Showing 135001 words to 138000 words out of 279257 words

Chapter 46 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34656

juya motar sannan Hurriya ta shiga suka kama hanya. At first Hurriya ta saka ido ne kawai tana sauraren inda Khairy zata kaita duk wani labari da take bata, bata yarda ya dauke mata hankali ba har suka isa gidan dake cike da yan mata suna ganin Khairy suka hau ihu ana rumgume juna irin an dade ba a hadu ba din nan, babu bata lokaci Khairy ta gabatar musu da Hurriya a matsayin kanwarta, Hurriya ta gaishe su sannan ta zauna. Aka kawo abubuwan tabawa ana ci ana hira, ita dai bata yarda ta ci komai ba domin zuciyarta bata natsu da gidan ba, kamar yadda bata gama yarda Khairy ba da sheri take bibiyarta. Tun suna abu tana binsu da kallo har ta kai ta kan yi dariya ko murmushi idan suka fadi wani abun ko suka yi wani abun, daya daga cikin kawayen Khairy ne ta dauko chewing gum ta mikawa kowa ciko har da Hurriya kowa ya karba ya ci, har dayar tana fadar a karo mata daya ba zai isheta ba.

 Zo ki karba idan kina da karfi, daman ke komai aka baki sai kin raina

 Ni zaki cewa haka kam bala'i

Suka fara kokawa da juna, Hurriya dai ta yi murmushi sauran kuma suna ta dariya, tana ta kallonsu gwanin burgewa rayuwarsu da alama babu mai wata damuwa a cikinsu sai nishadi suke ba kamar ita ba, tana tunani tana binsu da kallom sai hamma take har bacin ya fara fisgarta tun tana iya daga ido ta kallesu tana jin hayaniyarsu can cikin kamta har bachi ya sace ta gaba daya ta manta da wace duniyar take ma. Bachin da bata farka ba sai La'arsar shi ma kuma Khairy ce ta tashe ta saboda hadarin da ake da iska ruwan zai iya dadewa gashi basa gida.

 Kina ta bachi tashi mu tafi gida an fara ruwa

Ta mitsintsika idonta kamin ta cire gilashin ta murza idon ta maida.

 Karfe nawa?

Khairy ta duba agogo hannunta, Hurriya ma ta duba nata sai suka furta a tare.

 4:30pm

Hurriya ta yunkura da karfi zata tashi sai ta ji jikinta da dan nauyi saboda ta dade kwance gashin kanta ma duk ya sha birjice saboda ta sha murja akan gadon saboda nauyin bachin da ta yi, har zuwa yanzu kuma be gama sakinta ba. Khairy ta mike tsaye tana laka jakarta

 Ya aka yi? Ko zaki ci abinci?

Hurriya dake mika yana jin kamar ta kara yin bachi ta ce.

 Jikina yayi tsami

 Taimaka mata ta tashi mana wanda ya dade kwance ai dole zai ji dabam

Wata kawar Khairy dake daga zaune kan sofa tana kallon Hurriya da Khairy dake gurin bed ta fada. Khairy ta rika Hurriya ta mike tsaye.

 Baki tashe ni na yi sallah ba

Ta fada har lokacin tana hamma.

 Bachi naki ne ya ga yayi nauyi shiyasa hala baki yi bachi jiya ba?

 Na yi

Ta fara takawa tana jin jikinta kamar ba nata saboda nauyin da yayi mata na bachin da ta sha.

 Kowa fa ya wuce mu kadai muka rage, ita wannan yar iskar gidansu ne bata da matsala

Budurwa da Khairy ta fadawa haka ta mike tsaye tana dariya.

 Dan Allah yaushe zaku dawo?

 Wa zai dawo nan yanzu kam ai sai dai a hadu a gidansu wata kuma, Hurriya cira kafa kar ruwan yayi karfi sosai da alama fa zai kai magariba ana yi

 Eh gaskiya, tun dazun fa hadarin nan yake na dauka ma ma da rana za ayi ruwan

 Eh Wallahi

Kawar ta rakosu har Balcony, Khairy ta juya ta kalleta.

