Showing 102001 words to 105000 words out of 279257 words

Chapter 35 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34713

baki ji kai tsaye kike fadar haka

Hurriya ta saka dariya sosai, sannan ta matsa kusa da Namra.

 Yaya Namra maganar Allah mutumen be miki ba?

Namra ta yi shiru tana murmushi.

 Yaya, amman ba abun da kike tunani ne ba

 Zai zama abun da nake tunani soon Yaya Namra, daga ganinshi mutumen kirki ne dan Allah idan ya ce yana sonki karki ce aa

Namra ta girgiza kai tana dariya ganin Hurriya ba zata barta da zancen ba, ta dauki filo ta rumgume.

 Kyaji da shi ke dai

Hurriya ta yi murmushi. Haka Hurriya ta saka mata ido har yamma tana lure da yadda ta shirya turaren ma na musamman ta saka ta feshe jikinta ta ko'ina kamshi take. Ana gama Sallah Magariba before Isha'i Namra ta sauko tana sanye da wata Egyptian Abaya ko ina kyalli take gashi ta sha kamshi kamar wata amarya. Kusan wannan ne karon farko da wani ya ziyarci gidansu da sunan ganinta kuma shi ba dan makarantarsu ba kuma ba dan'uwanta ba. Har ta fita sai kuma ta dawo ta shiga dakin Hurriya dake kwance tana karatun Qur'ane.

 Hurriya ta so mu je

Hurriya ta juyo ta kalleta.

 Ya zo

Namra ta daga mata kai tana murmushi fuskarta har annuri take. Hurriya ta aje kur'anen ta dauko ta nufi Hijab dinta ta dauka ta saka.

 Amman Yaya Namra ki fadawa Momy? Kar ta fito nemanki ko nemana ba mu kusa

 Ban fada mata ba, dadina dake akwai zurfin tunani, bari na fada mata sai na sameki kasa

 Okay

Ta juya ta fita daga dakin ta nufi dakin Momy, daga bakin kofar dakin ta tsaya ta fada mata tana da bako a waje zata je su gaisa, a take Momy ta yanke wayar da take fuskarta ta cika da annuri.

 Maa Shaa Allah, haka nake son ji a gaishe shi

Ta yi murmushi ta yi baya ta ja mata kofar, kasa ta sauko ta samu Hurriya tsaye tana jiranta. Hannunta ta kama suka fita tare. Sai da Namra ta yi ta rabon ido kamin ta hango shi tsaye can gurin gate din gidan.

 Laa har can ya faka?

Hurriya ta fada tana ganin kamar ya tsananta ma kansa fakawa a nesa da apartment din Momy. Tun kamin su karaso ya bude motar ya fito, farar shadda ce a jikinsa da hula shi ma sai kamshi yake zubawa irin na manyan samarin nan dake gasar nuna ado a gurin yan matansu. Haka nan Namra ta samu kanta da kunyar kallonsa har suka karasa gurin.

 Salam

 Salam...

Ya amsa musu yana kallon Hurriya da murmushi a fuskarsa.

 finally yau dai an fito min da kanwar nan da ake ta min rowa

Namra da Hurriya suka yi dariya kusan lokaci daya.

 Ba rowarta nake maka ba, kai ne baka bukaci gaisawa da ita ba

 To ai tsoro nake ji, kar ki ce min na karya doka kuma kin san mai nema taka tsantsan yake

 Haka ne

Hurriya ta kalleshi ta ce.

 Barka da dare

 Hey Young Lady

 Lafiya Kalau

 Maa Shaa Allah, yau dai na ce zan zo na dubaki, even though dai aiki yana min yawa amman Yayanki tana min rowarki kullum idan ina cewa ina gaisheki bata ce min kina amsawa sai dai tace min zaki ji kina ji kuwa

Hurriya ta yi dariya tana kallon Namra dake girgiza kai tana murmushi kawai yadda yake da son ban dariya abun yana burgeta.

 Tana fada min, kuma ina amsawa

 Good

Ya fada still yana kallonta. Namra ta kalleshi kadan ta ce

 Ka shigo ciki

 No nan ma ya isa, kawai dai ki kawo min kujera na zauna

Hurriya ta wara hannunta

 Bari naje na dauko...

 No bari na dauko

Kamin Hurriya ta sake cewa komai ta juya ta nufi cikin gidan. Hurriya ta juya zata bi bayanta sai ya kirata.

