Showing 192001 words to 195000 words out of 279257 words

Chapter 65 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34657

dakin ya nufi wata kujera ya dafa kanta ya sauke kansa kasa ya rufe ido. Kamar an tsikare shi ya bude idonsa ya juyo da sauri ya fito daga dakin, tafiya yake mai kama da gudu ya sauko stairs din.

 Ina wayata?

Ya tambayi Ammynsa sai Momy ta bude jakarta ta dauko ta mika masa tana hawaye. Ya saka hannu biyu ya karba ya juya ya koma ciki.

 Yaya da gaske barinsa zaka yi ya auri yarinyar nan? Wallahi bata kai ba Yaya bata yi matsayin da zata zama surukar mu ba

 Idan aurenta ne abun da Captain yake so, zamu nemi aurenta kuma iyayenta za su ba mu ita dan dole ko da bata so, Allah ba hallatawa iyayen autawa Yayansu wanda basa so ba, ya dai mata ikon zaba musu na gari, kamar yadda ya hallata auren mazina idan sun tuba

Ammy ta dubi Engr

 Ni fa ban gane ba, da gaske zaka aura masa yarinyar nan kenan? Ni ba da yawun bakina ba ba zan yarda Captain ya zauna da wannan yarinyar ba, ai abun kunya ne ace wannan yarinyar ta zama surukar mu duk matan duniya a rasa wanda zai aura sai karuwa?

 Ina tunanin kin fi ni son farinciki Captain...

Ta kawar da fuskarta ta fashe da kuka.

 Wannan goyon bayan da zaka ba shi be yi ba Yaya, be kamata ka biye masa ba shi fa soyayya ce take dibansa lokacin da zata zubar da shi zai fada a mugun guri ne

Wata kanwarsa ta fada. Engr ya mike tsaye rike da takardar sammacin ya ce.

 Idan har kuna ganin akwai rashin dacewa a auren yarinya to ku roki Allah ya sauya masa da wanda ta dace, kuma ki kwantar masa da hankali ku nuna masa illar hakan, idan ya sauya ra'ayinsa Falillahil-hamdu 

Ya nufi kofar fita ya fice daga falon yana kiran wani Assistant manager. Sai da ya fita sannan Momy ta dubi Hajiya Turai ta ce.

 Karki yarda Wallahi ta ya za'a kawo miki wannan yarinyar a matsayin suruka? Taya? Ai da kunya ma

 Wani gine ne Captain yake son na dora wanda ba zai iya karasa ba, ni dai kam ba zan taba karbar yarinyar nan a matsayin suruka ba

Ammy ta fada tana share hawayenta. Wata step Mother din Engr ta dubi Momy ta ce.

 Kuma da gaske yarinyar nan ta aikata abun nan?

 Ba mu da tabbaci, ko da ace ba da gaske ba ne, ai be kamata ya aureta ba Hajiya, saboda duniya ta gama ganinta

 Idan shari aka yi mata bana ganin illar aurenta a gurin Jamal, illar kawai ace ta aikata ne, shi ma kuma idan ta tuba Allah zai karbi tubanta kuma yayi mata sakamako mai kyau, domin Allah yana son bayinsa masu komawa a gurinsa suna kuka suna rokon ya yafe musu, shin idan hakan ya faru da yarki zaki so wani ya juya mata baya? Ku yi tunani mana

 Ko ma dai minene Hajiya ba zamu yarda Captain ya auri yarinyar nan ba

Momy ta amsa mata kai a ranta tana cewa saboda ba jikanta ba ne take fadar haka. Safa da marwa yake waya a kunnesa yana jiran wanda ya aikawa kiran ya amsa.

 Nafi'u ka duba hotunan kuwa?

Ya gabatar masa da abun da yafi daukin ji fiye da gaisuwarsa da sallama.

