Showing 141001 words to 144000 words out of 279257 words

Chapter 48 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34720

fa a yanzu, ita kanta Iyami waya sani ko ta ji sauki ma zata iya bibiyata ga Nafisa ma, ga wannan sabuwar matar da Alhaji ya dauko maganar, tun da fata suke su shigo gida su mallake komai, ga wannan malamin ma yanzu idan ya fahimci bana son aikinsa zai iya bibiyata fa...

Khairy ce ta leko dakin ita kam nata jikin a sanyi ruwa, alamar ruwan sama ya fara dukanta kamin ta dawo gidan.

 Hajiya magana kike yi? Kofar dakinki na gani a bude da na matso kuma sai na ji kamar kina magana

Hajiya ta kalleta ta sauke ajiyar zuciya.

 Shigo

Ta shigo kamar yadda mahaifiyarta ta bukata.

 Ina kika je tun dazu? Gaba daya yau ba gida kika wuni ba, Yayanki ya shigo dazun yana ta min masifa wai ina barin kina fita any how ba tare da na san inda zaki je ba

 Dan Allah ki daina biyewa Yaya Hajiya, shi fa gaba daya rayuwarsa matsala ce, irin yadda yake son ya rika mana an wuce wannan yanzu how old I'm da zai ce a rika saka min irin dokokin nan! Kuma ma gidansu Habiba na tafi tare da Hurriya

 Hurriya kuma? Kika tafi da ita ko kuma ya?

 Da ita na tafi, yanzu muka dawo na ajeta a bangaren Momy

 Ni fa ban gane miki ba Khairy, wani sabon kawance ko kauna ce kika dauka kina yi ma Hurriya yanzu? Yarinyarda ita da uwarta bana da makiya kamar su? Ko kin manta halin da uwarta ta saka ni? Oh hudubar yayanki ce kika dauka kika bar tawa ko?

 Aa Wallahi Hajiya, ba dan wani abu ba da sai na ce miki na fiki tsanar Hurriya da mahaifiyarta fiye da ke ma, amman ya kamata komai zamu yi, mu yi shi cikin hikima da wayo, ta haka ne ma zamu rika sanin wasu abubuwan

 Karki kuskura ki ce zaki nuna min kin fini wayo, daga haka ban san iya abun da zai biyo baya ba, ga yayanki nan ya dauko zancen auren Rukayya gaba daya su kuke ku haukata ni na ga alama

 Aureta kuma?

Khairy ta tofar da yawu.

 Wallahi ba zamu tana yarda Yaya ya dauko mana wannan bakin jini ya kawo mana ba, tab....! An gama da yayarta ita kuma a dora da ita, ga yarta ma ba a gama da ita ba? Kara ma Amma da wannan Rukayyar kana ganinta kaga marar kunya, wato ba su hankaltu ba da har za su dauko wasu Rukayya su aurawa Yaya?

 Mai kwadayi kuma? Suna ganin sun samu a gurin Iyami ita ma ai suna saka ran samu a gurinta ne

 Amman shi Yaya har idonsa yayi rufewar da zai rasa matar aure sai Rukayya? Kamar be san alakarta da Iyami ba?

 Ai ni da Iyami daya yake kallonmu, amman matukar ina raye, wannan abun ba zai taba faruwa ba, gashi nan duk saboda Iyami abubuwan sun zo min ta yadda ban zata ba, dan kyaun nan ke janzu ba komai ba

 Shi ne fa, gaskiya ko kin kyale ni ba zan kyale ba Wallahi

Maganar take tana cika da batsewa gaba daya maganar ma ta bata mata rai.

 Allah kadai ya san sherin da suke bibiyata da shi, ko dan ma a samu sa'a ta ai zata iya aura masa ita, a mallake shi a juya shi yadda ake so, idan aka gama ruwan nan ki shiga ki kira min Hurriya

 Toh, amman Hajiya ki ja masa kunne gaskiya ba zai auri Rukayya ba

 Sha kurumin ki, idan kin shiga kiranta ma ki faki idon Nafisa ki kira min Kulu

Ta latsa kafarta tana runtse.

 Ciwo kika ji?

 Ture ni aka yi Wallahi

 Turewa kuma?

 Eh mana, ai ba faduwa ce haka nan ba, wannan ne karo na biyu, nan gaba ban san ina aka dosa ba kuma

 Ikon Allah

Hajiya ta amsa mata.

