Showing 225001 words to 228000 words out of 279257 words

Chapter 76 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34670

Turaki ba

Far'ar dake fuskar Captain sai ta soma disashewa, doman yayi tunanin hakan zai cire wani abu daga tsanar da Ammy take ma Hurriya.

 Tun farko kina kiyayya da ita ne saboda kina taya Momy kishi ne kawai saboda tana yar mijinta kuma Momy bata son Hurriya, Namra ma bata sonta, da kunnena na ji komai Ammy, kiyayyar da kike yi ma Hurriya ba na abun da ya faru ba ne kawai idan saboda shi ne ai kaddara ce da bata wuce kan kowa ba

 Haka ne, shiyasa mahaifinka zai yi mata komai ai, da yar wani mai arzikin ka aura kamar mahaifinka, ai ba zai yarda da wannan ba

 Shi ma ai be riga ya yarda ba, domin ba a taya masa ba kuma babu tabbacin zai amsa ko akasin haka shi ma yana son yarsa...

Ya koma ya kwanta ya rufe idonsa...



*** *** ***

Cike da girmamawa Appa ya amsar wayar sukirinsa ta bangaren biyu, suka gaisa cikin mutunci da far'a Daddy ya tambaye shi rayuwa da kuma kasuwa suka ya amsa masa da hamdallar Allah.

 Daman na kira ne akan maganar Hurriya...

Daddy ya dan yi shiru.

 Akan maganar tarewarta ne?

 Eh to...ba makasudin kenan ba, amman saboda ka fadi hakan bari na ce har da shi da na bar mata su yi wannan aikin ne

Appa yayi murmushi.

 Daman ina da niyar na yi maka magana akan hakan, saboda ina neman Alfarmar ka daga mana kafa har zuwa ta samu lafiya, yanzu haka na fara shirye shiryen abun da ya dace ayi ne akan idonta, abun ba zai yi kyau ba amarya da makanta...

Daddy yayi hanzarin tariyar numfashinsa.

 Ka kawar da wannan maganar, yanzu neman lafiyarta da cinta da shanta a abu ne da ya rataya a wuyan mijinta, kusan shi ne makasudin da ya saka nake son ta tare ai, saboda ya zama tana hannunmu mu zamu yi mata komai, ba lafiyarta kadai ba Alhaji Haruna har wata hidima da zaka yi akan Hurriya tun daga kayan daki har koma mun dauke maka

 Aa aa aa sam ba zan karbi wannan ba, na san kan yi kokari amman wannan bangaren kan a bar min shi, yarinyar tana daya daga cikin yaran da nake alfahari da su, kuma idan ban sakawa Hurriya na yi mata hidima mai kyau ba da me zan saka mata? Ni zan yi ma yata komai idan ka yi min haka ai kamar ka raina nawa arzikin ne ko kuma na ganin zan gaza ni kuwa zan baka mamaki

Daddy ya ce.

 Ba wannan ba ne duka na so na yi hakan ne saboda kyautatawa, amman ba zan hana ka Allah yasa hakan ne mafi alheri

 Ameen na gode sosai Allah ya bar zumunci

 Ameen Ameen. Akwai video da zan aje maka a whatsapp yanzu, video ne da Adam yayi yake ba da hakuri na abun da yayi kuma yake fadar gaskiyar abin da ya faru, wanke Hurriya sosai a video

 Maa Shaa Allahu Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Allah na gode maka Alhamdulillah

Appa yana ta maimaitawa cikin farinciki.

 Sai dai bana son Hurriya ta ji a yanzu, kuma ina rokon Alfarmar ka kai Hurriya a asibiti yanzu ta duba mijinta ba shi da lafiya yana can kwance an saka masa drip

 Subhanallahi, me yake damunsa

 Ba wani serious ciwo ba ne fever ce kawai

 Toh ranka ya dade zan yi hakan, kuma ni ma zan je na duba shi anjima

 Na gode

Daddy ya yanke jiran, Appa kuma ya shiga whatsapp dinsa ya kama number Daddy yana ta jiran sakonsa. Dilll sakon ya fado a wayar video ya fara bude kansa, daga kasan video kuma address din asibitin da Captain yake ne.

Natsuwa sosai Appa yayi yana kallon yadda Adam ya fara bada hakuri da neman yafiyar Hurriya hannunsa da dauri, kana ganinsa ka san baya cikin farinciki kuma ya sha wahala domin jikinsa ya nuna haka, daga bisani ya koro da bayanin yadda abubuwan suka faru. Appa na zaune a office dinsa sai gashi a tsaye yana kallon video cikin firgici da mamaki yana jin duniyar gaba daya kamar mafarki.

