Showing 9001 words to 12000 words out of 279257 words

Chapter 4 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34642



Umm Khairi ta rumgume Hajiya Kaltume da sauri tana murna.

 Wayyo Allah na dadi, amman me yasa ba ta fadawa Hurriya gaskiya ba?

 Waya sani? Toh ko ganin take zata dawo? Zama be gan ni ba ungo wannan kai min Kitchen bari na kira Hajiya Fatee

Ta mike tsaye da sauri, daga ita har yarta Umm Khairi kallo daya zaka yi musu ka fahimci farinciki dake zuciyarsu, da rawa Umm ta karasa kitchen ta aje plate din ta fito ta shiga dakinta ta dauki wayarta ta fara kiran yan'uwanta da basa gidan tana musu albishir domin sun dadi ba su samu wani labari mai dadi da faranta zuciya ba irin na yau.

Hajiya Kaltume na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta saka key dan tabbatar da ita kadai ce a dakin sannan ta nufi wayarta cikin nauyin jikin dake hana masu kiba da teba hanzari a duk lokacin da suka yi yunkurin yin haka. Sai da ta fara zaunawa sannan ta dauki wayar ta lalabo number aminiyarta Hajiya Fatee duk kuwa da kasancewar ta girme ta nesa ba kusa ba, sai dai friendship be duba age ko level idan jini ya hadu, cikin natsuwa Hajiya Kaltume ta aika mata da kira, zuciyarta har wani bugawa take irin na jindadi da farinciki da tun da aka auro Iyami rabonta da irinshi.

 Assalamu Alaikum Hajiya Kaltume

 Na'am Hajiya Fatee ke kadai kike?

 Ni kadai nake yanzu yar iskar yarinyar nan ta fita

 Ba dai Afra ba?

 Ita fa

 Ikon Allah yaushe kuma ta fara zuwa gidanki?

 Yanzu fa, ina zaune sai gata ta zo ita da yara wai an zo a gaishe ni, waya sani ko wani mugun abun aka kullo min a kawo min, ta mallake ni kamar yadda ta mallake min a

 Tsab kuwa zata iya shi, indai magani ne wannan yarinyar babu inda bata sani ba, gashi ta tsaneki ko maganin mutuwa ma zata iya miki

 Kamar an yi a gabanki, ai an sha fada min ta yi ta yi samun sa'a ne bata yi ba, shiyasa na tsaya a kafata bana wasa kar ta jedar da ni a zuciyarsa kuma Wallahi idan ina da rai sai Fadil ya kara aure

 To ke Hajiya Fatee anya wannan shedaniyar surukar ta ki zata yarda ta bar Fadil yayi aure?

Hajiya Fatee ta yi dariya.

 Hajiya Kaltume kenan kina magana kamar baki san wacece ni ba, ai idan ta kwana da shiri wani a hanya ya kwana, daga ita har uwarta sai sun kyale min ana, komai shige shigensu da tsafe tsafe da yardar Allah sai hankalin Fadil ya juyo kaina ni ma sai na sarrafa ana yadda nake so

Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana kara yarda da zancen Hajiya Fatee.

 Na yarda da haka, domin a yanzu na sarawa lamarinki, ni yanzu ma kira na yi na yi miki albishir, dazun da safe Alhaji yake ce min na kawo masa abun karyawa na cire Bedsheets din da Iyami ta saka, ni tun a lokacin na san wani abu zai faru, kuma na tambaye shi lafiya be fada min ba, yanzu kuma Hurriya ta shigo tana kuka wai Hamad ya daketa a nan take fada mana Amma bata gidan wai ta tafi gidansu har sai ta haihu zata dawo

Hajiya Fatee ta daki cinyarta da karfi ta kyalkyale da dariyar ?eta da jindadi.

 Ke daga jin haka ai kin san abun da muke nema ya samu, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha, kuma gadon ari sai fanna, sirrin iya sai marWibo, yanzu kam sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai yayi kallo, ai na faWa miki kowa yace zai iya haWeye gatari to sakar masa Sota, kuma idan ta sha mu ba mu karya ba, yaro baya ja da mu muja da ubansa...

Haka Hajiya Fatee ta rika jero kirari da karin magana cikin alfamari da tin?aho. Hajiya Kaltume ta mi?e tsaye ta fara yawo a Wakin tana jin kamar ta taka rawa.

