Showing 270001 words to 273000 words out of 279257 words

Chapter 91 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34641

ran sa yayi nisa kadan ya rage masa, i never give up na dauke shi daga wannan asibitin zuwa asibitin dake cikin garin sokoto wato asibitin anan suka karbe shi suka yi iya abun da za su iya kuma aka yi nasara numfashinsa ya dawo, sai dai sun fada mana abun ya taba kwakwalwarsa, da ya fara jin sauki sai ya zama be bude ido be cewa komai baya motsi numfashin ne kawai a duk tsawon lokacin nan yana karkashin kulawata ne, ni da kaina na nemi Salim ya taimaka min na je da yaro a kasar da mahaifiyarsa take, saboda mahaifinsa dan garin gusau ne, dan Sarauta Family's, sai dai mahaifiyarsa yar kasar Ethiopia ce aiki ya kai mahaifinsa a can ya aure suka haifi Salim da Ziaw sai suka rabu ya dawo nan Nigeria tare da Salim ya bar nata Ziaw a can wannan dalilin ne ya saka ke kiran Salim da Ethiopian saboda yana zuwa gurin mahaifiyarsa sosai yana zama a gurinta, be musa min ba ya amince sai na nemi transfer daga asibitin zuwa asibitin Medical Center Hayat MCM, saboda ina tunanin duk wanda zai saka ayi ma karamin yaro kamar Hamad haka zai iya kashe shi idan ya san yana raye, kuma gashi mu ba mu da full evidence na wanda ya aikata hakan balle mu kama shi, tun da ba mutanen aka kama ba gawarsa kawai aka samu, ko ba komai a can kasar zai fi samun kulawa fiye da nan, da Salim muka shirya komai bayan na fada masa halin da ake ciki shi kuma ya sanar da mahaifiyarsa sai ta yi mana duk abun da ya kamata muna isa aka karbeshi a asibitin, kuma sai aka yi sa'a yana ta samun sauki, sai dai hankalinsa ya tabu ya kan yi wasu abubuwan masara dadi yana yawan firgita da kiran sunayen Iyayensa sai likitocin suka tabbatar min da cewar matukar ba a sama masa abun da yake so ba zai iya haukacewa kuma zai yi wahalar warkewa, wannan dalilin ya saka idan na kai masa ziyara ko Ziaw take ko Mahaifiyar Salim mu kan cusa mata cewar bashi da kowa, na kan ce baka da kowa Hamad kai kadai yake rayuwa ko bachi yake idan na fada masa haka sai ya zabura, na fada masa kowa naka ya mutu a yanzu mu wasu Iyalin ne da ka samu wadanda ba ka sani ba, a haka sai da Hamad ya kwashe shekara daya a asibitin sannan ya ji sauki har suka sallame mu, sai na kai shi a gidansu Salim a gidan ya fara rayuwa kuma ya rayu da karyar dana cusa masa cewar ba shi da kowa

Captain yayi shiru yana jan numfashi kamin ya cigaba.

 Be cika damuwa ya bani labari ko yayi hirar rayuwarsa ta baya ba, wata kila saboda na riga na fada masa cewar ya rasa kowa ba, wata rana ya taba tambaya ya aka yi ya rasa kowa sai na fada masa, yadda na tsince shi, kuma a lokacin da yake nan asibiti ma nemi iyayensa sai na samu bakincikin rashinsa ya kashe su, sai ya tambaye ni ina da wata wata yar'uwa Hurriya ita baka ganta ba? Haka ne Hamad...?

Captain ya tambaya sai Hamad ya daga masa kai yana tuna lokacin.

