Showing 228001 words to 231000 words out of 279257 words

Chapter 77 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34629

kin koma ki fada mata mijinta ya riketa, daman ya fi Kaka iko da ita

 Zata min fada

 Fada kadai zata miki ashe, Wallahi Hurriya ba zata koma yanzu ba, akwai maganar da zan yi da ita so ki tafi kawai karamar uwa madaukar zunubi

Babu yadda Rukayya ta iya bayan yi masa fatan samun lafiya ta fice daga dakin Hurriya na ji kamar ya ce mata kar ki tafi. Captain ya matsa kusa da Hurriya jikinsa na taba nasa daman ficewar Rykayya kawai yake jira.

 Ni kike gudu?

Ta yi shiru tana jin kunya na rufe ta, sai ta ji dakin yayi mata girma daga ita sai shi daman tana jin alamar kamar su kadai ne a ciki. Ya saka hannayensa biyu ya zafaye ta ya dora wuyansa a kafadarsa.

 Fada min ya kike?

 Lafiya kalau

Ta amsa da sauri, tana kin bashi hadin kan tsuma yatsunsa a cikin nata. Ya sumbanci kuncinta ya kalli gefen fuskarta yana kai dayan hannunsa ya taba Lips dinta

 Ki yi hakuri na mari dukiyata na fasa bakin nan da kaina, ban jidadi ba I'm sorry

 Ba komai ya wuce

Ta mike tsaye tana jin wani iri, ya sauke kansa kasa yana murmushi kamin ya mike tsaye ya koma gabanta ya tsaya ya dafa kafadarta.

 Alhamdulillah komai ya wuce a yanzu ko?

 Ya wuce a cikin gida, amman yana nan a duniya za'ayi ta kallona da abun ko da na bar duniya

Ya kura mata ido kamar mai kokarin kure kallonsa. A hankali ya zaunar da ita ya zauna gefenta ya saka hannunsa a cikin nata ya kwantar da kanta a jikinsa.

 Abu mai muhimmanci a yanzu, mahaifinki be yarda kin aikata mahaifiyarki ma haka, Ubangijinki ma ya san baki aikata ba, mijinki ma haka duk wanda zai zargeki a bayansu ba shi da amfani

 Kai ma ka yarda ban aikata ba?

Yayi dariya marar sauti ya dagota daga jikinsa ya fuskance yana kallon kyakkyawar fuskarta.

 Na yarda amman ban tabbatar ba

 Zan iya rantse maka da kur'ane kamar yadda na yi ma Appa

 Ban karyata ki ba ai, zan tabbatar da kaina, na gaba kadan

 Yaushe? Me yasa ba saka tabbatar a yanzu ba?

 Kin matsu ne?

Ta daga mishi kai a bakin gaskiyarta, sai ya saki hannunsa ya mike tsaye yana murmushi domin ya fahimcin bata gane dawon garin ba. Kofar dakin ya nufa ya bude ya leka hagu da dama sannan ya dawo ya tsuguna a gabanta hananyensa a cinyarta yana kallon fuskarta a dora, sai fara kokarin mikewa tsaye tana ture hannayensa.

 Babu wanda zai ce wani abu a nan, ni mijinki ne, halak malak, ni zan bawa duniya shaidarki daga yanzu har karshen rayuwarki

Ya kama yatsansa yana murzawa a hankali.

 Mai tsada na yi yadda zan iya na ga mutunci ya karu a idon duniya, na iya kokarina na saka an goge hotunan wadanda suka wallafa hoton sun goge, sai dai wadanda ban sani ba

Ya sumbanci hannayenta duka biyu ya saka su a fuskarsa.

 I will fix what they broken, zan zama zama hasken da zai haska duhun dake rayuwarki, zan yaye miki damuwarki, zan saka ki yi alhari da ni a matsayin miji, da ace zan iya sauya lokaci na koma baya da na rayu da ke tun kurciya har tsufa, saboda ina bukatarki a rayuwata, i will spend every hour of the day keeping you safe Hurriya, na miki wannan alkawarin Hurriya, zan baki wata duniya mai cike farinciki, duniyar da babu kuka babu damuwa babu tashin hankali babu tsana babu kiyayya.... ?

Hawaye ke sauko mata jikinta yayi sanyi, ba a taba siyeta da kalamai masu dadin irin na yau ba, wani be taba yi mata kalam kwantar da hankali kuma ta ji hankalinta ya kwanta ta samu natsuwa irin yau ba.

 Is Okay is alright....

Ya mike tsaye ya zauna kusa da ita ya share mata hawayenta.