 Sir barka da yamma, eh na duba

 Ya ake ciki? Editing ne i know

 I'm sorry Sir gaskiya ba editing ba ne, na duba na yi bincike ni da entire team dina ba mu ga wata alama dake muna editing ba ne

Captain ya kai hannu ya shafa kansa ya runtse ido sosai.

 Maybe baka iya aikinka ba, maybe baka duba inda ya kamata ka duba ba

 Na iya aikina ranka ya dade kai ma ka sani, wata kila da wannan gaskiyar mai nauyi ce shiyasa ka kasa karbarta, amman na gano wani abu

Ya bude idon da sauri ya nufi bathroom ya bude ya shiga ba dan ya boyewa wani ba sai dan rudewa da yayi jin abun da yake nema zai samu.

 Alamu ya nuna yarinyar nan bata cikin hayyacinta aka yi hotunan, ko kuma tana cikin bachi mai nauyi domin jikinta ya saki sosai, yadda yake rikota da ace a hayyacinta take ba ta yi yaukin jiki haka ba, kuma babu inda take shauki ko murmushi shi ne kawai yake yi, shi ma kuma akwai alamar tsoro a tare da shi ko kuma rashin kwanciyar hankali, yadda hannayensa ma suke a jikinta ya nuna shi yake rike da ita

Captain ya zauna a jikin bathtub yana murmushi.

 Thank You, Thank You...? Ka gano wanda ya dora hotunan?

 Shi ne ban gano ba, na yi bincike na biyeye abubuwan da suka kamata ban gane komai ba, amman na bibiye wandanda na ga hotunan a account dinsu na Facebook wasu unverified pages ne masu neman labari wasu kuma daidaikun mutane ne, sai da na bibiye wanda aka fi sharing hotunan da ya rufe wasu bangarora na jikinta sai na samu wani dan jarida ne a Kano, and na dauki wayarsa na fada masa daga ina nake kiransa kuma na tambaye shi a ina ya samu hotunan sai ya ce min a wani account ne, ya fara gani, dayan kuma a bauchi yake shi kuma yace min turo masa hotunan aka yi, na bukaci ya fada min account din da na bincika sai na samu an goge account din

 Kana aje wayar nan, ka duba list din mutanen da suka dora hotunan karka damu da yawansu ka turo min su, tare da sunanyen gidanjen jaridun, ka hado min da account number dinka

 Okay Sir

Ya sauke wayar.

 Za su san sun taba mai gata, na miki alkawarin farinciki Hurriya zan cika miki shi... 

Ya fada sannan ya nufi madubin dake bandaki ya dora wayar ya cire tufafinsa ya sakarwa kansa shower. Ya bata minti arba'in a bandakin sannan ya fito yana rike da wayarsa jikinsa kuma na daure da tawul.

 Good Nafi'u

Yayi forwarding sakon zuwa mabanbanta gurare sannan yayi waya da mutane daban daban. At the end ya kira Namra.

 Hello Captain

 Wace asibiti aka kai Adam? Kanen Salim

 Ban sani ba, ya jikanka?

 Bincika min yanzu

 Toh

Ya aje wayar ya dauki wani tawul din ya goge jikinsa, sannan ya zauna gaban madubi yana hararo abubuwa da yawa. After like one hour yana zaune kan carpet bayan ya sallame sallah wani kiran ya shigo a wayarsa bayan na calls din dake ta shigo masa na yan'uwa da abokan aiki masu son tambayar jikinsa. Amman be amsa kiran kowa ba sai na Namra.

 Yana yana asibitin Yariman Bakura, layin ya hadurra

 Good

Ya yanke kiranta tun kamin ta kara cewa komai, ya shiga whatsapp dinsa ya sake sauke hotunan da Salim ya turo masa, ya yanke iya gurin da fuskar Adam take ya turawa wata number tare da address, sannan ya fito whatsapp din ya shiga contact dinsa ya nemo number the same person da ya turawa sakon ta whatsapp.

