Showing 255001 words to 258000 words out of 279257 words

Chapter 86 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34651

yayi ba, suka ji dadi suka daga mazan har matan suka fice suna murna tare da addu'ar alheri ga ma'auratan. Sai da kowa ya fice sannan Captain ya daga mayafin Amaryarsa ya leka fuskarta ya kalli hawayen dake zubo mata.

 Mai tsada... Idan ba ni ba wa za a kawo wa Amarya tana kuka har yanzu?

Ta yi murmushi cikin kukan ta ce.

 Idan ba kai ba, wa zai auri makauniyar amarya?

Sai ya rumgumeta yana dariya.

 Ni ne idonki ai, na huta baki bukatar kallon kowa daman a yanzu

Ta sauke ajiyar zuciyata tana lafewa a jikinsa kamar wata kyanwa. Ya kama hannunta ya rike yana murza yatsun a hankali.

 Na gode Allah da ya nuna min wannan ranar Alhamdulillah, ban yi tsamanin abubuwa za su zo mana haka da wuri ba, ko da yaushe tsarin Allah mai kyau ne

Ita dai bata ce komai ba tana kirjinsa sai shakar dadaddan kamshinsa take. Ya dago ya ssauke lifayar daga kanta zuwa wuyanta ya shafa kanta.

 Maa Shaa Allah, Amarya ta kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, kin ga yadda kika yi kyau yau kuwa?

Ta girgiza kai alamar aa. Sai ya fara fada mata yadda komai yayi kyau a jikinta yana tana hancinta da bakinta har sai da ta yi dariya.

 Taso mu yi alwala

 Na yi a gida

 Shi ne baki fada min ba na yi?

Ya ja lebenta a hankali sannan ya sake ta ta tashi ta cire babbar rigarsa Falo ya fara fita ta rufe musu kofar gidan sannan ya dawo ya shiga bandaki yayi alwala ya fito ya shimfida musu carpet ya daga matarsa yana rike da ita ita ya tsayar sa ita daga baya shi kuma ya matsa gaba kadan ya tsaya kabbatar sallar. Cikin natsuwa suka yi sallah Nafisa yayi musu addu'a ya juyo ya kama goshinsa ya karanta addu'a sannan ya kwanto da ita jikinsa.

 Yan mata na...

Ta yi shiru tana jin wani bakon al'amari da bata saba ji ba, wani yanayi take ji na dabam a tare da ita. Hannunsa ya saka aljihun rigarsa ya ciro dabinon da Daddy ya damka masa ranar da aka daura aurensu ya saka a bakinsa ya tauna dabinon da yawunsa sai da yayi taushi sannan ya saka hannunsa ya ciro ya kai mata saitin bakinta.

 Dabinon daurin aurenmu ne, ranar da Daddy ya ba ni a raina na ce zan aje sai kin tare mu ci a tare

Ta bude bakin da tunin yawunsa da ya tauna dabinon da su suka jika mata lebe, ya saka mata a baki sannan ya lashe hannunsa, ya sake tauna wani har yayi taushi sannan ya dago fuskarta ya hade bakinsu suka ci dabino a tare. Kamin ya cire bakinsa ya kalli fuskarta yatsansa ya saka ya matsa hancinta har sai ta ta fara masa kukan shagwaba.

 Da zafi

 Uhmmm wannan kawai tukuna ma

Ya tsakani idonta yana murmushi, kamin ya tashi ya dauko musu abun tabawa, sai da ya fara ciyar da ita ta koshi sannan ya ci, daga bisani ya kawar da komai ya dauki Amaryarsa cak sai kan gado. Wardrobe ya dauko musu kayan bachi, sai da ya saka nasa sannan ya fara kokarin rabata da lifayar dake jikinta.

 Ke me yake zuciyarki? Hummm me kike tunani?

Ya rada mata a kunnen kamin ya dago ya kalli fuskarta. Sai ta yi shiru domin bata da abun fada, tun da ba wani abu yayi mata ko yace mata ba.

 Kayan bachi zan saka miki

Ta kanne kafada.

 Aa da wannan zan kwanta

 Hey don't try to act smart here

Ta fara rare masa kuka a hankali, sai yayi murmushi yaje kayan bachin ya zauna kusa da ita ya rumgumeta. A dole ya hakura ya kyaleta ta yi bachi da lifayar har safe.



HAJIYA KALTUME POV.

