Showing 216001 words to 219000 words out of 279257 words

Chapter 73 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34685

kai cike da takaici ya ce.

 Duniya ta lalace, mun zo wani zamani da bayan tarbiyar dole dai muna hadawa da addu'a ga yaranmu, ban da abun zuciya da aikin shaidan miye abun chusa kai da nemana halaka akan me zaka dage sai yarinya ta so ka, bayan hakan be samu ba kuma sai ka ce sai ka nemi lalata rayuwarta? Yanzu ya bata sunansa ya bata nata da bata gidansu ina amfanin haka?

Alhaji Bashir Sarauta ya ce.

 Babu ai na fada masa da abu ne mai kyau da yanzu celebration muke muna murna amman ga abun da ya janyo mana, ita kanta abokiyar shaidancin tasa gashi ita ma ta janyowa kanta ta samu nata kaso

Daddy ya girgiza kai.

 Dole ai zata samu haka ko ma fi, ko bare ka aikatawa haka ai ba zaka ga daidai ba balle kuma yar'uwarka ta jini, sun jefa yarinya a damuwa ba tare da hakki ba

 Shiyasa na zo na baka hakuri kuma na roki yafiyar abubuwan da suka faru, daman aiko sammaci bana nan Iyalina suka yanki ticket suka aiko da sunana, gashi kuma shari'ar ta zame mana biyu, sannan yaron nan gashi babu lafiya, dan Allah ayi hakuri a janye karar nan da Captain ya saka gudun kar mu kara yin abin kunya, domin idan aka ce za'ayi shari'a har wadanda ba su da waya da redio zansu iya jin wannan abun kunyar, wani ma zai iya cewa da kai nake shari'a ranka ya dade ba domin canja labari be da wahala a gurin mutanen mu yanzu...

Daddy yayi jimmmm na dan lokaci, ya sauke dogon numfashi yana nazari, be kai ga yanke hukunci ba ya kalli Captain dake karanta sakon taya murna da Salim ya aiko masa ya ce.

 Captain yanzu meye abun yi me ye shawara, ko da yake ya kamata ace an ji ta bakin mahaifinta ma?

Ya dago kai ya kalli mahaifinsa.

 Daddy zan janye shari'a daman kuma yin haka ba abu ne mai wahala ba, zan yi hakan on one condition Adam zai yi video ya fadawa duniya gaskiya kuma ya roki yafiyar Hurriya if not na zan janye shari'ar nan ba kuma Monday nan zamu shiga Kotu, hakan ne kadai zai wanke Hurriya a idon duniya kuma daman na mata wannan alkawarin

Mahaifiyar Adam din ta dubi Captain ta ce.

 Haba ana wannan matakin be yi tsauri ba? Zai iya bata hakuri a sirrance kuma ya fada mata gaskiya, amman fitowa yayi video yaje viral sai kara lalata lamarinsa ne

 Ita da take mace ya lalata mata rayuwa balle kuma namiji? Da be aikata ba wata kila da duk hakan be faru ba

Yan'uwan Alhaji Bashir ne suka shiga rarrashin Captain ko zai sauko daga wannan hukuncin amman fir yace idan ba haka ba shi ba zai hakura ba. Alhaji Bashir ya dubi Daddy ya ce.

 Ranka ya dade a taimaka a saka baki lamarin nan

Daddy ya nuna Captain.

 Shi ne mijinta, kuma wannan case din a hannunsa yake, ina tunanin a yanzu ko ubanta be kai shi iko da ita ba, kuma ya saukaka muku a haka din ma, ni ban yi zaton zai yi saurin amincewa ba, yin haka zai wanke matarsa daga zargi da zagin da danku ya ja mata, kuma idan ma ba ku aminta yaron ya bada hakuri ta wannan sigar ba ko kotu aka je Kotu zata saka shi ya bada hakuri kuma ya fadawa duniya abun da ya faru, daga karshe kuma ya fuskanci hukunci

Mahaifiyar Adam ya fashe da kuka domin a gurinsu yin abun da Captain ya bukata ma cin mutunci ne da kara zubewar kimarsu. Daddy ya mike tsaye ya kalli Captain

 Ina ganin shi kenan nan ai, idan sun zabi haka sai ku aiko mana da video idan kuma kotun kuka zaba duk daya ne, akwai uzurin da zan yi kamin na bar garin yau zan wuce Kaduna

Captain ya mike tsaye sai suka fice tare da Daddy aka bar Alhaji Bashir Sarauta da matarsa da yan'uwansa da suka rako shi a falon.

