Showing 219001 words to 222000 words out of 279257 words

Chapter 74 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34712

dake sabbatu tana wani mashalo kamar mashayiya. Cikin gidan Hajiya Kaltume ta shiga babu ko sallama sai tafiya take a gajiye, daga a tsakar gidan ta fadi zaune tana kallon matansa dake zaune da kayaransa.

 Daga tsohon gidanku muke aka fada Malam ya rasu, dan Allah ku ce mana ba gaskiya ba ne

Karamar ta sauke kai kasa idonta na cika da kwalla, mai karfin halin ce fa amsawa Hajiya Kaltume.

 Malam kam rai yayi halinsa ya riga mu gidan gaskiya, sai dai mu bishi da addu'a, ba Malam kadai ba har da yara biyu

Hajiya Kaltume ta rushe da kuka tana dora hannu akai tana ihu kamar zata tara musu mutane.

 Kashi na ya bushe a yau, ashe shiyasa komai yaki daidai, na zuba kudi ina duban Malam yana nan yana aiki ashe Malam yana barzahu, na kira waya shiru ashe babu Malam

Matan suka taso suka rika Hajiya Kaltume suna kuka domin ta tsikaro musu bakincikin rasa mijinsu da suka yi. Hakuri suka rika bata sannan suka rikata suka zaunar da ita a ciki barandar gidan (Balcony) dayar ta debo mata fridge ta aje mata sannan ta zauna tana bata labarin abun da ya faru tana kuka.

 Kin ga gidan nan be dade da gama shi ba, ya saka komai a ciki tv da fridge irin na yan birni ya saka mana, kayan daki ma masu kyau ya zuba mana, na dubu 70k, duk kauyen nan sai labarin gidan nan yake ashe Allah be kaddara a koma tare da shi ba sai bayan ransa

Hajiya Kaltume ta sharce kwalla ta girgiza kai tana kuka, kai ka ce kukan rashin Malam kawai take da gaske ba kukan neman mafitarta ba.

 Yaushe ya rasu?

 Yau kwana tara, kuma mutuwarsa ta bawa kowa mamaki, shiyasa har wasu suke zargin ko jifansa aka yi, domin Malamai suna haka, idan aka ga ka taso ana yi da kai a gari sai hassada ta shiga ciki

Dayar ta karba mata.

 Ai ba kama ba ce wannan abun jifa ce kawai, domin yana cikin aikinsa karfe daya na dare sai wuta ta fara kamawa a dakin, ihunsa kawai muka ji muka fito aka yi ta dukan kofar ta ki budewa sai da ta cinye shi tass, kuma wutar bata tsaya nan na haka ta bi gidan nan ta cinye komai har da yarana biyu iro da dan inna, zane wannan na daurawa ba mu fita da shi ba, sai da makota suka kawo mana Hijabai, bayan wutar ta cinye komai ta kama ginin gidan ta kone kamar watsa fetur, wannan abun ya bawa kowa mamaki bayan an yi masarar kashe wuta aka bude dakin wuta ta ci Malam abun babu kyau gani, haka ma aka saka shi ba tare da an yi masa wanka ba sallah akwai aka yi masa aka saka shi a rame, saboda jikin ya kone wanka ba zai yi ba

Ta karasa cikin kuka.

 Dole ayi masa jefa mana, a kauye ne wane Malami ne yake irin aikinsa? Babu shi kuma gashi Allah ya amince masa komai girman gona ko gida sai aji Malam be ya siye va dole hankalinsu ya tashi ba, mota ma wannan wanda Malam yake hawa abar kallo ce

Hajiya Kaltume ta Kalli babbar matarsa tace.

 Amman duk wanda ya aikata nasa wannan abun mu ya aikatawa ba Malam ba, mu ya jefa a matsala

 Haka kowa yake fada, ga Malam da mutane manyan mutane kala kala gari gari zuwa ake saboda iya aikinsa, kowa ya zo cewa yake ba mu aka yi ma mutuwa ba su aka yi ma

 Wannan abu be yi dadi ba, Kawata na kiran wayarsa a kashe kullum ina sauraren ko zai kira amman shiru ashe wani labarin ake na dabam

 Malam ai be fita da komai ba, wayarsa ko ganinta ba ayi ba

Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya, idanuwanta suntun suntu tsabar kukan da tasha.

 Kuma be bar muku sakon komai ba?

