Showing 93001 words to 96000 words out of 279257 words

Chapter 32 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34718

lura da yawan zuwan da kike zata iya bata alakarmu, ni kuma bana son haka

 Shi ke nan

Tare suka sauko Masu aikin Momy suka gaishe da bakuwar Hurriya duk da kasancewar ta yarinya ta amsa cikin Ladabi domin bata hadu da su lokacin da ta shigo falon ba, sai yanzu da zata fita.
A karamin gate suka rabu Husna ta nufi babban gate din fita gidan, Hurriya kuma ta nufi bangaren Hajiya Kaltume gabanta na faduwa domin ta san ita kullum mai laifi ce a gurin Hajiya. Cikin tsoro da fargaba ta shiga falon kana kallon idanuwanta dake cikin gilashi zaka san babu kwanciyar hankali a tare da ita. Nesa da Hajiya Kaltume ta tsaya ta risina

 Hajiya ga ni

 Sako ne aka aiko miki, wannan dan iskan yaron da mahaifinki ya rabaki da shi wato baki ji ba ko?

Ta girgiza kai da sauri.

 Wallahi na kyale shi Hajiya, daman ni ban san shi ba sai a bikin Yaya Khairi

 Amman mai gadin daya karbo sakon ai cewa yayi yace ga sakon da yace zai aiko miki nan

 Ban yi da shi zai aiko min da sako ba, Wallahi Allah Hajiya

Khairi ya yamutsa fuska tana jan tsaki.

 Karya kike munafuka, baki hadu da shi a Mall ba, jiya ai sai da kika saka yayi ta min masifa sai da na kai miki waya kuka gaisa, amman yanzu kin wani narke kina rantsuwa kamar gaske, sannu kitse

 Ni ba wani abu zan ce miki ba, zo ki dauki kayanki kamin Mahaifinki ma ya gani ace na hadaku

 Ko dai yayi mistake ne, Wallahi ban yi da shi za a kawo min komai ba, Hajiya ki yarda da ni

Khairi ta taba hannu.

 Yau ina Yaya yake ya zo ya ga abun da salihar nan take aikatawa ana ganin kamar sai mu kadai ne zamu aikata, gashi nan kin aikata fiye da na mu ma

Hawaye ya fara saukowa Hurriya jikinta ya hau rawa, domin bata san yadda zata wanke kanta ba idan maganar ta kai ga Yayanta ko Appanta da take tsoro yanzu kamar mutuwa.

 Yaya Namra ma tana tsaye a gurin a kira ta a tambayeta

Hajiya ta tabe baki.

 Ita da Yasir ai ko rai kika kashe ba zasu fada ba, saboda kin iya kirsa da munafurci da kalailayar mai rai kin bi kin lafe a jikinsu uwa macijiya, ni ba wani abun zan fada ba dauki kayanki ki tafi

 Aa ni ba nawa ba ne

 Daukar shi ne rufin asirinki Malam domin Wallahi idan baki dauka ba, Yaya na shigowa zan nuna masa su

Hurriya ta mike tsaye ta iso gurin ta saka hannu ta dauki kwaton kwalin da aka yi ma kwalliya aka rubuta. From Adam to Hurriya in stylish way. Kuka be kamata ba sai da ta fita daga bangaren na Hajiya Kaltume sai ta zauna a balcony ta fara kuka marar sauti saboda ta san daukar ma zai zame mata laifi ne. Ta yi minti talatin a gurin sannan ta tashi ta nufi bangaren Momy, a bude ta samu kofar falon, a lokacin da ta shiga babu kowa a cikin falon, sai ta maida kofar ta rufe, ta nufi stairs tana jin kamar ace Adam din yana kusa da ita ya yakuta masa fuska ta yaga tufafinsa ta watsa masa ruwa da yawu a jiki da fuska, tana tunanin haka ne iya karshen wulakanci. Maida kofar dakinta ta yi ta rufe ta zauna bakin kofar ta fashe da kuka kuka sosai mai sauti, domin gaba daya ta rasa ma ya zata yi, ta kira Yayanta ta fada masa kamin Hajiya ko Khairi su fada masa ko kuma ta samu Appa da kanta ta yi masa bayani, ko kuma dai ta zauna a gurin har sai an nemeta. Sai da ta ci kukanta ta koshi sannan ta a ga daga ta tura kwalin karkashin gadonta bata ma tsaya duba meye a cikinta. Ta shiga bathroom ta wanke fuskarsa ta fito ta kwanta saman gadonta, ana daf da kiran sallah Magariba Momy da Khairi suka dawo gidan, ita dai tana dakinta bata leko ba, abun duniya ya isheta, saurare kawai take ta ji an aiko cewar Appa ko Yayanta yana kiranta.
Immediately after gama Sallah Magariba tana zaune saman carpet din da ta yi sallah, Namra ta turo kofar dakin ta shigo cikin yanayin damuwa.