 Wallahi sai a yau na ji wannan ?unci da nauyin da ya tsaya min a zuciya ya sauka, tun da Alhaji ya auri Iyami farinciki ya gagareni, duk wani abun da zan samu a duniyar nan farincikina raggage ne, saboda Iyami, yarinya daga zuwa aiki kin aure mai gida har da su ?a?a gashi ya murje ido ya nuna kamar ya fi sonta da kowa, ?a?anta ma kamar ya bude ciki ya saka su ya rufe haka yake ji

 Toh daman ina ke ina kwanciyar hankali da farinciki Hajiya? Mai aiki ta aure miki miji? Ai haka suke shiyasa ake cewa an iska na birni shege na kauye sai tsoron Wansa, ai da zarar sun yalla ido sun ga ana jindadi a gida to sai sun aure miki miji, ita wannan shegiyar gorar Afra da ta fahimci duniya kin ga duk bokonta bata son ko mai raino balle kuma wata mai aiki

 Tana da gaskiya Wallahi, sai dai haka kuma ba zai hana an mu kara aure ba

 Aure kadai? Ai sai ta bar gidan nan matukar ina raye, duk wata mallaka da ta yi ma ana sai na kwance ta, kuma ki zuba ido ki gani ba dai wannan Malamin ya iya aiki ba zaki sha mamaki

 Yanzu so nake ki shirya mu kai masa sallama kuma na sake fada masa bukatar domin ina gudun kar ya maida ita

 Karki damu, bari sai kura ta laba zamu sake komawa, daman ai na fada masa duk abun da aka ba shi karin alkalami ne kawai, biya sai bukata ta biya

 Lallai kuwa zan masa biya mai kyau, domin ya yaye min bakincikin da nake kwana na tashi da shi, a kullum burina Iyami ta tafi ta bar min miji, yau kuma wannan burin ya cika Alhamdulillah

Dariya suka yi a tare sannan Hajiya Kaltume ta yi mata sallama ta sauke wayar tana jin kamar an mata bushara da gafara.
[10/18, 5:34 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2ܠ? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?


5???5???5???5??? 4??


 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Shi ne abun da Hajiya Binta take ta nanatawa idonta a rufe domin danta be zo mata da labari mai dadi ba, a cikin matansa daga wanda ta rasu har wadanda suke a gidansa yanzu babu wanda take so irin Iyami, domin macece wadda ta san kanta take bata girma take rawar jiki da ita tana kyautata mata kamar uwarta.

 Subhanallahi Tsoho baka kyauta ba, ka yi gaggawa kuma daman gaggawa aikin sheidan ne, ina ma baka aikata ba ka dan daga mata kafa ko kuma na turata gidansu har sai ka samu natsuwa

Cikin wani kalar rauni da rashin sukunin abun da ya aikata ya sake noce kansa kasa ya sauke ajiyar zuciya.

 Hajiya natsuwar ce ta gagare ni samu, ba yau na fara jin bana da sukuni idan bana tare da Iyami ba, ji nake kamar wani abu ne a saman kaina, sai a yanzu da na sauwake mata sannan na ji nauyi ya sauka, ni kaina ina son Iyami amman bana jin natsuwa a zamantakewarmu yanzu, kuma na yi ta addu'a ina fatan samun sauki abun amman hakan ya gagara wata kila sakin shi ne mafi alheri daman aure rai ne da shi

 Har saki nawa ka yi mata tsoho?

 Daya na yi mata Hajiya

 To da sauki idan abubuwa suka daidai wata kila za a iya gyarawa, ko dan yan diyanta Tsoho, dubi Hurriyya da Hamad ga cikin dake jikinta yaran nan ba za su taba jindadin zama a gidan idan bata ciki ba, ko ma kallon iyayen kowa na nan ta su bata nan sai ya saka su jin wani iri

 In Sha Allahu zan ba su duk wani jindadi da farinciki da yaya suke bukata a gurin uwa da uba, ban taba fadar maganar nan a gaban kowa ba sai yau a gabanki, Hajiya duk cikin yayana na fi kaunar Hurriya, saboda kokarinta ga kuma lalurar da take tare da ita, Allah ya saka min tausayin yarinyar nan, fitowa daga gida zuwa nan Wallahi yaran nan kawai nake ta tunani a raina

 Tsoho

Ta kira sunansa sai ya dago ya kalli mahaifiyarsa da fatar jikinta ta fara zazzaga saboda tsufa.

 Dan Allah idan ka samu sukuni ka dawo da Iyami dakinta, ko ba komai ta saba da rayuwar jindadi ga kuma ciki ga tunanin yaranta be kamata ka saka mata da haka a irin wannan lokacin ba, idan ma baka yi hankali ba tana cika idda wani zai dauke ta mace mai kyau da kurciya haka nan, ka kusan haihuwarta fa amman tana zaune gidanka gwanin sha'awa ga girmama mutane yarinya mai hankali da tarbiya

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi.