 Ina zancen barin sako a mutuwar da ba a san da zuwanta ba balle a shirya mata, kuma ko da ya bar wani abu ai wuta ta kone komai ina za a gani ma

 Ba shi nake nufi ba, sako haka ko na kalami cewar an turo masa kudi ko kuma kudin da filin da yake guri kaza ba nasw ba ne? Ko gona?

 Aa babu kayan kowa a hannun Malam, domin idan ya siye gida ko gona ko fili ya kan kiramu ya fada mana cewar gidan da yake guri kaza ko fili ko gona sun zama mallakinsa ya siye, har takardun da ake yi na shaida yana nuna mana, kuma yawanci idan sai siya da aminsa yake zuwa Malam Musa, bayan rasuwarsa kuma Malam Musa ya hannata mana komai na Malam kuma ya bi mutane da dan abun da yake hannun malam na mutane aka biya, babu hakkin kowa a gurin Malam yanzu

 Da dai zan samu ganin Malam Musa na yi magana da shi, saboda akwai mai yawa da na turo masa a account da sunan zai tafi gurin Malaminsa yayi min aiki, kuma kawata ma Hajiya Fatee ta bashi kudi mai yawa ya siya nata gona da fili a kauye, da zan ga Malam Musa sai na tambaye shi ko ya san wani abu a kai

 Gaskiya babu, kuma wani be taba zuwa mana da irin wannan maganar ba sai ke, amman saboda kaucewa zargi, bari a kira Malam Musa sai ku yi magana da shi

Amaryar ce ta aika yaro gurin da ta san aminin mijinta na zama aka kirashi, da ya iso ya shigo cikin gidan suka gaisa da Hajiya Kaltume ta yi masa gaisuwa sannan ta kora da bayani.

 Ni sunana Hajiya Kaltume akwai kawata Hajiya Fatee tana mota yanzu haka, mutuwar ta taba ta sosai ba zata iya takowa nan ba, ni na tura masa kudi kwana goma da suka wuce ko sha daya, ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kudi mai yawa akan cewar zai kawai Malaminsa ayi min aiki domin wannan aikin ya fi karfinsa, yace Malaminsa zai siye rakumi da kayan aiki, shi ne nake tambayar ko ka san wani abu akan haka

Mutumen da ake kira da Malam Musa ya girgiza kai.

 Aa Wallahi be yi wata magana kamanciyar wannan ba, kuma Malam ai Malaminsa ya dade da rasuwa shekara kusan goma sha wani abu yanzu

Hajiya Kaltume ta yi tagume.

 Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un...

Tana jin wani sabon kuka na taso mata.

 Ita kawata dake mota har filaye take bashi kudi ya siya mata da gona ita be yi maganarta ba ko? Ko kuma ya bar wata wasiya? Ko a cikin gidajen da yake siye yace wannan na Hajiya Fatee ne ko na wata

 Aa babu wannan, Malam be taba fada min haka ba, Maimuna a cikinku akwai wanda ta taba jin magana makamanciyar wannan abakin Malam

Uwar gidan ta girgiza kai.

 Aa ai na fada mata ba mu san wani abu da Malam ya siye ya ce na wani ne ba, sai dai idan sheri za'ayi masa anji ya bar dukiya a haka kai da mutanen birni azo ace za a kwace

 Aiko ba zata sabu ba, komai ai sai da hujja ake yinsa, Malam yana kafa shaida idan zai siye abu, har takardu ana yi sai dai wutar da ta kone komai yasa ba a tsira da takardun ba, amman shaidu ai suna nan da ransu, babu wanda ya isa ya zo mana daga wani guri da sunan dan boko ya karbi duniyar Malam, idan ma manufar ku kenan to tun wuri ku tashi ku kama hanyar garinku ko na tara muku mutane yanzu nan

Hajiya Kaltume ta daga kai ta kali mutumen da ya mike tsaye yana nuna mata kofar fita bakinsa da asuwaki hannunsa kuma rike da carbi.

 Indai kai aminin Malam ne tabbas ka san gaskiya sai idan cinye dukiyar zaku yi, zan tafi amman ba zamu kyale wannan maganar ba

Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fice a gidan cikin bacin rai tsabanin shigowar da ta yi da zullumi. A mota ta tararda Hajiya Fatee ta fito da kafafuwanta waje tana zaune daga ciki ta jingina da motar.