 Adam ne ya ja mana wannan wulakanci, ni ban ga dalilin ma da zai sa a nemi janye shari'ar ba a bar shari'ar ba, da abar shi kotu ta koya masa hankali

Cewar daya daga cikin kanen ubansa. Alhaji Bashir ya ce.

 Ba za'ayi haka ba, shi ma ai sai ya wahala kuma ko kotun muka je ba nasara zamu yi, tun da kudi za su zuba kuma su suke da gaskiya

Mahaifiyarsa ta kalleshi.

 Yanzu kenan Alhaji dole Adam sai yayi haka? Babu wani abun da zaka iya yi? Shi Captain ba zai duba abotar dake tsakaninsa da Salim ba?

 Kina kallo Salim din ya tashi ya fice be ma tsaya aka yi magana da sho ba, wata kila sun samu matsala da Captain din akan haka, kuma shi Adam ai ya fada mana cewar Captain ya masa video idan ma ba mu saka ya bada hakurin ba zai iya sakin video kuma ga shari'a a kotu, yara ne idan za su yi abu basa tunani, yadda Alhaji Turaki ya fice ya bar a falon nan ai kin san akwai abun da yake zuciyarsu da jira kawai suke

Cikin kuka Hajiyar ta mike tsaye ta fice daga falon sannan sauran ma suka mike tsaye.

 Alhaji ka tashi mu tafi, babu amfanin zama ai domin ba saurarenmu za su yi ba

Alhaji Bashir ya mike tsaye.

 Zan samu mahaifinta na yi magana da shi, zamu samu mafita a can

Cikin rashin jindadi suka fice daga falon. Dayan falon Daddy ya shigo tare da dansa sai suka samu Ammy zaune tana jiransu, fuskarta a hade kamar ba ita ba.

 Ina tunanin ya kamata kaje ka samu mahaifinta ku yi magana, domin za su iya bi ta can su siye shi da kalamai ya yafe musu, bayan kuma ba su cancanci hakan ba matukar ba su aikata abun da ka umarce su ba

Kamin su zauna Daddy yake fadar haka, Captain ya rausayar da kai

 Okay Daddy

 Daga yin aure matsalar har ta tattara ta dawo mana a gida? Mu miye na mu da za su zo mana a nan?

 Saboda danki ne ya shigar da karar kuma mijinta ne a yanzu, sannan lalama suke bi suna neman yadda za a kashe wutar ne cikin ruwan sanyi

 Idan wani abu ne da ya shafi Hurriya ko mahaifinta kai ya kamata ka yi magana da shi kai tsaye, ba Captain ba yaron da lafiya ma bata wadace shi ba, tare da shi zamu tafi kaduna a yau....

Captain ya kalli Ammy da sauri, Daddy kuma yayi murmushi ya ciro wayarsa yana lasawa.

 Kin kawo shawara mai kyau, haka ya kamata yi tafiyarka Jamal zan yi magana da mahaifinta da kaina

Ya amsa masa da kai sannan ya juya ya fice daga falon.

 Ba zan tafi Kaduna na bar ana ba, ko dai na fasa tafiyar ko kuma ka fada masa ya shirya mu tafi, kuma a fadawa iyayen Hurriya tun da an daura aure a ba mu amaryarmu zata tare

 Wannan hurumin iyayenta ne ba na mu ba, ki je ki same su ku daidaita idan sun saka ranar da ta yi miki shi ke nan, amman dai ki sani duk wani abun na zubar da mutunci ba zan bari ya faru ba

Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya shige bedroom ya barta a falon zaune kunshe da bakincikinta.





Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 45
HAJIYA KALTUME POV.

 Wai ni kam ya ma sunan addu'ar nan da ake idan za a bar gida, wanda aka ce idan ka karanta babu abun da zai same ka har ka je ka dawo?

Hajiya Fatee ta yi shiru alamar nazari tana kokarin tunanin addu'ar amman ta kasa.