 Toh mu kam idan Momy ta zo ki ce muna gaisheta

 Zata ji, Allah ya kiyaye sai mun yi waya

Ta koma ciki su kuma suka nufi motarsu, Khairy na hadawa da gudu dan kar ruwan ya jikata Hurriya kam ta tsaya tana tafiyarta a hankali, wata zuciyar na raya abun da be zo mata a rai ba sai yanzu, why take ta jin bachi bayan kuma ita ta san jiya ta yi bachi ko da ma ace bata yi ba chi ba ai be kamata ta rika irin wannan mashalon da nauyin bachin just because of bata ta yi bachi ba na rana daya, balle ma ta yi. Kamin ta shiga motar ta raya ma zuciyarta cewar ba zata sake yarda ta sake raka Khairy wani gurin ba, domin idan wani abun be faru a yau ba, zai iya faruwa wata rana, kuma ta fi kyautata zaton wata kila kwaya ta saka mata ta yi bachi, waya sani ma ko so take ta koya mata shan wani abu, daman ana kishen kishen tana sha kuma ta lura da hakan domin ta ga tarin mutanen da ta tara a birthday ta babu na kwarai, gashi kuma Adam din da ya nuna yana sonta shi ma yana shan shisha.

A ranta take ta sake sake bayan ta daukarwa kanta alkawarin ba zata sake rakata ko'ina ba ko da kuwa ta yi mata magijiya haka kuma ba zata sake cin wani abu da zata janyota ta ci su ci ba, ko da kuwa yunwa zata kasheta, domin mutum ba zai ?i ka da da maraice da dare ya ce yana kaunarka ba, idan bata da masu mata fada su nuna mata mata daidai da kuskure, ya takama ta fadawa kanta.

 Kina bachi wata kawarmu ta zo na so kin ganta

Khairy na tuki tana bata labarin abubuwan ?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 da suka faru kuma tana tambayarta wai bata ji lokacin da aka yi kaza da kaza ba.

 Ban ji ba, na yi bachi ne sosai

 Ai na ga alama kam, shiyasa na ce ki koma ki kwanta baki yarda ba, Allah yasa jibi idan zamu fita kar ki yi irin haka, dan Allah ki rika yin bachin dare Hurriya ki daina sakawa kanki damuwa ta hana ki bachi, na san ba zai wuce tunanin Amma ba ko Appa, Amma zata samu sauki da yardar Allah

 Amin

Hurriya ta amsa a takaice, hakan ya saka Khairy ta kalleta jin ta katse mata magana ba tare da ta kare ba, kuma ta amsa da Amin. Sai kuma ta dauke kai ta cigana ta tukin ba, bata sake cewa wani abu ba har suka isa gida by that time ruwan yayi karfi sosai. A gaban gate din Momy Khairy ta faka Hurriya ta bude ta fita ta rufe mata motar sannan ta yi baya kadan ta nufo gate dinsu. Da tafiyar da ta fi kama da kasaita ko kuma ace tausayin kasa Hurriya ta rika takawa ruwan saman dake sauka da karfi suka ce me suke jira da ita ba su jikata ba. Tun da ta hango mota fake a harabar dake kusa kusa da Entrance din Momy ta san suna bako ko bakuwa a gidan domin ba motar da ta sani ba ce. Tana isa daf da motar aka bude farar motar mai farin gilashi Captain ya fito rike da System dake cikin jakarta da wasu takardu, da kuma wata yar jakar karama a hannunsa, shi kan da gudu ya rufe motar ya haye Entrance din. Gudun kar ta isa gurin Momy ko Namra su zo bude masa kofa su disgata gabanshi ya saka ta sauya hanya ta nufi hanyar da zata kai ta bayan dakunan bangaren na Momy. Sai da ta kusa shigewa sannan Captain ya juya ya bita da kallo yana kai hannunsa yayi knocking din kofar falon, ya hada da taba bell. Mai aikin Momy ce ta bude kofar tana zaton ma ko Hurriya ce ta dawo domin sun san bata gidan.

 Sannu da zuwa Yallabai

Ya amsa mata da kai.

 Momy fa?

Ya tambaya yana cire talkaminsa

 Sun fita da yamman nan ita da Namra

 Okay

Ta mika hannu zata karbi kayan da suke hannunsa sai ya hanata.

