Showing 24001 words to 27000 words out of 279257 words

Chapter 9 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34640

kalar laifi Amma ta yi masa da har ya yanke wannan tsatsauran hukunci haka.



*** *** ***

Ruma ta turo kofar dakin ta tsaya daga jikin kofar ta kalli Khairi dake zaune gaban madubi tana shafawa bakinta magani ta ce

 Khairi wai Ina Hajiya tace miki zata tafi?

 Ba ni ta fadawa ba, Maama ta ce gidan Hajiya Fatee zata tafi

 Toh amman har yanzu zata dawo ba? Na kira wayarta be shiga

 Maybe can zata wuni, ai dole dai idan dare yayi kin san zata dawo

 Khairi karfe 6:30pm ake magana fa, kuma ta fita tun safe

 Aa Ruma kin cika matsala, Hajiya ai ba yarinyar ba ce idan lokacin dawowa yayi ai ita zata dawo, kika san abun da ya saka ta dade? Kin san dai Hajiya Fatee aminiyar Hajiyarmu ce, waya san me taje yi a gidan

Khairi ta amsa mata da kamar fada domin ta hana ta shafa maganin da take cikin salama sai damunta take da tambayoyi. Ruma ta tabe baki ta fito taja mata kofar tana sake gwada line Hajiya domin ita idan Hajiya bata a gidan duk jinsa take ya zama dabam wannan ya saka wani lokacin ma har bin Hajiya take idan zata fita, kusan duk kawayen Hajiya sun san yar autar Hajiya Ruma saboda yawan lake mata da take. Har ta isa dakinta gwada line take amman kiran yaki shiga baturiyar sai tabbatar mata take da ba a samun Hajiya.
[10/18, 5:35 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2ܠ? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?


5???5???5???5??? 8??

Suna shigowa cikin gidan Gwaggo Hurriya ta shiga dakin da sauri tana neman Amma. Gwaggo ta yi dariya tana daurawa jikarta dankwali

 Maraba da Hurriya yanzu ake tafe

 Eh Gwaggo ina wuni

 Lafiya kalau ina Hamad?

 Shiga nan shigowa, Gwaggo Ina Amma?

 Tana dayan dakin dake kusa da na su Rukayya

Da sauri Hurriya ta tashi ta fice daga dakin Kakarta zuwa dakin da Amma take, tana shiga dakin ta fada jikin Amma kamar bata san tana dauke da cikin kanensu ba, sai kuka ya biyo baya ta kankame Amma sosai kamar za a kwace nata ita. Cikin karfe hali da dauriya irin na uwar da bata son raunin yayanta ya kamata har ta yi kuka a gabansu ta shafa bayan Hurriya tana dariyar da sautinta yaki fitowa, hakan kuma ba karamin taimakawa idonta yayi ba gurin zubar da ruwan hawayen da a da su kwana a idonta. Kanwarta Rukayya ta bata fuska sosai kamar ta fasa kuka.


 Amma da baki nan gidan babu dadi, kuma Appa ya kwashe kayanki daga gidan

 Na sani, ya aiko min da su nan ai, suna nan a zuba a gareji, wasu an saka a falon waje

Hurriya ta dago tana kuka ta kalli Amma.

 Ba zaki dawo ba kenan? Khairi ta fada min Appa ya rabu dake?

 Na fada miki tun ranar ai, abincina ya kare a gidanku, ina Hamad

Amma na rufe baki Hamad ya karaso gurin kofar sai ya tsaya yana kallonsu kamar wani bako.

 Hamad shigo mana ya ka tsaya a jikin kofa

Rukayya ta fada, sai ya nufo cikin dakin yana jin wani irin tausayin mahaifiyarsa da ya kasa nunawa a fuskarsa, sai dai sanin halinsa da Amma ta yi ya saka ta fahimci akwai damuwa a tare da danta domin fuskarta babu walwala kuma ba hade rai yayi ba alamar fushi, yana a wani yanayi ne da ita kadai take gane damuwarsa.