 Kin ba ni kunya Khairy ban yi zaton zaki iya haka a gaban mutane ba, idan ma neman yafiyarta zaki yi ai sai ki yi daga ke sai ita a cikin mutane ba, yanzu ai ta ji dadi ita da Iyami sai su ce gashi nan kina kuka kina neman yafiyarta

 Hajiya wanda aka yada video shi a duniya kamar ni da yana da sauran jin kunya ne? Ni fa yanzu rayuwata ta kare, da ina tunanin auren Fadeel zai rufe abubuwa da yawa akaina kuma ya saka ni jin sanyi amman haka ya gagara, shi ma ya juya min baya

Ruma ta kalli Hajiya cike da damuwa ta ce.

 Hakan da ta yi ba laifi ba ne Hajiya, idan ba irin yau ba yaushe zata roki yafiyarta?

Hajiya Kaltume ta ja tsaki, bakinciki ya zame mata kashi kashi. Khairy ta mike tsaye tana kuka ta haura sama ta shiga dakinta sai ta kife akan gado ta fashe da kuka.

 Ka cutar da ni Adam.. Ka gama da rayuwata ka ruguza shiri ka tarwatsa duniyata wayyo Allah na...

Kuka take sosai tana jin kamar ace adam din yana kusa da ita ta kashe shi ko ta rage zafi, can kuma ta dago ta nufi wayarta ta dauka ta kama number Adam ta aika masa da sako.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
*Shafin nan sadaukarwa ce gareki? UMMU FAISAK my albasa my tomato my pepper, jikar Iya kawar Amo da Hajiya Kaltume. Alherin Allah ya kai miki har a gadon baccinki*


***? ? ***? ? ***

_Wallahi baka taba yin farinciki a rayuwarka ba Adam kamar yadda ni ma ba zan yi ba, ba zaka taba ganin haske ba, sai na bayyanama duniya abun da kake boyewa sai na hana ko wace mace aurenka, baka da zabin rayuwa daga yanzu har zuwa mutuwarka, idan ban auru ba ba zaka auru ba Adam..._

Yana gama karanta sakon ya dan dago ya kalli mutanen dake falon sannan ya maida kansa yayi mata reply.

_Mu zuba zuwa Khairy, ni da za a ga shege, kuma ni sai na auri macen da nake so nake ra'ayi amman ke ba zaki taba auren mijin da kike so ba, saboda kowa ya san me na yi miki kuma idan kika matsa asirin ba nawa kadai zai bayyana ba har da naki domin ke ma yanzu ya shafe ki kin ga sai mu yi jinya tare_

Yana bata amsa ya aje wayar ya cigaba da kallon tv rai a bace, Salim ya taso daga inda yake zaune ya nufo Adam.

 Ara min wayarka zan sauke app wayata ya ki sauke shi

Without second though Adam ya mikawa Salim wayar ya tashi ya hanyar dakinsa. Salim ya zauna a gurin da Adam ya tashi yana.

 Akwai pin a jiki

Adam ya dawo ya cire masa pin sin sannan ya shige dakinsa. Kai tsaye a Salim ya shiga whatsapp dinsa yana duba recent chat ne ga wani abun daga hankali ko bata rai ba, yana kokarin fitowa daga whatsapp din sakon Khairy ya sake shigo ta SMS.

 Mu zuba zuwa ni da kai shege ka fasa Adam

Ya haka ya samu bin sakon ya karanta har wadda ta aiko masa da farko. Salim ya dan dago da mamaki kamin ya sake maida kansa, wannan ne karo na biyu da ya sake ganin wani abu da ya daga masa hankali a wayar Adam. Da kansa ya shiga dakinsa ya mika masa wayarsa sannan ya fito harabar gidan zuciyarsa na zafi. Domin ganin yakw yanzu ya zama loser shi ya fara son Hurriya amman abokinsa yayi masa overtaking duk kuwa da irin yadda aka bata sunan Hurriya,? it pain him yadda abokinsa yayi betrayed dinsa. Number Namra ya kira domin sauke mata haushin dake ransa.

Namra ta share hawayenta sannan ta kalli wayar dake gefenta ta dauka.

 Hello

 Burinku ya cika? Kun nani Hurriya kun bawa wani?

 Wane irin magana ne wannan? Wa yake murna da wannan auren ne? Kai kanka ka san Hurriya bata dace da Captain

 Bata dace da shi ba ta aure shi? Na yi zaton ma kina can gurin raka amarya ai

 Zan aje wayar idan baka da wata magana mai muhimmanci, ina cikin damuwa ba zan yarda ka kara min wata ba

 Baki da matsala daman saboda ba ke kika rasa ba

 Idan har da gaske kake kana kaunarta me ya hana ka fitowa ka aureta kamar yadda Captain yayi?

