Showing 180001 words to 183000 words out of 279257 words

Chapter 61 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34693

kuma ba fasawa zata yi ba

 Yanzu kuma Gwaggo ai ba zata iya komai ba, daman can rashin kula da addu'a ne da kuma tsarin jini, amman yanzu babu wannan sakakacen duk abun da zata yi kanta zai koma, wannan sakin da aka mata ma kar ki yi mamaki ace wani sharin ne ta dauko ya koma mata, Dan Allah Gwaggo karki hana Alhaji maida matarsa idan ya bukata, ita kanta Iyami da yayanta za su fi samun hankali idan suna guri daya, ba baki nake ba amman da zarar shi kansa maganin ya sake shi ba zai barku ku zauna lafiya ba sai an maida masa da natarsa ai yana kaunarta sosai shiyasa aka raba su, ba zai taba barinta a gidan nan ba

Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya.

 Ni kam da na tsorata sosai, har ina cewa ko da wani auren zata sake yi ba zan bari ta auri ta auri mai mata ba, wai wanda matarsa ta mutu ko kuma ba shi da auren gaba daya, ina ganin kishi kala kala amman na Kaltume ya tsorata ni sosai, mata babu tsoron Allah a ranta

 Karki ji komai, da yardar Allah karshenta ne ya zo, ni akwai wani Malami ma da na ji yana bada taimako kuma ana dacewa gashi babu wani kashe kudi da za'a gwada na Iyami ko Allah zai saka a dace

 Shi kuma a ina yake? Lamarin maganin ne yi ake kamar ba 'ayi, sai an yi kamar za a samu sauki sai kuma ki ga abun be yi ba, kin ga ko wanda muka gwada kwanan baya har ta fara samun sauki tana daga hannun sai kuma abu ya zo yayi mana shiru

 Komai ai sai Allah ya yarda Gwaggo kuma shi magani dace, abun da be yi ma wani ba sai ki ga yayi ma wani, ba san inda dacen yake ba shiyasa ba a gajiya da yi, balle ma wannan baya karbar kudi mai yawa

 A ina yake? Kuma ina fatar ba irin masu tsafin nan ba ne

 Aa babu tsafi a lamarinsa magani ne zallar magani kuma babu kashe kudi, ba zai wuce ka biya dubu biyar ba shi bakwai takwas zuwa goma, idan mai jinya ya ji sauki shi ne zai fada maka tukaicinsa sai ka biyashi, kuma yana bada maganin tsari ma idan Allah yasa yayi maya na warakar ta ji sauki sai ya bata na tsarin jikinta, kuma ga addu'a tana yi shikenan

 A wane gari yake?

 A Neja yake mazauni cibiyarsa na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. kuma ya bada number wayarsa ma ba dole sai mutum ya tafi ba, za'a iya masa magana ta Whatsapp ko a kira zai aiko da magani a duk garin da kake

 Toh Maa Shaa Allah, hakan ya fi ai, domin daukar marar lafiya zuwa wani gari akam ai ya zama aiki sai dole musamman garin da ba kusa ba, kamata yayi ki kira shi ki yi magana da shi sai mu ji yadda za'ayi

 Toh daman dai na ce bari na fara fada miki kamin na yi karanbani kin san ni ba zuciya ce da ni ba, Iyami ta watsa min kasa a ido tun a can baya amman dai ban daddara ba

Gwaggo ta yi dariya.

 Ba a biye Iyami ai, ita kanta yanzu ai ta ji jiki gobe ba sai an bata shawara ba

Hindu ta yi dariya ta ciro wayarta ta kama number wayar da ta ji ana sanarwa a gidan radio ta dauka. Sai da tabbatar number ce sannan ta kira ta saka a speaker, bayan ya daga suka yi magana ya ta fada masa yadda ciwon Amma yake da abubuwan da ake zaton asiri ne.... Ya ba su amsa daidai gwargwadon abun da ya fahimta sannan ya fada musu yadda maganinsa yake da kuma kudin da za su biya, Gwaggo was shock ta ji kudin da be wuce 6k amman wasu guraren sai an karbi kudi mai yawa ake ba su magani.
Suna gama waya da Hindu ta tura masa kudin har da doriya, sannan ta kira ta fada masa ta saka kudi, shi kuma ya fada musu ranar da zai aiko musu da magani tun daga Neja har garin Gusau.

 Kin ga ai haka ya fi ba sai mutum yaje ba, kuma kina ji yace idan ta samu lafiya aka biyasa hakkinsa zai bata na tsarin jiki wanda zata yi amfani da shi ita da yaranta gaba daya, Allah dai yasa karshen wahalar ne ya zo, a huta ba ma sai an fitar da ita waje ba

Hindu ta yi murmushi tana amsawa da Ameen.