 Hurriya wa kika bari ya shiga dakin Momy da nawa?

Hurriya ta dago ta dubeta ta cikin gilashinta.

 Babu wanda ya shiga

 Tuna dai ko wani shiga?

 Babu wanda ya shiga Yaya Namra me ya faru?

Kamin Namra ta amsa mata Momy ta shigo dakin a kufule fuska kamar bakin hadari, ta nufi wardrobe dinta ta fara watsa tufafi tana zubarwa a kasa, kamin ta juyo ta yi gurin gadonta ta daga Bedsheet din, sai kuma ta juyo ta kalli Namra.

 Ke sauka ki kira min masu aikin nan

Namra da rashin jindadin abun da Momy take yi ya bayyana a fuskarta ta ce.

 Momy dan Allah mu bi abun nan a hankali

 Zaki sauka ki kira su ko sai na bata miki rai?

Namra ta juya da sauri, domin ta fi kowa sanin yadda Momy take idan ranta ya bace. Hurriya dai na zaune a gurin da ta yi Sallah faduwar gabanta a yanzu ya fi na kallum, duk wani sake sake da take a ranta na dalilin shigowar Momy a dakin da kuma tambayar da Namra take mata be kawo mata cewar zarginta ake da abun da bata taba aikatawa ba ko a mafarki, har sai da masu aikin har uku suka shigo dakin.

 Ku bincika min ko'ina na dakin nan, ku duba min sarkar Namra da tawa da kuma kudin

Hurriya ta mike tsaye da sauri irin mikewar nan kamar wanda aka lakawa wutar nepa.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, ni kuma? Momy ni...? Momy ban taba ba, Wallahi ban dauka ba, Momy ban zan miki haka ba

 To waya aikata? Da zan fita waye na bari a bangaren? Waya shigo ya dauka?

Hawaye ya fara mata zuba.

 Ban sani ba Wallahi amman ban dauka ba, ban taba sata ba Momy ko tsintuwa ban taba yi ba, balle har na shiga dakinki na dauki kudi ko sarkar zinari, dan Allah karku min haka, idan baku son zama na a gidan nan ku kure ni amman dan Allah karku laka min abun da ban yi ba

Namra ta ta yi saurin rika Hurriya dake kuka kamar zata narke.

 Momy da dai an zafafa bincike Hurriya bata taba daukar abu ba, kuma a jininmu babu barawo

 To waya dauka? Shekarata nawa da masu aikin nan balle har ace su suka yi

 Haba Momy taya zaki shaidi bari ki bar na gida, Wallahi Hurriya ba zata dauka ba

 Ke fice ki ba ni guri, ba ke da bakinki kika fada min Hurriya ta tambaye ki kudi ba? Kuma su ma sai na saka an duba dakunansu ai sai an bincika ko'ina na gidan nan

 Eh amman bana jin Hurriya zata aikata haka Wallahi, kuma wannan ai na dabam ne, a maganar da na yi miki na ni na fi zaton ko zata siye anko ne ko wani abu dabam

Momy ta watsawa Namra wata kalar harara da ke karantar da ita ranta yayi kololuwar baci, ita kuma zata iya bata nata rai a take. Ganin haka ya saka Namra sauka ta kira masu aikin, Momy na tsaye aka fara binciken dakin Hurriya tana ta kuka, sai da aka daga komai aka bincike har kwalin da Adam ya kawo mata sai da aka bude ba aga kudi ko sarka ba.

 Wato har da soyayya kike da wani a boye ko?

 Aa aa aa sako ya kawo min, na je bangaren Hajiya na karbo kuma ban san zai aiko da sakon ba

Ta amsa daker tana kuka sosai.

