ba, kai ko gurin da ya bi ya wuce bata bi ba

Amma ta share hawayenta bayan ta gama sauraren Gwaggo dake fada mata abun da ya faru.

 Ni yanzu ba ta Kaltume nake ba ko Alhaji, ta dana nake burina ma ga ya fito, kuma tun da har ya kai ga furta cewar ba zai bada kudin ba, ni zan bada albashi shi sai ya bada na Ruma

 Ko daukar yaron nan da aka yi bana raba dayan biyu, Kaltume ce ta saka aka sace shi, yadda na ga ta sha ado ta sauko hankali kwance har tana neman fada min magana ya isa ya tabbatar da cewar da sa hannunta aka sace yaron nan, tasan yarta tana cikin kwanciyar hankali shiyasa hakan be daga mata hankali ba, kuma yanzu na kara tabbatar da ita ce ta aiko Maama gidan nan saboda ta rabaki da dan abun da kike da shi, ni dai da zaki yarda da shawarata da kin saurara karki kira su ki kyale su da yaron ki gani shi za a karbo Ruma ba a karbo Hamad ba?

Amma ta daga kai ta kalli Hurriya dake zaune a waje tana cin indomie da Gwaggo ta dafa mata kamin ta fita.

 Gwaggo shin idan wani yayi garkuwa da ni yace sai an bashi kudi alhalin kina da hanyar za ki bi ku bada kudin nan zaki bada ko kuma zaki tsaya jiran sai ranar da wani ya bada ne?

 Zan fada

 Toh ki saka kani a matsayinki, ni ma fa uwa ce tun daga lokacin da na baro gidan uban yaran nan kullum da kalar tunanin da nake kwana a raina balle kuma yanzu da yarona yake hannun wasu mutane da ba mutanen kirki ba, marasa tsoron Allah, duk abun da nake da shi a duniyar nan be kai ran Hamad ba, Gwaggo ko rayuwata suke ce sai na basu sannan za su sako Hamad Wallahi zan ba su

Tana maganar hawaye masu zafi na sauko mata, ita kadai take iya jin abun da ko wace uwa take iya ji idan danta ya shiga mugun hannu.

 Kana ina dana? Ka ci abinci baka ci ba? Wane kalar abinci suke baka, ina kake kwanciya? Suna azabtar da kai ko basa yi? Ka yi marmarin gida?

Amma ta gargiza kai tana kara jin ba zata iya jure har lokacin da Appa zai ga dama ya biya kudin ba. Haka kuwa aka yi, Bappa ma ya bata goyon baya domim ransa ya bace sosai akan abun da Alhaji Haruna yayi masa, Amma da kanta ta kira number da aka bata sai suka tararda line a kashe, sai dai mai neman baya fitar da rai, jajircewa suka yi ta yi suna kiran line kullum ba dare ba rana ba safiya, har suka yi sa'a a rana ta uku kiran ya shiga da misalin karfe goma sha daya na dare. Abun da baka saba ba zuciyar Amma ta hau zillo tsoro ya kamata kamar suna gabanta, duk kokarin da Bappa yayi na ba su Hamad su yi magana da shi sai mutanen suka ki, Bappa ya tambaye ina za a kai musu kudin suka fadi gurin da za akai musu kudin a aje, wani kasurgumim daji ne dake tsakanin mafara da Gusau.

Bayan sun gama wayar Bappa ya ce.

 Allah yasa dai yaron nan yana raye, na ga duk kokarin da muka yi sun ki yarda su ba mu shi mu yi magana

Amma ta girgiza kai.

 Yana nan raye Bappa, yana raye In Shaa Allah

 Yanzu waye zai shiga wannan guri ya kai kudi mai yawa haka? Ai shi ma sai su rike shi kamar yadda suka yi ma kanen Hajiya Kaltume, ni dai da zaki hakura mu ga abun da hukuma za su yi, ko kuma idan za a je kai musu kudin aje tare da police

Bappa ya kalli Gwaggo dake maganar ya ce.