 Ameen Gwaggo, daman ciwon ba na asibiti ba ne, irin ciwon nan ne da ake aikowa mace duk abun da ta tara sai ya kare, ta ma yi arziki da ba a haukatata ba, wasu haukata su ake ko ma a kashesu gaba daya

 Allah ne ya tsare ita ma ai haukar aka so ta yi, kuma da abun da muke da shi duk ya kare me ya rage mana? Allah dai ya bata lafiya kuma ya isar mata

 Ameen bari na duba Iyamin tana ciki?

 Eh tana dakinta, Allah ya saka miki da alheri Hindu ke ma kin yi kokari

Hindu ta mike tsaye tana fadin.

 Haba Gwaggo taren mu da Iyami ai ya wuce haka, miye Iyami bata min ba? Babu kalar arzikin da ban ci ba a lokacin da take gidan Alhaji kuma tun kamin nan Iyami mutum ce har da rabin mutum

Gwaggo ta yi murmushi tana kallon aminiyar yarta, Hindu na fitowa daga dakin Gwaggo ta shiga dakin da Iyami take da sallama. Hurriya da Rukayya da suke rike da qur'ane suna karanta mata suratul Bakara suka amsa suna rufe qu'anen.

 Aa ku cigaba mana, wannan ayar Allah shi yake kareta daga duk wani sheri

 Mun gama ne ai Anty Hindu, sannu da zuwa

Rukayya ta fada sannan ta mike tsaye ta fice, Hurriya ta bi bayanta bayan ta gaisa da kawar mahaifiyarta. Hindu ta zauna kamar yadda ta saba tana ta hira da Iyami, sai dai kai kawai Amma take iya daga mata ko da girgiza ko ta tabe baki, wani zubin kuma ta yi hawaye, sai dai bata iya cewa komai saboda an rike maganar. Hurriya bata bari Magariba ta yi mata ba ta yi ma Amma sallama da Gwaggo, Rukayya ta rakota har bakin Titi ta samu abun hawa ta hau ya kawo ta gida, a ranar Hurriya bata gwada cin abincin dare ba domin ta san za su iya samun matsala da Momy ko Namra ganin yadda kowa ya kullace akan Captain, daman kuma kamin ta fito gidan Gwaggo sai da ta ci abinci, a daki kuma sai ta dora da dan abun tabawar da Captain ya bata da be kare ba har lokacin.


*** *** ***

Ranar Friday Misalin karfe goma sha daya daya da rabi, Hurriya ta fito wanka tana daure da tawul ta tsaya gaban madubi tana tattara kitson dake kanta ta daure da ribbon sannan ta ya dauki tissue ta cire gilashinta ta goge sannan ta zauna ta fara shafa mai, slowly ta ji an bude kofar dakin, ta cikin madubi ta hango Captain tsaye yana kallonta immediately ta mike tsaye ta juyo ta kalleshi, facing cap din dake kansa ya cire da hannunsa na hagu ya rike yana kallonta, da sauri ta nufi gurin da Hijanbinta yake ta dauka sai a lokacin ya kawar da idonsa.

 Subhanallahi what is happening here

Da sauri Hurriya ta nufo kofar dakin dake bude ta rufe sannan ta dawo gabansa cikin tashin hankali.

 Me kake yi nan?

Ya kalleta sai yayi murmushi sai kuma ya nufi gadonta ya dora karamin kwalin dake hannunsa, daga bisani ya saka dayan hannunsa aljihu ya ciro wani box.

 Wannan zan baki

 Minene?

Ya bude box din ya ciro wani abun hannu na azurfa ya duka ya aje kwalin.

 Kawo hannunki

 Yaya bana so dan Allah

Ya daga kansa sama ya rufe ido. A take ta fara masa kukan tsoro da shagwaba a lokaci daya.

 Ina bindigarka take?

 Tana mota

Ya amsa ba tare da ya bude idon ba, domin kokarin kwantar da fushinsa yake that's why ya amsa mata kai tsaye, if not dauke ta zai yi da mari a gurin kuma bata isa ya tsaya yana neman ta yi abu tana masa wasa ba.

 Na san baka maimaita magana amman idan Momy ko Yaya Namra suka ga wannan abun a hannuna zai iya zame min matsala

Ya bude idonsa ya kalleta.

 Baki murna da dawowarta Hurriya? Baki min sannu ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da zuwa ba, ban ga shaukin murnar dawowa ta a fuskarki ba why? A madadin haka sai tambayar kike me ya kawo ni dakin nan?