 Captain ne silar lalata komai, a duk lokacin da na yi masa maganar Hurriya ture min maganar yake, saboda yana min kallon wani dan iska, daga baya na fahimci sonta yake shiyasa kansa yake yi ma campaign

 To kai miyasa baka kirkiri taka Jam'iyar ka yi takara da shi ba? Da ka yi hakan da auren nan yanzu be faru ba

 Ban yi tunanin zai yi jihadin aurenta a haka ba, na dauka zai hakura da ita ni da shi duk mu rasa...kuma na yi tunanin da gaske din ta aikata sai bayan da gaskiya ta bayyana abun ya zo min a wani iri

 Ya fika kaunarta shiyasa ta tari yakin gaba da gaba, gashi kuma daga karshe gaskiya ta bayyana cewar bata aikata ba, ka ga ya ci riba, kark sake kirana Salim

 Ni zaki ce kar na sake kiranki?

 Ubana ne kai? Alakar dake tsakanina da kai saboda Hurriya ne, yanzu kuma ta yi aure dan haka babu sauran wata alaka? tsakaninmu, gaskiya Captain ya fada kana wasa da zuciyar mata shiyasa ko wace macen ka gani sai na nuna kana sonta, da farko ni daga baya kuma ya koma gurin Hurriya, ai kara da ya hana ka aurenta hakan zai koya maka darasi

 Ko kuma ya koya masa darasi ba, idan har aboki zai iya cin amanar abokinsa na kurciya ya karbe masa yarinyar da yake sannan ya datse alakarsu har ya nuna shi da bindiga kuma yayi masa barazanar rasa aikinsa me kike tunani? Dole shi ma hakki zai bibiye shi

Namr taja tsaki ta yanke kiran. Daga ita har Salim Momy Hajiya Kaltume da kuma Khairy kwanan bakinciki suka yi a ranar duk saboda bikin Hurriya.

WASHE GARI...

Misalin karfe goma na safe Hurriya na kwace jikin mijinta yana gyara mata baki bayan sun gama cin abinci da breakfast da aka aiko musu daga Family house din su Captain.

 Tashi mu zagaya na fada miki yadda gidanki da dakinki yake

Ta dan dago kamar bata son motsi, cikin siffar shagwaba da son kuka ta ce.

 Ni dai da ka bar shi, ba amfani tun da ba gani zan yi ba

 Zaki taba ai, kuma idan ya bude zaki gani

 Wannan idon abu ne mai wahala ya bude, Appa ya kashe kudi mai yawa akan ido, kullum kara rufewa yake ba budewa ba, yanzu kuma ya rufe gaba daya

Ya dora gemunsa a saman kanta yana taba fuskarta.

 Zai bude Hurriya zai bude da yardar Allah... Ina ta shirye shirye akwai abun da nake jira ina son nan da dan lokaci zamu tafi Ethiopia akwai wani asibiti ido mai kyau zan saka a dubaki a can zasu Miki aiki kuma ina da yakinin Allah ba zai kunyata mu idonki zai bude

Ta yi shiru tana sauraren yadda yake gangarawa da hannunsa zuwa gurin da bata tsammani.

 Idan kuma idon be budewa gaba daya fa?

 Zai bude, ki daina fadar hakan ki yarda zai bude

Ta zabura ta tashi zaune daidai da sauri ta ture hannunsa. Sai yayi murmushi ya cige baki ya kashe mata ido kamar tana kallonsa.

 Iya daga kafar na yau ne kawai, you better get ready for tonight...

Ya rada mata a kunne sannan ya mikar da ita tsaye tana bata fuska kamar zata yi kuka, gaba daya sai ta ji tausayin kanta ya kamata.

 Kin tuna ranar da kike fada min na yarda dake na ce miki na yarda baki aikata ba, amman ban tabbatar ba, to anjima zan tabbatar

Ji ta yi kamar kasa ta bude ta shige ciki tsabar kunya a yanzu ta fahimci inda zancensa ya dora tun a karon farko da yace mata zai tabbatar. Dariya yayi ya rumgume ta ta baya tana takawa a hankali har suka fita dakin. Kitchen suka fara yana fada mata abubuwan dake ciki wadanda aka siya gurin Khadeeja Candy, sannan suka fito suka shiga dayan dakin nan ma ya fada mata abun da ke ciki idan ya fada mata sai ya kai hannunta ta taba ta ji yadda yake da haka har suka fito harabar gidan nan ma ya rika fada mata yadda tsarinsa yake.