 Khairy... Umm Khairi... Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Ya koma ya zauna, yana ta neman daukin Allah ta hanyar ambatonsa kamin ya sake mikewa tsaye ya maida video baya ya kalla, ya sake kalla ya sake kalla.

 La'ilaha Illallahu... 

Ya karasa a zuciyarsa domin bakinsa ya masa nauyi kirjinsa ya kau yaji, kansa yayi nauyi har ya rasa abun da zai fara tunani. Ya aje wayar a tebur ya zauna yayi shiru na wasu mintuna yana kallon wani gurin kamin ya soke kai kasa yana sauke ajiyar zuciyar da ta ki sauka a zuciyarsa. Tunanin yake ta ina ya gaza a matsayinsa na uba, ta ina ya kyautata ta ina ne be kyautata ba? Me ya kawo haka a cikin familynsa ga yaran da suka shi ya haife su? Ya kai hannu ya dauki wayarsa ya shiga contact dinsa ya nemo number da ya kwashe shekaru be ji daga gareta ya kira. Sai da jiran ya yanke ya sake yin wani shi ma ya yanke a uku aka daga.

 Assalamu Alaikum

Appa baya iya amsa sallama a yanzu dan haka be amsa ba, maganar ma kamar wanda aka dannewa numfashi haka yake yinta.

 Zan aiko da mota yanzu, za a dauki Hurriya taje asibiti ta duba mijinta ba shi da lafiya

 Wane irin magana ne wannan? Tun da ace mana an daura auren nan yau kwana biyu mutunen be zo ya ganta ba, fari ne ba ki ne mu ba mu san kamaninsa ba, sai kuma yanzu ka ce zata je ta duba shi?

Ya daga yatsansa yana nunawa kamar ance masa tana gabansa a zaune.

 Dan Allah Iyami karki musa min, karki kara min bakinciki da bacin da nake ciki a yanzu, baki san halin da nake ciki ba matukar ba so kuke na fadi na mutu ku huta... 

Jin wannan kalamin ya saka Amma bata sake cewa komai ba har Appa ya kashe wayar, Direbansa dake gida ya kira ya fada masa yaje ua dauki Hurriya ya kaita asibitin, sannan ya dayan direbansa ya fada masa ya kunna mota za su tafi gida yanzu nan. Yasir ne last mutumen da ya kira ya fada masa ya same shi gida yanzu nan, sannan ya mike tsaye cike da nauyin zuciya irin na uban da yake jin kamar ya gaza ta wani bangaren ya fice daga office din.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
47
Amma ta kalli Gwaggo mamakin bayyane a fuskarta.

 Alhaji ne, wai zai aiko da direba a dauki Hurriya ya kaita asibiti ta duba mijinta

Gwaggo ma mamakin ne fal a ranta.

 Ba shi da lafiya ne?

 Da alama kam, amman Gwaggo ta ya zata tafi duba shi mutunen da be taba zuwa gidan nan ba tun da aka daura musu aure ni ban san shi ba shi ma be san ni ba?

 Ko dai shi ma baya son auren ne? Ko kuma marar lafiya ne aka aura mata?

 Shi nake tunani Gwaggo, kar abun yayi ma Hurriya yawa, na ji mahaifinta ma kamar a cikin damuwa

 Allah dai ya kyauta, wannan abun da daure kai yake

 Kuma kin ga Kaltume da Nafisa ba za su so Hurriya da al??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????heri ba, za su iya zugawa mahaifinta ya aura mata kowa saboda ta sha wahalar rayuwa

 Amman a yanzu ina ganin kamar Alhaji ya fara dawowa hayyacinsa ai, Allah dai kadai ya san me yake nan

Amma ta fada tana aje kofin maganin dake hannunta sannan ta yunkura ta tashi tsaye cikin rashin kuzari irin na wanda be gama warkewa daga ciwo ba ta taka ta fita daga dakinta. Dakin Rukkayya ta nufa domin a can Hurriya take rayuwa a yanzu, lalulen dakin Amma ta fara yayewa sannan ta shiga dakin, Hurriya na jin yanayin tafiyar ta Amma da bata gama kwarewa ba ta tashi zaune idanuwanta cike da duhu tana kallon saitin kofar. Amma ta zauna kusa da ita tana kallonta.

 Hurriya ina son ki ba ni aron hankalinki

Hurriya ta juya ta gefen da take jin muryar Amma ta mika mata dukan natsuwarta.