 Oh to ke kika bar min kofar daki a bude kenan aka dauka min sata, ko kuma kika sata

 Na ga kofar a bude lokacin da na dawo kuma ban ga kowa a falon ba, amman Wallahi ban dauka ba

Still Momy bata yarda da ita ba saboda tana ganin ita ma ai talaka ce kuma mabukaciya saboda halin da Amma take ciki, kuma gashi Appa ya daina kula da ita.

*I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaWar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah...!*

Yadda Momy ta saka aka bincike dakin Hurriya haka ta saka aka bincike, dakunan masu aikinta, a nan ma ba a samu sarka ba, ba a samu kudi ba. Daga nan kuma sai labari ya canja Momy ta fara zargi ko Hajiya Kaltume ce ta aiko aka shigar mata daki saboda ta aiko kiran Hurriya, a karfin hali da nuna isa irin na Momy ta aika da masu aikinta kai tsaye a bangaren Hajiya Kaltume wai su bincike mata komai na bangaren saboda an dauke mata sarkar zinari mai tsada da kudi mai kauri, a nan Hajiya Kaltume ta fara nata masifar ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, ita da Khairi, har Yasir abun be masa dadi ba ganin an lakawa mahaifiyarsa sata. All this while kuma Hurriya na dakinta tana rusar kuka abun ya zame mata biyu ta rasa gurin jin sanyi, domin ta san a yadda mahaifinsa ya tsane ta yanzu zai iya yarda ta dauki kudin, gashi bata san yadda zata yi ta fidda kanta ba, secondly ga gift din da Adam ya aiko mata ta san Khairi sai ta fadawa Appanta. Kuka take sosai kamar ranta zai fita gaba daya ta gama fita daga hayyacinta tunani ma ta rasa wanne zata yi.

9:30pm Appa ya aiko kiranta bayan kowa ya hallara a falonsa, cikin matukar tsoro da firgici ta fito daga bangaren Momy tana tafiya kafafuwanta na yin kamar za su zameta. Hankalinta be kara tashi ba sai da ta shiga falon ta ga kowa yana nan ciki har da Yayanta da Hajiya Kaltume mai karawa miya gishiri, ga kuma Momy da ta rumgume hannaye ta hakimce babu alamar sassauci a tare da ita, sanin kanta ne a yanzu babu wanda zai wanketa domin babu mai kaunarta a gidan, kuma bata da tabbacin za su shaideta, dan haka ta bi shawarar dake karya mata zuciya. Idonta yana a gurin mahaifinta tana kallonsa zuciyarta na rawa kalaman da za su fito daga bakinsa kawai take saurare. Sai da ta zauna kusa da Ruma sannan Appa ya dubeta duba na tsanaki ya ce.

 Hurriya ina son ki fada min gaskiya, na san baki taba min karya ba, kin shiga dakin Nafisa a lokacin da ta fita ko dakin Namra

 App...

Ta kasa karasa furta sunansa ma saboda kukan da ya ci karfinta, hawaye kam ko kai waye sai ka tausaya mata yadda take zubar da su.

 Kin shiga

 Ta girgiza kai

Sai Hajiya Kaltume ta kada baki ta ce.

 Ai fa akwai iya kukan kamar yar drama, ba a dai taba sata a gidan nan ba sai yanzu, kuma babu wanda yake bangaren nan sai ke, sai dai kuwa masu aiki, ko da yake bari na rufe bakina ai ita wannan yar karuna ba a mata gwaninta, ni ma bata raga min ba ni din ma da na fi karfin shekara biyu rabona da kofar falonta

Momy ta dago tana harar Hajiya Kaltume ta ce.

 Kwarai kuwa, a gidan nan ba a shaidar kowa, domin kowa shegen kansa ne, rufin asirin da Allah yayi min na san ai tsonewa wasu ido

Hajiya Kaltume ta nunata da hannu.

 Ina arziki yake? Me kike da shi Nafisa? Babu abun da Allah ya baki wanda be bani ba, zan iya siye abun da kike siye to miye zai saka ma na aika a dauko min wani abu dakinki saboda gaki diyar Bill Gates ko?

 Karya kike yi Wallahi, ki ce me nake da shi, ai ke kin san na fi karfinki sai gani sai hange, ni ba irin Iyami ba ce, ahe

Appa ya daka musu tsawa rai a bace.