 Baki ji sun sake jaddada mana kar mu kuskura saka police a ciki ba, kai kuma kuma zan iya zuwa na kai, indai za su sako yaron nan hankalin kowa ya kwanta zan aikata haka, kawai ku yi ta mana addu'a

Cikin yanayin damuwa Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya.

 Kowa ke da hannu a cikin lamarin Allah ka wulakanta shi ka tona asirinsa

 Ameen

Bappa ya amsa. Gidan da Appa ya bata a lokacin da zai sake ta aka fara sakawa a kasuwa, domin filayen da ta mallaka guda biyu a gidan Appa ta san idan ta saka su a kasuwa ba lallai ne ayi saurin siya kamar gidan da yake gyararre ba, duk da haka kuma sai da aka siyar da shi a nakashe, gidan da zai yi miliyan 45-50 aka siyar da shi a miliyan 35 ta hada da kudin da Appa ya bata da dan abun da take da shi ciki har da sarkar gold din da Appa ya siyawa Hurriya duk ta siyar ta hada kudin ta bawa Bappa, ranar da za aje kai kudin babu yadda Gwaggo bata so a saka police a cikin lamarin ma amman Amma ta ki yarda ganin take idan aka yi haka an bata lokaci kuma za su iya kashe mata da kamar yadda suka yi ikirari, Gwaggo kuma na ta ganin rautar Bappa da Amma taya za a dauki kudi mai yawa haka a shiga daji a kaiwa barayi ba tare da sanin sami'an tsaro ba, abu dai kamar a shirin film.

Cikin karfin hali da yarda da kaddara Bappa ya shiga dajin tare da wani dan'uwansa, bayan yayi addu'o'in da be san adadinsu ba, Gwaggo da Amma, Rukayya da duk wani dan'uwa ma suka raka shi da addu'a. Dan'uwa ya tsaya daga waje shi kuma ya shiga ciki ya kai kudin ya aje a gurin da suka bukata. Har ya kai ya fito babu abun da ya same shi, a lokacin da ya fito ya kira gida ya fada musu ya fito sai kowa yayi ta hamdala ana jin sanyi. Kamin hankali ya karkata gurin ganin kiransu ko sakon inda za su ce a je a dauki Hamad amman shiru. Daga bisani suka bi sawun kiran da number da suka kira da ita last time, domin kullum canja number suke idan za su kira. Haka aka kwashe two days babu kira daga garesu kuma babu wani sako kuma idan aka kira wayar bata shiga, hankali Amma sai ya kara tashi, ta kai bata iya cin komai rashin lafiya ta taso mata har sai da aka kwantar da ita asibiti kowa yayi zaton haihuwa ce duba da tsohon cikin da take da shi, sai dai likitocin sun tabbatar musu ba haihuwa ba ce hawan jini ne, har suka so riketa saboda jinin nata ya hau sosai kuma bata iya cin komai sai dai ruwan da suke saka mata suna taimaka mata ta bangaren kuzari. Sai dai yadda ta nuna bata son zaman asibitin da kuma rokon da aka yi ta musu sannan suka yarda suka sallame ta bayan sun fada musu cewar a rika kokarin kwantar nata da hankali if not idan ta zo haihu zata iya samun matsala ta kasa haihuwar da kanta ko ma arasa danta ko ita ko a rasa duka. All zaman da ta yi asibitin Appa be zo ya dubata ba, even for once be daga waya ya kira ya ji jikinta ba, Hajiya Binta kan kwana ne kawai bata taba yi aabitin ba amman kullum can take wuni, babu yadda bata yi ba Appa ya zo ya duba tsohuwar matarsa, na dan Hurriya da Hamad kadai ba har dan cikinsa da take dauke da shi, amman ya kasa zuwa bayan be saba mata musu ko jayyaya mai tsauri haka ba. Yaran Kaltume ma babu mai mata fatan tashin sai na mutuwa, Yasir ne kadai yayi ta zirga zirga a asibitin gurin dubata ta kuma biyan duk wani bills na magani ko na gado, Namra ma taje duba sau daya tare da wata Neighbor dinsu kawar Hurriya da suke good time da ita, shi ma a sace domin idan Momy ta sani sai ta karya kafafuwanta. Hankalin Hurriya ya tashi sosai ta fara nata zazzabin a tsaye, tunanin sai ya hade mata biyu tana ganin kamar zata rasa mahaifiyarta ta kuma rasa dan'uwanta ne a lokaci daya.
Washe garin ranar da aka sallamo Amma asibiti bayan ta shafe kwana biyar a asibitin, Yasir ya zo gidan sake dubata yake musu albishir da cewar Appa zai bada kudin a yau, sun ce a yau din nan za su fadi gurin da za aje a dauko Hamad da Ruma.