 Ban taba fada miki wannan ba Hurriya, bari na fada miki yau.... I LOVE YOU... INA KAUNARKI HURRIYA fiye da duk wani namiji da ya nuna miki soyayya a duniyar nan

Wasu hawayen ne suka sake zubo mata, sai ya kai bakinsa ya sumbanci hawayen nata ya hade goshinsa da nata yana goga mata hancinsa, numfashinsa da nata yana tarayya.

 Ina jin wannan din ma kamar mafarki ne

Ta fada cikin sautin kuka, sai ya dora bakinsa akan nata ya rufe ido.

 Gaskiya ne... Zahiri ne wannan Hurriya... Lokacin da Daddy yace min mai tsada ta zama taka sai na ji kamar ba a taba bani farinciki irin na ranar ba, saboda ke ce Hurriya

Yana maganar lips dinsa na taba nata, kamin ya bude idonsa yana kallon nata idon dake rufe. Sannan ya sumbanci banki ya sumbanci hancin ya mike tsaye ya dauko wayarsa ya dawo kusa da ita ya zauna.

 I have another surprise for you

Ya kunna mata video sanin bata iya gani sai ya kara mata muryar a kunne. Kamin ta gama saurare hawaye ya jika gaban hijabinta, sai ta kasa jin farinciki kuma ta kasa jin bakinciki ta tsaya a tsakiya tana jin ba gaskiya ba ne.

 Taya yar'uwa ta jini da uba mai daraja ya hada su, zata aikatawa yar'uwarta wannan abun? Ko dai sheri yake mata? Na san Yaya Khairy bata shiri da ni amman wannan yayi muni, mai kiyayya da ta yi zurfi da kai ne kawai zai iya aikata wannan! Idan ma bata raga dan ni ba ai ta rangwanta ko dan mutuncin gidanku, a karkashin inuwa daya muke da ita wannan abun ya taba mutuncin kowa a gidan bata gane ba? Na ma kasa yarda ita ce ta aikata haka

Captain ya rumgume ta, domin kukanta a yanzu yana daga masa hankali.

 Zamu kara tabbatar da hakan nan gaba kadan, gaskiya zata kara bayyana

Hurriya ya rushe da kuka a kirjin mijinta ta kamkame shi.

 Na tuna... Na tuna ranar da ta fita da ni... Ranar da tace na raka ta gidan kawayenta, Yaya Khairy ta cuce ni yar'uwa ta cutar da yar'uwarta ta jini, me na mata amman me na mata

Captain ya dagota jikinsa da sauri ya rike fuskarta da hananyensa.

 I know this not easy, baki mata komai ba Hurriya, makiyinka baya bukatar ka yi masa laifi sannan ya hukuntaka baki mata komai ba

Ta saka hannu ta rufe bakinta tana girgiza kai, yayi mata nauyi yyi mata muni ace yar'uwarta ce ta aikata haka. Ya sake rungume.

 Shiiiiiiiiiiiiiiiiiii wannan ya wuce yanzu, ita ya kamata ta yi kuka ba ke ba

Be dagota daga jikinsa ba sai da ya tabbatar ta daina kukan. Sannan ya dagota daga kirjinsa ya kalleta.

 Kin rame wannan abun ya saka miki damuwa sosai, yaushe rabon da ki ci abinci

Ta kasa yin magana. Ya shafa fuskarta.

 Kina bukatar cin wani abu?

Ta girgiza kai.

 Kwanta a nan ki huta

Ya kwnatar da ita kan gadon na dora mata kafafuwanta sannan ya subancin fuskarta goshinta da saman idanuwanta da suke rufe. A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya matso da kujera ya zauna yana kallon fuskarta, ya matsa da kujerar ya shafa fuskarta zuwa hancinta yana gaba lips dinta. Can kuma ya matsa baya ya kalli drip din da ya cire dazun, sai ya janyo karfen ya maida ruwan da kansa ya daidaita komai a yadda yake, kana yayi relaxing akan kujerar yana kallon kyautar da Allah yayi masa.

 Ajiyar da na baki ajiya ce ta har abada, na gode da kika ba ni hadin kai, lallai kasancewa da Hurriya abu ne da kike muradi, akwai farinciki a auren matar da kake so kake tausayi... Na ji hakan yau, na yarda na karba na aminta wannan din mai tsada ce, ta canja min siffa, ta sauyan lissafina ta rike linzamina... I will take every risk for her, i will bend the rules... Thank you.... She's my world... My Hayatie... My Rayuwa.. Thank you for this cause I know you feel the same... 

