Showing 150001 words to 153000 words out of 279257 words

Chapter 51 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34683

maybe ta jefa wayar wani gurin ne

Cire wayar ta yi a kunneta ta mikawa Namra.

 Karbi Captain yana son magana dake

Namra ta mika hannu ta kara ta kara wayar a kunnenta.

 Hello

 Ina wayarki

Ta juya ta kalli stairs.

 Tana daki

 Me ye amfanin waya idan ba zaki yi yawo da ita ba?

 Sorry

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kokarin sauke fushinsa yake yana kass da numfashinta ya daidaita bugun zuciyarsa.

 Ki shirya yanzu ki tafi Mall ki samo min wasu abubuwan i will send you the list

 Okay

Ta cire wayar a kunnenta tana murmushi, ta mikawa Momy.

 Wato idan kana son ka ga tashin hankali a duniyar nan ka batawa Captain rai, wai ya kira ni be samu ba, kuma fa ba zai wuce one missing call ba, shi da baya jera mutum kira ma, amman a wayar nan ina jin yadda yake ta huci

 Wani lokacin kuma fa, idan namiji yana son mace, idan ta bata masa rai ya fi fusata fiye da kowa, ya kamata ki fara sabawa ai, iyayensa ma hakuri suke da shi ta wani bangaren ina ganin kamar har da laifinsu fa, saboda tun yana karami sun nuna masa basa son bacin ransa, shiyasa idan ransa ya bace abun yake masa zafi sosai saboda be san bacin rai ba, ko kuma ki ga abun kadan ya taba shi, su kuma hankalinsu duk ya tashi

 Akwai haka amman Momy na fi yarda da abun har da hallita, duba ki ga yadda Hamad ma yake yi a da

 Haka ne kuma, to sai ko hanzarta kar ki kara bata masa ran domin na lura kwana biyu nan hankalinsa yana karkata a kanki

Namra ta yi murmushi ta nufi saying

 Ke dai Momy kina son canja manufar komai

 Saboda ina fatar manufar tawa ta faru ba

Ita ma dai da murmushin kasaita ta yi ta kana ta amsa wata wayar.

 Wa'alaikussalam



*** *** ***

Sanin halin dan'uwanta ya saka bata wani Sata lokaci ba shirya ta dauki jakarta, atm wayarta da kuma key mota ta fice. Lafiyarta da kamar minti ashirin da biyar Captain ya sake kiran Momy.

 Captain ta dauki wayar ya dai kuma ta tafi

Momy ta bashi amsar tambayar da take kyautata zaton zai tambayeta.

 Eh mun yi waya da ita ai, an gama abincin rana

 Ina tunanin an gama kam, ban leka Kitchen din ba, amman na san an isa gamawa zaka zo ne?

 Aa ina da aiki da yawa ba zan iya zuwa ba, amman zan aiko mota yanzu a karba min a zuba a kula a bawa Hurriya zan turo wanda zai dauketa

 Direba zai iya kai maka ai ba dole sai ita ba

 Momy we have trust issues here, shiyasa ba ko'ina muka cin abincin ba, sai inda muka yarda, kin ga wanda zan aiko ma ban yarda da shi ba, amman idan tare da na gida ne i know I'm safe

 Okay ka aiko shi yanzu

 Okay Thank you

Momy ta mike tsaye tana kiran masu aikinta dake kitchen, sai da suka shirya komai aka zuba masa a coolers masu kyau ta saka plate da spoon a karamin kwado. Hurriya na zaune dakinta mai aikin Momy ta shiga kiranta.

 Momy tace ki shirya ki fito yanzu nan da mayafinki zata aike ki

Huriyya ta sauko daga kan gadonta ta nufi gurin da dogon hijab dinta yake ta dauka ta saka ta cire flat shoes ta saka ta bi bayan mai aikin da ta dade ta sauka masa. Ko da ta sauka Momy na tsaye dinning sai wani sham kamshi take tana yi ma masu aikinta fada. Hurriya ta tsaya a daga gefe sai da Momy ta gama fadan ta juyo sannan ta yi magana.

