Showing 264001 words to 267000 words out of 279257 words

Chapter 89 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34627

ya juya min baya, na gagara neman lafiyata na gagara zaman dakina kullum bana gurin wannan boka bana gurin wannan malamin, amman har yanzu shiru, yanzu fa na dawo daga wani gurin, sai kuma ka zo min da labarin wai Hamad yana raye? Yaron sa aka kashe tuntuni? Yaushe zai rayu? Hamad ya mutu wani ne dai ya dawo yana son a kai ni gidan yari, burin Iyami ya cika... Shikenan tawa ta kare

Cikin rashin fahimta da mamaki Yasir yake kallon mahaifiyarsa, be da dalilin daga hankalinta saboda Hamad ya dawo ba har da zancen gidan yare, above all ta gama fada masa tana bin malamai da bokaye.

 Ta ina dawowar Hamad zata saka a kaiki gidan yari idan ma gaskiya ne?

Tana tambayarta ne a daidai lokacin da Ruma da Khairy suka sauko domin har dakunansu suna jin muryar Hajiya Kaltume saboda yadda take daga murya.

 Saboda ni na saka aka sace Hamad... Ni na saka aka dauke shi tare da Umm Ruman, Hurriya na ce su dauka sai aka yi kuskure aka dauki Hamad... Amman ban ce su kashe shi ba, Danja ne ya aikata hakan ba da umarnina ba..?

 Waye kuma Danja?

 Wanda na saka ya sace Hamad, a gidan Hajiya Fatee na hadu da shi.. Ni na saka shi aikin saboda ina son a karbe kudin Iyami ne da Alhaji ya bata lokacin da ya sake ta ya damka mata kudi da gida ga sarkar zinari ya siyawa Hurriya wannan ya saka na aikata... Iyami ta hana ni jindadi ta hana ni zaman lafiya ta saka na rasa komai daga zuwa aiki ta aure min miji sanadinta na rasa Salma ni na kashe yata da kaina... Iyami na ce a halbe sai aka halbe Salma ta cikin madunin Tsafi nan ma ni na saka mai aikin Nafisa ta kai ni duk saboda Iyami ne... Shikenan na lalace rayuwa ta ta kare...

Kama ganin yadda take maganar yana murza jikinta zaka san bata a cikin hayyacinta. Khairy da Yasir ne mamaki ya cika su, Ruma kam kuka ta fashe da shi domin ta san asalin gaskiyar.

 Hajiya... Wannan maganar ba a cikin hayyacinki kike yinsu ba...

Yasir ya fada tana tasowa daga inda yake zaune ya dafa mahaifiyarsa ta kai kasa tana kokarin cire riga.

 Ni na saka aka dauke shi Wallahi... Ni na ce a sace Hurriya su kuma suka dauke shi ina ta murna asirina yana rufe sai kuma ka ce min wai Hamad ya dawo? Gidan yari zan tafi kenan? Gidan yari zani Yasir?

Ya rike rigarta yana kuka, ya dago ya kalli kenansa.

 Akwai wanda ya san wani abu a cikinku...

Cikin kuka Ruma ta ce.

 Eh gaskiya ta fada, ita ta saka aka sace Hamad, kuma Hamad da ni duk mun ji muryarta lokacin da take magana da su, Har yake cewa Hajiya me na yi kika ce a kawo mu nan? Idan na dawo sai na fadawa Appa, sai ta fara fada tana cewa ya ji muryarta zai tona mata asiri, bayan ta kashe wayar ne suka buga mishi karfe akai kan ya fashe yana ta jini, Hamad yana ta ihu yana kiran sunan mutane har da ni, suka fitar da shi daga dakin suka bar ni daga nan ban san me ya faru ba...


 Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'u ??

Yasir ya furta har sau biyu sannan ya mike tsaye ya rike bakinsa. Khairy kuma ta fadi zaune tana kuka domin bata taba jin wannan ba sai yau. Hajiya Kaltume kuma bata fasa tonawa kanta asirin abun da ta yi ba, tana ta firgar rigar jikinta da zanenta.