 Na ce mishi ita ma na yi mata irin yadda aka yi maka, shin kana sha'awar komawa garin da babu kowa sai yace min aa, da haka na samu ya fuskanci rayuwarsa na saka shi makaranta a can, saboda ya fada min lokacin da yayarsa yake raye yana da burin zama likitan ido saboda ita, na karfafa masa guiwar yin karatun saboda ya cika burinsa, har kai inda yake a yanzu, a lokacin da ya gama high school sai na nema masa makaranta a kasar kuma muka nemi bangaren da yake aka ba mu, saboda sun yaba da hazakarsa, a yau Hamad yana cikin best students na makaranta mai su kwazo da maida hankali, na taba daukar hotunan Hurriya na tafi da su na zimmar nuna masa sai kuma na kasa hakan, saboda ban san ta yadda zan amsa masa tambayar da zai min ba, kuma a lokacin ba ni da kakkafar alaka da ku kamar haka, kuma na san mahaifiyarsa ba zata iya daukar wani mataki ba, tun da ga Hurriya ma a lokacin ana musguna mata babu wanda yace komai na san wanda ta aikata wannan zata samu wanke kanta cikin ruwan sanyi ko ma ta sake kashe shi

Captain yayi murmushi yana tuna bawa.

 Na bawa Hamad labarin sabuwar budurwar da na yi, har nace mishi ya dauketa a matsayin yayarsa sai ya ba ni abun hannu a matsayin kyauta kuma na kawo miki Hurriya gashi nan a hannunki

Hurriya ta kalli abun hannun ta kalli Hamad Hamad ma ya kalli abun hannun da ya taba bawa Captain.

 Ta yadda zan juyar da karyar da na yi ta zama gaskiya ne abu mai wahala a gareni, shiyasa na bar abun a haka har zuwa lokacin da gaskiya zata yi halinta, kuma wannan ne dalilin da ya saka na zabi zuwa Ethiopia aikin idon Hurriya fiye da ko wace kasar, lokacin da na yi wacan lafiyar tare da Salim muka tafi a lokacin ya gane ina son Hurriya hakan yasa har yanzu nake kyautata zaton shi ya yada hotunan Hurriya a kafofin sada zumunta, kuma zatona ya tabbata domin hacking din da na saka ka yi min da kuma bincike sirrin wanda na saka aikin ya fada min haka, sai dai yadda ya samu hotunan ne abun da ya daure min kai, a lokacin da yayi min furucin cewar yana da sauran amfani a gurina sai na saka aka dauke ka daga gidansu aka kama mata masauki a makarantarku saboda gudun kar zuciya ta saka shi ya cutar da kai, na san akwai tsaro a makarantar ta yadda ko da ya aikata maka hakan za gane ko waye...

Sai a lokacin Hamad ya gane dalilin? Captain na maida shi hostel din makarantar da yayi.?

 Wata kila ya samu hotunan ne ta hanyar Adam

Hurriya ta fada, Captain ya daga mata kai.

 Ni ma haka nake zato, ko da sanin Adam ko kuma a sirrance domin dan'uwansa zai iya fada masa matsalarsa shi kuma kishi da haddasar ni na same ki ba shi ba ya saka shi aikata hakan....

Amma ta share hawayenta tana taba Hamad dake zaune kusa da ita yan biyu suna zaune a cinyarsa.

 Na dauka da gaske Hamad ya mutu, na karbi wannan kaddarar amman Hurriya ta ki ta karbi wannan

Hamad ya kalli Hurriya ta kalleshi. Captaim ya ce.

 Ya taba fada min cewar Yana fada yawan fada da yar'uwarsa yanzu kuma yana son neman lafiyarta kuma gashi bata nan...

Suka yi Murmushi. Yasir? ne mutum na farko da ya fara mikewa tsaye ya fice daga falon. Sai da ya dauki lokaci sannan Rukayya ta bayansa. Gingine ta same shi jikin motarsa ya rike kansa ya rasa me ke masa dadi a duniyar nan.

 Yasir...

Ya dago ya kalleta sai ya kawar da idonsa.

 Minene Rukayya?

 Ya kake?

 Lafiya kalau

 Dan Allah karka boye min ya kake?