 Ina zaki je?

 Zan taya ta daukowa ne

 Hmmm baki son yayarki ta wahala kenan, ni kuwa na saba bata wahala kullum saboda sai na ce ina gaisheki

Hurriya ta yi murmushi ta bi bayan Namra, a tare suka dauko kujerun biyu ta nufi bangaren da Motar Momy take suka aje a gurin, yana ganin haka ya san baya bukatar ace masa ya karaso ya zauna, dan haka ya cira kafarsa ya gurin ya zauna a kujerar da Hurriya ya aje. Namra kuma ta zauna a dayar, sannan Hurriya ta koma ciki ta dauko musu ruwa da cups ta aje a gabansu.

 Ke ina taki kujerar?

Hurriya na kallon Namra sai suka yi ma juna murmushi saboda tunawa da ta yi da cewar ta fada cewar zata tsaresu da ido har sai ta gano komai.

 Tana falo tana jirana, a sha ruwa lafiya

Ta bar shi a gurin ta wuce, sai ya bita da ido har sai da ta kauce daga ganinsa sannan ya juya ya kalli Namra.

 Kanwarki nan tana da kirki, kuma tana da kyau ba zan yi karya ba

 Yeah haka ake yawan fada duk ta fimu kyau, kuma maganar gaskiya ta fi mu kirki, Hurriya tana da kirki sosai

 Maa Shaa Allahu haka ake so, ina take karatu?

 Tukuna nan dai bata fara jami'a ba

 Why? Takardunta ba su fito ba ne?

 Sun fito kuma sun yi kyau domin tana da kokari sosai, akwai abun da Appanmu yake jira ne shiyasa be saka ta ba

 Ko aure za'ayi mata?

Ta yi dariya.

 Mu ma da muka gama jami'a muke maganar zuwa NYSC ba a yi mana aure ba balle ita, ita ce karama a gidanmu yanzu

 Oh... Na tambaya da tsoro fa, i thought answer ki would be yes

Ta yi murmushi mai alamar tambaya.

 She's too shy bata son tsayawa ma, tana son saka glasses kuma yana mata kyau

 That's because of her illness bata gani sai da gilashi

 Whoo..what... Wow...

Ya juya ya kalli part din Momy kamar zai ganta tsaye a gurin.

 Wow...

 Wow... 

He said for the third time.

 You make me like her more.. Gaskiya duk wanda ya samu yarinyar nan ya dace, and i think I'm the luckiest guy

Namra ta kalleshi tana murmushi da ya zame mata kamar na dole ne.

 Hmmm

 The true is i like your Sister so much Namra, kuma na zo nan ne saboda na yi magana da ita, amman na ga tana da kunya sosai ko tsoron mutane take ne i don't know

Namra ta sauke idonta kasa zuciyarta ta fara bugawa da mugun karfi, but she managing to wear her light smile on her face. Ya mike tsaye ya nufi gurin motarsa sai ta bishi da kallo har ya isa ya bude ya dauko abun da zai dauko ya kamo hanyar dawowa. Sai da ya kusa isowa sannan ta share hawayenta, not because of tana sonshi but because of disappointed, all her life ta dauka ita yake so ba Hurriya ba, yawan tambayarta Hurriya da yake ba saka ta kawo a ranta son Hurriya yake ba. A gurin da ya da ya tashi ya zauna ya mika mata ledar farko kamin ya mika mata ta biyu

 This one is for you, wannan kuma na Young Lady ne, last time i asked for her contact kika ce bata da waya, so na saka mata waya a ciki, ban sani ba ko za a barta ta yi amfani da ita, idan ma ba a barta ba, ba ki iya amfani da ita, ni dai abun da kawai nake bukata ta fahimci me yake tafe da ni, kuma ta tsaya ta saurareni, ta nan zamu fahimci juna da ita kamin iyaye su shigo ciki, idan Allah yayi, amman kna son ta san cewa ba da wasa nake ba, so ina ganin ke zaki min wannan kokari ki fahimtar da ita

Ta amsa mishi da kai sannan ta mike tsaye rike da ledodin ta fara tafiya.

 Sai da safe...?

Ya fada. Sai ta mayar masa ba tare da ta juyo ta kalleshi.

