Showing 51001 words to 54000 words out of 279257 words

Chapter 18 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34621

ya zauna ya rika yarsa.

 Hurriya

 Na'am Appa

 Ki kwantar da hankalinki kin ji, Hamad zai dawo soon da yardar Allah, babu abun da zai same shi, kuma na ji dadin da baki fadawa Iyami abun da ya faru ba, kin ga tana da ciki zata iya daga hankalinta,

Ta daga kai ta kama hannun Appa ta jimke da karfi.

 Appa bana ganin komai yanzu, bana ganin komai sai abun da ya faru, me yasa suka dauke Hamad? Me yayi musu?

 Wallahi dukanmu ba su sani ba, amman dai an san ba zai wuce su ce a ba su kudi ba, kamar yadda suka yi ma Kaltume kuma shi ma za su sako shi

 Hadda Ruma aka kama

 Na sani duka zamu biya kudi mu karbo su Da yardar Allah, amman yanzu zamu tafi dake gurin police za su miki tambayoyi akan abun da ya faru, saboda kun sanar da ya sanda, kamin nan kuma ina son ki min alkawarin ba zaki fadawa Iyami ba, kuma ki daina kukan nan har sai mun karbo shi

Kamin Hurriyya ta dauki alkawarin suka jiyo Amma daga jikin curtains din kofar dakin tana furta.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un.
Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un
Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un

Daga Appa har Hurriya ba su san Amma ta yi labe ba sai a lokacin. Appa ya taso ya fito da sauri yayinda Gwaggo ma ta fito da sauri daga dakin Amma ta nufota.

 Gwaggo sun dauke min Hamad, su biyu Allah ya ba ni sun dauke daya, kashe shi za su yi Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Gwaggo ma ambaton Allah ta shiga yi tare da rike Amma dake shirin faduwa.

 Allah yasa kaddara ba musanya zata min ba, Allah yasa ba Hamad za a dauke a ba ni wani ba, La'ilaha Illallahu, Allah kasa kari zan samu ba musanya ko ragi ba, su wa suka dauke shi? Na san ana be jin magana amman su yi hakuri dan Allah idan wani laifin yayi, kowa ya min haka be kyauta min ba, me suke so Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un

Gwaggo ma sai da ta fashe da kuka saboda kukan da Amma take yi. Appa kuma yayi tsaye a gurin hopeless yana kallon tsohuwar matarsa dake dauke da cikinsa ya rasa m???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e zai yi.




Littafin nan kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

________________


https://chat.whatsapp.com/F1ch00M9VNvFxrVVgCEeXo

Ina Yan uwan Yan gayu makotan Masu Kudi?
Daku nake Magana.
Matan da suka san ciyon kansu masu hada goma ta zamo ishirin kuzo ku sari Kaya acikin sauki da rahusa a Ummu Ahmad store muna kawo kayan mu ne daga Lagos masu quality da karancen farashi akwai kayan kitchen akwai shoes and bags, Akwai kayan abinci na awo laces,kayan yara,da sauransu
Sannan akwai kayan gyara irin su tsimi kala kala gumbar mata daban daban maganin sanyi
Akwai kaza me rubutu da wadda akeyi da sanyun magani
Akwai taimako na haihuwa ga wadda taje asibiti akace batada matsalar komai akwai rubutun da muke badawa Wanda idan ta gama Al adarta zatayi amfani dashi za adace da yardar Allah
Akwai kayan kamshin daki da na jiki

Location dinmu zamfara
Muna tura Kaya a koina kk cikin aminci da yardar Allah payment validate ur order Ummu Ahmad 08032350261

Ni Khadeeja Candy nake tabbatar muku ba zaku taba nadamar siyen kayan Little Mommy na ba, uwata ce ta jini ba lake lake ba, please patronize her tana siyar kaya masu kyau da imganci, zaku iya tuntubarta ko ma ku tuntube ni kai tsaye =؃? sai ku zo >?p?


5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


5??5??5? ?5?? 2??

Sai da Gwaggo da Mama Rukayya suka yi da gaske sannan suka iya rarashin Amma ta yi shiru, suka dagata suka shigar da ita falon har lokacin Appa ya tsaye ya rasa abun cewa, Hurriya ma kuka take sosai tana tausayin kanenta tana tausayin mahaifiyarta.

 Dan Allah Gwaggo a kwantar mata da hankali, ba yau aka saba daukar mutane kuma ana dawowa da su lafiya, na san dai ba zai wuce su ce suna bukatar kudi ba, kuma ba mu biya mu karbo shi

 Toh Allah ya bayyana shi cikin aminci

Gwaggo ta fada cikin kuka, sai a lokacin Appa ya samu courage din fice daga cikin gidan tare da Hurriya, a mota ma Appa ya wahala kamin ya samu Hurriya ta yi shiru, hankalinsa be kara tashi ba sai a lokacin da take bada labarin yadda abub faru. Duk wani abu da ya kamata su tambayeta sun tambaya kuma ta ba su amsa sannan Appa ya dauko ta a motarsa tare da Direbansa suka nufo gida.