Da ya dube ta sai ya ga hawaye take zubarwa shi ma sai na shi hawayen dake makale suka zubo.

 Ban sani ba, ko za su zabi kai Hajiya gidan yare ko akasin haka, amman ba zan iya zama garin nan matukar mahaifiyata ta kasance a gidan yari, ba ni da sauran farinciki a yanzu. I respect your parents decision da suka hanani aurenki suna da gaskiya

 Yasir shin har yanzu kana so na?

Ya dubeta da kyau sai yayi murmushi ya dago wayarsa ya nuna mata hotonsa da yake a screen din wayar, sannan ya sauke ya tafi ya bar a gurin tsaye. Amma da yan'uwanta suka koma bangarensu suna tattauna abun da ya dace Appa ma yana tattauna da nasa yan'uwan. Captain kuma ya fito yana magana da Hurriya, so yake ya dauketa su je family house dinsu su ganta even though Magariba ta gabato, ita kuma tana son kasancewa da yan'uwanta a yanzu.

 Idan mun tafi can Nene zata iya cewa na kwana a can ai ko?

 Ya za'ayi tace miki haka bayan kuma ta san kina da MiJinki?

Ya duba yaga babu mai ganinsu sai ya kama fuskarta yana kallon kwayar idonta.

 Alhamdulillah you can see now my baby my heart my soul my duniyata

Ta yunkura zata yi dariya sai amai ya cika mata baki, da sauri ta ja baya ta juya ta fara kwarara amai a gurin kamar zata amayar da yan hanjinsa. Captain ya shiga cikin ya dauko mata ruwa ya wanke mata bakinta sai da yayi d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a gaske sannan ya iya danne zuciyarsa domin shi ma aman ya ji yana taso masa. Ya taba jikinta.

 Sannu kina jin rashin lafiya ne?

 Aa amman kai jikinka da zafi, ko zaka tafi asibiti ne?

 Maybe gobe, amman ba yau ba dare yayi, ki shiga ciki ki huta gobe zan tafi na kai ki gurin su Nene

 Toh.. Sai da safe..

Har ta juya sai ta ji an riko hannunta an dawo da ita.

 Hurry na.. Me kika ci ya saka ki aman nan? Me yasa kika yi amai?

 Ban sani ba

Ta dan yamutsa fuska.

 Turarenka nan ne bana so yanzu

Yayi murmushi ya rika hannunta ya nufi gurin motarsa.

 Me ye ina zamu je?

 Asibiti

 Babu asibiti da yamma fa..

 Ta barrack zamu tafi likotocinsu kullum available

 To ai ni lafiyata kalau

 Ni zaki raka

Ya bude motar ya saka ya zagaya ta dayan bangaren ya shiga yayi ma motar key. Sannan ya kama hannunta daya ya rike yana tuka motar.

 Ban a kwashe aman ba, idan wani ya gani zai ji kazanta

 Idan mun dawo sai ki fada a kwashe

Be tsaya ko'ina ba sai asbitinsu na Barrack yana zuwa aka hau yi mata gwaje gwaje mamaki ya hana ta magana bayan kuma yace shi zata raka, ba ayi taru ba sai a gurin da za a debi jininta a auna, nan kam sai da ya zauna a kujera ya rumgume da karfe ya rike hannun sannan aka dibi jinin. A nan ya barta ya tafi yayi sallah ya dawo sannan ya karbi results. Be bude ba sai da suka isa gurin mota yana karantawa yana murmushi.

 Me suka ce? Ka shafa min rashin lafiya ko? Kai ne fa mai ciwo

 Baby na kin dai shafa min laulayi

Ya kashe mata ido daya, sai ta yi fuskar rashin fahimta.

 Ban gane ba?

 Minene Albarka aure?

Ta dan yi shiru...

 Kwanciyar hankali da zaman lafiya

Ya daga kansa sama yayi dariya sannan ya jata jikinaa ya rumgume yana jin wani irin kaunarta a ransa.