 Baka saba shigowa nan ba, be kamata ka shigo ba idan Momy ta gani zata min fada, kuma Yaya Namra zata ji babu dadi kuma ko wacece ba zata jidadi ba ace saurayinta yana kula wata

 Saurayinta...!?

Ya fada as question as surprised.

 Ita tace miki ni saurayinta ne?

Hurriya ta sauke idonta kasa.

 Na gane

Ya fada yana dan hade rai, domin ya fahimci idan yana yi mata magana da sakewar fuska ba zata amsa masa yadda ya kamata ba.

 Ba ni hannunki

A take ta fara masa kuka.

 Zata yi fada idan ta gani

 Ba ni na baki ba? Wallahi wannan ba daga ni ba ne?

 Waya ba ni Salim?

 Come-on ya za'ayi Salim ya ba ni abu ya ce na baki kuma na baki har na bukaci ki saka

 To ya ba ni

Har yayi kamar zai yafa mata bakar magana sai kuma ya ji ba zai iya ba.

 Wani ne ya ce na baki, na ba shi labarinki yadda kike da kirki da tarbiya da kokari, sai ya yaba halinki kuma ya bukaci na baki wannan as gift kuma yace na gaishe ki

 Ban san shi ba....

 Ba dole sai kin san kowa ba....

Ya daka mata tsawa.. Sai ta matsa baya ta fashe da kuka. Hannu ya kai ya dafe kansa.

 Please please ki daina min musu, idan ni na baki abu ba zan ji kunya ko tsoron fada miki ba, kuma ba zan miki karya ba

Hannu ta miko masa, ba dan tana so ba sai dan tana tsoron wani ya tarar da shi a dakin. Matsawa yayi ya bude abun hannun ya saka mata ya rufe da abun rufewarsa. Ta kai dayan hannunta ta taba awarwaron da aka rubutawa sister a jiki, ta ji gabanta ya fadi wani tsumayi ya saukar mata.

 Na gode

Domin al'adarta ce yin godiya a duk lokacin da aka yi mata wani abun alheri.

 It's my pleasure... Daga Ethiopia na zo miki da shi

Kallonta yake kamar zai fada cikin idonta, tana jin kamar motsi a jikin kofar dakin sai ta dago da sauri ta kalleshi a razane.

 Wani zai shigo

Tsoron kar Momy ko Namra ta shigo dakin su ganshi ya manta ita haramci da halarcin taba jiki ko hannun da ba muharraminta ba, bata san lokacin da ta kama hannunsa da sauri taja shi zuwa bandakinta ba, shi kuma ya bita kamar wani hoto, hannu biyu ta saka ta turashi ciki ta rufe bandaki, ta dawo da sauri zuciyarta na rawa ta bude kofar dakin ta leka, ganin babu kowa ya saka ta rufe kofar dakin ta dawo ta bude kofar bandakin.

 Fito babu kowa

Ya fito kamar yadda ta bukata sai ta rufe kofar bathroom din ta kalleshi a kunyace.

 I'm sorry bana son wani ya same ka a dakin ne

 Okay

He said sannan ya nufi kofar fita sai kuma ta yi saurin dakatar da shi.

 Aa karka fita karka fita

Ya juyo ya dawo ya tsaya gabanta yana kallonta, hakan sai ya kara tsanananta bugawar da zuciyarta ke yi fiye da kima, musamman da ta daga kai ta kalleshi sai idanuwansa dake kanta suka fada a cikin nata idon. Ta dan matsa baya shi kuma ya nufi gadonta ya zauna yana kallonta

 Aa karka zauna idan wani ya same ka a nan na shiga uku

Ta fashe da kuka sai ya mike tsaye ya nufo kofar fita, sai ta kara sautin kukan da take wanda ya fi kama da shagwaba har da buga kafa a kasa, ba kuma ta yi dan shagwabar ba sai dan ta rasa yadda zata yi.

 Karka fita

Ya juyo ya kalleta.

 Ya kike son na yi? Kin ce kar na zauna kuma yanzu kin ce kar na fita what do you want to do?

Ta share hawayen ta nufo kofa.

 Ka tsaya a nan zan sauka falo na duba idan babu kowa sai ka sauko

Samun kansa yayi da amsa masa.

 Okay...

Ta nufi kofar ta bude sai kuma ta juyo ta kalleshi.

 Karka sake shigowa nan dan Allah, idan ba haka ba zaka saka ni a matsala

A nan kam be ce mata komai ba kallonta kawai yake.