 Amman wata zata zauna da ni ko? Idan ka fita

 Saboda me?

 Zan ji tsoro ni kadai ai, kuma ban zan iya komai ba ai

 Baki bukatar yin komai for now, kuma idan zan fita zan tafi dake gida gurin Ammy ki zauna idan zan dawo sai na dauko ki kamin su bar garin nan

 Wani garin za su koma

 Kaduna? suke zama, ni ma ai da zarar lokacin da aka ba ni a nan ya kare can zan koma a zamu zauna, amman kamin mu zauna can sai mun fara tafiya ayi miki aikin idonki tukuna...

 Da ace idon zai bude, kai nake son na fara gani Captain...

Ya kwantar da kansa a kafadarta.

 Ba zan ce Aa ba, amman maybe zan zama mutum na biyu da zaki fara gani saboda iyaye suna raye

Ta juyo ta saka hannayenta ta lalaba inda saitin fuskarsa yake ta rike fuskar.

 Kana karfafa min guiwa, kai kake fara yarda da ni kamin kowa, na jihadin lokacin da ka yarda ban aikata ba, kuma idan a rufe ido da kunnenka daga jin duk wani abun da za a fada a kaina, har ranar yau ta kasance, duk wata macen mai dacen aure a bayana take a yau...

Ta yi dage ya duka mata da fuskarsa ta sumbanci shi a gurin hancinsa.

 We deserve each other shiyasa Allah ya hada mu a tare kuma ya tare duk wani abu da zai shiga zuciyata ya bata zamanmu har yau ta kasance

Hawaye ya sauko mata.

 Ina kaunarka Yaya

 Yayanki yana gida wannan? mijinki ne, My Baby Pearl...

Ya kwantar da ita a kirjinsa yana shafa bayanta. Cikin gidan suka dawo duk yadda ta so ta ki be barta ba sai da ya taimaka mata ta yi wanka, sannan shi ma yayi suka fito ita da shi suna daure da tawul daya, ita tana ta gabansa shi kuma yayi mata rumfa a baya, har gaban madubin dakin suka tsaya ya cire tawul din sai ta yi saurin juyawa ta rike shi dariya ya sa domin shi ma babu tufafin a jikinsa.

 Idan ba ni ba wa za a kawo w? tsaleliyar budurwa kamar wannan kuma ya kyaleta

Ta saka mishi haka, hakan ya saka shi dauko mata tufafinta ya taimaka ta saka sannan ya shafe mata jikinta da mai kyau ya saka nasa tufafin ya dauki hoda da kansa ya shafa mata ya saka mata man lebe ya saka mata turare sannan wasan ya canja salo. Be kyaleta ba sai da ya ga lokaci na tafiya tukuna ya shiga ya sake tsabtace kansa ya fito ya sumbance ta.

 Zan tafi na gaishe da su Ammy na san yanzu wasu za su fara zuwa ganin amarya kar ayi gulma da ni

 Ni kadai zaka bari?

Ya saka bakinsa cikin nata ya sake sumbanta tukuna ya sake ta.

 Mutane za su shigo yanzu ai

Ya amsa ta sannan ya nufi wayarsa dake kara ya dauka ya duba mai kiran.

 Nafi'u...

Ya furta sannan ya amsa kiran.

 Hello oga barka da safiya ya aikin

 Sorry na kira ban sani ba ko kana cikin wani aiki

 Go ahead

 Hotunan nan ne aka sake yadawa tsakanin jiya da dare zuwa yau, kuma mun bibiye account din sai kuma samu an goge na alhani amman mun samu information din dayan da ya saka hotunan umarni kawai muke jira mu kama shi a Bincike ina ya samu hotunan

 Irin wannan ma baku bukatar umarni na Nafi'u just do it ina yaron yake...

 Kaduna... Ka yi duk yadda za'ayi ku kama shi please kuma ku bincike shi da kyau

 Okay Sir

Ya sauke wayar cike da mamakin mai kokarin hana su jindadin rayuwa a yanzu.

 Me ya faru?

Ta tambaya domin jin yadda yake amsa wayar da kuma yadda yayi shiru bayan amsa wayar ya tabbatar mata da ba kalau. Kallonta yayi sai yayi murmushi ya nufo inda take ya saka zauna.

 Babu komai Babyna wani abun? ne da ya shafi aikina

 Ka tabbata?

 In Shaa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login