 Silly Girl, albarka aure haihuwa


Ta dago da sauri ta kalleshi tana kwalo ido baki sake, sai ya daga mata kai ya sumbaci goshinta.

 Uhmmm

Ya shiga sumbantar fuskarta ta ko'ina, kamar ba a public place suke ba, he just got lucky inda suke babu kowa gurin aje motoci ne kuma ko akwai bariki babu ruwan kowa da rayuwar kowa.

Ya bude Mota ya saka matarsa sai da ya sumbanci hannunta sannan ya rufe motar ya zagaya dayan side din ya shiga ya sake sumbantar ya kama hannunta ya rike yana tuka motar.
Wani irin farinciki yake ji marar misaltuwa a zuciyarsa, be taba tunanin haka ake ji ba idan mace tana dauke da cikin an mijinta sai yau, baya iya bayyana yadda yake ji a zuciyarsa son matarsa ya ninku a ruhinsa.

 Ki kula da kanki please

Ya fada a lokacin da ya bude mota ta fito. Ya waiga ya ga idan babu mai kallonsu sannan ya juyo ya rumgumeta ya sumbanci goshinta. Ya kama fuskarta ya aika mata da wani killer look.

 I Love You so much sanyin idanuwana, thank you for this

Ya taba cikinta. Hawaye ya zubo idonta ita kanta she can't believe ciki ne a jikinta so she's going to be a Mother now..

 Ni ya kamata na gode maka, you came in to my life by accident sai kuma ka zama cikar farincikina, abokin rayuwata, silar share hawayena, ka min alkawarin kyakkyawar duniya mai ciki da farinciki kuma ka fara va ni tun a yanzu... Buri yana ta cika saboda kana kusa da ni, ina matukar kaunarka Jamal duk mace da ta samu namiji irinka a matsayin miji hakika ta dace da Abokin Rayuwa na gari mai son farincikinta, kai din wata babbar kyauta ce da Allah yayi min ta inda ban yi zato ba kuma a lokacin da ban yi zato ba...

He weep her tears yana murmushi ya sumbanci bakinta ya latsa kasan lips din.

 My cute Baby my happiness, anything for this Girl

Ta yi murmushi ta sauke hannunsa kasa.

 Kar wani ya gan mu fa...

 Zaki kwana gidan nan ne just for today, i can't wait na bude ido gobe na gan ni a kusa da ke, i love you

Zata amsa masa da i love you too Hindu da Inna Uwani suka fito, sai ta yi saurin juyawa daga fuskantarsa da take ta kallesu.

 Hurriya ke kika yi amai dazun? Twin yace mana ga aman nan a waje Rukayya ta kwashe kuma sai ba mu ganku ba..

 Eh Captain ne yayi ba shi da lafiya tun a gida shi ne yau sai yayi amai, yanzu ma na raka shi asibiti ne aka ce malaria ce take damunsa

Captain ya kalleta da sauri, jin yadda ta daure shi a take tace shi yayi mai kuma shi ta raka asibiti.

 Subhanallahi... Jamal babu lafiya?

Hindu ta tambaya, sai dan yi shiru kamar wanda ya rasa me zai ce.

 Eh...... Amman da sauki asibiti muka fito yanzu suka ce Hurriya...

Ta kalleshi da sauri tana zare masa ido. Sai ya sauya maganar daman yayi haka ne kawai saboda ya tsorata shi ba zai iya fadar tana da ciki ba a gurin yan'uwanta.

 Sai suka ce ma Hurriya ina dauke da malaria

Ta daga mishi kai alamar haka ne daidai.

 Sannu har da gajiya ai, kana kokari sosai Wallahi....

 Na gode zan tafi sai da safe...