 Malam ya mutu, kuma ta tafi da dukiyarmu amman na ke kin yi wauta Hajiya Fatee kuma kin yi sakarci irin haka ake gudu daman, Malam be bar wata wasiya akan kudinki ko gonakin da yake cewa ya siya miki ba, kuma babu wata shaida ke ma kuma baki nemi ya baki shaidar komai ba lokacin da yake raye, yanzu ga irin ta nan nan ke baki ga duniyarki ni kuma ba ni ga aiki ba kudin rakumi....!

 Ni ai idai wannan abun ba zai tashi ba, kudin mai sauki ne indai wannan abin kunyar ba zai bayyanar min ba to zan iya hakura da komai

Direban ya kai dubansa garesu.

 Subhanallahi wai Malamin da kuka zo gurinsa ne ya rasu?

 Ba a sani ba, ina ruwanka? Ka kama bakinka ka yi abun da ya kawo ka, ba gulma da sa'ido ba

 Ah Hajiya daga tambaya Allah ya baku hakuri, ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni

Ya bude da yake jingine ya shiga ya rufe.

 Shiga mota mu tafi Hajiya Kaltume, zancen gida da gona zamu yi tunanin abun da ya kamata mu yi daga baya

Hajiya Kaltume ta juya ta dayan bangaren ta shiga motar, tana kuka.

 Abubuwa duk sun lalace min, idan na taba nan wani gurin ne zai kwance, idan na dawo ta nan wani gurin kuma sai ya balle, ina saka ran za'ayi min aiki na samu sauki wannan rayuwa da nake ciki sai kuma mu zo mu tararda bakin labari wannan abu da me yayi kama... 

 Ke naki ai duk mai sauki ne, ni cw a ruwa tsundun kuma babu tudun dafawa

Haka suka yi ta juya zancen suna bakinciki da kukan da ya mantar da su akwau bandits a hanya, direban yana sauke su a gidan Hajiya Fatee yayi tafiyarsa. A bakin kofar dakin Hajiya Kaltume ta zube zaune ta cire mayafi ta je jaka a gefe tana kuka.





NAMRA POV.

Gaba daya ta jika screen din wayarta da hawayen dake zuba a idonta, hoton Captain take kallona gurin da yake sanye da kayan sojoji yana daga tsaye aka dauke shi hoto. Ta san ta yi rashi na har bada domin abu ne mai wahala a yanzu Captain yace zai dawo ya aureta ko da kuwa ya rabu da Hurriya, ta san ba haramun ba ne amman ai da kunya, ace miji ya saki kanwa ya auri yaya, kuma yadda ta san halin dan'uwanta ba zai aminta ya aikata haka ba.

 Tun farkon zuwanki bangaren nan, ban miki komai ba sai alheri, ke kika saka na canja ashe ma kara da na canja domin kin nuna min cewar ke ba halak ba ce mai tausayi, kin raba ni da Salim na hakura ina murna Allah zai musanya min da an'uwan sai kuma ki zo ki karbe min shi? Baki ji kunya ba? Kin raba yayarki da samari har biyu?

Ta runtse ido tana kuka.

 Ina sonka Captain ina sonka me yasa baka gane ba, duk zuwan da kake gidan nan baka fahimci hakan ba? Ko kuma dai Hurriya ta dauke maka hankali ne saboda ta fi ni kyau? Me ya rude ka ka auri yarinyar da ba ajinka ba, yarinyar da bata dace da kai ba, irin wannan jihadin da ka yi a finafinai nake ganin yana faruwa, ko kuma a wasu kasashen turawa amman ba gidab Malam Bahaushe ba, waya ce maka hakan zai baka kwanciyar hankali? Me yasa zuciyarka bata shawarce karka aikata ba?

A firgice ta bude ido ta kalli wayar da ke ringing, zuciyarta ta shiga shawarar ta daga kiran na Salim ko kuma ta kyale shi. Bata gama yanke hukunci ba ta samu kanta da amasa kiran.

 Hello

 Namra... Ai da kin fada min dan'uwanki Captain zaku bawa auren Hurriya da ban wahalar da kaina ina neman ta so ni ba

Namra ta yi shiru hawaye na sauko mata.

