Showing 171001 words to 174000 words out of 279257 words

Chapter 58 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34663

dadi ta ce.

 Gwaggo ko da tana son komawa? Yanzu idan Appa ya zo yace ta yi hakuri ta dawo ba zata dawo ba?

 Bata ma so! Auren babanki da Iyami rabuwa ce ta har abada

Hurriya bata saurari maganar Gwaggo ba, ta matsa kusa da Iyami ta kama hannunta ta rike.

 Amma wai baki son komawa ki zauna tare da mu? Idan kika ji sauki? Kowa yana da uwa a gidan mu kadai ne ba mu da

Amma bata ce mata komai ba, daman kuma ba zata ce ba domin bata iya magana a yanzu.

 Amma ki matsa hannuna sau daya idan zaki koma, idan ba zaki koma ba ki matsa hannuna sau biyu

Babu bata lokaci Amma ta matsa hannunta sau biyu ta girgiza mata kai. Gwaggo ta ce.

 To ki cire rai daga yau, ki dai fatan uwarki ta samu lafiya, kuma ta samu talaka irinta mai mutunci ta aura, kishi da Kaltume kam an gama har abada, miji dai take tutiya, to an bar mata shi ta dafa ta ci, wannan bakin kishin ya isa haka akan ?ata, tsabar hauka har Rukayya take son jajibo mana wani aiki, sakaryar yarinyar kawai

Hurriya ta mike tsaye tana jin kamar ta fashe da kuka ta fice daga falon ba tare da tayi musu sallama ba. A lokacin da ta fito cikin gidan sai tausayinta ya kama Yasir ba dan ya san abun da ya gudana a tsakaninsu ba, sai dan a yanzu ya san yadda zafin rabuwar auren iyaye yake, saboda abun da ya faru tsakanin Appa da Hajiya Kaltume a yau, shi da yake babba kenan balle kuma ita da abun da ya faru tana karama, a yanzu ya kara yarda idan iyaye suka samu tsabani har ta kai ga rabuwa yara yake taSawa fiye da yadda yake taSa iyayen, ya ga halin da kanensa suka shiga da kuma mahaifiyarsa ga shi shi kansa abun ya haifar masa da damuwa balle kuma Hurriya da take karama da kanenta da su ma a yanzu suke tasowa.
Ta bude motar ta shiga ta rufe motar tana jin kamar ta fashe da kuka. Be mata uffan ba shi ma ta shi damuwar ta isheshi baya son ya tambaya ta fada masa Gwaggo ta fadi wata magana akansa ko ga Rukayya ko kuma ta mata fada saboda shi.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
34
5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


After ya rufe motarsa ya bude back seat ya dauko katuwar ledar ya rufe motar ya nufi falon Momy. Sai da ya fara danna door bell sannan ya murda kofar ya shiga. Momy na zaune falon Namra ma kwance a doguwar kujera suna zancen Hajiya Kaltume, sai dai shigowar Captain ya saka duk suka yi shiru, Namra ta tashi zaune tana masa sannu da zuwa, but still yana jin babu dadi a yadda ya nunawa Hurriya kulawa a dazun.

 Captain yanzu ake tafe

Momy ta fada, sai ya dora ledar a kujera yana daga tsaye yana murmushi ya amsa mata.

 Ni ma ban sa ran zan dawo yanzu ba, tafiya ce ta kama ni gobe da safe zan bar garin nan?

 Lafiya dai?

 Yanayin aikin ne, zan yi 1 week a Kaduna

 Da sauki ai, gida zaka je

 Da can nafi son Kaduna, yanzu kuma na fi son nan

Namra ta yi murmushi.

 Gashi kuma ka kusan gama aikinka na nan ai, ka koma KD gaba daya

 Ina tunanin Daddy zan yi ma magana, a san yadda za'ayi a bar ni garin nan, domin idan na koma Kaduna ba zan samu zuwa nan ba. Ina Hurriya?

Momy ta sake dubansa bayan kallon da take masa da dan mamaki ta ce.

 Hurriya kuma?

 Yea na siyawa twins dinta abu ne, kin san yadda nake son yara

Ya amsa yana murmushi acting like bakin gaskiyarsa yaran ya kawo wa.