 Ba dan kina yata ba, hakika ke yarinya ce mai hakuri da sanin ya kamata, kuma kin hadu da kalubalen rayuwa da kananan shekaru daman haka tsarin rayuwa yake, wani da dadi wani babu, eani kuma na sirka masa, dan haka ina son ki kara hakuri akan wanda kike da shi kuma ki karbi kaddara a duk yadda ta zo miki, a matsayi na uwa zan yi ina nawa kokarin na ga baki cutu ba a rayuwar gidan aurenki, sai dai kuma idan na hango wata matsala ko wahala da zaki sha zan tare ko da bani da karfi haka zan ta yaki har Allah ya mu nasara

 Na gode Amma

 Allah ya miki albarka, Hurriya kin san mutumen da mahaifinki ya aura miki? Kin taba ganinsa ko da sau daya?

Ta yi shiru na wasu dakiku kamin ta daga kai.

 Na san shi

 Marar lafiya ne? Ko yana da wata nakasa ko aibu?

 Ba shi da shi ko daya Amma, a lokacin da nake gidan idan Momy ta hanani abinci shi yake kawo min wani abu na ci, ko lokacin da Namra ta shake ni shi ya mareta yana da kirki, amman yana da saurin fushi da zuciya kamar Hamad

Amma ta ji sanyi a ranta jin kadan daga hallaya da siffar mijin da yarta ta aura. Zuciyarta kuma sai ta karkata akan furucin Hurriya cewar Namra ra makureta.

 Me kika yi ma Namra ta makureki?

Hurriya ta bata labarin abun da ya faru, Amma ta girgiaza kai, ta sani daman jininta ba zai sha da dadin a gidan Momy ko Hajiya Kaltume ba. Ajiyar zuciya ta sauke

 Appanki ya kira yanzu, yace direba zai zo ya dauke ki ya kai ki asibiti ki duba mijinki wai ba shi da lafiya, ki shirya Rukkayya zata rakaki

 Toh Amma

Amma ta tashi ta fice daga dakin, Hurriya ta kai hannu tana tana awarwaron da Captain ya saka mata a hannu da sunan wani abokinsa ya bata, tana jin kamar babu dadin jin cewar ba shi da lafiya, ko dai baya son auren ne dole aka masa? Ko kuma wani abu ya faru? Kwantawa ta yi kan tana tunani kala kala a ranta, zuciyarta na raya mata taya mutum kamar Captain zai yarda ya aureta bayan duk abun da ake cewa ta yi? Kuma gashi bata gani a yanzu, wata kila dai dole aka yi masa, amman kuma yadda Momy take jinsa anya zata masa dole? Bayan Namra ta mata gargadi akansa Momy ma ta yi mata. Sai da direban ya shigo sannan Rukayya ta shigo dakin ta saka Hijab dinta ta sakawa Hurriya ta kama hannunta suka fita Amma na Allah ya tsare, Gwaggo kuma na fada mata idan ta shiga ta gaishe da kowa.




CAPTAIN POV.

Idanuwan da ya rufe ne ya sake budewa sakamakon bude kofar dakin da aka yi, Salim ya sake dawowa hannunsa rike da leda ya nufi gurin da aka tana da ya aje ledar sannan ya kalli Captain.

 Sannu Allah ya baka lafiya, ga apple nan na san kana son Apple na siyo a waje ne, anjima zan dawo Allah ya kara afuwa

Sannan ya kalli Ammy dake zaune.

 Ammy zan tafi sai anjima zan dawo Allah ya ba shi lafiya

 Amin Salim an gode

Har ya fice Captain be ce masa komai ba.

 Abun da kake yi wani lokacin baka kyautawa Captain, na san kana da fushi amman danne zuciya ake, ko sai anjima baka cewa yaron nan ba, ba dan kana da aboki kamar Salim ba da yanzu ba ku shirya ba, amman yana mutunkata yana sonka, duk abun da kake masa baya dubawa yana nan tare da kai, duk da yana karkashinka yana baka girma da kulawa na abokantaka ba na aiki ba

Nan ma be ce komai ba, Ammy zata sake wata maganar wayarta ta yi ringing sai ta mike tsaye ta fice daga dakin. Captain ya sauke ajiyar zuciya ya ya dan dago kadan, ya sake bude wayarsa ya kunna video ya sake kallo.

 Ina fatan hakan ya saka ki farinciki Hurriya, and Sister nan da ta aikata miki wannan abun i hope bakincikin da zata shiga zai ninka wanda ta saka ki

Ya fita daga whatsapp din ya shiga contact dinsa ya kira Nafi'u. After sun gaisa ya gabatar masa da bukatarsa.