 Hello Sir

 Uzairu na turo maka hoto da addreshin wani dan'iskan yaro yanzu a whatsapp, ni ya taba so the fight is between me and him.. Ka duba address din ka dauki mutanenka ki shiga cikin asibiti ku dauko shi ku aje min shi wani gurin da babu haske kuma babu rahma, ku masa doka irin dukan da idan na masa tambaya zai ba ni amsa a take amman ban ce ku kashe shi ba, ku aje shi a gurin for 10 hours

 Yes Sir... 

Ya sauke wayar, sannan ya amsa dayan kiran daya fito daga bachi.

 Yeah good so nake ku kama mai gidan jaridar ku bincike shi a ina ya samu hotunan, at the end ku sa ya rubuta cewar sheri aka yi mata kuma yana neman yafiyar Hurriya, ku saka yayi hakan tun a cikin office din ku idan be yi haka ba ku karya kafarsa

 Amman Captain me yayi maka?

 Yarinyar da suka batawa suna yarinya ce mai tsada she is innocent, please karku ragawa kowa a gurin

 Subhanallahi, aiko za su ga aikin DSS

 Thank You My friend

Ya sauke wayar ya amsa wata wayar, haka yayi ta bata umarni a inda umarninsa suke jira a inda alfarma yake nema sai ya roki ayi masa haka.



HURRIYA POV.

 Daure ki sha tea ne kuma ba mai yawa ba

Hajiya Binta na lalabata tana hada mata tea. Gwaggo ta ce.

 Babu yadda ban yi da ita ba amman ta ki cin komai tun safe har yanzu

 Bana iya cin komai ne, ko na ci bana iya hadewa

 Hurriya wannan abun duk zai wuce, wata kila an buga an buga an ga babu sa'a ne shi ne aka bullo ta nan, amman duk wanda ya sanki ya san ba zaki aikata ba, babu wanda zai yarda kawai ana son a jefaki a damuwa ne, dan haka karki bari damuwar da suke son jefaki ta tasirantu akanki karbi ki sha

Ta mika hannu tana lalaben kofin ta karba ta kai bakinta ta kurba kadan sai ta gagara hadewa.

 Hajiya bana iya hadewa

Hajiya ta karbi kofin ta rike tana kallon jikarta cike da damuwa sosai a fuskarta.

 Jibi zan wuce Ummara zan miki addu'a mai karfi a can, da yardar Allah wanda ya aikata miki haka ba zai sake sanin rahma a rayuwarsa ba

 Amin Hajiya

Gwaggo ta amsa, sannan suka daga kai gaban dayansu suka kalli kofar dakin da aka turo. Cikin wani irin yanayi kamar na kunya kamar tsoro Yasir ya shigo dakin fuskarsa a raunane.

 Yasir

 Na'am Hajiya

Hurriya ta sauke kanta kasa duk da kasancewar bata ganin kowa tana jin kunyar aga fuskarta saboda an yada tsiraicinta. Yasir ya tsaya daga tsaye suka gaisa da Hajiya da Gwaggo be ce da Hurriya komai ba ita ma bata iya dagowa ba balle tace masa wani ba sai hawaye take.

 Appa ya ce na zo da Hurriya

 Ka zo da ita kuma? Be san tana asibiti ba?

 Ya sani, yace na yi magana da likitan ya bata sallama

 Saboda me? Be san idonta ya samu matsala ba?

 Ya sani Namra ta fada mana komai, Hajiya idan za ayi mata aikin idon a ba nan za'ayi ba kuma abu ne da yake bukatar shiri da tantance inda ya kamata da kuma likitan da ya dace

Hajiya zata sake magana Gwaggo ta dakatar da ita

 Je ka karbo sallamar, zamu tafi da ita mu ga iya gudun ruwansa amman ba zan bar Hurriya ta zauna a gidan nan ba har bada...!