 Hamad kuna nan kuna ta fadan ko?

 Ba mu yi fada ba, ba mu yi fada ba Amma, amman dai gidan babu dadi...

Dorawa ta yi da labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan ciki har da komawarsu bangaren Momy da suka yi.

 Daman gidan ko da ina ciki ya kuke zaune balle bana nan, sai dai ku yi ta hakuri karku saka komai ranku

 Ni dai na ce Bappanku ya tafi gurinsa yayi magana da shi, yaran nan ya bar su zauna a gidan nan idan ba haka ba, wannan matan uban na su za su iya saka musu guba su mutu ma

Cewar Gwaggo a lokacin da take kokarin shigowa dakin. Sai Amma ta amsa mata tana hawaye.

 Allah ya fi su Gwaggo, na san Allah baya bachi kuma baya son zalinci, zai kare su, amman abu ne mai wahala Alhaji ya yarda yaran nan su zauna a gidan nan

 Amma me yasa Appa ya sake ki?

Hamad ya tambaya kai tsaye yana tsare ta da ido.

 Ban sani ba Hamad, Wallahi ban sani ba, da ace na san laifin da na yi masa wata kila da zan fi jin sanyi fiye da yadda nake ji a yanzu, shi kan shi ya ce ban masa laifin komai ba

 Saboda Hajiya ne? Ko Kuma Momy

Amma ta kama hannunsa ta rike

 Ba saboda kowa ba ne, kar kaje ka yi ta fada da mutane wahala zaka sha a gidan nan, dan Allah ka zauna lafiya da kowa Hamad wannan fushin da saurin kai hannu ka daina, ku kenan Allah ya ba ni sai wannan idan na haifa, ban sani ba ko zan kara wani ko kuma iyaka kenan, dan Allah ku hada kanku ku zauna lafiya, ina gidan nan amman tunanina yana can tare da ku saboda na san yadda kuke yawan samu tsabani da juna, ba ku mai raba ku a yanzu idan kuka yi fada ma dadi za su ji

 Be ci abinci Amma tun da kika bar gidan nan, da safe ma tea kawai ya sha

Amma ta dauke idonta daga barin kallon Hurriya dake fada mata ta kalli Hamad.

 Saboda me? So kake ka jawa kanka wani ciwo kuma?

Kamar an zunguro idonsa haka ya fara hawaye yana kallon mahaifiyarsa, duk yadda ta so ta daure sai ta kasa ita sai da kukan ya ci karfinta balle Hurriya da ke da raunin zuciya. Rukaiyah ta share hawayenta.

 Kai Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, Wallahi idan raba ku aka yi an ci amanarki an ci amanar yaran nan, mu ma kuma anci amanarmu an daga mana hankali

Gwaggo ta girgiza kai cike da tausayawa.

 Toh Allah ya kyauta, arzikinsu ma suna da wayo da ace kanane ai da sai sun fi shan wahala, kuma ubansu yana sonsu za su samu sauki ta wani bangaren

A gidan suka wuni har dare, abincin da Hamad ya kasa ci a gidan Ubansa sai gashi ya ci a gidan kakarsa kasancewar Amma ce ta dafa masa da kanta, kuma ta saka shi gaba ya zauna ta cinye abincin tass ya dora da lemu, tukuna hira ta biyo baya, sai da dare yayi misalin tara da rabi sannan Yasir ya zo daukarsu daman ya fada musu a lokacin da direba zai kawo su cewar shi zai dauko su. Nasiha sosai Amma ta yi musu sannan ta aika Hamad ya shigo da Yasir ya zauna saman kujerar karamin falon suka gaisa.