Ya musu sallama ya bude Motarsa ya shiga yana jin zazzabin da Hurriya ta kira masa yana kara rufe shi. Hindu da Inna Uwani suka nufi gate Hurriya kuma ta shiga bangaren mahaifiyarta tana jin komai kamar ba gaske ba. Ta daga kai tana kallon bangaren bayyana yadda farinciki yake a gurinta yanzu abu mai wahala, mahaifiyarta ta dawo a karkashin inuwar mahaifinta a yayinda ita kuma take karkashin kulawar nata mijin, ga dan'uwanta a kusa da ita. To yanzu me ya rage mata? Mai hakuri mawadaci wahala ko bakinciki basa taba daurewa a rayuwa, haka ma dade da farinciki basa dauwama har abada, sai an bude ko wane shafi na rayuwa... Ta shafa cikinta tana murmushi ta samu amincewar ubangiji zata iya ganin abun da ta haifa nan gaba. Jin kukan Rukkaya ne ya kawar mata da duk wani tunani da take a lokacin sai ta yi hanzarin shiga cikin falon dake dauke da mahaifiyarta, Gwaggo da kuma Rukayya.

 Ashe baki da hankali har yanzu? Ke yanzu duk wannan abun da ya faru har sha'awar auren Yasir kike...

 Allah yana fitar da mai kyau daga mummuna gwaggo kuma yana fitar da mummuna daga mai kyau, ni ban ce sai na auri Yasir ba, ban zan iya auren mutumen da zuciyarku bata gamsu da shi ba, amman dai na sani farinciki ko wane a yana tare da uwarsa, idan aka kai Hajiya Gidan yari, Yasir ba zai sake farinciki ba, ni kuma nawa farinciki yana tare da Yasir, dan Allah Yaya Iyami karki saka a rufe ta Allah ya riga ya gama miki komai...

Tassss Gwaggo ta wanke fuskar Rukayya da mari.

 Ke yanzu soyayya har ta isa ta rufe idonki ki ce kar a hukunta Kaltume akan abun da ta yi?

Amma ta bata rai sosai tana kallon Gwaggo da alamar dake nuna bata jidadin marin da Gwaggo ta yi ma kanwarta ba.

 Da baki mareta ba Gwaggo, soyayya babu abun da bata sakawa, idan har so zai rufe idon mutum kamar Jamal ya yarda da Hurriya ya aureta a lokacin da take cikin tsananin rayuwa da damuwa, me zai hana so ya rufe idon Rukayya? Kuma gaskiya ta fada, ni Allah ya gama min komai daman idan mutum ya cutar da kai karka ce sai ka rama kawai ka bar shi da Allah sakamakon da yake zuwa daga gurin Ubangiji ga azzaluman mutane mai tsanani ne, irin wanda ruhi baya iya jurewa. Kuma Yasir ya cancanci ko wace kalar alfarma a gurina ko a gurin yayana, yana da kirki be taba nuna min banbanci da mahaifiyarsa ba ko sau daya...

 Ko ma dai minene ba za a kyale ta ba, tun da na gane hankalinki da nata ya zama iri daya

 Daman maganar ba a gurinmu take ba, tana gurin jami'an tsaro ne sai yadda suka yanke..

Gwaggo ta ja tsaki tana jin haushin yadda Amma take da sanyi a wannan bangaren. Hurriya ta karasa ta zauna a kusa da Rukayya tana bata hakuri.

 Barta ta yi ta kukan, ta dade bata mutu ba yara ba su da kunya soyayya na rufe musu ido su kasa ganin daidai

Cewar Gwaggo cikin tsawa. Hurriya dai bata ce komai ba ya ta tashi ta fice daga falon zuwa bangaren Hajiya Kaltume a nan ta samu kofar falon a bude bata yi tunanin babu kowa a ciki ba sai da ta shiga, tun ranar da yan'uwan Hajiya Kaltume suka tafi da ita suka tafi tare da Khairy da Ruma. Yayanta ta gani zaune ya hade kai da guiwa yayi shiru gwanin tausayi. Ta matsa kusa da shi ta zauna a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login