Yana maganar hannunsa dafe a saitin da zuciyarsa take aje, idanuwansa kuma suna ta bawa abun da ruhi yake bukata... Mursa kofar dakin da aka yi ne ya saka shi juyo sa kai ba dan ya gundura da kallon rayuwarsa ba ya kalli kofar. Daga Momy har Ammy Momy Ikilima da Hajiyar Maru tsaye suka yi suka kallon ikon Allah, Hurriya na kwance a kan gadonsa shi kuma yana zaune a kujera da drip a hannu.

 Minene haka? Me yarinyar nan take yi a nan? Waya kawo ta?

Ammy ta tambaya a tsawa, Hajiya Maru ta yi hanzari tariyar numfashinta.

 Turai ki saurara mana

 Hajiya haba mana? Yaron da bashi da lafiya aka kawo asibiti shi ne za a kawo ta? Shi yana zaune a kujera da ruwa a hannu ita tana kwance a gadon asibiti? Makauniyar me zata masa?

Hurriya ta zabura ta tashi zaune da sauri sai kuma ta sauko ta yi tsaye gabanta na bugawa da karfi, bata san su waye ba, bata ji muryar wadanda ta sani ba, gashi bata gani balle ta matsa daga gurin. Captain ya mike tsaye ya kalli mahaifiyarsa cikin damuwa.

 Haba Ammy kamar baki san wacece ita ba? Kin tsorata ta kuma ba laifin be laifina ne... 

 Really..... 

Ammy ta furta tana masa kallon mamaki, sannan ta juyo ya kalli Captain din ta saki jakar dake hannunta.

 The only thing you care about is her, baka yi tunanin ya zan ji idan na ganta ba? To na bar mata sai ta yi jinyarka

Ta juya ta fice, Hajiyar Maru ta bi bayanta tana kiranta, Momy kuma ta duka ta dauki jakar da Ammy ta saki tana yi ma Captain mugun kallo sannan ta juya ta fice, Momy Ikilima ce kadai ta iya karasowa ta aje kayan dake hannunta ta kalli Hurriya ta kalli Captain sannan ta fice cike da takaici. Captain ya kama hannun Hurriya ya rike

 Karki daga hankalinki da yawa Hurriya when i meet you i tell myself that i will love you and protected you at any cost....

Hurriya ta sake hannunsa ta dan matsa baya.

 Yaya... Ina son na tambayaka...

 Ask me any question, zan amsa miki



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 48

Yayi murmushi ya matsa kusa da ita kadan.

 Babu ruwanki a wannan Ni kika aura kuma da ni zaki zauna karki saka damuwar kowa a ranki

Ta yi shiru.

 Zauna

Ta kasa zaman kamar yadda ya bukata gashi bata gani balle tace zata tafi gida ita kadai, gaba daya sai ta ji zaman a dakin ya gundireta.

 Dan Allah ko zaka kira a kai ni

 Ba yanzu ba, nan zaki wuni sai dare zaki koma

Ta yi shiru a karo na biyu bata son zaman kuma bata son musa masa, hakan kuma ta kasa komawa ta zauna a gadon da Ammy ta tarardar da ita. Hankalinta be kara tashi ba sai da Ammy ta dawo dakin tana ta masifa tareda Momy da Hajiyar Maru wadda ta yi aikin bata hakuri har ta hakura ta dawo. Hurriya ta sauke kanta kasa duk da kasancewar bata ganin komai.

 Ya jikan nata Jamal

 Alhamdulillah

Ya amsawa Hajiyar Maru.

 Allah ya kara sauki, zan tafi da amaryar taka sai mu sauke ta a gida

Ya daga kai ya kalli matar da take zaman kakarsa.

 Hajiya bata dade da zuwa ba, Daddy ne ya saka aka daukota saboda ta dubani kuma mu yi magana akan video da Adam ya saki na bada hakuri

 Ko ma dai minene yayi wuri ace ta biyo sawunka, be kamata ace iyayenta sun barta ta zo asibiti dubaka ba, makauniyace me zata yi a nan? Da iyeyenta sun san mutunci ba za su yarda ta zo ba...

Hajiyar Maru ta dakawa Ammy tsawa.

 Ba na ce ki cire bakinki ba? Ba na ce ki dauke kai daga wannan ba

 Zan iya cire bakina amman ba zan iya dauke kai ba, ni dai bana maraba da auren nan bana son yarinyar nan bata dace da ana ba

Furucin Ammy yayi daidai ta saukowar hawayen Hurriya sai ta kame jikinta sosai ta natsu.