 Momy gani, Inna Shatu tace zaki aike ni

 Ga abinci nan da zaki kaiwa Captain, ki jira direbansa ya iso, sauran kuma idan kika tafi ki yi karabanin bata masa rai ki dawo ki ga yadda zan ci ubanki na yi kasa kasa dake a gidan nan

 Shi dai wannan mutum suna jinsa kamar wani sarki

Ta fada a ransa a zahiri kuma sai ta amsa da toh, ta nemi guri ta zauna har sai da direban ya iso, sannan mai aikin ta daukar mata kayan aka saka a motarsa. Mutumen da ya bude mata gidan baya ta shiga Soja ne dake sanye da uniform dinsa Complete, tana zaune cikin motar shiru tana kallon titi har suka isa. Tun a bakin gate din gabanta ya fara faduwa sakamakon arba da ta da fara da soldiers rike da makamansu, tafiya suka yi sosai ciki sannan suka isa wani bangere da aka ware dabam da sauran bangarori, daman gurin part part ne, a gurin da take ma part part ne. Fitowa yayi ya bude mata motar after ya faka, ta sauko kafafuwanta ta fito ta dauki kwandon shi kuma ya rika coolers din ya wuce gaba ta bi bayansa, gabanta sai faduwa yake saboda tsaron dake gurin, kusan wannan shi ne karo na farko da ta taba arba da sojoji da yawa haka. Wani gurin ya zagaya da ita dake bayan wasu manyan gine gine dake gurin suka isa wani part da aka kawata da furannin daga gaba. A nan din ma akwai masu tsaron wasu kuma suna ta aikin da takardu wasu da system. Can ciki aka wuce da ita ya lasa wani gurin kofa ta bude sannan ya matsa baya yayi mata alama da ta shiga.

Captain ne zaune a kujera cikin katon office din yana mikawa wani files din dake hannunsa. Mutumen ya karba ya tsare masa sannan ya juya ya fice, shi ma wanda ya riko mata cooler sai da ya tsare masa sannan ya aje, da zai fita kuma ya sake sare masa, yana fita kofar ta rufe kansa. Hurriya ta dago idonta kadan ta kalleshi sai ta yi sa'a ita yake kallo daga inda yake zaune sanye da uniform dinsa complete abun da bata taba gani ba, ita bata ma taba sanin soja ne ba sai yau. Da sauri ta maida idon har da dan rufesu kwarjininsa na yau ya fi na kullum wata kila saboda yau yana sanye da kakin na soja ne, dake karawa ko wane namiji kawarjini balle shi da Allah ya wadata da six-packs.

 Baki iya sallama ba? Baki iya gaisuwa ba?

 Assalamu Alaikum ina wuni

Ta hade sallamar da gaisuwar a lokaci daya ta fada da sauri, har lokacin tana rike da basket din ne tun da be bukaci ta aje ba. Ya aje pen din hannunsa ya mike tsaye ya zagaya ya fito daga gurin table din ya nufi wasu kujeru da suke can gefe visitors chair ya ware daya ya ja baya.

 Zo nan ki zauna ki ci

Ta fara tafiya tana rike da basket din, ta ci? Ita? Ko kuma dai bata ji daidai ba? Maybe nufin yake ta aje. Dan haka da ta aje basket din ta ta dauko coolers din ta kai gurin ta aje.

 Na kai

Ta fada, ba tare da bari sun hada ido ba. Ya mata banza ya cigaba da aikin da yake. A nan ta soma fahimtar manufar.

 Ni fa na ci abinci

Ta fada kamar a shagwabe.

 Saboda ke na saka a kawo abinci nan, ina nan aikin ya min yawa kowa aiki yake yau, amman my mind was telling me kina can baki ci abinci ba you must eat...!

Ya karasa a tsawace domin tana kokarin bata masa rai ne kawai, matsawa ta yi baya a zarane ta dan saci kallonsa tana bata fuska ita dai ta san yana neman ja mata matsala ne kawai a gurin Momy, kamar zata yi kuka ta ce.

 Na ci abinci fa

Ya tsaya cak daga aikin da yake, ya dubeta. Kamin ya saka hannunsa aljihu ya ciro pistol dinsa ya aje kan table.

 Bana maimaita magana, kina cikin headquarter soliders ne you should be careful...