 Kai.. Allah ka sasauta mana mutanen nan ba su da imani ko kadan, yanzu bayan kudin da suka karba gurinmu kuma za su za su karba?

Cewar Gwaggo tana ta juya zancen.

"Wallahi kuwa, ni da kun yi shawara da ni ba za ku bada wannan kudin ba, komai dai ta kama daman na san dole Appa zai biya kudin

Rukayya ta kalli Yasir tana masa alamar yayi shiru ta ido.

 Kasan jiya muka dawo daga asibitin nan kuma ta nanata zancen nan sai ku saka ranta ya bace

Amma ta kalleta tana murmushi.

 Rukayya kenan, rai ba zai bace ba dan na bada kudin, ni dai burina su dawo min da ana

 In Shaa Allah, zai dawo inda ba sun yaudare mu ba to zai dawo yau din nan tare da Ruma

Hindu ta kalli Yasir dake maganar ta yi masa tambaya.

 Waye zai je ya kai kudin?

 Rilwanu me zai kai, yace zai iya zuwa domin gurin da suka fada hanyar garinsu ce yana yawan bi ta gurin?

 Waye haka dan'uwanku ne?

 Eh da yake ga Hajiya ta bangaren kanenta

 Allah sarki Allah yasa su cika alkawari

 Ameen

Daga haka babu wanda ya sake wata magana a falon, har Yasir ya mike tsaye ya yi musu sallama ya fice. Hindu ta kalli Rukayya ta ce.

 Je ki raka shi mana

 Anty Hindu ban saba yi masa rakiya ba

 Toh ki fara daga yau, je ki raka shi mana, daga can ba sai ki jiyo mana wani labarin ba

Tashi ta yi ta bi bayansa ba dan ranta ya so ba sai dan ba zata iya musawa kawar Yayarta ba. Ko da ta fita yana tsaye bakin kofar tsakar gidan tsaye yama jiranta kamar ya san zata fito. Suna hada ido sai yayi murmushi ya juya ya cigaba ta tafiyarsa ita kuma ta bi bayansa har gurin mota, ta tsaya yana juyawa kunya duk ta rufeta.

 Ke lafiya kike?

 Lafiya kalau sai anjima

Ta juya da sauri ta bar shi tsaye ya bita da kallon mamaki, before murmushi ya baibaye fuskarsa. Misalin karfe hudu na yamma Yasir ya kira wayar Amma yayi mata bushara da cewar an kai kudin kuma sun fadi gurin da za a je a dauko su Hamad da Ruma yanzu haka suka hanyar daukosu tare da Kanen Appan Alhaji Sa'idu sai kuma Kawu Garba wani dan'uwan Hajiya Kaltume da kuma Yasir din duk a mota daya.

 Alhamdulillah

Amma ta bada tana sauke wayar, jikinta ya hau tsuma ma dadi farin ciki ya ziyarci zuciyarta ya mamaye ilahirim jikinta, dan zazzabin da take ji sama sama da rashin kuzari duk sai ta neme shi ta rasa. Hurriya ta mike tsaye da sauri tana murna.

 Amma zan hau Napep na tafi gidan yanzu ina son Hamad ya dawo ina nan

 Ai ni ma ba zan iya jira a nan ba, kira Gwaggo na fada mata

Hurriya ta fita dakin da sauri ta kira Gwaggo, a nan murna ta kaure Gwaggo sai Hamdala take, ta waya Gwaggo ta fadawa Bappa halin da ake ciki, sannan ta dauki permission din fita tare da Iyami, sanin yadda a da uwa suke ya saka Bappa ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login