 Sai da safe

Tun da ta saka gaba bata juyo ba har ta shige falon Momy. Tsaye ta yi da ledodin a falo not knowing what to say or do, Hurriya dake kokarin mikewa tsaye ta amsawa Momy dake fadawa Appanta yana nemanta a bangaren Hajiya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Kaltume, ta kalleta ta yi murmushi irin murmushin nan na zolaya.

Namra ta kasa mayar mata da murmushi kuma ta kasa barin kofar falon da take tsaye, Momy ma dake tsaye stairs kallonta take kamar mai karantarta. Hurriya dake sanye da Hijab dinta ta nufi kofar falon ta bude ta fita ba damar ta tambayi yayarta me ke faruwa saboda Momy tana stairs tana kallonsu. Sai da ta fita daga bangaren Momy sannan hankalinta ya koma gurin kiran da Appa yake mata, tana ta tunanin laifin me ta yi?

 Hurriya...

Ta juyo ta sauri ta kalli bakuwar motar dake fake kusa da motocin da suke bangaren Hajiya Kaltume.

 Na'am

Ta amsa ba dan ta fa mai kiranta ba, sai Khairy da ta gani tsaye ta daure fuska ta rumgume hannayenta kamar an mata dole ta tsaya a gurin. Fadeel ya bude motar ya fito ya tsaya kusa da Khairy, Hurriya a ganinsa ta matsa ta gaisheshi.

 Barka da dare

 Sannu Hurriya, ya kike?

 Lafiya Kalau

 Dan samo min ruwa ciki na sha

Ta kalli Khairy kamar ta ce wani abu sai kuma ta ji ba zata iya ba, ta juya ta nufi bangaren Hajiya Kaltume ta shiga, babu kowa falon dan haka ta wuce Kitchen kai tsaye ta dauko ruwa da cup ta dawo ta mika masa da hannu biyu. Ruwa ya fara karba ya bude sannan ya ta rika masa cup din ya zuba ruwan ya ya mika mata da dayan hannunta ya karbi ruwan ya sha ya mika mata Empty cup.

 Dama ace... Ke ce..., da raina ba zai ba ce ba, kuma zuciya ba zata ki yarda ba

A ransa yake maganar yana binta da kallo bayan ta isa kofar falon surukarsa Hajiya Kaltume. A dinning ta aje cup din da bottle water ta nufi upstairs gabanta na faduwa domin yanzu ta san abu ne mai wahala Appa ya kirata akan wani abun alheri balle kuma a bangaren Hajiya Kaltume, waya sani ko wani sherin suka kulla mata. Cikin tsoro da fargaba ta tura kofar dakin ta shiga.
After Hurriya ta wuce, Fadeel ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Khairy dake tsaye kamar an sassaka itace ya ce

 Ni zan koma

 Toh a gaishe da gida

Ta fara tafiya sai ya tsayar da ita, ya bude Motarsa ya dauko leda ya mika mata.

 Thank You

Ta furta sannan ta wuce ta yi gaba, shi kuma ya shuga motarsa ya zauna, har sai da ta shige ciki sannan ya yi ma motar key ya juya. Har ya isa gidan Hajiya Fatee be daina tunanin yadda za'ayi su yi rayuwa haka da Khairy ba tun a waje balle kuma ace ya aureta, tun ba yau ba ya lura ita ma bata ra'ayinsa kamar yadda baya ra'ayinta. Domin wannan ne zuwa na biyar da yayi a gurinta idan suka gaisa baya sake cewa komai ko da ya gwada ma sai ya ji baya iyawa ita ma kuma bata cewa kuma bata sakewa, haka za su yi ta zama kamar wasu hotuna. Be kashe motar ba ya fita domin ba dadewa yake son yi a gidan ba so kawai yake yayi magana da Hajiyarsa. One step forward a falon Hajiya Fatee yayi arba da bako da ya fito daga dakinta sanye da shadda ruwan kasa, kana ganinsa ka ga bakauye, and instead of ya karasa fitowar sai ya juya da sauri ya koma cikin dakin na Hajiya. Fadeel yayi tsaye a falon yana kallon kofar dakinta with curious face, sai ga Hajiya Fatee ta fito tana ganin Fadeel ne ta saki fuska.

 Ashe ma Fadeel ne, yaya Malam fito ai danka ne

Fadeel dai kallonta kawai yake.

 Waye wannan?