Yana aje bindigar ya mike tsaye ita kuma ta fadi zaune jikinta na rawa kamar mazari, ta bude cooler ta fara zuba abincin wani na zubewa saboda tsoro. Ficewa yayi daga office din ya barta daga ita sai bindigarsa dake kan teburin aikinsa. Ta daga plate din ta dora a cinyarsa tana ci tana kallon bindigar, daman tana jin ana fadar soja basu da imani yau ta tabbatar. Captain be dawo Office din ba sai da ya dauki lokacin da yake kyautata zaton ta isa cinye abincin. Ta mike tsaye da sauri.

 Na cinye

Ya kalli plate din sannan ya kalleta. Yanayinta so innocent da raunin dake tattare cikin kyawawan idanuwanta, suka saukar masa da tausayinta, fiye da wanda ya ji a lokacin da ya mareta Namra ta fada masa makauniya, fiye da wanda ya ji a lokacin da aka dauke dan'uwanta, fiye da wanda ya ji a lokacin da ya same ta tana cin abinci a kitchen din Momy irin cin yan yunwa tana kuka, fiye da tausayinta da ya ji a lokacin da ya ji maganar Momy da Namra akanta.
Dauke kai yayi ya nufi teburinsa ya bude wani guri daga kasa ya dauko box din gilashin da ya taba bata a lokacin da ya fasa na ta, a yanzu yana son ya bata gilashin ne da ya siya da hard earned money, da hannunsa a England, as an apology na marin da yayi mata a lokacin da yayi zaton tana sane ta bugu kirjinsa.

 Cire gilashin idonki

Cikin wata muryar data fi kama da shagwaba da kuka ta ce

 Idan na cire hudu zan gani, bana gani komai sai da shi

Kansa ya daga sama, yana addu'a a zuciya, na neman Allah ya kara masa hakuri da juriyar iya controlling kansa, domin babu abun da ya tsana a duniyar nan kamar musu. Hannunta ta kai ta cire gilashin ganin kamar zata bata masa rai a rashin aikata hakan, bayan kuma Momy ta gargadeta, a take kuwa ta ganin komai da kyau hudun da take tsoro ya mamaye idonta, da can tana ganin dishe-dishe idan ta cire gilashin sai dai bayan tafiyar da dan'uwanta daya tilo yayi ya barta sai idanuwan suka kara lalacewa saboda kukan da ta sha, da kunnuwanta take auna sautin takunsa har kwakwalwarta ta sanar mata yana tsaye a gabanta. Tsakiyar cikin kwayar idonta yake kallo, ya sani ko da zai saka wuka ya barka cikinta, ko ya dora mata bindigar da take tsoro a kai ko yayi mata dariya ba zata shaidar abun da ta gani ba, domin ita ta rasa wannan ni'imar. Kansa ya sauke kasa ya busar da iska bakinsa a hankali.

 Alhamdulillah

Ya furta da nuryar da shi kadai sai muhallinsa za su ji, domin shi ya samu abun da Hurriya ta rasa, daman kuma hausawa sun ce mutum dan tara ne be cika goma ba, Allah ya mata gomai ya rage da ido, shi ne kadai tawaya a gurinta. Kamar an kunna wuta haka jijiyoyin idanuwanta suka sanar da kwakwalwarta dake raba sako, ta karbi sakon hoton fuskar Captain dake tsaye a gabanta hannayensa kuma suka zagaye tsakanin dama da hagu na kyakkyawar fuskarta. Dauke hannunsa yayi bayan ya saka mata gilashin sannan ya karbi na hannunta a lokacin da hawaye suka sauko a idonta irin saukowar da wanda yayi arba da su a fuskarta zai tausaya mata. Ya nade gilashin ya dora a kan teburinsa ba tare da ya kalli hawayen da suka zubo mata ba.

 Direba yana waje yana jiranki

Daga haka be kara cewa komai ba ya fice daga office din, gafen hijabinta ta saka ta share hawayenta, sannan ta nufi gilashinta ta dauka ta cire wanda ya saka mata ta maida nata sannan ta nufi kofar ta bude. Taku daya biyu kamin ta yi na uku wanda ya kawo ta ya nuna mata hanyar da za su ba, ba wanda suka zo dazun ba. Ba musu ta bi bayansa har suka isa gurin motar ya bude mata ta shiga ta zauna, shi kuma ya shiga mazaunin tuki yayi ma motar key, amman shiru shiru ta ji yaja motar sun kama hanya ba, bata ankaro ba aka bude back seat inda take zaune, Captain ne ya shigo cikin motar ya zauna, tana kallonsa ta yi saurin maida idonta kasa, sai ya kai hannu ya dago fuskarta ya cire gilashin idonta ya saka masa nasan data cire ta aje masa a office, sannan ya bude motar ya fita da nata ya rufe motar.
Damdamdam.. Ya buga bayan motar sai sojan yaja motar suka fara tafiya.