 Akwai dai Bismillah a ciki, Bismilah da wani abu a ciki ni ma fa na manta addu'a

 Kin ga da kin rike ai da mun karanta yanzu, mu tafi cikin kwanciyar hankali

 Duk abun da za'ayi fa ba zan samu kwanciyar hankali ba, domin ba mu da shi a yanzu, tafiyar nan dai ta zame mana dole ne kawai, domin ni ma ina son na san lafiyar Malam

 To kin gani, dole a haka zamu daure mu tafi, Allah dai ya kaimu lafiya, amman tashin hankali da nake ciki a yanzu ai ya fi na yan kidnapping

 Babu wanda ya di wani, fatan dai Allah ya kaimu lafiya

Cikin tsoro suka shiga motar ta suka dauki shatarta tun daga tasha direban ya zo gidan Hajiya Fatee ya dauke su. Hajiya Fatee ce mai rike carbi tana ja tana leka lake waje, Hajiya Kaltume kuma shiru take sai da suka iss cikin garin sannan hankalinsu ya kwananta Hajiya Fatee ce ta yi ta nuna ma direban hanyar gidan Malam be sauke su ko'ina ba sai a kofar gidan da yayi baki kirin har wani bangare na ginin ya zube. Hajiya Kaltume ta kalli kawarta.

 Anya akwai lafiya a gidan nan kuwa?

 Ina lafiya kina kallon gida kamar an yi gobara

 Ni ma abun da ya daure min kai kenan, amman dai bari mu shiga cikin gidan mu ji

Hajiya Kaltume ta zagoyo ta gefen da Hajiya Fatee take suka jera suka nufi gidan da kusan ma za'a iya cewa ya zama kango.

 Ke yaushe rabonki da nan?

 Wai ni? Ai tun zuwan da muka yi tare da ke van sake zuwa ba, to me zai kawo ni irin wannan gurin ma sai dole

 Yanzu wai da gaske kike filaye da gonakin da kika ce mutumen nan ya siya miki duk baki ga ko daya ba?

 Ai yarda ce ta kawo haka, ni na yarda da ko ban zo na duba ba na san ba zai cuceni ba

A bakin kofar gidan da aka zagaye da ?aya suka tsaya suna kallon yadda gaba daya gidan yake kone kuma babu alamar ana rayuwa a cikinsa.

 Hajiya wannan gidan da kike gani gobara aka yi, kuma kina kallon gidan ya zan kango babu kowa a ciki

 Amman Hajiya Fatee ni da ke a nan muka san matan malam suna rayuwa?

 Bari mu tambaya, ba mamaki ma ace ya tashi tun da yanzu linkafa ta yi gaba

Juyowa suka yi suka fito daga zauren gidan suka yar tafiya sannan suka isa gida daman makotansa suka yi sallama. Hajiya Fatee ta shiga ciki Kaltume kuma ta tsaya daga waje tana waige waige kamar wanda bata yarda da garin ba.

 Sannu ina kwananku?

 Sannu dai muna lafiya

 Alhamdulillah dan Allah Malam muke tambaya ko ya tashi a nan ne shi da Iyalansa? Mun shiga gidan babu kowa a ciki na ga kamar ma ginin ya fadi

 Ayyah wai Malam? Malam ai yau kwanansa tara da kwanta dama, Malam ai lokaci yayi

Hajiya Fatee ta dora hannunta akan tulun kirjinta ido a waje kamar za su yi magana.

 Malam kike nufin ya rasu?

 Malam ya rasu lokaci yayi, gobara yayi cikin dare wutar ta ci shi ta cinye yaransa biyu kuma bata bar komai da yake gidan ba, amman sauran yaransa da matansa sun fita da rai suna nan lafiya kalau

Hajiya Fatee ta kai zaune tana dafe da kirji.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, na shiga goma na lalace yau kashi na ya bushe, Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Wayyo Allah na ni....

Kuka da ambaton Allah da take ne ya saka Hajiya Kaltume shigowa, sai kuma ta shigo a sa'a, domin ta shigo ne a daidai lokacin da matar take kara radawa Hajiya Fatee cewar.

 Matansa sunan na yamma da mu kadan, a sabon gidansa suke takaba, ai Malam ya kowa ya ji mutuwarsa duk wanda ya zo nan kuma yake mana

 Mutuwa? Malam din ne ya Mutu?

Hajiya Kaltume ta amsa a razane da karfi tana kallon matar dake rike da tabarya tana surfe.

 Yau kwana tara kuwa, gobara aka yi a gidan, komai ya kone, zane wannan na daura sai da aka taimakawa matansa da shi a lokacin da lamarin ya faru

 Shi nan na shiga uku, ni kam ta kare min.... Al'amurra sai kara rinchabe min suke.... Yanzu Malam be tashi tafiya ba sai da wahala ta tunkaro ni gaba da yamma, na shiga uku na lalace

 Ba ke kika shiga uku ba Kaltume ni na shiga uku, wayyo Allah wayyo ni kaina

 Sai hakuri haka mutane suke ta kuka idan suka zo, ai mutuwar Malam ta taba kowa musamman customers dinsa

Hajiya Kaltume ma ta kai kasa ta zauna kusa da kawarta suna kuka kowa da dalilin kukansa kuma da abun da yake yi ma fargaba. Tun matar na ba su magana har ta gaji ta zuba musu ido, domin ko da matansa ne iyakar kuka da bakinciki da za su yi kenan.