 Appa ka kar ni a gurin Amma please bana son nan

 Zan maida ke can Hurriya, ita ma ai ganinki zai saka ta dan ji sanyi, zaki dauki tufafinki, sai kuma Yasir ya baki dayan glass dinki da yake can

 Toh

Daga haka bata sake cewa komai ba har suka isa gidan. A harabar Momy Appa ya umarci direban ya faka, sannan ya fito direban ma ya fito da sauri ya budewa Hurriya mota Appa ya rikata ta fito, suka nufi bangaren ransa a jagule gaba daya shekarar nan ta zo masa a yadda be yi zato ba. A hankali ya tura kofar falon Momy sai da ya fara shiga sannan ya rikota ta shigo. Captain dake zaune ya mike tsaye yana amsa sallamar Appa, Appa ya karaso cikin falon cikin yanayin dake nuna yana cikin tsananin damuwa.

 Momy bata nan

 Oh to ina taje? Ina zuwa Hurriya

Ya saki hannunta ya juya ya fice daga falon.

 Ance kananki?

Captain ya furta a hankali yana kallon kwayar idonta dake ta juyawa alamar bata ganin komai. Kamar ya tsikaro mata allurar kuka sai ta fara hawaye tana rawar murya.

 A yadda Namra ta fada min ke suka zo dauka, kin san su waye?

Ta girgiza kai.

 Waye kai?

Ta tambaya domin bata wayanci ko waye ba. Yayi shiru yana juya invitation card din dake hannunsa for some seconds.

 Soja ne...!

Ta mika hannu ta fara lalaben inda take jin sautin muryarsa.

 Dan Allah zaka nemo min kanena?

Tana daf da taba fuskarsa ya kawar da fuskar ya kai hannunsa ya rika hannunta, ba tare da ya amsa mata da eh ko aa ba.

 Dan Allah ka nemo min kanena idan zaka iya, shi ne farincikinmu, shi yake tare min fada dan Allah ka taimaka Malam Soja ka nemo min shi

Yayi shiru har lokacin be ce komai ba ya saki hannunta daman ya rika hannun ne kawai a kokarinsa na kawaicewa taba fuskarsa. Shi dai abun da ya kawo shi gidan dabam ya zo ya tararda wannan tashin hankali.

 Malam Soja...

Jin shiru kamar babu kowa a gurin. Sai ya kai hannunsa ya rika 5 fingers dinta ya matsa a hankali domin tabbatar mata yana tsaye a gabanta har lokacin.

 Dan Allah ka nemo min kanena, ku ne sojoji ai ku kuke kama masu aikin yan ta'adda

Kallon fuskarta yake kamar ance masa tana ganinsa.

 Dan Allah ka taimaka mana, Appa na kudi zai iya ba ku please

Ya sake rika 5 fingers dinta ya matsa hannunta.

 Idan ka min alkawari ka matsa sau biyu...

It take him ten seconds kamin ya sake matsa 5 fingers dinta for the third time, sannan ya saki hannunta ya zari Invitation card daya a cikin wadanda suke dayan hannunsa na dama, ya dora su akan mini table dake kusurwar kujerar ya juya bayan dayan card din ya yaga ya ciro pen dinsa yayi rubutu akai sannan ya maida pen din ya sake barkar takardar ya kama hannunta ya danka mata rabin.

 Karki fadawa kowa, kuma karki taba jefar da wannan takardar matukar ina fatar Kanenki ya dawo

Ta jimke yar ficikar takardar a hannunta tana sauraren takun tafiyarsa har ta ji lokacin da ya bude kofar falon ya rufe. Bayan kamar minti biyar tana tsaye a gurin aka sake bude kofar falon aka shigo.

 Hurriya Appa ya ce na zo dake

Yasir ta karaso ya rika hannunta yaja suka fita daga falon.

 Na duba ko'ina ban ga gilashinki, zamu je asibiti a siya miki wani yanzu kamin a ga wadancan

 Ya Yasir yaya zai dawo ko?