 Asiri na tuno na abun da ya faru da yarinyar nan so zan turo maka video yanzu ina son ka yadashi iya yadda zaka iya, ya karade ko'ina a kafofin sada zumunta Please

 Za'ayi haka ranka ya dade ka aiko da video

 Okay, ba zan baka komai ba a yanzu dai na ga yanayin aikinka, idan ka cancanci da yawa zan baka

 Zaka gani Sir

Ya sauke wayar ya sake komawa Whatsapp dinsa yayi masa sharing din video. Ya sake kiran wani yayi requesting irin abun da ya bukata a gurin Nafi'u shi ma ya tura masa video sannan ya koma ya kwanta. Bayan kamar minti talatin ya ji an bude kofar dakin sai ya sake bude idonsa Rukkaya ta fara daga kai ta kalli sake kallon kofar dakin domin ta tabbatar nan din ne sannan ta kasara turo kofar dakin tana sallama.

 Sallamu Alaikum

Be amsa mata ba domin be san ta ba, be kuma san manufar shigowarta ba har sai da Hurriya ta bayyana a bayanta.

 Oh My god

Ya tashi zaune da sauri farinciki ya cika fuskarsa, hannu ya saka ya kashe ruwan ya cire a hannunsa? ya rufe gurin da jinin zai iya biyowa sannan ya mike tsaye ya gyara rigarsa kamar ance masa Hurriya tana ganinsa. A tsakiyar dakin Rukkayya ta ja ta tsaya tana kallonsa.

 Direban Appan Hurriya ne ya ce mana nan zamu shigo, dan Allah ko kai ne Jamal?

 Yes... Angon Hurriya

Ya fada yana nufar Hurriyar dake bayanta tana rike da hannun Rukaiyah. Hannunsa ya kai ya kama dantsen hannunta ya rikata yana kokarin fitowa da ita bayan Rukayya.

 Assalamu Alaikum

Hurriya ta fada tana jin tsoron da wani yanayi na dabam, domin wani be taba kaiwa a jikinta haka ba a take jikinta ya fara rawa. Murmushi Captain yayi Rukaiya ma ta yi murmushi tana mamakin a yadda ta samu Captain domin dukansu ba su saka ran namiji ne mai kyau da tsari da cikar kalama ne ba irin Captain.

 Ban san ya kike da Hurriya ba, dan Allah ce ta sake hannunki ko kuma ke ki sake hannunta

Ya bukaci haka ne saboda Hurriya ta ki yarda ta saki hannu Mama Rukaiya.

 Ni kanwar Mahaifiyarta ce

 Oh Ashe mamanmu ce, sorry ban amsa sallamarki ba, a yafe min Momy

Rakayya ta yi murmushi ta saki hannun Hurriya, Captain ya mika hannunsa ya rika hannun da Rukkaya ta saki ya jata har gurin gadonsa ya zaunar da ita. Sannan ya nunawa Rukkayya kujera.

 Bismillah

Ta karasa ta zauna tana masa ya jiki.

 Alhamdulillah, ko da aka daura auren ba ni da lafiya shi ya hana ni fita ko'ina balle na je na gaisa da ku mu san juna

 Idan ka samu lafiya ai sai ka yi Allah ya kara afuwa

 Amin thank you

Ya zauna kusa da Hurriya yana kallonta. Baya bukatar tambaya ya san wannan duk shirin mahaifinsa ne, dan haka ya dauki wayarsa yayi ma mahaifinsa text.

 Thank You, you're the best Dad in the whole world

Ya aje wayar a gefensa ya maida hannunsa a gurin Hurriya dake matsawa a hankali domin tana jinsa daf da ita.

 Ya jikin?

A madadin ya amsa mata sai ya kalli dan space din dake tsakaninsu yayi murmushi, wani kalar nishadi da farinciki ne zuciyarsa na ganin matarsa labarin zuciyaa tambayi fuska in ji hausawa, sai yake jin ya warke daga fever ma. Rukayya ta mike tsaye tana rike da wayarta.

 Bari na jira a waje

 Dama dai kin wuce gida zai fi, domin Hurriya ba yanzu zata koma ba sai dare

 Gwaggo bata ce na barta ba, cewa aka yi mu zo mu dubaka mu koma, direban ma yana waje

 Wacecw Gwaggo?

 Kakar Hurriya mahaifiyata

Captain ya dariya.

 Ashe ma kaka ce, idan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login