 Ku yi hakuri bayin Allah mutuwa ai ta gaji haka shiyasa kullum ake son a shirya mata, Salmanu tashi ka kai su gidan matan Malam

Ta fadawa babban anta, domin kukan da suke ya fara yi mata yawa har makota na lekowa ta katanga wasu kuma na shigo suna kallonsu. Hajiya Fatee ta mike tsaye rike da jakarka ta tana kuka, taku daya ta yi kamin ta yi na biyu wani hudun zuciya da ido ya rufeta ta saki jakar ta fado kan Hajiya Kaltume da ko alamar tashi bata yi ba, domin jikinta ya mutu kamar an mata allurar kasala.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un idan kika mutar min a yanzu ai sai abun ya taru yayi min yawa ku taimaka min jama'a

Matan dake kofar gidan suka karasa shigowa suka rika Hajiya Fatee suka daga ta daga jikin Kaltume, suka shimfidata a kasa wasu suka fara mata fifita matar idan kuma ta tashi da gudunta ta debo ruwa aka kwarawa Hajiya Fatee. Sai gata ta farko tana hakki.

 Malam ya mutu, Malam me yasa ka mutu a yanzu? Asirin an tonu na shiga uku wayyo Allah, Malam ya mutu ya bar ni da wahala wayyo Allah na....

Wani irin shidewa ta yi luuuuuuu jikinta ya sake saki, har sai da matan suka jin tsoron wannan suman nata na biyu, Hajiya Kaltume kuma tana zaune a gurin ta kasa aikata komai sai kuka take kamar ita kadai ta rasa Malam. Ruwan aka sake zuba mata sannan ta farfado tana kallon matan karkarrar dake juya mata tana jin sannun da suke mata kamar a mafarki, fada mata da matar ta yi cewar Malam ya rasu ma sai ta ji abun shi ma kamar mafarki ne ba gaske ba.

 Abun da zai fi akaisu gidan Matan Malam ko kuma a kaita asiri

Wata daga cikin matan dake rike da ita ta fada, Hajiya Kaltume ta kalleta da jajayen idanuwanta ta ce.

 Ina ne gidan

 Daga nan ne yamma kusa da kuka uku, Sslmanu wuce gaba ka kaisu

Yaron da aka kira da Salmanu ya dauki tayarsa da karen kada tayar ya wuce gaba yana zumuncin nuna musu hanya, ganin mutanen daga birni suka zo. Ba dan taimakon Allah da rahmarsa ga bayinsa ba da Hajiya Kaltume bata kai kanta gurin motar da suka shigo ba, domin gaba daya kafafuwan rike mata suka yi, Hajiya Fatee kam sai da aka riko aka saka ta motar idonta sai juyawa yake kamar bata san inda take ba. Yaron ne ya wuce gaba da tayarda yana turawa su kuma suna cikin motar zaune a baya, Hajiya Kaltume ce kadai ke iya kuka a yanzu Hajiya Fatee kam kai kawai take juyawa kamar mai kokarin fita daga hayyacinta, direbansu na biye da su har suka isa katon gidan ginar bolu kana ganin gidan da ba'ayi ma filista ba ka san ba duk kauye ba, ko a kauna sai wanda ya tsaya da kafafuwansa.

 Wai yanzu da gaske Malam ya mutu Hajiya Kaltume? Shikenan Malam yayi tafiyar da babu dawowa? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, shi ke nan ta kare min dari ta hade min da dubu, Wallahi ganin nake kamar ba gaske ko dai mafarki nake Kaltume?

Hajiya Kaltume kam kaddara ta riga fata, bata iya cewa Hajiya Fatee komai a yanzu domin ita ma bata da wannan kwarin guiwar. Hajiya Fatee ta unkura zata fita ta kasa saboda jiki yayi nauyi a zaunen da take ma jiri ke debanta yana zubarwa.

 Dukiyata.... Cikin nan..... Ga Afrah... Indai Malam ya mutu a yanzu Malam be kyau min ba

Direban motar ya juyo ya kalli Hajiya Fatee

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login