 Yaran ma ta tafi ta kai gida ai, ba nan suke zama ba

 I know tsaraba ce bari na aje a dakinta

Ya dauki ledar sai Namra ta mike tsaye.

 Let me help you

 No please ajewa kawai zan yi na fito

 To ai bata nan kuma yaran sun riga sun tafi

Cewar Namra tana kallonsa da shakku a idonta. A take ransa ya bace ganin tana kokarin kure shi.

 That's right idan ta dawo sai ta zuba ashara

Ya dauke kansa ya nufi stairs rike da ledar, har dakinta ya shiga ya aje mata ledar kan gado ya juyo zai fito sai kuma ya juya yana karewa dakin kallo, karamin gado ne daidai ita sai mirror da closet dinta daga gefe. Ya taka ya isa closet din ya bude yana kallo, can kuma ya rufe ya dawo gurin mirror yana duba kalolin mai da turare dake gurin, ya kai hannunsa ya bude durowar dake jikin mirror a nan kuma yan kunne da sarka ne sai agogo daga kasa kuma hotuna ne. Hotunan ya dauka ya shiga dubawa, wani gurin ita da Hamad ne wani da Amma wani kuma family pictures ne su hudu, wani kuma ita da Appa babu wanda take ita kadai sai wanda take karama, inda take rarrafe wani kuma ta fara tashi dayan lokacin da ta kare primary. Murmushi yayi ya juya ya kalli kofar dakin dake bude sannan ya dawo da idonsa gurin mirror ya sake dauko wasu hotunan dake aje gefe daya, su kan nata ne inda take ita kadai sai kuma wandanda ta yi ranar birthday ta sun yi kyau sosai ko'ina kuma tana sanye da abokin rayuwarta ne wato glasses. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya dora hotunan yana ta dauka hoto sai da ya gama sannan ya maida su a muhallinsu ya dauko awarwaronta ya duba ya dauki zoben dake tare da sarka ya duba sannan ya aje ya rufe mata gurin ya maida wayarsa aljihu ya fice daga dakin ya ja mata kofa. Da sassarfa ya sauko stairs din kana ganinsa ka san a hanzarce yake.

 Momy zan tafi sai mun yi waya, sauri nake akwai mai jirana

Mamaki ya hana Momy ce masa komai har ya fice. Namra ta daki hannun kujerar.

 Me na gama fada miki yanzu Momy? Kin ga gani ko?

 Toh ni ma dai abun ya daure min kai, amman kin san Captain yana da son yara fa

 Maganar ba ta son yara ba ce kawai, ko last time da ya aike ni siyo masa a Mall na je office dinsa na samu glass din Hurriya and he was telling me wai ya bata wani gilashin ne, kin tuna ko ranar da ya saka ta girki, and dazu da safe karki ga yadda ya damu saboda ya same ta tana kuka

 Kuka me?

 Na munafurci da neman jan hankali mana, ni ma ban san dalilin kukan ba kuma kin ga ko lokacin da ya tarar ina fada da yarinyar ita ya goyawa baya, saboda ita har marina yayi fa

Momy ta dan yi dariya kamin ta yi murmushi sai kuma ta sake yin murmushi abun kamar zai kama kanta sai kuma ta ji be kama kanta ba.

 Amman Captain yafi karfin wannan yarinyar ai, beside idan ma zai so wata a gidan nan ai ke ce kuma ina jiyo kamshin hakan

 Babu macen da tafi karfin namiji Momy, yarinyar ta san yadda take ta sace zuciyar maza, haka ta yi min a Salim har yanzu idan na tuna sai na ji wani iri, and now Captain

 Idan ma haka ne ke kike yin saka, kuma idan har ta dauki hankalin Salim ba zata sami Captain ba

 Na yi sake? Momy ni fa mace ce i don't run after a men, idan su ba su nuna suna ra'ayi ba, ni ba zan iya zubar da ajina na yi kasuwanci kamar yadda take ba

Namra na rufe baki Hurriya ta turo kofar falon ta shigo cikin yanayi na damuwa sallamarta ma can ciki ta yi, Momy da Namra kuma babu wanda ya amsa mata, ta iso kusa da Momy ta risina.

 Momy sannu da gida

Ta mike tsaye sai Momy ta bita da kallo kamin ta ce.