 Hajiya ban sake ta sai da na bata kyauta gidana da yake samaru, kuma na bata kudin da zata iya rike kanta da su naira miliyan ashiri, kuma babu abun da zan karba daga kyautar da na taba mata, kayan dakinta da komai ma gobe zan saka a kwashe a kai mata har gidansu, wata kila dai zaman auren ya kare gaba daya, dan Allah karki cilasta ni aikata abun da zai hana ni samun natsuwa ki yi mana addu'a kawai

 Toh Tsoho Allah yasa hakan shi ya fi alheri, ya kawo mafita a tsakaninku

Hajiya ta fada muryarta na rawa hawaye na cika idonta har suna kokarin zubowa, mikewa ta yi tsaye ta shige dakinta ta bar shi a katon falon dake cike da sanyi ac. Hannu ya saka ya dage kansa yana jin wani karin rashin natsuwar da bakinciki na kusanto shi, ada yayi tunanin idan ya rabu da ita zai samu sakewa, sai dai bakinciki rabuwa da ita ba dan zuciyarsa na so ba, da kuma tunanin damuwar da yaransa za su shiga ya hana shi samun natsuwa, arzikinsa daya a yanzu ya daina jin wannan nauyi da yake ji a lokacin da yake tare da ita. Ya dade zaune a cikin falon kamar wanda ya rasa makama sannan ya tashi ya fice yana gyara babbar rigarsa. Yana fitowa direbansa ya fito ya bude masa motar ya shiga ya maida kofar ya rufe sannanya zagaya ya shiga mazaunin tuki ya tashi motar suka fice daga gidan, kamin ya isa gurin da yake gudanar da kasuwanci kiran Bappa ya shigo wayarsa ya fi a kirga amman yaki ya daga saboda ya san maganar Iyami za su yi masa.




HURRIYA POV.

Yassar na riga da hannunta har suka isa part dinsu, shi ya fara tura kofar falon ya shiga sannan ya rikota ta shigo.

 Careful

Ya fada yayinda take saukowa kan karamin stairs din dake bawa mutum damar shiga cikin falon.

 Hamad....!

Yassar ya kira sunansa a tsawace sai ya juyo rike da kofin kankara yana kallon kofar falon fuska babu annurin ido sun masa ja alamar yayi kuka sosai.

 Akan me zaka daki Hurriya kuma ka fasa mata glass?

Yassar yana fada ya saki hannun Hurriya ya nufi inda yake tsaye cikin bacin rai, a maimakon Hamad ya gudu kamar yadda sauran yara ko kuma kanen Yassar suke idan zai dake su, shi sai yayi tsaye yana jiran isowar Yassar idan ma yanka shi zai yi sai dai yayi, amman taurin zuciyarsa da jin zai iya karawa da kowa a gidan ya hana shi tsoron kowa.

 Ba magana nake maka ba?

 Ita take shiga min hanci

 Ba hanci ta shigar maka ba ido, ko laifi ta yi maka ba ita ce Yayarka ba? Kana namiji zaka rika fada da mace? Kuma macen ma yar'uwarka? Sannan duk abun da zaka mata be isa a fatar baki ba sai ka kai ga fasa mata gilass gashi nan ai ka ja Musib ya mareta

Yassar na kaiwa ayar karshe Hamad ya ji ransa ya yi mugun baci zuciyarsa ta kawo kamar wani babba.

 Me ta yi masa to?

 Ba a sani ba, da baka fasa mata gilashin ba zata tafi tana lalaben fuskarsa ne har ya kai ga marinta? Haba Hamad kai baka jin tausayin yar'uwarka ne? Kowa yana zaune lafiya amman kai ban da kai? Gidan ka fitini kowa? Ita din ma ba zaka raga mata ba?

Yassar ya juya ya kalli Hurriya.

 Hurriya zo nan

Daga inda take tsaye ta fara takowa cikin abun da Allah ya yassare mata na gani har ta iso gurin ta tsaya daidai inda Yayanta yake tsaye.

 Ka bata hakuri

Hamad ya kara murtuke fuska.

 Ita zata fara ba ni hakuri ai ita ta fara taba ni

Kasancewar Hurriya mai son zaman lafiya ce ta tsoron fitini ko tashin hankali yana rufe baki ta bude nata.

 I'm sorry

Yassar ya kai mata duka a saman kai

 Waya aikeki shi ya kamata ya fara baki hakuri ai, ba ki ce babba ba

 I'm sorry too

 Okay bata hannu ku gaisa

Yassar ya fada, nan kam ba musu Hamad ya mika mata hannu, sai ta mika hannayenta duka biyu ta lalabo hannunsa ya mika masa nata suka yi musabaha.

 Good ba fada daga yau kun yarda

Hurriyya ta daga kai, shi kuma goga ya ki cewa komai. Yassar ya juya yana fadin

 Bari na dauko miki glass dinki da yake dakina

Yassar na fita falon, Hamad ya kama hannun Hurriya suka isa dinning yaja mata kujera ta zauna, ya aje kofin kankarar dake hannunsa sannan ya juya ya nufi sama, kai tsaye dakinta ya shiga yana shiga ya bude gurin da take aje kayanta ya dauko box din glass din daya daya rage dakinta ya sauko da saurinsa ya tsaya gabanta ya bude glashin ya saka mata da kansa, sai gata tana murmushi ganin ganinta ya dawo da kyau kamar kowa.