 Yasir ga kanenka nan, na san kana kokari amman Dan Allah a kara, a rika ja musu kunne idan suka yi ba daidai ba, kuma a rika duba su dan Allah

 Amma dan Allah ki daina wannan maganar, ko minene Allah ya kawar da shi ya kawo maslaha ki dawo gidan kamar yadda aka saba

 Toh Ameen, duk da haka dai a kula da su musamman Hamad

 In Shaa Allah

 Allah ya taimaka ko a kawo maka abinci

 Aa idan na koma gida zan ci, yau Rukayya bata gidan

 Tana ciki karatu take yi kasan idan suka samu littafan nan na hausa basa son tashi, yanzu haka bata ma san ka shigo, bari a kirata ku gaisa

 No kyaleta Amma, a gaisheta dai, bamu mu tafi kar dare ya kara yi

Yana rufe baki wayarsa ta bude nata ta fara kuka, hannu ya saka aljihu ya ciro wayar ya duba ganin mai kira ya saka ya amsa da sauri.

 Hello Appa

 Yasir Hurriya bata dawo ba?

 Gasu na zo dauko su

 Sai yanzu? Kasan bana son ana kaiwa dare a waje ko? Me yasa direba be je dauko su tun wuri ba?

 Affuwan Appa, laifina ne ni nace zan dauko su kuma yanzu haka ina gidan

 To ku dawo yanzu nan, karka sake yaran nan su ce zasu kwana a nan

 In Shaa Allah, yanzu zamu taso

 Sai kun iso.....ka gaishe da Mamansu

Ya fada daga karshe bayan yaja dogon numfashi, da mamaki Yasir ya amsa masa da toh sannan ya sauke wayar.

 Appa ne, ya ce na gaishe ki

Wani irin faduwa gaban Amma yayi, mutumen da ya sake ta ya kwaso kayanta ya yace a kawo mata kuma shi zai ce a gaisheta.

 Ina amsawa

Mikewa yayi tsaye yayi mata sallama Hamad da Hurriya suka bi bayansa, Amma kasa raka su ta yi har suka fice daga gidan. Daga gidan Gwaggo Yasir be tsaya ko'ina ba sai ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?gidansu ya faka a bangaren Hajiya Kaltume, Hamad ya riga fitowa motar sannan Hurriya, Yasir kuma ya tsaya gyara parking din.

 Me yasa baki fadawa Amma na fasa miki gilashi ba?

A jere suke suna tafiya Hamad ya tambayeta domin abun da ya tsaya masa a rai kenan tun a lokacin da ta boyewa Amma cewar sun yi fada.

 Idan ta ji zata ji ba dadi ba, baka ji tana cewa mu zauna lafiya ba? Idan kana yin fada ran Amma zai bace

 Ni dai bana son Hajiya bana son Momy bana son kowa a gidan nan

Yana fada yana wani cin magani kamar wani babban saurayi, Hurriya ta tsaya kallonsa da mamakin furunci, shi kam tuni ya juya ya fasa shiga bangaren Hajiya Kaltume ma ya nufi na su bangaren duk kuwa da ya san Amma bata gidan. Hurriya ta cigaba da tafiya har ta isa bakin kofar falom ta muda kofar ta shiga da sallama farin gilashin dake kara mata kyau yana fuskarta.

 Wa'alaikassalam

Fadeel ya amsa mata yana zaune daga gefen kujera yana gwada kiran Hajiya Fatee.

 Ni yanzu hankalina ya tashi sosai, ace har karfe goma Hajiya bata dawo ba? Ga wayarta baya shiga, daman tun da Ruma ta dawo makaranta take ta damu na da ina Hajiya

Cewar Maama tana gwada kiran Hajiya Kaltume.

 Amman fa ce mana ta yi gurin Hajiya Fatee zata je

Fadeel ya ce

 Bata gidan, domin daga can na fito masu aikin suka ce min tare suka fita da Hajiya, shiyasa na zo nan ko tana nan domin wayarta har yanzu bata shiga

Yasir ne ya shigo falon yana motsa keys din dake hannunsa.