 Ke...

Hurriya ta kalleta tare da amsawa a hankali

 Na'am

 Tafi ki dauko min ruwa a kitchen

 Toh

Ta juya sai Momy ta ce.

 Cire hijab din ki aje a nan

Ba musu ta cire hijab din ta aje ta nufi hanyar Kitchen, Momy ta bita da kallo da ta fito ma Momy kare mata kallo take tsab sannan ta karbi ruwa.

 Toh tafi dakinki

Hurriya ta dauki Hijab dinta ta nufi hanyar stairs, sai da ta haye sama gaba daya sannan Momy ta kalli Namra ta ce.

 Na ga dai idan farin nan ne ke ma kina da shi, kuma ko mazaunai kin fita ban san wani abun ja mata hankali a jikinta ba

 Tana da kyau Momy kuma munafuka ce ta iya kisisina kala kala

 Ko dai minene ki cire wannan a ranki, ni da Hajiya Turai babu wanda muke so Captain ya aura sai ke, idan ma be aureki ba ai ba zan bari ya auri yarinyar da ba ajinsa ba irin Hurriya

Namra ta mike tsaye tana rike da wayarta.

 That's mean idan Hurriya tana gidan nan wani ba zai taba cewa yana so na ba

 Ki bude idonki Namra yanzu lokaci ya wuce da zaki ce sai anyi yaki a same ki, idan kina son Captain to ki takawa yarinyar nan birki, ko da ma baki son shi ya kamata ki hana alakarsu ko dan abun da ta yi miki amman idan kika kyale kin bata dama kenan, sannan ni da ke mun san Captain ya fi karfin yarinyar nan waya sani ma nan gaba kadan zata iya makancewa gaba daya, kuma yadda uwarta ta zo ta yi mana milki a gida yarta ma tace zata auri Captain ta yi yadda take so, abu ne da ba zan dauka ba, idan Khairy ce ko wata a cikin yayan Kaltume kina ganin zata kyale Hurriya ne?

Fada sosai Momy take ta wani bangaren tana ganin kamar har fa laifin Namra na saken da take yi har Hurriya take son damar yi mata. Namra ta sauke ajiyar zuciya ya nufi stairs ta sani tana son Captain fiye da yadda ta ji tana son Salim da farko, har tana murna tana ganin kamar sauyi ne Allah yayi mata saboda ta rasa Salim yanzu kuma Hurriya na son sake jefata a cikin wata damuwar, idan har bata auri Captain ba to be kamata ace ya auri kowa daga familynsu ba sai dai daga wajen familynsu balle kuma ace cikin gidansu kuma kanwarta da suka hada jini daya. Ko da soyayya ce kadai be kamata Hurriya ta yi da Captain ba balle aure, sai dai yadda ta san halin Captain wata kila ko da wata alakarce ba zata dade ba saboda yanayin fushinsa da saurin daukar zafi kamar kofin tasa, sai dai duk da haka Momy tana da gaskiya be kamata ta zuba ido Captain yayi soyayya da Hurriya ba ko da be aure ta ba, hakan zai lalata alakarsa da gidan idan suka samu tsabani kuma zai juya mata baya ba zai yi tunanin ya aureta ba. Jingina ta yi da kofar dakinta bayan ta rufe, abu ne mai zafi da ba zata iya rike hawayenta ba, ko da tafiya kuke a hanya wani yace yana son kawarta ba ita ba zata ji babu dadi balle kuma ace cikin gidansu. Bayan kuma duka mazajen nan biyu sun nuna ita suke so amman gashi yanzu Hurriya tana dauke hankalinsu, ta saka hannunta a baki tana ciza kumbarta, gaba daya ta ma rasa me zata yi, ta wank bangaren tana ganin kamar yunkurin yin wani abu zubar da kimarta da martabarta ne ne mace.

 Amman Ina son Captain, Hurriya me yasa kike min haka? Why?

Ta fadawa kanta kamin tambayar karshe ta biyo baya. Ajiyar zuciya ta sauke ta share hawayenta ta nufi gadonta ta zauna tana busar da iskar bakinta, zuciyarta na mugun zafi wani fitinannen kishi take ji marar misaltuwa, kamar an fisgeta haka ta tashi ta fice daga dakin.