 Ikon gaskiya, na fi karfin kowa nan gani nan bari sai gani sai hange, kowaye ba zai iya da ni ba Wallahi

Khairy ta dan yi dariya yadda Hajiya take maganar da fada kamar wanda yayi mata hakan yana gabanta. Kamin ta mike tsaye ta fice daga dakin.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 27

HURRIYA POV.

 Assalamu Alaikum Warahamatullah
Assalamu Alaikum Warahamatullah

Ta sallame sallah magariba ta karo da azkar din sallah, sannan ta daga hannunta ta yi addu'a kusan rabin kowace addu'arta Amma ce, burinta Allah ya bata lafiya ta tare kamar da, sauran addu'o'in bukatu na rayuwa suna biyo baya ne bayan ta yi ma mahaifinta. Daf da zata shafa addu'ar Namra ta shigo dakin, saman gadonta ta jefa mata ledar dake hannunta kana ganinta kasan Hurriya ta shigar mata hanci da yawa.

 Na gaji da ajiyar wayar nan, idan ma baki bukata ki jefar ko ki kyautar, bana bukatar wani abu naki ko na Salim

Ta juya tana jan kofar dakin da karfe Kamar zata ballata. Hurriya ta juya ta kalli ledar sannan ta mike tsaye ta nade carpet din ta zauna a bakin gadonta ta dauki ledar tana dubawa. Babbar waya ce har da sabon line da chocolate sai turare mai kamshi. Komai sai da ta bude ta gani musamman ma wayar da take jin kamar ta yi amfani da ita, sai dai tana tsoron kar Yayanta yayi magana domin bata taba rike waya ba, kuma kowa zai tambaye ta ina ta samu, idan ta amsa da cewar Salim ya bata za a tambaye ta miye alakarta da shi, to me zata ce? Wannan tunanin ne ya saka ta maida wayar a ledar ta cire chocolate din da turare ta janyo kwalin da Adam ya bata ta saka wayar a ciki, turaren kuma ta dora a mirror tare da sauran turarukanta da suke gurin. Sannan ta hau gado ta dauki chocolate ta fasa ta fara ci tana lumshe ido, daman ta san dadinsa domin Appa na siya mata lokacin da Amma take gidan, Amma ma da kanta takan siya mata ko ta bata kudi ta siya wani lokacin amman ban da wannan lokacin da komai ya canja. Knocked din kofar dakin aka yi, ta tashi da sauri tana cin chocolate din, kamar zata tambaya ta ce waye sai kuma wata zuciyar tace tashi ki duba mana, ta sauka saman gadon ta nufi kofar ta bude, Khairy ce tsaye tana lasa wayarta suna hada ido ta sakar mata murmushi ta kunno kai cikin dakin.

 Hurriya ruwa be saka ki zazzabi ba?

 Aa

Ta juyo tana amsa mata. Khairy ta kalli bakinta da hannunta.

 Me kike ci?

 Chocolate

 Eyyyy yar gayu, wannan mutumen da na gani a falo ya kawo miki?

Tambayarta take irin tambayar nan mai halshen damo, tana wani murmushi ta kalailaye ido ita ga mai wayo. Ita kam Hurriya sai ta ji cewar ta samu mafita ai daman bata san ya amsawa mata ga wanda ya bata ba dan haka ta amsa mata da.

 Eh shi ya ba ni

Khairy ta kama hannunta suka zauna bakin gado.

 Ba ni labari shi ma sonki yake?

 Aa ni aa
????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ?
 To ai kin san ke din mai kyau ce ga farinjini, tsaraba ce?

 Haka nan dai ya ba mu

Hurriya ta amsa tana jin kanta guilty saboda ta yi karya, abun da ba halinta ba.

 Dan'uwan Momy ne ko, ina yawan ganinshi ai ance dan yayanta ne

 Eh

Ta amsa tana daukar dayan chocolate din ta mika mata, a nan Khairy ta juya ta kalli bayanta, Chocolate ta gani ba daya ba ba biyu ba uku ba zai kai 12 kala dabam dabam kuma duk masu tsada.

 Kin ce ba sonki yake ba, amman ya kawo miki chocolate haka, maybe dai baki son na sani ne ko? Haba Hurriya ki dauke ni kamar kawarki mana, ko da yake dai be kamata na takuraki ba

Ta mike tsaye.

 Daman Hajiya ce ta ce na kiraki

 Ni kuma? Me na yi to?