 Kawuka ne na kauye, zauna sai ya fito ku gaisawa, yau ya zo nan zai kwana yanzu haka ma zancenka muke sai gashi ka zo, Yaya Malam fito mana ku gaisa da Fadeel

Fadeel ya zauna yana kallon kofar dakin da Yaya Malam ya ki fitowa.




_____________________

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 1?? 7?


 Be taba zuwa nan ba sai yau, kakaninmu ne guda da shi, amman su a nijar suke, sai bana Allah ya kawo shi

Hajiya Fatee ta fada tana ta yan kama kame. Fadeel ya motsa hannunsa sai kuma ya mike tsaye ba tare da tunanin komai a ransa ba ya ce.

 Maybe da safe zamu gaisa, ni ma gida zanje yanzu, daman na fito gurin Khairy ne na biyo nan saboda akwai maganar da na so mu yi, amman zamu yi da safe

Hajiya Fatee ta kalleshi tana murmushi.

 Okay Allah ya maka albarka

 Sai da safe Hajiya

 Allah tashemu lafiya

Ya nufi kofar fita ta bude ya fice, sai da Hajiya ta leka ta ga motarsa ta bar gurin sannan ta tashi a fusace ta shiga dakinta.

 Haba Malam haba na fada maka kwana gidan nan ba zai yiyu ba, ka ce dole sai an yi haka saboda Aljanin da dare zai zo, kuma na fada maka karka fita daga dakin nan idan kana neman wani abu ka fada min zan dauko maka, saboda gudun irin haka, kullum dana sai ya zo da safe ko dare ya gaishe ni, yanzu ba dan yana da zuciya mai kyau ba ai sai ya wani tunanin ya zo masa

Malam yayi yar dariya mai cike da tsoro abun ka da bakauye.

 Hajiya ban san cewa danki zai zo ba, ni ma kawai na so na fita na dan zagaya ta can baya ne akwai abubuwan da zan karanta saboda kiran rauhanai

 Kuma ina ta kiranka ka fito mu gaisa baka fito ba, bayan na masa karyar cewa kai dan'uwana ne

 Akwai dalilin da ya saka, amman karki damu danki ai wata rana zai ganin har sai ya gaji da gani na

Kallon rashin fahimta ta yi masa.

 Kamar ya? Ai bana fatar haka, Malam bayan wannan za su sake neman wani abu ne?

 Aa ba za su sake neman komai ba, yanzu din ma, ai shegen kwadayi ne da son mata irin na manyan aljannu, kin san yadda farar mace take da daukar ido ko tsohuwa ce balle ke da ba za ace kin yi shekarunki ba, shiyasa kullum ake fada muku ku rika rufe jikinku amman baku ji

Ta sauke ajiyar zuciya, ranta bakikirin kamar an mata bushara da mutuwa.

 Abubuwan sun yi yawa Malam, bana fatan sake aikata komai bayan wannan, tun bayan rabuwata da miji wani abu be sake shiga tsakanina da kowa ba, sai da kaddara nan ta fada min yara kanana suka ci mutunci, duk shi ne silar wannan bakincikin

 Karki damu Hajiya, daman tuntuna saboda kin dauki lokaci ne da tuni ma an wuce gurin, gashi har cikin ya kara satika, amman har yanzu ba mu makara ba. Amman Hajiya na yi miki wata tambaya mana, miye sa ba zaki yi aure ba, wato a lokacin da ina zurfafa bincike a kanki sai na hango maza da yawa da suke kaunarki, kina da wannan kwarjin na hallita

A kaikaice ta kalleshi kallon da ya fi kama da harara.

 Miya kawo wannan maganar Malam? Ina ruwanka da rayuwata ko aurena? Samun gurin har ya kai haka?

 Karki manta dai da Malam kike magana, kuma ina son na fada miki babu mai iya miki irin aikin da zan miki duk garin nan, ki ga aiki kamar yankan wuka, ai kin yi ta sake sake shi ya dauke ki lokaci, da kika ga babu mafita ne kika kirana kika ce kin amince, ina bibiyar duk wanda nake yi ma aiki, ina ganin duk halin da suke ciki

Ta rufe zancen da rufe kwalbar turare mai tsananin karfi, irin mai hawan kanka ya tashi mai aljannu. Hajiya Fatee ta mike tsaye daga kan gadonta da take zaune ta kalli Malam dake zaune a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login