 Hurriya ke da Hamad Appa yace na kira ku, Ina Hajiya?

Ya karashe zancen yana kallon Maama da hankalinta ya tashi sosai kamin ya karasa ya mikawa Fadeel hannu su gaisa.

 Ita muke ta nema?

 Ban gane ita kuke nema ba?

Tambayar Fadeel dake fadar haka yake da mamaki.

 Dazu na shiga na gaishe da Hajiya aka ce sun fita tare da Hajiyarka, yanzu kuma na dawo masu aikin suka ce min bata nan, na gwada kiran wayarta kuma ba a samu shiyasa na zo nan ko zan sameta sai kuma na tarar nan din ma kanenka neman Hajiyarka suke

 Wai tun fitar da ta yi da safe bata dawo ba? I thought ta dawo ba fa, yanzu ma Appa ne ya ce a kirata

Maama da tuni ido ya raina fata ta fara kuka ta ce.

 Wallahi bata dawo ba har yanzu, ni hankalina ya tashi

 Subhanallahi, to ina ta ce zata je?

Maama da Salma suka amsa masa, duk abun da ake Hurriya da ido kawai take binsu, Fadeel kuma yana jefa mata kallo time to time, farar fatarsa sai daukar masa hankali take kasancewarsa baki, ba shi kadai ba har Yasir da duka yan matan Hajiya Kaltume babu fari ko daya, sai wanda ya dara wani baki, domin an yi gadon bakar fata ta uwa ta uba, kamar yadda shi ma yake baki sai dai nasa bakin mai kyau ne irin mai shaike da ya dace da fatarsa ya karawa hancinsa fa fararen hakoransa da idanuwa kyau. Hurriya ta mike tsaye ta nufi kofa domin amsa kiran mahaifinta Fadeel ya bita da ido yana kallonta kasa kasa har ta fice, ba wannan ne karon farko da ya fara ganinta ba, amman a yau ta tafi da shi, domin ta kure iyakar ganinsa ta cika idonsa.



*** *** ***

Wasa-wasa aka nemi Hajiya Kaltume aka rasa babu amo babu labari, duk inda ake saka ran za'a gane an bincika bata nan, haka ma Aminiyarta Hajiya Fatee ita ta bangaren danta Fadeel babu inda be bincika ba amman be same ta ba, gashi be san direban da ya daukesu ba balle ya neme su, wayoyinsu kuma idan an kira ba mai shiga, shi kansa Appa sai hankalinsa ya tashi balle kuma yayanta da bachi ma ya gagaresu, Hurriya ma da ba yarta ba sai da nata hankalin ya tashi domin bata son ta ji wani abu marar kyau ya same mutum.

Tun ana maganar kwana daya, biyu har aka yi sati, sai da Hajiya Kaltume da Kawarta Hajiya Fatee suka yi kwana goma cif sannan aka kira wayar Appa ana neman ya fada miliyan dari, domin sun tambayi Hajiya kuma ta fada musu waye mijinta, ta bangaren Hajiya Fatee ma haka suka nema gurin anta. A lokacin Appa ya zo musu da labarin yana mamaki su ma mamakin suka yi, ba su mamakin jin cewar tana hannun kidnappers ba daman sun saka tsammanin haka domin sun bincika ko'ina ba a same ta ba, kuma su kai report gurin police an saka addu'a amman duk shiru, kudin da suka bukata ne abun mamaki.

 Miliyan dari kuma? To a ina suka samu number ka Appa?

Yasir ya tambaya cike da mamaki da kuma tashin hankali a lokaci daya.

 A gurinta suka samu, na yi magana da ita na ji murayarta?

 How taya suka kama su? Wannan abun sai idan da na gida aka hada kai

 Ban sani ba, amman dai mai maganar yace sun kama su a wani kauye dake kusa da gidan zalla nan kwatarkwashi

 Ikon Allah, amman dai tana lafiya ko Appa

Ruma ta tambaya tana kuka.