 No bari na shiga dasu ciki

Ya karasa shiga cikin falon sannan ya nufi stairs, dakin Miwan ya bude ya shiga, yadda dakin yake a gyare yana kamshi sa ka rantse da Allah ana zama a ciki ne ko'ina clean an gyara komai tsaba. Saman gado ya fara zuba kayan da ya shigo da su, sannan ta shiga bandaki ya kama ruwa ya fito ta nufi kusa da windows yana cire safarsa, sai da ya jefa safar a cikin kwandon dake gurin sannan daga curtains din Windows yana kallon yadda ruwa ke sauka a itacen gidan, ba ruwan ko itacen yake son gani ba dan haka yayi kasa da idonsa zuwa inda zuciyarsa take muradin gani.
Hurriya ce kwance daidai tsakiyar filin, ta ware hannayenta fuskarta da cikinta suna fuskantar sama ruwan yana sauka a kanta, be san dalilinta na yin haka ba amman sai iya fadar akwai natsuwa da nishadi a cikin wasa da ruwan sama a lokacin da suke yara, kamin girma yayi talking over. Tana ganin anyi walkiya ta tashi zaune da sauri ta rufe kunnenta, tsawa na biyo baya jikinta ya fara rawa sai ta tashi gaba da sauri ta koma gefe ta tsaya. Sai da aka gama ta sake dawowa cikin ruwa tana ganin wata walkiya ta sake komawa da gudu kamar wata yar yarinya, da ta ji ba ayi tsawa ba ta sake shiga cikin ruwa, this time around jumping take tana ajijiya cikin ruwa. Murmushi ya samu kansa da yi, he miss alot daga kurciyarsa zuwa yau, and wanka a ruwan sama are one of his childhood memories.

Fararen curtains din ya saki ya saka hannunsa aljihu ya pistol ya bude jakar dake ka yi gado ya sakata a ciki, sannan ya dauki jakar System din da takardun ya saka talkamin Musib da suke dakin ya nufi kofar fita ya bude ya fito yaja kofar a hankali. One after the other ya rika bin dakunan da suke gefen dakin da Namra take yana budewa har ya ci karo da wanda yake kyautata zaton an Hurriya ne, tsaye yayi yana kallon dakin kamar mai nadar bayanai sannan ya ja kofar ya rufe ba tare da bari ta yi kara ba. Downstairs ya sauko ya zauna a sofa ya ja wani karamin tebur gabansa ya bude system dinsa ya aje a kai, takardunsa da wayarsa kuma ya da wallet dinsa da pistol ya dora sama gefen kujerar da yake zaune.

 Ranka ya dade kana bukatar wani abu?

Inna Shatu ta tambaya tana mikewa tsaye.

 Aa na gode

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

 Toh

Ta nufi kitchen domin ba zata iya fita cikin ruwa ba balle ta tafi gurin da suke zama, kuma ta san Momy tana hana su zama a falonta idan tana ciki ko bakinta suna nan. System din ya bude ya fara tabawa, yana tsaka da typing kofar falon da yi kara alamar da mutum a waje. Inna Shatu ta fito daga kitchen da saurin da nufin zata tafi ta bude.

 Lemme Handel it bari na bude

 Tou

Ta juya ta koma. Dauke hannunsa yayi daga typing din ya mike tsaye ya nufi kofar ya bude. He thought Hurriya zai gani domin ita ya san da shigowarta gidan, sai kuma yayi arba da Momy da Namra rike da umbrella suna mamakin ganinsa.

 Captain kai ne kuma?

 Eh na zo baku nan ai

Ya matsa jikin kofar suka shigo.

 Ka dade a nan?

 Aa ban jima ba, Momy sannu da zuwa

 Yauwa, ya aikin?

 Alhamdulillah shi na zo na yi a nan ai

 Captain sannu

 Sannu Namra

 Bari naje na canja

 Okay

Ya amsa mata ta siga biyu amfani da kai, da kuma furtawa. Momy ma ta bi bayanta tana fadin.

 Ai da na san zaka zo ba zan fita ba ma, gashi nan ruwa duk ya jika mu

 Be kamata ai ka ki fita saboda ni ba

 Babu wani abun da ya fi uwa ta saka danta a gaban ta yi ta kallo, da ka san irin dadin da nake ji idan ka zo gidan nan wata kila da kullum sai ka zo