 Sai kin yi laifi za a kiraki? Haba Hurriya karki ma Hajiya wannan kallon mana

Hurriya ta hade yawu tare da sauran chocolate din dake makoshinta, gabanta ya shiga faduwa ita dai ta san alheri baya sakawa Hajiya Kaltume ta kirata, sai da ta wuce gaba sannan Hurriya ta bi bayanta gaba daya ta saka mata tunani cewar Hajiya Kaltume tana nemanta sai ta fara tunanin ko fitar da suka yi ne a dazun, ko dai wani abun aka shirya mata? Ko Hajiya Binta ta sake yi ma Hajiya Kaltume wata maganar ne? Da tambayoyi kala kala ta sauko stairs din, a daidai lokacin da Captain yake hada takardunsa Namra na saka masa laptop din a jakarta. Sai da ta fara kallon Khairy kamin ya kalli Hurriya dake biye da ita a baya, a shi da alaka ta Hurriya dan haka ba shi da hurumin tambayar ta ina zata je ko kuma da waye take tare. Sai da suka fice sannan ya kalli Namra ya ce.

 Amman wannan yarinyar tana shaye shaye ko?

 Me ka gani?

 Fada min kika yi?

Ya jefa mata bakar magana kamar yadda ya saba.

 Allah ya baka hakuri, tambaya ce kawai

 Ni m amsa na bayar, ke ma idan kika fara yi zan gane

Namra ta yi murmushi tana mamakin yadda yayi saurin ganewa bayan kuma bata fada masa ba.

 Amman ba a tabbatar ba, haka dai ake zargi saboda friends dinta wasu daga ciki suna yi

Be ce mata komai ba ya daga kansa ya kalli Momy ya kalli agogonta.

 Tun dazun ake ta kirana Momy sai gobe idan na dawo

 Zaka dawo

Ta tambaya daga inda ta tsaya ganin kamar yana sauri, ya daga mata kai.

 Kullum zaku rika ganina har na gama watannin da zan yi In Shaa Allah

 Haka nake so, Allah ya taimaka ya maka albarka Jameel

 Ameen

Ya amsa suna hada baki da Namra, sannan ya karbi Laptop dinsa.

 Dauko min wasu kayan da suke dakin Musib

 Okay

Ya fita Momy na binsa da kallo, Namra kuma ta nufi stairs domin dauko masa sauran kayansa. Dan lokaci da ta bata kamin ta kawo masa jakarsa da ipod da agogon daya cire a dazun, har ya fusace ransa gaba daya bace, tana bude kofar falon ya ja motarsa ya barta nan tsaye rike da kayan tana kallonsa.

 Kuma har ka yi fushi?

Ta juya ta koma cikin falon.

 Be karba ba?

Momy ta tambaya tana operating remote ganinta da rike da jakar ga kuma fuska na bayyana labarin zuciya.

 Wata kila cewa zai yi na bata lokaci, wai har yayi fushi

 Ya kamata ki saba, ki lura da duk wasu abubuwan da baya so ki rika kiyayewa, kin ga yanzu hankalinsa ya dawo gidan nan wata kila ma saboda ke ne, kuma kin san halin Captain ba sai an fada miki ba shi da fushi da zuciya da saurin kai hannu ba su da maraba

 Amman Momy wani lokacin abun sa ya kan yi yawa, dauko kaya kawai sai ya zama laifi?

 Toh haka Allah yayi dan'uwanki ya zaki yi? Je ki aje kayan amman make sure kin kira shi a waya kin bashi hakuri

Ta lumshe ido ta bude alamar damuwa.

 Shiyasa ya kasa zama da budurwa, komai aka yi masa bacin rai ne

Momy bata bi ta kanta ba ta cigaba da kallon tv ba. Namra ta yi wuce da kayan ta fara taka stairs.




HURRIYA POV.

Da tsoro ta shiga bangaren na Hajiya Kaltume, da farko ta ji tsoro ganin Yayanta da Salma a falon sai ta yi zaton za ace ta yi wani abun ne, cikin karfin hali ta gaishe shi ta gaishe da Salma, yanayin yadda ya amsa mata ya fahimtar da ita bata da laifi a gurinsa. Khairy ta zauna kusa da shi.

 Wai yau na gaji da yawa, ina yin Sallah Ishan'i zan sha magani na kwanata

Yasir ya dubeta

 Maganin me? Aikin me kika yi kika gaji?