Yasir ya juya ya fita daga dakin ba tare da yace komai ba, Hajiya Binta kuma ta hau masifa ta daga wayarta ta kira shi kiran be shiga ba. Misalin karfe biyar da mintuna Yasir ya faka a harabar Appa, Gwaggo ta fara fita sannan ta fito da Hurriya Hajiya Binta ma ta fito tana kara shiryawa duk wani abu da anta zai yi. Hurriya ta kama hannun Gwaggo ta rike da karfi.

 Gwaggo tsoro yake kar Appa yace be yafe min ba

 Ko da ya fada ba zai kama ki ba, domin ba ki aikata ba kuma Allah mai adalci ne

Cikin karayar zuciya da duhun idanuwa Hurriya ya shiga bangaren na Appa Gwaggo tana mata jagora komai bata iya banbance komai a yanzu. Yanayin yadda ta ji numfashi na tashi ya karantar da ita falon cike da mutane da bata san su waye ba, yan gidansu ne kadai ko kuma dai duka familynsu da suke garin. Me Appa zai fada akanta shi ne abun da ya fi tsorata ta, da lalabe ta zauna a falon kusa da Gwaggo, hawaye na mata zuba, ta wani bangaren tana gode Allah da bata iya ganin komai, a yanzu da bata san da wane ido zata kalli Appanta ba.

 Hurriya...!!!

Gabanta ta kasa amsa kiran da Appa yayi mata gabanta sai bugawa yake da karfi.

 Kina da wata hujja ta kare kanki akan abun da muka gani tsakanin jiya zuwa yau?

Ta yi shiru, Gwaggo ta ce.

 Ka san dai ba zata aikata ba...

 Gwaggo dan Allah ki yi hakuri ki bari ta amsa min

Appa ya bukata cikin yanayi da ke nuna shi ma yana cikin damuwa kwatankwacin wanda Hurriya take ciki.

 Appa akai ni na yi alwala

Tana fada ta mike tsaye tana kuka.

 Ba sai kin rantse ba abun da duk ba halinki ba ba zaki aikata shi ba

Hurriya ta girgiza ma Hajiya Binta kai ba dan tana ganinta ba.

 Idan ban rantse ba babu wanda zai yarda da ni, ni ma kuma ba zan samu sukuni ba, dan Allah ku kai ni bandaki

Yasir ya kalli Ruma.

 Tashi ki kaita

Ruma ta tashi ta rika hannunta suka shiga bandakin dake cikin falon, Hurriya ta yi alwala ta fito ta bukaci a bata kur'ane.

 Bari zaka yi ta yi rantsuwar nan Tsoho?

Appa ya kasa amsawa mahaifiyarsa, shi ma ji yake kamar Hurriya ba zai aikata hakan ba sai dai zuciyarsa ta kasa natsuwa. Yasir ya tashi da shiga bandakin da Hurriya ta fito yayi alwala ya shiga bedroom din Appa ya dauko mata alkur'ane ya kama hannu ya mika mata, shi kansa idan ta rantse zai fi jin natsuwa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, domin ya shirya ui mata mummunan hukuncin idan har ta tabbata ta aikata. Hurriya ta rike qur'anen da dayan hannunta sai ta dora hannunta na dama a saman kur'ane ta dafa.

 Na rantse da littafin nan, abun da yake cikinsa da wanda ya aiko da shi ban aikata ba Appa

Ta karasa cikin kuka... Gwaggo ta saka kalma shahada.

 La'ilaha Illaha Muhammad Rasulullah

Sai gaba daya falon ya amsa suka karasa a tare.

 Sallalahu Alaihi Wassalam...

Appa ma ya sauke kansa kasa ya fashe da kuka, babu wanda be yi hawaye ba a falon kuma babu wanda be tausaya mata ba ciki har da Momy. Yasir ya sa hannu ya karba yana hawaye da murmushi a fuskarsa, yar'uwarsa ta tsarkake kanta a gaban kowa hakan ya kwantar masa da hankali yanzu kam ya yarda hundred percent bata aikata ba.. Appa ya dago hawaye na zubowa daga idonsa ya mika mata kamar ance masa tana ganinsa.