 Hajiya me yasa baki ki tunanin makomarki ba da ta mu kamin ki aikata? Wane irin abun kunya ne wannan? Har yaushe zuciya zata bushe ki aikata hakan ga dan mijinki dan be miki komao ba, be tare miki komai ba? Idan ma kishi kike da mahaifiyarsa shi meye nasa a ciki? Gashi har kina fadar sanadinki Salma ta mutu...

Hajiya Kaltume ta kyalkyale da dariya ta buga kafa. Ta janyo jakarta ta ciro maganin da ta dawo da shi ta zube a gurin.

 Ai ba Shikenan ba, ni na saka Khairy ta dauke gilasan da suke dakinka na Hurriya, ni na yi ma Hurriya da Appanta farraqu, aka saka masa tsanar Hurriya, ni na saka aka saki Iyami Yasir ni na yi mata wannan asirin kuma na ce a kwantar da ita ciwo, kuma na ce ayi mata asiri kar wani ya ganta ya aureta, yanzu wannan maganin shi kuma bokan ya fada min idan na yi amfani da shi Alhaji zai zo Jiki na rawa ya maida aurensa, kuma Fadeel zai dawo ya auri Khairy... Kawata Hajiya Fatee ita take kai ni ko'ina ita ma kuma tana can da ciki cikin haihuwa wanda ta saka malam ya danne, na biyawa Malam makka saboda na jidadin aiki, na mallaka Alhaji sai abun da nace yake min... Tabbas na aikata Hamad kuma ni na dauke shi ni ce nan na aikata, kuma na yi shiga gaban Alhaji da Sapna na kawar masa da ita a zuciya ya fita maganarta na shashantar da ita a zuciyarsa...

Kusan duk wani abu da Hajiya Kaltume ta aikata tun cancan da har zuwa yau sai da ta fadawa yaransa da wanda suka sani da wanda ba su sani ba. Yasir sai ambaton Allah yake be taba tunanin mahaifiyarsa ta yi nisa haka ba sai yau be taba tunanin ita ce sanadin barin Amma a gidan ba sai yau, be san ita ta shiga tsakanin Hurriya da Appa ba sai yau, be san ita ta aikatawa Hamad haka ba sai yau. Ya rasa ta ina zai fara ya rasa ina zai saka kansa ya samu sassaucin rayuwa.

 Ku shiga da ita cikin daki ku rufe karku bari ta fito

Ya fada sannan ya share hawayensa yana jin kamar ace ya mutu kamin yau. Ruma ta kalleshi tana kuka.

 Yaya yanzu idan da gaske Hamad ya dawo gidan yari za a kai Hajiya Kenan?

Ya cije baki ya saka cewa komai sai hawaye ke sauko masa. Tashi yayi ya fice daga falon ya nufo bangaren mahaifinsa ya zauna a gurin yana jin wani bala'in gabas da na yamma yana hade masa, da ma ace wata ce daga cikin kannensa zai ji sauki amman uwarsa? Abun yayi masa muni gaba daya ma sai ya rasa abun da zai yi, tun farko be ga dalilin Hajiya na aikata hak??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an ba, domin bata rasa komai a gidan Appansa ba idan ma ta tasa me yasa ba zata barwa Allah ba. Yanzu wa gari ya waya? Karshenta jifan akan wa ya dawo? Waye yayi mummunan karshe? A yanzu ya kara jin kaunar Amma a ransa domin ita da ta wakkala ga Allah gashi yayi mata mafita kuma yana kan mata, Hurriya ma haka, Amman Khairy gashi ta girbi abun da ta shuka tun abun be yi nisa ba, Hajiyarsa ga abun na kokarin taba hankalinta ko ma ya taba.

Allah kawai yake ambato ya rasa me zai yi, wa zai tunkara da maganar ya rasa ina zai bullowa lamarin. Yana zaune a gurin har la'asar, sallamar ma yana yi ya sake dawowa gurin ya zauna tunani yake amman tunanin ya ki tsaya masa ya tasa wanda zai ba shi shawarar abun da ya dace ya aikata. Asibiti zai dauki Hajiya ya kaita? Ko kuma dai ya sanar da Iyayenta da kanenta domin babu iyaye a yanzu, ko kuma dai ya samu mahaifinsa da maganar. Daga balcony din da yake zaune ta bangaren Appa ya hango shigowar motar Maama, hakan ya saka shi tashi ya nufi bangaren mahaifiyarsa, a dakin ya sameta tare da sauran yan'uwanta Khairy da Ruma suna kuka har lokacin Hajiya Kaltume bata daina tonawa kanta asiri ba.