Murmushi kawai yayi ya bi su da kallo har suka haye stairs din. A madadin ya rufe kofar falon ya samu kansa ta takawa ya fita tare da janyo kofar ya rufe daga waje, balcony ya tsaya yana kallon yadda ni'imar Allah ke sauka ko'ina a gidan tana jika gidan. Dan matsawa yayi kadan yana takawa a hankali har ya isa gurin da ruwan yake zuba ya tara jikinsa ya saka hannunsa aljihu ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali, sanyin ruwan saman dake sauka a kansa suna ratsa zuciyarsa da ilahirin jikinsa, da abun ya masa dadi sai ya daga kansa sama daga tsayen da yake ruwan na sauka a fuskarsa and the thing is so funny kana jin ruwa na sauka a fuskarka kamar an watsa maka wani abu. Haka ya jike kansa shakaf da ruwan saman hannayensa biyu duka cikin zube cikin aljihu daga ipod din dake kunnesa da wristwatch da wallet dinsa babu abun da be jike ba, shi ma ba wai ya shirya hakan ba ne, zuciyarsa ce ta ingiza shi har ya samun kansa da bukatar aikata abun da ya ga wata ta yi. Is he a teenager like her ya tambayi kansa kamin ya juyo ya kalli Namra dake masa magana...




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 26
 Ruwa duk ya jika ka fa

Ya kalli jikinsa ya daga fadunsa.

 Na tuna baya ne

Ya fita daga cikin ruwan ya karaso bakin kofar ruwan na siyaya a jikinsa. T-shirt din dake jikinsa na bayyana yadda Allah ya zuba hallita a jikinsa saboda jikewar da rigar ta yi da ruwan sama.

 Rayuwar baya kuma Captain? Ko dai akwai abun da yake damunka? Baka saba irin haka? Zuwa ka yi aiki a gidan nan, ga kuma tsaya a ruwan sama kamar wani karamin yaro kalli fa har wristwatch dinka ya jike

Ya kalli agogon.

 Kudi ne nan ba zallar agogo ba, ruwa baya masa illa, lemme go and change set the table please ban ci abincin rana ba

Yana fadar hakan ya nufo gurin da take tsaye sai ta masa ta ba shi hanya tana binsa da kallo gabanta na bugawa da mugun karfi, har sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ta samu sa'ida. Hakika Jameel ya kai namiji ya cika ta ko'ina irin cikar da ake so a jikin kowane jarumin namiji, Allah ya hada masa abubuwa da yawa ya bashi kyauta ba tare da ya roka ba. Da kallo ta bishi har ya haye sama sannan ta dauke idonta ta nufi dinning domin duba abun da babu. Abu na farko da ya fara yi bayan shiga dakin shi ne canja tufafinsa ya saka wadanda ke karamar jakarsa. Ya saka kai wadanda ya cire a toilet sannan ya bude kofar na saka kafarsa waje Hurriya ta juyo da sauri tare da ihu domin bata san da mutum a dakin na Miwan ba, ya janyo kofar a hankali ya rufe yana kallonta ko'ina na jikinta siyayarda ruwa yake.

 Aljani kika gani?

Ta girgiza kai.

 Karki sake min ihu

Ta daga mishi kai tana kallonsa ido kamar za su fado.

 Daina kallona

Ta yi saurin sauke idonta kasa, ta juya ta bude kofar dakinta da sauri ta shige ciki ta rufe. Murmushinsa mai tsada yayi sannan ya taka ya fara sauka stairs din da sassarfa.

 Tafiya zan dafa maka, saboda na san baka cin tuwo, ni san na manta ma tuwo aka yi yau Wallahi

Namra ta fada tun kamin ya karaso dinning din. And she's right baya son tuwo baya cin tuwo ko da yunwa zata kashe shi ba ya iya cin tuwo. Ya dafa kujerar yana kallonta

 Ina yarinyar nan kanwarki?

Ta dan motsa ido gafe da gafe.

 Hurriya?

 Yea kira ta ta girka min

 I can cook for you

 You don't have to stress yourself Pretty, kira ta girka

The way he said kar ta yi stressed kanta ya saka ta ji she's special kuma hakan ya nuna har a gurinsa tana da muhimmanci.

 Okay

Ta amsa da murmushi sannan ta nufi hanyar stairs, shi kuma ya nufi gurin da ya zauna dazun ya zauna. Ya cigaba da aikin da yake, Namra bata dauki lokaci ba ta sauko.

 Sallah take amman na fada mata zata sauko idam ta gama

Ya amsa mata da kai hankalinsa da natsuwarsa gaba daya yana gurin aikin da yake a yanzu. Momy ce ta sauko tana sanye da bakar abaya tana murmushi.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login