 Zo nan gareni yata, fada min wa kika tarewa farinciki ya aikata miki haka?

Hurriya ta fara takawa ta inda take jiyo sautin muryarsa tana kuka tana lalaben hanya, Yasir ya rika hannunta ya karasa ta ita gurin Appa, hannayensa ta fara kamawa sannan ta zube kasa a gabansa ta kwantar da kanta a kafarsa.

 Allah ya tsinewa wanda ya aikata miki wannan abun Hurriya, ba zai gama lafiya ba, bakinciki da ya saka mana da neman bata miki da sunan gidan nan Allah ya ninka masa shi...

Kowa ya amsa da Ameen ban da Khairy da Namra dake ta kuka kai ka rantse da Allah su aka aikatawa haka ba Hurriya ba.

 Ba zan bar maganar nan ba, sai na yi shari'a da yaron nan, ya ci mutuncina ya ci mutuncin ?ata ba zan kyale shi ba

 Ni ma na yi wannan tunanin Appa, na kudirta a raina idan har ta tabbata Hurriya bata aikata abun nan ba, ba zan kyale maganar nan ba

Yasir na aje aya Hajiya Binta ta ce.

 Da kun kyauta daman be kamata a kyale ba

Momy ta tashi ta fice ba tare da tace komai ba, Ruma ta bi bayanta. Gwaggo ma ta mike tsaye fuska a daure ta ce.

 Zan tafi gida, kuma zan tafi tare da Hurriya saboda a can zata samu kulawa

Appa be ce komai ba bayan shafa kan Hurriya da yake, har Gwaggo ta iso gurin ta kama hannunta suka fice. Sai da suka kusa isa gate sannan Yasir ya cin musu da mota ya bukaci su shigo ciki ya sauke su gida, Gwaggo kamar bata shiga ba saboda yana dan Hajiya Kaltume sai kuma ya daure ta shiga saboda saukaka Hurriya wahalar fita titi zuwa neman abun hawa. Back seat suka shiga ita da Hurriya har suka isa Yasir be yi wata magana ba, balle kuma Gwaggo da ta matsu su sauka a motarsa. Har cikin gidan ya faka ya fito ya budewa Gwaggo ta fito ita kuma ta riko Hurriya ta fito suka shiga cikin gidan. Yasir ya bisu da kallo gaba daya Hurriya ta zama abun tausayi a yanzu.

 Kina ganin jarabawa Hurriya

Ya furta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya bude motarsa ya shiga. Rukayya na ganin Hurriya ta shigo falon tana lalabe sai ta fashe da kuka ta saki kofin kurar da zata bawa Amma ta nufi Hurriya ta rumgume ta suna kuka. Gwaggo ta girgiza mata kai domin bata son Amma ta sani, sai dai abin da bata sani ba Rukkaya ta fada ma Amma komai bayan tafiyarta.
Jin kukan Hurriya sai ya saka Amma ma ta fashe da kuka, kukan da ta shekara hudu bata yi irinsa ba, kukan da tun da ciwon ya kamata bata taba kuka anji muryarta ba sai yau. Hurriya na jin sautin kukan Amma ta saki Rukkayya ta fara lalaben gurin da Amma take, Amma ta rika fuskarta ta saka hannunta ta bude cikin idonta tana kuka.

 Bana gani Amma bana ina ganin komai....

Amman ta girgiza kai ta fashe da wani idin kuka mai taba zuciya.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un...

Amma ta furta da wani irin karfi irin an mai kwancen murya. Rukkayya ta kalleta da sauri ta rufe baki tana kuka, Gwaggo kuma ta zauna kusa da ita ta fadata.

 Iyami... Allahu Akbar....

 Na jefaki a halaka Hurriya na je kaina, sun kashe min Hamad ke ma kuma so suke su ga bayanki, da na san haka GOBENA zata kasance da ban auri Alhaji

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login