 In Shaa Allah

Yasir ne ya kaita asibitin gurin likitan da ya saba dubata, suka bata wani gilashin da ya dace da idonta, sai dai idon nata sun sake samun matsala ko da ta saka gilashin bata iya gani da kyau kamar da, hakan ya saka likitan ya sake duba idonta kamin ya rufe ta fada da kuma Yasir wai an barta ta yi kuka mai karfi da yawa har yana son tana gilashin idonta, daman idon lafiya be ishe shi ba. Magani ya bata wadanda zata shafa a idon safe da kuma dare idan zata kwanta sannan ya bata wanda zata diga a idon kamin ta kwanta. Sannan suka dawo gida, kusan duk wanda ya kalleta ita yake tausayawa domin ita ce bata da uwa a gidan kuma ita ce kadai take da kane daya, Hankalin Hurriya be kara tashi ba sai da ta zo zata dauki tufafinta da suke bangaren Momy ta kalli dakin Hamad sai sabon kuka ya taso mata, tana ganin kamar mutuwa yayi ya barsu. Ta saka tufafin da zata iya diba a jaka, ta fito tana kuka ta fice daga falon Momy. Momy dake aikin duba invitation card din da ta tarar a falonta ko kallo gurin da Hurriya take bata yi ba sai yana katin take, Namra ta tashi ta bi bayan Hurriya ta rakata har gurin motar Appa, domim shi yace zai kaita gurin Amma da kansa, sakamakon kiransa da Hajiya Binta ta yi ta ce ya zo ya dauketa ya kaita gurin Amma kuma ya kawo mata Hurriya. Namra ma sai da ta yi kuka saboda yadda Hurriya take ta kuka. Sai da suka fice sannan Namra ta dawo bangarensu tana share hawaye.

 Wallahi duk wani mai imani sai ya tausaya, kowa ya aikata haka Allah ya hana shi zaman lafiya

Momy ta daka mata tsawa.

 Ina ruwanki shegiya yar iskar yarinya yar neman suna, ke aka sata? A gidan nan wa kika ga yana damuwa da rayuwar wani?

 Haba Momy idan aka sace ni ya zaki ji?

 Allah ya mayar miki da aniyarki, ni ai wanda ya sace yaron kuma ya gama da yar wajen Kaltume ya kyauta min Wallahi, daman shi Hamad ya fitini kowa, karshen mai cin amana kenan, ita kuma Ruma satarta zai hana Kaltume kwanciyar hankali

Miwan dake saukawa ya karbawa Momy.

 Wallahi kin fadi abun da yake zuciyata, daman shen yaron nan ya isheni, saboda shi nan kwanan baya babu fadan da Appa be yi miki ba, har kuka sai da kika yi, kuma saboda shi aka mari Musib Allah yasa ma su kashe shi

 Ato... Da ma Hurriya ce wata kila na tausaya mata, amman Hamad shegen yaro. Kaji min yarinya wai ita mai zuciyar tausayi, ke idan ke aka kama waye zai yi wannan kuka? Kuma ni bana raba dayan biyu, Wallahi Kaltume zata iya sakawa a sace yaran nan saboda muguwar mata ce, yaushe ta dawo? Ta sace kanta kudin be mata ba yanzu kuma ta koma gurin yara, balle kuma ta san Hurriya Alhaji yana ji da ita, ke ma kuma idan baki kula ba sai ta saka an dawo kanki, wannan bakar matar mutuwa kawai zata yi kowa ya huta, ni daga yau ma ba zaki sake komawa makarantar ba, canja miki makaranta zan yi, kuma direba dabam zai rika kai ki yana dawowa dake

 Amman Momy baki ga yadda Hajiya take kuka ba, haba Momy za'ayi ta sace yarta?

 Kukan munafurci ne, ke yarinya ce baki san kan duniya ba, ni dazun da na san Captain zai zo ai ba zan ma shiga bangarenta ba, ke kuma kika ki kirana gashi har sake zuciyar ya tafi

 Shi yace kar na kira ki na barki sai kin kare abun da zaki yi, bayan ya tambaye ni abun da ya faru

Miwan ya zauna yana daukar katin ya duba.

 Wallahi Momy Captain yana sonki sosai if not wulakancin nan da aka yi ta masa ba zai sake dawowa ba

 Ai nima na san haka, shiyasa nake son zage dantse na kyautata masa a bikin, ga abu dai ya matso kusa

Daga haka suka dauko zancen bikin kamar babu ruwansu da damuwar kowa. Appa sai da ya biya unguwar Gidan Dawa ya dauko Hajiya Binta sannan ya nufi gidan Gwaggo, a mota Hurriya na kara fadawa Amma abun da ya faru tana kuka. Appa be shiga ciki ba, daga Hajiya Binta sai Hurriya suka shiga, Hajiya ta hadu ita da Gwaggo suka yi ta bata magana suna kwantar mata da hankali. Sannan taja ma Hurriya kunne kan fita waje duk kuwa da ta san Hurriya ba ma'abociyar yawo bace, daman kuma Appa yayi mata nasa jan kunne a mota.