 Ai kara ta fada mata irin zaman da zata yi da uwar Captain tun a yanzu, gaba daya gidan? nan babu mai goyon bayan wannan bakin aure

Momy ta dora da nata, tabbas da ba su suka fadi hakan ga Hurriya ba da sai gurin da karfinsa ya kare amman ba zai iya musu da iyeyensa ba ba zai iya fada musu magana marar dadi ba, saboda haka ya kalli Hajiyar Maru ya ce.

 Hajiya zan kira a dauketa

Ya juyar da idonsa gurin Hurriya

 Kina da number wani da za a iya kira?

Ta daga kai. Sai ya runtse ido ya bude hawayen dake mata zuba suna kona masa rai.

 Fada min...

 08....0...

Ta karanta masa number Amma sai ya kira kamin Ammy ta daga ya tambeyeta number waye ta fada masa. Hakan ya saka shi natsuwa ya gaishe da Amma cikin mutunci da girmamawa sannan ya ce.

 Hurriya ce ta bukaci gida, gashi kuma direban da ya kawo su ya tafi kuma wanda zai kaita yanzu be san gurin ba, kuma kin ga akwai lalura a tare da ita ba zata iya nuna masa hanya ba

 Toh Rukayya zata zo ta tafi da ita yanzu

 Toh na gode sai ta zo

Ya sauke wayar, amman ya kasa daga kai ya kalli kowa. Ammy ta ce

 Ta jira wanda zai zo ya tafi da ita a waje ko kuma ni na fita na bar mata dakin har sai ta tafi tukuna na dawo

Sai Momy ta karbe mata.

 Aa ai ba ayi haka ba, ke da danki? Ita zata fita ta jira a wajen

A nan ma Captain be dago kai ba kuma be ce komai ba, Hajiya Maru ta girgiza kai ta isa gurin da Hurriya take ta kama hannunta ta fice da ita sai a lokacin Ammy ta zauna.

 Duk abun da kuke yi ma Hurriya ni kuke yi ma ba ita ba, domin ni nake aurenta ba zata iya kawo kanta dole a gareni ba, kuma da ban aureta ba ba zaku mata haka ba, na gode da kalar soyayyarku na gode

Ya fada yana taba wayarsa sannan ya dago ya kalli Momy ya ce.

 Momy ina son ki sani, ko da kaddarar mutuwa zata raba ni da Hurriya domin ita kadai ce abun da zata raba mu a yanzu ba zan taba auren Namra ba, domin ban taba sonta ba ban taba jin ina kaunarta ba, kuma abun da kike yi ma Hurriya ko kike ziga Ammy ba zai canja komai ba, face kallon da nake miki na yar'uwa uba mai daraja zuwa wani dabam, ina son Matata! Ni dai ina son ku san wannan

Ammy ta saki baki tana kallonsa Momy kuma ta kasa rike zuciyarta.

 Namra ba kwantai ta yi Captain balle ka ce idan Hurriya ta mutu ba zaka aureta ba, kuma da yardar Allah Namra sai ta samu mijin da ya fi ka a komai, ina da rai wata rana sai ka zo kana fada min bakinciki da damar da ka yi na auren Hurriya, laifin ai ba naka ne kadai ba har da na Yaya

Ta juya a fusace ta fice daga dakin tana barin kofar dakin a bude.

 Miye amfanin haka? Saboda wata yar iska wata bare zaka batawa kanwar mahaifinka rai? Matar da bata san gurin da zata aje ka ba saboda soyayya? Me ya shiga kanka ne Captain? Anya kai ne?

Ita kam be ce mata komai ba har ta ci ta cinye.




HAJIYA KALTUME POV.

 Ya jikin nata Hajiya?

Khairy ta tambaya. Sau Hajiya Kaltume ta yaye mayafin dake jikinta ta aje jakarta gefe.

 Jiki da godiya, amman kam Hajiya Fatee bata da lafiya sosai, yanzu ma daker ta yarda muka dauke ta muka kaita asibiti muna zuwa suka ba mu gado, ni ma kadan ya rage na fadi jiri sai kwasheni yake damuwa ce ta mana yawa Khairy ba ita ba ba ni ba, kara ita ta wani bangare, duniyar nan bata da dadi a gurin kowa yanzu sai azzaluma, tun da muka dawo kauyen nan Hajiya Fatee bata sake lafiya ba, sai kin ga yadda hankalin Fadeel ya tashi

Khairy ta kwanto a hannun kujerar dake falon na Hajiya Kaltume tana fadin.

 Ni kaina bana cikin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login