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 29
Sai da suka wuce sannan ya dawo office dinsa, yana shiga ya aje gilashin na Hurriya a saman teburinsa ya zagaya ya zauna ya cigaba da aikin da yake. Few minutes Namra ta kira wayarsa dake gaban teburin sai ya amsa ta bluetooth din dake kunnensa yana duba wasu takardun.

 Ni fa na zagaye garin nan kaf duk inda nake saka ran samu wannan turaren Kapter Bokur Perfume ance min babu shi, wasu sunce sai Abuja da Kaduna ake samunsa ko Kano, wasu ma cewa suke ba su sanshi ba

Ya dago daga aikin da yake yana murmushi ya jingina da kujerar da yake zaune yana lilo, shi kanshi daman ya san ba za a samu turare ba domin abun da babu ne be ya fada mata, shi ya hada sunan turare and ya san babu turaren dake da exiting mai irin sunan.

 Okay, na baki zabi ki zabo min turare mai kamshi

 Aa ka fada dai, kar sai na dauko maka turare ka zo kana min fada ko ka ce mai warin albasa ne, kasan wata rana ba a maka daidai, garin gwaninta sai a bata maka rai

 Ssi ka ce ni nafi kowa muguwar zuciyar? Please select ina jiranki

 Toh

Ta kashe wayar, sai ya juyo kansa a hankali ya kalli gurin da Hurriya ta zauna, rabin abincin da ta zuba a duk a kasa yake garin sauri ta zuba kuma ta ci.

 Mtscheeeeee

Yaja tsaki ya tsani guri da datti ko kadan ne balle kuma na abinci, telephone dinsa yayi using ya kira aka shigo aka gyara gurin aka maida komai gafe daya, bayan kamar awa daya Namra ta kira sai ya fada mata inda zata zo ta same shi, a lokacin da ta iso gurin ita kanta sai ta tsoro ya kama ta even though ta taba zuwa amman yadda aka gyara gurin aka canja komai da tsaurara tsaro ya fi na da, arzikinta daya ya aiko aka shiga da ita har ciki. Tana shigowa Office din ya dauke hannayensa daga aikin da yake yana murmushi.

 Allah yasa kin zabo mai kamshi

 I try my best na ga na samu mai kamshi kuma mai dadi, shiyasa na siyo kala biyar ba daya ba

Ta matso kusa da teburin ta dora bag din da turaren yake ciki ta fara cirowa tana nuna masa. Ba laifi duka suna da dadi kuma duka na maza ne, amman babu kalar nasa a ciki, haka yayi mata godiya ya karba ya aje, a lokacin da take kokarin dauke idonta daga teburin idanuwan nata suka yi arba da gilashin Hurriya dake kan teburin a take ta kai hannu ta dauka tana dubawa.

 Kamar gilashin Hurriya

 Nata ne

Ya amsa mata kai tsaye ba tare da tunanin komai ba.

Ta juya ta karewa ko'ina na office din kallo sai ta dora hasashenta akan abinci ta kawo masa saboda kulolin Momy da ta gani.

 Abinci ta kawo

Ashe kuwa ta yi hasashenta daidaita, sai dai wani abun ne ya tsaya mata a rai da ta kasa hadewa har sai da ta tambaya.

 Me ya kawo gilashinta a nan?

 Sato shi na yi kin san ni barawo ni

Ta dan yi murmushi.

 Ni ban ce ba, na san bata gani sai da gilashin ne shiyasa

 Na bata wani, ki zauna mana

Ta zauna tana jin numashinta kamar zai shake zuciyarta na bugawa da mugun karfi.

 Kuma ta karba?

 Da na yi mata ta karfi ba, kin san kanwar nan taki akwai musu da kafiya, amman kuma tana samun sa'a na duk fushin nan nawa na kanyi kokarin controlling kaina na daga mata kafa saboda kawai lalaurar da take tare da ita

Yana aikin yana amsa nata da babu alamar wasa ko second thought a tare da shi.

 Ka taba bata wani abu kamin yau ta bata karba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login