*** *** ***


Wasa wasa aka kwashe kwana uku shiru babu Hamad da Ruma babu labarinsu, police din da aka damkawa case din kuma ba su samu wani bayani ba, sai dai suna ta kokarin zafafa bincike iya yinsu. Tun daga ranar kuma Amma bata iya bachi, dare take rayawa tana fadawa Allah bukatarka ya kare mata danta ya dawo mata da shi cikin aminci. Abinci ma Amma bata iya ci sai Gwaggo ta yi da gaske. Hurriya kuma tun daga ranar bata sake zuwa makaranta ba saboda tsoron fita da take ko kofar gidan bata yarda ta tafi, daman kuma Appa ya daukarwa yaransa hutun sati daya a school dinsu har zuwa lokacin da abun zai dan sake su. Appa ma ya yarda Hurriya ta zauna a gurin Amma ne kawai saboda Hurriyar ta zaki haka, kuma ya san hankalin Amma zai dan kwanta idan Hurriya tana kusa da ita, ba dan ransa yana so ba, domin gani yake ko a can za a iya tafi a dauki Hurriya ko Amma.

Ranar da Ruma da Hamad suka cika kwana bakwai da sacewa su aka kira wayar Appa ana neman miliyan dari na Hamad, miliyan dari na Hurriya. A ranar hankalin Appa ya tashi sosai ya nemi su hada shi da yaransa su yi magana, sai suka ce mutum daya za su ba shi wato Ruma, suka bata wayar ta yi magana da shi tana kuka sosai tana fadar sun ce za su kashe su idan ba a kawo kudi ba. Appa ya bukaci ta ba sake ba su wayar, ta mika musu suna karba Appa yace yana neman ragi sai suka jaddada masa babu abun da za su rage masa kuma idan be biya kudin da wuri ba za su kashe su. Kamin Appa ya sake cewa wani abu suka kashe wayar a take ya sake sanar da yan sanda. Bayan ya sauke wayar Hajiya Kaltume ta share hawaye ta ce.

 Alhaji ka ba su kudin nan dan Allah su sako yaran nan kar su kashe su, kana jin sun ce za su kashe su fa, mutanen nan ba su da imani ko kadan ni na san yadda suke yi ma mutane

 Dole ai za mu nemi sassauci ai, miliyan dari biyu wasa ne?

 Amman ai kana da su, ba su fi karfinka ba, dan Allah ka ba su kudin nan, idan ma sun maka yawa, ni zan hada da dan abun da yake hannuna ita ma Iyami a fada mata ta bada abun da take da shi a hada a karbo yaran nan

 Aa babu kudin da zan karba, kuma idan za a fadawa Iyami sun kira ba sai kun ce mata yace zai kashe su ba

Hajiya Kaltume ta sake fashewa da kuka.

 Alhaji kenan kana jin matar nan kamar ranka, waya ke ta tashin hankalinta a yanzu? Ni ta yara nake ba nata ba

Appa ya mike tsaye ya fice daga falon. Hajiya Kaltume ta dauki wayarta ta fadawa Hajiya Fatee abun da ya faru tana kuka kamar ba ita ba, Hajiya Fatee sai hakuri take bata, sai da suka gama wayar sannan ta fito bangaren Appa ta dawo nata bangaren ta fadawa yaransa abun da ya faru, haka suka yi ta juya maganar suna kuka, daga karshe ta umarci Yasir ya je ya fadawa Iyami halin da ake ciki.

 Kar naje kuma Appa ya zo yana fada

 Amman ai tana da hakkin sani, tun da danta aka sace, shi kansa be hana a fada mata ba, yace dai kar a fada mata sunce za su kashe su, fada mata mana ta hado dan abin da take da shi ni na hada a karbo yaran nan

 Amman kudin nan be fi karfin Appa ba, kamin ku yi wannan yunkuri da dai kun ba shi lokaci ku ga abun da zai yi

 Ni zan iya jira ba, na san yadda mutanen nan suke ba zan so ko kwana daya Ruma ta kara hannunsu ba, idan ita ba zata yi ba ni zan bada nawa a sako min yata

Yasir ya girgiza kai.

 Gaskiya ni ba zan iya zuwa ma Amma da wannan labarin ba

 Ina fa zaka iya, da dai ni ce da gudu zaka zo ka fada min ai

Ta fashe da sabon kuka, Yasir ya tashi ua fice daga dakin. Yana fita Hajiya Kaltume ta kalli Maama ta ce.

 Maama shirya direba ya kaiki tafi ki fadawa Iyami yadda suka fada

 Sai kin masa magana Hajiya kin san tun da abun nan ya faru Appa ya saka dokokin fita masu tsauri

 Zan masa

Hajiya Kaltume da kanta ta fita ta yi ma masu gadin magana da kuma direban. Burinta dai a fadawa Iyami abun da mutane

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login