 Idan ka ji na yo tafi sai ka fito

Nan ma be ce komai ba, ita bata jira abun da zai ce ba ta fara lekon waje tana takawa a hankali kamar wanda zata yi sata, murmushi yayi ya bi bayanta. A hankali ta fara saukowa stairs tana karewa falon kallo tana duba Dinning sai ta hango Momy da Namra zaune suna kallonta, juyawa ta yi da sauri sai ta bugu kirjin Captain dake bayanta ba tare da ta sani ba, kamar a rikice haka ta juyo da sauri ta sauko stairs din gaba daya, shi ma ya biyo bayanta ya sauko. Ta dago ta kalleshi kadan ganin hawaye ya taru a idonta ya saka shi juyawa zai taka stairs din ya koma tun da bata bashi umarnin saukowa ba ya biyo bayanta gashi kuma yanzu zata yi kuka.

 Captain....

Momy ta kira shi sai ya juyo amman ba Momy ya kalla ba Hurriya yake kallo. Hurriya ta kalli Momy da sauri hawayena sauko mata ta ce.

 Daman dakin Yaya Namra yake nema sai ya fada dakina

 Kamar ya Namra nake nema na fada dakinki? Sai ka ce wani kwarto ko dan'iska? Already sun san zan shiga dakinki ai, yau na dawo na kawo musu tsabarsu na tambaye ina kike aka ce kina dakinki shi ne na shiga na kai miki taki tsabar dakinki da kaina, you can't lie

A take ta fashe masa da kuka domin dai yaja mata fitina a gurin Momy kuma yanzu ya saka ta yi karya a gabansu.

 Yaya miye haka? Ba kyau me yasa ka bari na yi karya?

Ta nufi stairs din tana kuka sosai domin bata shiryawa tashin hankalin Momy da Yayarta Namra ba. Binta yayi da kallo yana jin kamar ya bi bayanta ya rumgume ta rarrasheta. Momy ta taso daga dinning din da take zaune ta nufo da mamaki karara a fuskarta.

 Yaya? Na dauka baka son kowa ya kira da wannan sunan?

Ya juyo ya kalleta.

 Ita ai bata sani ba, shiyasa da ta kirani da Yaya ban hana ta ba

 Abun da mamaki, yarinya har ta samu damar tambayarka me yasa ka bari ta yi karya? Tun yaushe wannan abun ya fara?

 Ni ma ban sani ba Momy kawai tsintar kaina a duniyar

Ya sauke ajiyar zuciya ya nufi cushion ya zauna.

 To ya zama na karshe daga yau, karka sake shiga sha'anin Hurriya, ba tsaraba ba ko kallonta bana son ka sake yi?

 Saboda ita nake yawan zuwa gidan nan Momy? Me ye illar kula Hurriya?

 Saboda ita din ba ajinka ba ce, bata kai macen da za mu bari ka so ba balle kuma har ka aura idan ma wannan abun kake tunani to ka farka tun wuri

Da mamaki yake kallon Momy da ranta a bace har wani cika take tana kallonsa kamar wani wanda ya aikata abun kunya

 Tana da kyau ai

 Ba daga hallita ba ne

Ya rausayar da kai sai kuma ya sake kallonta

 Tana da tarbiya

 Ba daga tushe ba ne

 Tana da mutunci da kamun kai, ta san ya kama

 Ba daga martaba ba ne

Da kakkausar murya take amsa masa tana jin bacin rai akansa wanda bata taba ji ba.

 To daga minene Momy? Miye illa idan na ce ina son Hurriya

 Idan babu wanda kake so a Familynmu, ba za'arasa a wajen jininka ba, amman ban da wanda bata kai matsayinka ba

 Bana son auren zumunci, shiyasa wata bata taba burgeni daga cikin family mu ba

Momy ta taka ta isa inda yake zaune ta kai hannunta ta dafa kafadarsa.

 To ka so kowa Captain amman ban da Hurriya, ba zan taba bari hakan ta faru ba, ka fita tsabgar yarinyar nan idan ba haka ba, wahala kawai zaka ja mata, ni kaina bana da alaka da ita balle kuma kai, Namra ce kawai zata iya ikirarin wannan amman ba ni ko kai ba, know your limit....

Ta juya ta barshi a gurin zaune da mamaki, Namra na ganin Momy ta haye sama ita ma ta bar dinning din, sai da ta kawo kusa da gurin da Captain yake zaune sannan ya mike tsaye yana mata kallon takaici ya ce.

 Ke kika cewa Hurriya ni saurayinki ne? Is that what you told Momy? Shiyasa take ta masifa saboda na nuna ina son Hurriya?

 Haka Hurriya ta shirya maka? Daman ta saba munafurci ai

Ya watsa mata harara irin wanda ta dace da ita.

 Ni na shirya, tare da ni take munafurcin

Fuuuu ya fice daga falon kamar walkiya, Namra ta rufe ido hawaye na sauko mata, bata taba sanin tana son Captain ba sai a yanzu da ya fitar da abun da ke

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login