 Miye haka wai? Na taraku a nan ne saboda ku fara sa'insa? Musamman ma ke Nafisa kin fi kowa fitina a gidan nan, na fara gajiya da matsalalolinki

 Allah ya raba ni da matsala, ka ga Matsala can

Ta nuna Hajiya Kaltume sannan ta cigaba.

 Kuma daman ai dole ka ce ni ce mai fitina saboda ita wa'eh ta mallakeka baka ganin kowa sai bakar kaza, daman idan ta shiga akurki bata barin kowa ya shiga, idan ka gaji da matsalolina sai ka san yadda zaka yi da ni, amman ina mai tabbatar maka zama daram dam dam dam, domin babu inda zan tafi na barwa wata makira yar kasan wuta ta samin hannu a yaya

Khairi ce ta yi karaf ta ce.

 Momy ba dai Hajiyarmu ce yar kasan wuta ba Wallahi sai idan ke

Tana rufe baki Namra ta mayar mata da martanin.

 Ba dai Momy ba, sai dai ke Khairi yar shaye shaye kawai mai banzayen abokai

Appa step on his feet ya sake daka musu tsawa sai da falon yayi tsif.

 Ku tashi gaba daya ku fice min daga falo, saboda kun raina ni, ku yi sa'insa a gabana yaranku ma su yi ko? Toh wannan ya zama na karshe, kuma daga yau sai yau kar wanda ya sake dorawa yata sata, ni na haifi Hurriya ko mahaifiyarta bata fini sanin halinta ba, Hurriya ba zata yi sata ba, Nafisa ki tafi can ki nemi wanda ya shiga dakinki ya dauki sarka da kudi, ki bincike masu aikinki amman Hurriya ba zata aikata haka ba, duk abun da nake yi ma Hurriya ina mata ne ba dan bana kaunarta ba, kuma haka ba yana nufin kowa ya kwaso shararsa ya watsa mata ba

Ya kalli Hurriyya With Angry face.

 Hurriya tashi ki yi tafiyarki

Hurriya bata san lokacin da wani sanyi ya ziyarci zuciyarta ba, hawayen da suka banbanta da na dazun suka zubo mata. A nan kam ta samu courage din yin magana.

 Na gode Appa

 Ba zata zauna a bangarena ba

Momy ta fada cikin zafin rai da daga murya. Appa ya watsa mata harara.

 To sai ki hada komai na ki ki bar mata bangaren, domin duk wanda ke gidan nan yana karkashin iko na ne

Hurriya ta mike tsaye tana share hawayenta ta fice daga bangaren tana jin kamar an watsa mata ruwan kankara a kunar da zuciyarta take mata.


_____________________

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??



Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 1?? 5??


 Sam Sam Sam ni hukuncin da Alhaji yayi a gidan nan be yi min ba

Cewar Hajiya Kaltume da shigowarta falonta kenan. Khairi ta yi karaf ta ce.

 Ba ke kadai ba Hajiya, ni Wallahi na dauka ma korar Hurriya zai yi, domin zata iya satar kudin nan

Hajiya Kaltume ta zauna tana fadin.

 Ai ba nata ne ya ban mamaki ba, na Nafisa ne, yadda ta ci mutunci na ta dora min sata ban ji ba ban gani ba, amman ace Alhaji ya kyaleta ba tare da yi mata wani hukunci ba? Ni wane irin rashin godiyar Allah ne zai saka ni sata a bangarenta, ni ban ma san ta fita bangaren ba, amman da yake ta raina ni haka ta laka min sata, saboda bata da ta ido har da wani aiko masu aiki wai su zo duba mata bangarena, haka fa matar ta taba dora min laifin fasa tayar bakinta, ta maida ni kamar wata karamar yarinya

 Wallahi Hajiya abun da Momy take yi a gidan yana wuce gona da iri, da zarar an taba ta sai tace ita mai kudi ce, mu gaba daya ganinmu take kamar wasu awaki ita kadai ce mutum

Hajiya ta kara kashe ido domin laka mata sata da Momy ta yi da kuma kyalewar da Appa yayi be yi komai ba ya fi komai bakanta mata rai.

 To wai waye zan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login