 Ku kira su Hajiya Fanna da Mama Zainab ku fada musu halin da ake ciki, idan asibiti za a kai ta sai mu tafi...

Maama ta juya ta kalleshi tana hawaye

 Haka Jarabawar ta zo mana Yaya? Ni gidan aure babu dadi Hajiya kuma nata auren ya kare, Khairy an fasa yanzu kuma wannan ya biyo baya?

Yasir ya daka mata tsawa kamar zai daketa.

 Laifi duk na waye ba naku ba? Idan ta kauce ko zata aikata wani abun da ba daidai ba kun fi kowa sani, me yasa ba zaku nuna mata illar hakan ba? Amman ke kuke zugata kuna tayata kishi ku nuna abunda take daidai ne, ke Khairy lokacin da kika aikatawa Hurriya haka bata ma sani ba, saboda zuciyarku babu kyau, ke kuma idan abun kwarai ne gashi yanzu kin yi aure kin girba, kar wanda ya sake saka min baki akan lamarin uwata kar wanda ya sake wata magana ku bar ni na ji da zafi daya


Ya share hawayensa ya fice daga dakin, ya sauko kasa wayarsa tana ringing da ya duba sai yayi arba da number Appa, and for the first time sai ya ji ba zai iya amsa kiran ba, a yayinda wayar yake rike a hannunsa tana ringing. Ya jingina da kofar falon ya cije bakinsa ya buga ginin ya girgiza kai. A karo na biyu wayarsa ta sake yin ringing ya dago ya duba wayar Appa ya sake kira wannan ya dauka sai dai yana kara wayar a kunnesa sai ya fashewa Appa da kuka kamar mace.

 Subhanallahi... Yasir.. Lafiya kana ina?

 Ina gida Appa.. Amman ba lafiya, ji nake kamar na bar garin nan kamar na tafi a inda babu kowa na rayu a yau, duk na ji duniya ta isheni

 Toh gani nan zuwa gidan

Appa ya sauke wayar yana jin karin wata damuwar, daman ya kira ya fada masa yadda suka yi daman ya kira ne ya fada masa yadda suka yi da Amma da kuma Captain sai dai jin halin da dansa yake cike har yana kuka ya saka shi jin babu dadi domin be san Yasir da bayyana damuwa idan ma akwai.
Yasir ya share hawayensa yana kokarin ganin yayi halin maza wajen hana kansa kuka da jin tsanar duniya da halin da yake ciki, ya nufi bangaren Appa, a Balcony ya zauna kamar dai dazun yana jiran Appa, sai dai Yayyun Hajiya Kaltume da Maama ta kira ta fada musu halin da ake ciki sun riga Appa zuwa, hakan kuma be saka Yasir tashi ya koma bangaren ba, domin baya son ya sake kallon mahaifiyarsa a cikin wannan halin. Direban Appa ya fakawa Yasir ya mike tsaye Appa kuma ya fito mota da sauri yana kallon Yasir.

 Mu shiga ciki

Yasir ya wuce gaba sannan Appa ya bi bayansa, a babban falonsa suka fara zaunawa Appa ya dubi ansa cike da damuwarsa ya ce.

 Lafiya Yasir? Me ya faru..?

Nauyin furucin da kunyar abun da mahaifiyarsa ta aikata sai ya saka shi kasa furta komai a gaban Appa.

 Yasir daga kanka ka kalleni mana fada min damuwarka ni kaina da nake mahaifinki wani abun ai kai nake samu mu tattauna balle kuma kai da kake ana me yake faruwa?

 Appa a game da Hamad ne... Dazun ban mun gama magana da kai na shiga cikin gida na fadawa Hajiya abun da ya faru...

Ya kwashe abun da ya faru ya fadawa Appansa domin be san a inda zai bude damuwarsa bayan nan ba. Appa ya mike tsaye yana ambaton Allah yana jin kamar duniya zata rikito ta fado masa tsabar tsorata da abun da Hajiya Kaltume ta aikata.

