Showing 87001 words to 90000 words out of 279257 words

Chapter 30 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34624

amfani da shi, me ya faru

 Ba komai kawai ina mamaki ne, wani muka ji ana fadarsa wai Sarauta

 Sunan da suke bearing ne, kuma ba laifi suna da kudi kamar dai mu, yanzu kuka dawo?

 Eh na ji gidan sai kamshi yake an sauke girki

Momy ta yi murmushi ta mike tsaye, ta nufi bathroom Namra kuma ta kwanta a gurin ta dauki wayar Momy tana tabawa.

After fitar Namra Hurriya ta nufi gurin da turaren yake ta kai hannu ta dauka ta bude kamin ta shinshina kamshinsa Khairi ta turo kofar dakin ta shigo a kufule, waya a hannunta ba tare da ta ce komai ba ta mikawa Hurriya wayar. Sai da Hurriya ta fara kallon wayar sannan ta kalleta. Khairi ta daka mata tsawa.

 Ki karba mana

Ta karba da sauri ta kai kunnenta ba tare da sanin waye ba.

 Hurriya i wanted to talk to you so badly duk wani abun da kika ji akaina karya ne, kawai Khairi tana fadar son ranta ne

Hurriya kallon Khairi kawai take wayar a kunnenta ta kasa cewa komai.

 Hello... Are you there

Ta sauke wayar ta mikawa Khairi ba tare da tace komai ba, Khairi ta karbi wayar ta kai kunnenta.

 Bata son magana da kai ya kamata ka gane mana

 Yeah that's because you told I'm a bad person, dazun nan babu kalar maganar da bata fada min ba a gaban mutane kuma duk laifinki ne

 Ta ina abun kuma ya zama laifina Adam? Ni ban fadi wata magana marar kyau akanka ba, idan ma zan bata ka ko na zage ka ai kamar na yi ma kaina ne

Cikin fushi ya tsinke kiran ba tare da ya sake cewa komai ba, ita kuma ta kalli Hurriya daman kowa da wanda ya raina.

 Cikin mutane kika ci masa mutumci? Kuma kika ce masa na ce yana shaye shaye?

 Ni ban ce kin ce ba

 Amman dai kin masa cin mutunci a gaban mutane ko?

Ta yi shiru, a take Khairi ta kai mata duka a baki daman tana da haushinta, tana ganin saboda ita Yayanta yaya mata duka ya ci mutuncinta a gaban friends dinta, yanzu kuma saboda ita Adam ya kira yana fada mata magana son ransa.

 Haba Yaya Khairi

 Au haba ne? Ni banza kika saka aka yi min duka? Munafuka yar kasan wuta, haka kawai kika ja min cin mutunci da duka a gaban jama'a

Ta kai mata duka a fuska, Hurriya ta matsa baya ganin tana son yi mata illa.

 Wallahi tallahi sai na miki fiye da abun da kika min Hurriya, sai na dandana miki bakinciki

Hurriya dai bata ce mata komai ba sai kallonta take, Khairi ta yi kwafa ta juya ta fita daga dakin, sai kuma ta dawo da sauri ta nuna da yatsa.

 Sauran kuma ki fadawa Yaya Adam ya kira na kawo miki waya, ki ga yadda zan taka wuyanki wannan kassan na jikinki duk sai na karya su

Ta yi kwafa a karo na biyu sannan ta fice, Hurriya ta zauna bakin gadonta tana taba bakinta dake mata zugi...

 Allah ya saka min in one way or the other

Ta fada idonta na cika da hawaye, sai da ta gama taba bakin sannan ta tashi ta dauko pen ta dubuta account dinta ta fice daga dakin, kofar dakin Namra ta fara turawa ganin bata ciki ya saka ta aje mata takardar a kan gadonta juyo ta fito. Dakinta ta sake komawa ta dauki littafin da Gwaggo ta bata na addu'o'in ta sauko, Garden ta nufa sai da ta zauna sannan ta bude ta fara karanta addu'o'in yamma.



HAJIYA KALTUME.

A waya ta labartawa Malaminta abun da ya faru, tana hada masa da magiya tare da alkawarin yi masa duk abun da yake so matukar ya taimaka mata Maama ta samu kan mijinta.