 Thank You

 Ki sha cornflakes dinki zamu tafi Islamiya

 Kai ba zaka sha ba?

 Na sha zobo

 Amma ta ce... 

Tunawa da ta yi da cewar idan ta fada masa Amma tace su daina zama da yunwa zai iya rufe da fada wata kila ma ya hada mata da duka ya saka ta fasa fadar hakan.

 Toh

Hannu ta mika ya janyo kofinta na dazun da ta jika cornflakes din ta fara sha, bata juyo ba sai da ta ji karar bude kofar falon.

 Kin dauko wani?

 Hamad ya dauko min, daman shi daya ya rage

Yassar yayi murmushi daman ya san masu saurin fushi da fitina sometimes sun fi kowa zuciya mai kyau.

 Ya kyauta bari naje na aje wannan

Ya juya sai Hurriya ta kira shi.

 Yayana

Ya juyo

 Thank you

Yayi mata murmushi.

 Ur welcome

Ya fada sannan ya fice daga falon ita kuma ta juya ta cigaba da shan cornflakes dinta. Yana rike da box din glass din ya shigo part dinsu, stairs ya hadu da Hajiya Kaltume tana saukowa shi kuma yana kokarin hawa, kiran sunanta yayi sai ta tsaya tana kallonsa.

 Hajiya me kika fahimta da maganar Hurriya?

 Wace maganar?

 Cewar Amma zata tafi gida har sai ta haihu

 Ikon Allah Yassar ina ce dai ni da kai duk kunne biyu muke da shi kuma kai ma ka ji maganar nan, bakin halin ne da tashi da zaka ce me na fahimta? Ina ruwanka da fahintata? Aunata fahimtata akan wane dalili?

 Haba Hajiya magana ce kawai fa, tsoro nake ji kar dai a wani abu ya faru?

 Koma minene ai idan ta yi tsami zamu ji, miye a hannunka?

Ta tambaya a kokarinta na kawar da maganar. Ya kalli box din.

 Gilashin Hurriya ne

Hajiya Kaltume ta yi murmushi.

 Sai ka yi dan gatan Hurriya, gar yanzu kana ajeye da gilasanta

 Uku ne kawai a hannuna, biyu suna hannunta Hamad ya fasa dayan yanzu sauran hudu

 Yayi kyau ka cigaba da aje su da kyau, Allah ya raya maka yar kanwar nan taka Yassar

 Ameen

Ya amsa sannan ya wuce ya haye sama, Hajiya Kaltume ta bishi da harara.

 Kai kan ba dan a cikin gida na haife ka ba, sai na ce canja min kai aka yi, yaro sume sume sai munafurci fal a ciki oh ni Kaltume

Ta ja tsaki sannan ya karasa saukar ta nufi kitchen dinta, tana shiga hannunta ta fara wankewa sannan fara juya miyar dake kan wuta, da gudu Umm Salma ta shigo kitchen da wani irin murna har haki take.

 Hajiya Khari ya kira ni tace Appa ya saki Amma?

Hajiya ta yi mata alama da ta yi shiru da sauri tana nuna mata kofar kitchen din.

 Bari sai Yayanki ya fita kume farincikinki

Salma ta daga kai cikin murna ta fice daga kitchen din tana tsalle saboda jindadi. Sai da Hajiya ta gama miyarta tsab sannan ya kwashe ta kawo ta a dinning kana ta nufi stairs tana kwalawa yaranta kiran

 Umm Salma ko Umm Khairi waninku ya zo ya jera mana abinci a dinning

Salma ce ta fito har wani tangadi take tana rawa kunneta na makale da ipod, Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta dauke kai ta shige dakinta, da sauri ta karasa gurin gadonta cikin nauyin jiki irin nata ta dauki wayarta da kiran ke daf da tsinkewa.

 Hello Hajiya ina wuni

Daga dayan bangaren Hajiya Binta ta amsa.

 Lafiya Kalau, Kaltume ke kadai kike?

Hajiya Kaltume ta yamutsa fuska daman a gurinta uwar miji bata da wani muhimmanci.

 Eh Hajiya ni kadai nake, Lafiya dai?

 Toh Lafiya ba kalau ba, magana nake son yi dake akan yaran nan Hurriya da Hamad

 Me ya faru da su?

Hajiya Binta ta sauke ajiyar zuciya.

 Dazun mijinki ya zo nan ya fada min hukuncin da ya yanke akan Iyami, ba mu san abun da Allah zai yi a gaba ba, amman kamin nan Kaltume ina son ki ji tsoron Allah ku rike Hamad da Hurriya amana, domin su da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login