 Na ji an daura aure a yau, ina taya ku murna, amman ki sani amana ba zata bar dan'uwanki ba, ya ci amanata ya aikata abun kunya, ya aure budurwar abokinsa abokin ma na kusa da shi, yanzu na gane dalilin da ya sa baya son ma na yi masa zancen Hurriya ashe kansa yake yi ma campaign, kuma bukata ta biya tun da yayi nasara sai dai ina son ku sani KARMA is real kuma kowa ya aikata mai kyau zai sani

 Salim bana da masaniya akan komai, laifin ba na Captain ba ne na Hurriya ne, daga mahaifiyarsa har mu ba musa san da zancen daura auren a yau ba, sai sanar mana aka yi, wata kila ta yi magana da shi ne ta roki yayi mata haka, amman Captain ba zai yarda a aikata hakan da son ransa ba, waye zai so ya auri Hurriya bayan duk abun da ya faru a yanzu, kuma idonta ya rufe bata ganin komai a yanzu...

 To me yasa ya aureta?

 Shi ne abun da nake kokarin ganewa, ni kaina a rikice nake Salim...

Be sake ce mata komai ba ya katse kiran, sai ya jefar da wayar a kasa ta fada a gadonta tana kuka mai karfi, bata taba jin kaunar Captain ba irin yau bata taba sanin tana sonsa so mai tsanani ba sai yau.




CAPTAIN JAMAL POV.

Babbar rigarsa ya cire ya juyo ya dauki wayarsa ya amsa kiran dake shigowa.

 Ranka ya dade barka da yamma

 Barka dai Allah yasa akwai labari mai dadi

 Akwai ranka ya dade, duk mutanen da ka aiko mana da sakon sunayensu mun kama wasu mun bincike su wasu kuma mun musu barazana a waya sun goge posting din sun bada hakuri, sai dai dukansu sun ga horunan ne a wani gurin ne suka kwafa suka yada abun, su ma kuma duk mun bisu mun saka sun goge kuma sun bada hakuri, mutum daya ne ya ce mana wani ya turo masa hotunan da bayani shi da aka turowa da kuma mu da ya fadawa mun bincika account din sai muka samu an goge account din.

 Na gode sosai already a nan mun riga mun gane wanda ya aikata abun, daman dai bukatar mu a batar da hotunan daga internet, thank you so much, zan tuntube anjima

 Thank You Sir

Ya sauke wayar Adaidaita lokacin da mahaifiyarsa ta biyo bayansa ta daga bangaren Daddy. Kallonta yake yana rike da wayarsa har ta karaso inda yake tsaye tana murmushin takaici.

 Congratulations ka yi aure Jamal, ka auri yarinyar da haukan ka yake nuna maka kana sonta, alhalin kanka ka wulakanta, makiyi zasu mana dariya su maka, ka zama abun kwatance a cikin sa'ainka da friends dinka, saboda ka auri makauniya kuma yarinyar da a yau idan na bude data na zan iya ganin siraicinta, wani ya rigaka taba jikinta, yarinyar da mahaifiyar da kuma kaf danginka ba a maraba sa zuwanta amman a haka farinciki kake kana jindadin ka samu mata, a daura aurenka a cikin gida, daga mahaifinka sai masu aikin gida sai uban yarinya, kai da ya kamata duniya ta san ka yi aure labarin aurenka ya cika kafafen sada zumunta sai gashi ya kare a karamin gida kamar wanda ya aikata sheri

Ya rage tsawonsa ya zauna akan gado.

 Ammy na san baki son yarinyar nan, ba zan iya sakawa ki so ta ba, amman dai ina son ki sani ni dai ina kaunar yarinyar nan irin kaunar da ban taba jin ina yi ma wata mace ba, kuma jifanta da kike da kalamai marasa dadi ni kike gogawa bakinciki domin ita din matata ce a yanzu

Ta kara yin murmushi tana daga gira.

 Haka ne Romeo uban soyayya, matar ka ce tabbas babu wanda ya isa ya goge wannan, ni kuma uwarka ce na fi matarka karfin ikonka a kanka, kuma har abada ba zan taba karbar Hurriya a matsayin suruka ba, ba zan taba sonta ba

Har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleshi ta nuna shi da yatsa.

 Jamal ni na haifeka ka nuna min karfin soyayya, mahaifinka kuma ya nuna min karfin iko, ni kuma a yau zan nuna maka karfin hakki...

Da kakkausar murya ta fada masa haka ta juya ta fice daga dakin. Captain ya soke kai kasa damuwa na baibaiye shi.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo...

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login