 Haba Malam kai da ka ra kwafar min da Alhaji, kuma ga Iyami ma sai labari za ace wannan ya gagareka

 Ba gagarata yayi ba Hajiya, wato yaron nan iyayensa suna tsaye akansa, duk lokacin da zamu yi aiki ba ma samunsa ko da ma ya kama zaki ga abin ya bi ruwa, amman duk da haka zamu kokarta zam sake yi masa aiki mai karfi

 Dan Allah a taimaka Wallahi yanzu ba ni da tashin hankali sai na yarinyar nan, kasan yadda uwa take jin idan ta aurar yarta a gidan tashin hankali, burina ace tana zaune da mijinta lafiya kamar yadda nake da nawa

 Karki damu zamu yi haka, yau da daren nan akwai wuridin da zan yi mata, komai zai wuce

 Toh shikenan zan sako mata na goro yanzu a account in Shaa Allah

 Hajiya kenan toh sai na ga sakonki

Daga haka suka yi sallama, bata aje wayar ba ta kira aminiyarta, sai da ta fara shimfida mata halin da suka sami Maama sannan na Malam ya biyo baya.

 Oh wannan yaro dai ya zama butulu, an yi aure lafiya lafiya ashe mugu ne

 Ai ni da na san haka yake Wallahi ba zan yarda ta aure shi, daman can ni be wani kwanta min ba

 To yaran zamani ne ko kin hana ta ai ba zata hanu ba saboda tana son shi, kuma wani ba za a gane halinsa ba sai an yi auren ba

 Amman dai Malam yace min zai yi aiki yanzu

 Ai haka yafi, ni wasu mamaki suke ba ni fa ki duba ko yarinyar nan Afrah yadda aiki be kamata, da yana kamata da yanzu ta bar gidan nan amman sai kashe kudi nake a banza ko gezau

 Shi ma yace iyayensa suna tsaye a kansa, amman duk da haka na san ba zai gagara ba, karki so ganin yadda Maama ta lalace kamar marar lafiya saboda babu kwanciyar hankali a gidan miji

 Ai kam dole a tashi mata tsaye, ni ma na kiransa domin ina jin alamar motsi a cikina

Hajiya Kaltume ta zare ido kamar kawarta na gabanta

 Motsi kuma?

 Wallahi, na fada masa sai yace na bashi lokaci zai bincika yake ga me kenan a jiya na fara jin abun

 Haba Hajiya Fatee kuma kike magana kamar kina kalau? Ai zama be gan mu ba, kira shi yanzu nan idan ma zuwa ya kamata yayi sai ya zo ayi abun da ya dace, an samu danne abu shekara uku yanzu kuma ace Labari ya canja, ai yanzu ne zamu fi shiga tashin hankali ma fiye da baya

 Ni ma ai hankalin nawa ba a kwance yake ba, ina jiran na ji daga gareshi ne

 Muna aje waya yanzu nan ki kira shi, har sai kin jira ya kira ai mai nema bi yake, kira shi yanzu nan

 Toh Hajiya

Hajiya Fatee ta katse kiran, ta shiga contact dinta ta nemo number sa da ta yi saving da Yaya Malam saboda badda kama. Fuskarta shimfide da damuwa ta kara wayar a kunne, sai dai har kiran ya katse ba daga ba, ta sake kiransa ya sake katsewa ba daga ba sai a na biyar a lokacin da hankalinta yayi kololuwar tashi. Yana daga kiran sai da ta sauke ajiyar zuciya tana jin wata rahma na sauko mata.

 Salamu alaikum Malam ina ta kira baka daga wayata ba lafiya

 Toh Hajiya gani dai Alhamdulillah

Tana kokarin karantar damuwar dake son aika mata ta sautin muryarsa ta ce.

 Ba lafiya ba Malam, me ya faru? Akwai wata matsala ne?

 Babba ba karama ba, shi ya hana ni daukar wayarki, ni kaina ina cikin tashin hankali

Ta mike tsaye sai kuma ta koma ta zauna.

 Malam fada min me ya faru

Malam yayi shiru kamar baya gurin can kuma ya numfasa ya ce.

 Wato Hajiya cikin nan ne ya sake tashi

 Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, garin ya Malam? Ya aka yi haka ta faru

 Ni kaina abun ya ba ni mamaki, shiyasa na ce ki ba ni dama na yi bincike kuma da na yi bincike na gane yadda matsalar take, sai dai maganinta ne da wuya

 Kamar ya Malam na shiga uku

Ta mike tsaye again ta fara safa da marwa tana kuka da babu hawaye mai cike da tashin hankali.