 Ba mu sani ba dai, ba mu gama magana ba suka yanke wayar kuma na kira bata shiga

 Kamata yayi a sanar da police tun wuri

 Zan kira yanzu na sanar musu

Appa ya juya ya fice, cikin wani karin tashin hankali sa be gama warkewar daga na Amma ba an kara masa wani.



HURRIYA POV.

Hurriya na zaune falon Momy plate din shimkafa a gabanta tana cin abincinta na dare, Namra zaune saman kujera tana duba dogayen rigunan dake zube gefenta kan kujera. Momy ta shigo daga bangaren Appa. Namra ta mike tsaye da sauri tana nuna mata rigar da ta zaba.

 Momy wannan nake so, Hurriya ta dauki bakar

Momy ta tsaya kallonta.

 Idan ta dauka ke zaki biya? Ka ji min wani rainin hankali

 Momy toh ai na ga na shagonki ne

 Idan na shago ne mutuwa na yi balle ki ci gado har ki dauka riga mai tsada ki ce abawa Hurriyya?

Namra ta juya ta kalli Hurriya sannan ta juyo ta kalli Momy tana mana alama da zata iya ji.

 Ta ji mana, tsoronta nake? Ke ce baki san ciwon kanki ba har kika hada kanki da ita, kina kallo a gidan nan duk kudin da mahaifinsu zai bada na siyen abu sai na ciya na siyo muku wanda ya fi na sauran yan'uwa, amman yanzu har kika maganar ki saka riga Hurriya ta saka irinta

Da kamar mamaki Namra ta ce.

 Ubanmu daya da ita fa, kudin da Appa zai bata su zai ba ni duk daya ne

 Eh amman ai ina kara miki? Tufafin da kuke sakawa wake sska su a gidan nan? Karki sake min wani abu makamancin wannan, rai na a bace yake kin kara min wani

 Me ya faru Momy

 Kaltume ce wai kidnappers sun kamata suna neman milyan dari

Momy ta fada tana kiran sunanta domin ita kadaice a gidan bata sakawa Hajiya Kaltume ta ce Hajiya sai dai ta ce Kaltume kawai. Hurriya ta juyo da sauri jin abun da Momy take fada, Namra kuma ta zaro ido.

 Innalillahi daman sai da na fada tana ina yanzu?

 Ke kin yarda? Ai talaka babu abub da ba zai iya ba, wannan Kaltume zata iya kidnapping din kanta da ta karbi wannan kudin gurin Alhaji, balle tana ganin yadda nake tafiyar da kasuwanci ai abun yana tsone mata ido

 Haba Momy taya? Kuma har wannan kwanakin bata fito ba?

 Ke makira ce wannna matar fa, ni na san yadda na zauna da ita, kin ji ta a waya sai kukan munafurci take wai wani idan ta kara sati a gurin mutuwa zata yi, tana cikin bala'i da masifa a Alhaji ya taimaka ya kawo kudin da wuri hmmm

Momy har wani kwaikwayon muryarta take tana nufar hanyar Kitchen Namra ta rufa mata baya dan kara jin labari, ita sam bata yarda an sace Hajiya Kaltume ba ta fi yardar Hajiya Kaltume ce ta sace kanta. Hurriya mamakin ya hana ta cigaba da cin abinci mamakin jin cewar an sace Hajiya Kaltume take, da dayan bangaren kuma tana mamakin yadda Momy take ganin kamar ita da Namra suna da banbanci bayan uba daya ya haife su, tana mamakin yadda Momy take duban Hajiya Kaltume ma dake da tarin rufe asiri a gidan tana ganinta talaka. Da sauri Hurriya ta cire hannunta a abinci ta fice daga falon zuwa bangaren su Khairi.
[10/18, 5:35 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login