 Pain killer nake son cewa, zan shafa a kafa driving na yi yau mun yi yawa sosai

 Good shiyasa na yi ta shigowa ina ganin kowa ban da ke, ke kawai kin fi son rayuwar waje, ki je yi ta abubuwan da kike so babu mai ce miki uffan, kawaye ma idan an rabaki da wannan gobe da wata za'a ganki? Khairy abun da kike yi fa ba shi da kyau, kuma ina miki fada ne ki gyara ba dan ni kadai ba sai dan ke kanki da future dinki, idan kika dauko wani abun magana ko, mutane za su zageki kuma kimar gidan nan zata zube, amman ke da Hajiya kun kasa gane haka

Salma ta ce.

 An kusa aurar da ita Yaya ka kusa hutawa

 Mtscheeeeee

Tsaki Khairy ta yi ta mike tsaye, ita dai har yanzu ba wani son auren take ba, ganin take gana cikin cin lokacin ta ne za a yanke mata, ko da wani ne balle Fadeel da ke da mata kuma da dukan alamu ba zai dauki irin rayuwar nan ta barin mace ta yi wasu abubuwan da suka tsabawa dokar Musulimci da al'adar Malam Bahaushe ba.

 Hurriya shiga ciki Hajiya na kiranki

 Toh

Hurriya ta nufi stairs din tana jin cewar idan dai ba mahaifinta zata tarar a dakin ba irin wacan karon da aka koreta, to komai mai sauki ne domin zagi da wulakanci na Hajiya Kaltume ta saba da shi dan haka be daga mata hankali. Sai da Hurriya ta haye sama sannan Khairy ta kalli Yayanta cikin sifar magiya da lalama ta ce.

 Yaya dan Allah ka daina irin fadan nan a gaban Hurriya

 Hurriyar bakuwarki ce? Ko kuma ita wata bare ce da ba zan miki fada a gabanta ba? Kuma da kin zama yadda nake so zan miki magana ne? And Salma was right idan an miki aure dole ai ki tsanu, and wannan ya zama na karshe da zaki fita ba tare da kowa ya san gun da zaki tafi ba! Dazun na tambayi Hajiya tace min baki fada mata gurin waye zaki je ba, ki daina wannan dabi'ar tun a yanzu

 Zan daina Yaya ba zan sake fita ba tare da na fada

 Ya fi miki, ai saboda kun samu Appa yana musu sauki ne yanzu, ace kamar baya ne da yake daukar zafi baku isa duk ku yi wannan ba, kuma ko. Yanzu idan kika sake irin haka sai na fasa miki jiki

Ya mike tsaye.

 Yaya, ka yi hakuri dan Allah ba zan sake ba, ko dazun ma fa ba ni kadai na fita ba, tare muka fita da Hurriya ita tace gidan so boring shiyasa muka dan fita ta samu ta sake ita ma

 Ki dai koya mata fitar kike so, shekara nawa tana zaune a gida bata gidan so boring sai a yanzu, ita ma ta fara raina wayon mutane, wata fadawa da zata fita?

 Ita ai bangaren Momy take laifin ba na Hajiya ba ne

 Shiyasa kullum Rukayya ke fadar na kula mata da Hurriya, wani lokacin sai a rasa ta ina ma za'a fara controlling dinku Mtscheeeeee

Ya karasa yana jan saki, Khairy da Salma suka kalli juna a gurin da Yasir yake ambatar sunan Rukayya. Sai dai babu wanda ta isa tace wani abu domin sun san halin yayan na su. Sai da ya fice sannan ya Khairy ta koma kusa da yar'uwarta suka tasa gulmarsa da na Rukkayya.


HURRIYA POV.

Ta shiga dakin na Hajiya da Sallama ta zauna a kasa tana gaisheta, Hajiya Kaltume ta amsa irin amsawar nan kamar ta dole fuska babu yabo ba fallasa, idan ta kalli Hurriya wani kololin bakinciki ke taso mata saboda tuna Iyami da take yi.

 Lafiya Kalau, ya jikin Iyami? 

 Ta ji sauki

 Eh

Ta daure ta kirkiro murmushin ya?e.

 Maa Shaa Allah, haka ake so ai, Allah ya kara rikawa yanzu tana tafiya ko?

 Aa bata tafiya

 Ah ah kuma kika ce ta ji sauki?

Hurriya ta yi shiru idonta da kanta a kasa kana ganinta ka ga natsantsiyar yarinya.

 Tana iya tashi zaune da kanta?

Huriyya ta yi shiru na dakiku kamin ta girgiza kai.

 Ashha dai, Allah yasa jinya ta zama kaffara, ni fa ina son naje na dubata amman ina gudun ka ce na ce, idan kin je dai ki gaisheta

 Toh Hajiya

Hajiya Kaltume ta dauko wayarta ta bude Gallary ta kama hoton wani

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login