 Ba ki shiga uku ba, indai zaki iya domin wannan mafitar da na samu na sha wahala kam amman kuma karshe ce

 Malam fada min kai tsaye dan Allah ka saka ni cikin rudani

 Wato Aljannun da muka saka suka yi aikin nan, su suka warware shi, kuma suka waiwayo suna bukatar wani abu a gurinki mai girma....

Hajiya Fatee bata san lokacin da gumi ya karyo mata ba, ta ji kamar ta dora hannu akai.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?

5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


5??5??5? ?5?? 1?? 3?


 Fada min Malam na ji idan abun da zan iya ne, kana ta kara jefani cikin tashin hankali

 Wato Hajiya maganar ce da nauyi, sai dai ya zama dole a fada, Hajiya Aljannuna nan suna bukatar kwanciya dake

Hajiya Fatee ta dora hannu saman kai ta matsa baya.

 Ni kuma? Ina Aljanni ina mutum Malam

Yayi dariya dake kara tabbatar da gaskiyar abun da yake fada.

 Hajiya kenan ai suma suna son mata sosai fiye da yadda maza bil'adam suke son mata, shiyasa suke auren matan hausawa

A take hankalin Hajiya Fatee ya kara tashi.

 Malam ni ai ka kara firgita ni, ni ba yarinya ba balle ace sun ga wani abu a jikina ya burgesu

 Ko tsohuwa ce ke babu ruwansu matukar kin yi musu, balle ke Hajiya jikinki ma ba za'ace kin yi shekarunki ba ga ki fara kin san aljannu suna son farar mace, dan haka ki natsu ki yi shawara da zuciyarki, kuma karki kuskura ki fadawa kowa domin suna nan tare da ke kuma sun ce basa son magana, saboda haka ki yi shawara da zuciyarki duk abun da ta yanke miki sai ki yi amfani da shi, amman lallai kin ji abun da suke bukata

 Amman Malam ba za'a iya ba su wani abun ba su hakura?

 Babu wani abu da suke so sai abun da na gabatar miki, wato abun da baki sani ba shi ne, kamin na same ki da maganar nan sai da na yi ta lallaba su amman ina suka ki yarda, dama na san zaki tsorata ai amman ina son ki kwantar da hankalinki ba wai zai zo miki a mutum ba ne, a cikin jikina zai shiga, kuma babu wani abu nawa da zaki ga ya canja, ni zaki gani a zahiri amman a badini ba ni ba ne Aljanine

 Shi ke nan Malam zan yi shawara

Ta sauke wayar cikin tashin hankali, ta rasa ta ina ma zata fara tunani, anya aljannu ke bukatar haka ko kuma Malam? Ta ina aljannu zasu ce sai sun shiga a jikin wani za su kwanta da ita, har ta fara lalaben number Hajiya Kaltume sai kuma ta tuna ya ce mata aljannun sun ce basa son magana.

 Kai.... Kai.... Kai... Wannan bala'i da me yayi kama? Wannan tashin hankali duk na minene? Abun da ban yi kurciya ba zan yi yanzu? Haka ina ji ina gani yara kanana suka keya min rigar mutunci, yanzu kuma ga wata sabuwar matsalar ta fuskanto ni, karshenta kuma idan ban amince ba zai ce cikin nan bayyana zai yi idan kuma haka ta faru ya zan yi da duniya

Ta fashe da kuka sosai ta sauko kasa ta zauna tana kuka har wani gurnanin ke fita.

 Wanna yarinya Afrah kin cuceni ba dan ke ba da ban san kofar gidan ko wane malami ba, da yanzu duk wannan bala'in be same ni, saboda ke dan abun da Alhaji ya bar min duk ya kare, kuma ban samu biyan bukata ba, ko da Matsalar ba taki ce ke kadai ba, tun da zuwan na Kaltume ne, kuma ita ba a mata komai ba, gashi ta samu biyan bukata ni kuma ina cikin bala'i