A kasale Hurriyya ta shiga dakinta bata lura da ledar dake kan gadonta ba saboda hankalinta gaba daya ba a gurin yake ba, ya tafi gurin tunanin rayuwarta ta baya, alamar da Amma ta bar mata na cewar ba zata dawo gidan ba ya saka ta kewar lokacin da take gidan, tana ayyana yadda zata cigaba da fuskantar wahala da kalubale na rashin Amma a gidan. Daf da zata zauna ta yi arba da bakar ledar daman hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba. Hannu ta saka ta lalaba ta juya ta kalli kofar dakin dake rufe tana mamakin waya kawo ledar a dakin. Zaunawa ta yi sannan ta saka hannu biyu ta bude ledar wani dan karamin kati ne a sama dauke da wasu takaitattu kalmomin.

_Tafiya ta kama ni yau din nan, kuma zan yi sati a KD, na san kuma ba ki samu abinci in time na siya miki wannan i hope zai taimaka, karki ci da yawa so that yayi miki sati lol_

_Yaya_

Tana gama karanta sai ta ji kamar an cire mata damuwanta gaba daya, sai murmushi take tana sake karantawa, and the part da yace kar ta ci da yawa ya saka ta nishadi. Ta aje takardar a gefe ta shiga ciro kayan, kwalin dabino ne uku sai chocolate da kilishi da aka busar tare da biscuits kala kala da kuma karamin kwalin cornflakes da madara cube sugar and different varieties of sweet Candy. Chocolate daya ta dauka ta bude ta fara ci tana tuna abun da ya faru a dazun tsakaninsu murmushinta ne ya fadada zuciyarta kuma ta shiga bugawa da mugun karfi kamar zata fasa kirjinta ta fito, numfashinta yana yin sama kamar yadda ta samu kanta a lokacin da ya matso daf da ita yana mata magana.

 Hurriya?

Ta kalli kofar dakin a zarane tana amsawa Namra dake tsaye rike da kofar.

 Na'am

 Ina fatan dai ba rokon Captain kika yi ya siya miki wani abu ba?

Ta girgiza mata kai.

 Good saboda wannan iskancin da karuwanci da kika rika yi ma Salim be kamata ki koma gurin abokinsa ba bayan kuma kin nuna masa baki sonshi, sannan Captain ba sa'arki ba ne zaren ba kalar yadin ba ne, yana da kyau ki yi hankali tun wuri, bana son kina shige masa, karki sake yi masa magana daga yau, saboda ni yake zuwa gidan nan so daga yau bana son na sake ganinki idan yana nan, ban ma rashin hankali irin na ki me Captain zai yi da makauniya

A nan sai Hurriya ta kasa hade maganar da Namra ta jefe ta da ita.

 Zan kiyaye, ni daman ba ni nake mishi magana ba ni babu wata alaka a tsakanina da shi, wata kila ba ki fahimta ba ne, zancen makanta kuma wannan ba da ni kike ba, da mahallice ma kike ke ma kuma ba ki wuce ya dora miki ba

 Idan be dora min ba, ke ai zai ki zo ki dora min shashasha kawai

Taja tsaki sannan ta ja kofar dakin ta rufe da karfi. Hurriya ta ja dogon numfashi ta sauke.

 A haka Amma kike cewa ba zaki dawo ba? Haka zan yi ta zama a gidan nan ina ganin wulakanci kala kala? Idan wannan ya wuce wani zai zo? Tun da kika bar gidan nan ban sake farinciki ba, na koma kamar wata bare kowa taka ni yake yadda ya so

Ta share hawayenta, ta sake daukar takardar ta karanta, this time around sai ta ji karatun be mata dadi ba kamar dazun ya manta da ita damuwarta ya sauya shafin bakincikin zuwa fari ba, mikewa ta yi tsaye ta nufi gurin da wadacan takardun da ya bata suke ta saka wannan a ciki. Sannan ta dawo ta sauke kayan daga kan gadon ta jerasu a closet dinta ta dawo ta kwanta saman gadon feeling so boring ba tare da dalili ba.




A WEEK LATER.....

Khairy ta cije baki tana jin kamar ta buga wayar a kasa kuma babu dama.

 Haba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login