Kuka take sosai tana kara jin tsanar surukarta a cikin ranta, kuka ta yi sosai har sai da idonta ya kumbura bakinciki ya hade mata, idan cikin bayyana babu wanda zai yarda a daji ta samo shi, domin shekara uku yanzu da faruwar abun, sannan kuma bata san abun da zata fadawa danta da yan'uwanta ba, gashi kuma ba zata iya amincewa da bukatar Aljannu Malam ba, idan ta tuna da fason dake kafarsa ma sai ta ji kamar zata yi amai balle kuma ace ta kwanta gado daya da shi, bakauyen da gora ya gama yi ma fenti a hakora, mutumen da be wuce zama mai gadin gidanta ba. Har aka kira Isha'i kuka take ko da ta hakura idan ta tuna sai ta ji kukan ya dawo mata, ita ba da samun nasara ba ita da kwasar ciki ga kuma bukatar Malam a yanzu, da zuciyarta take shawara ko dai ta kyaleshi ta nemi wani Malamin ne, ta wani bangaren kuma tana ganin kamar kamin ta samu Malamin da zai iya kwantar mata da cikin kamar yadda wannan yayi abu ne mai wahala kuma bata san sherin da zai iya binta da shi ba, ta kuma san cikin ba zai cire a yanzu ba a lokacin da yake wata uku ma aka fada mata akwai matsala a zubarwa bayan kuma ta sha magani be zube ba balle kuma yanzu da ciki ya sha kwanci shekara uku. Carbin dake hannunta kawai take ja ta rasa ma ta ina zata fara, salati zata yi ko tasbihi ko istigifara gaba daya ta rasa abun kamawa sai kuka kawai take tana juya carbin.

 Sallamu Alaikum

Ta yi gaggawar kawar da fuskarta ba tare da ta amsa sallamar ba, sai dai haka be hana danta Fadeel fahimtar kuka take ba, ya fahimci fushi take dashi domin dazun da ya shigo gaisheta da safe bata amsa masa ba.

 Subhanallahi Hajiya Lafiya

Ya fada bayan ya zauna a gefenta yana kallonta damuwar dake tattare da shi ta gagara boyuwa. Kamar mai nema sai kawai ta fashe da kuka, abun yana cinta a rai kuma bata isa ta yi labarin da kowa ba, domin babu wanda ya san komai sai aminiyarta Kaltume, ko da zata fadawa kowa a duniya ba zata yi gangancin fadawa Fadeel ba, tana jin kamar ace abun da zata iya fitarwa ne ta tattauna amman babu hali.

 Allah yasa ba ni ne silar zubar hawayen nan ba Hajiya

Ta kara kawar da kai ta tsakaiga kukan ta share hawayenta, sai dai bata yarda ta kalli gefen da yake ba ma, hakan kuma sai ya kara daga masa hankali.

 Hajiya... Ki yi hakuri dan Allah idan ni na bata miki

 Fadi ba shi da amfani domin na sha fada babu abun da ya canja, amman dai zan baka zabi uku a yanzu, Fadeel ko dai ka saki Afrah, ko ka kara aure, ko kuma na yafeka yafewa ta har abada...!

Be san lokacin da jikinsa ya saki ba yayi nauyi a gurin.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Hajiya ta tabbata dai saboda da ni kike zubar da hawayen nan. Hajiya ina son matata sosai domin ina jindadin zama da ita, amman Wallahi zan iya rabuwa da Afrah matukar hakan ne burinki, kuma zan kara aure idan har hakan zai saka ki farinciki, amman ba zan iya hakura da ke ba, ba zan yarda ki yafe ni ba, ba nida wani abu da ya fi ki muhimmanci a duniyar nan, gaisuwar da na yi miki dazun ma na tafi baki amsa min ba, ban wuni cikin farinciki ba

Ya sauke ajiyar zuciya ya sauke kansa kasa.

 Na ji dadin da kika saukaka min kika ba ni zabi har uku, kuma na zabi na uku zan kara aure kuma na miki alkawari matar da kike so ita zan aura, Allah ya huci zuciyarki

Ya mike tsaye yana fadin.

 Zan tafi Allah ya tashe mu lafiya

Har ya fice bata juya ta kalli inda yake ba, bata jin tana da wata makiyiya a yanzu fiye da Afrah, saboda tana ganin saboda ita danta baya mata biyayya kuma ya canja mata. Ada can baya kamin Fadeel yayi aure shi din Mommy's Boy ne kullum yana gida

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login