 Yanzu da saka hannun Kaltume aka dauke ana? Da sa hannunta a rabuwata da Iyami? Me na... Me.. Mena rage ta da shi? Akwai ta inda na canja mata ne bayan auren nan? Ba Iyami da yayanta kadai ba har da Sapna? Ita me ta yi mata? Wace irin mata ce Kaltume? Me yake damunta? Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un

Duk yadda Yasir yake tunanin abun ya gigita shi sai ya tarar ya gigita Appa fiye da shi domin sai da ya tsorata da yadda Appa ya rike kirjinsa ya dafe saitin da zuciyarsa take, tsoron rasa mahaifinsa ya saka shi nadamar sanar masa abun da yake faruwa.

 Appa dan Allah ka zauna

Yasir ya rika shi ya zauna yana girgiza mai shi ma abun ya daure masa kai, ya san be rage Hajiya Kaltume da komai ba, akan wane dalili zata azantar da kanka ta azabtar da shi kuma ta bi ta yayansa da matarsa? Ta wani bangaren kuma yana ganin laifin ba nata ba ne nashi ne saboda be rike addu'a ba tun farko, kuma be tsaya ya zabo mai addini ba da bata so ta masa wannan aika aikarba a gidansa. Hankalinsa be kara tashi ba sai da ya shiga da kansa ya duba halin da Hajiya Kaltume take ciki, a nan ya tabbatar da abun da dansa ya fada masa yan'uwanta kuma suka bukaci tafiya da ita gida a tare da su, Appa ua daga hannunsa sama yace ba su bukatar umarninsa domin ba aurenta yake a yanzu ba. Momy da Namra sai suka shigo suna kallonta a lokacin da labarin ya isa kunensu, Momy wani sabon tsoron Allah ya kamata daman can ta san Kaltume zata iya aikata fin haka ma, amman ba ta yi zaton da hannunta dumu dumu a satar Hamad ba, a nan ta gane ita kanta Allah ne kadai ya tsare wata kila ita din ma ta an sace mata Namra ko Miwan ko Musib.

Ta bangaren Iyami ma haka ta kasance cikin mamaki ta tashin hankali a lokacin da Appa ya sanar mata halin da Kaltume take ciki, sai ta fashe da kuka tana mamakin tsananin kiyayya da zafin kishi da zai saka mace aikata irin wadannan munanan abubuwan, daman can sun yi tsammanin da hannu a cikin lamarin saboda yadda ta nuna bata damu ba kuma yake nunawa yaran kiyaya ta zahiri. Hakan sai ya kara sanyaya guiwar Amma dake shirye shiryen tarewa a gidan Appa, duk kuwa da ta ji cewar a yanzu Hajiya Kaltume bata cikin hayyacinta, kuma ita ma ta rike addu'a da tsarin jiki ba kamar da can ba, ta wani bangaren Gwaggo da Iyami suna ganin kamar Hajiya Kaltume ta yi haukan karya ne saboda ta san asirinta yana daf da tonuwa. Faruwar hakan ya sakawa Amma yarda cewar yaron da zai baro Ethiopia tare da Hurriya da surukinta da kanwarta lallai danta ne wata kila Allah ya raya shi ne saboda zuwan wannan ranar da asirin Kaltume zai tonu, domin wani abun tun a duniya yake bayyana. Ba sai an je ba, lahira karbar sakamako ne kawai da sanin makoma.



HURRIYA POV.

Cikin tsoro Mama Rukayya take kallon Hamad da ke zaune a masaukinsu, Hurriya na zaune a kusa da shi tana kuka shi kuma yana hawaye.

 Taya wai za ace wanna Hamad ne ni fa ban gane ba..

 To ke da kika san kan labarin kenan balle ni da ban san komai akai ba

Cewar Momy Ikilima. Captain ya dan dago ya kallesu kamin ya dauke kai ya cigaba da amsa wayar Appa.

 Hakan nake tunanin zai fi, sai mu dunguma gaba daya mu dawo tare, saboda bana son karatun nasa ya samu matsala ka san su nan sai da doka suke komai ba kamar kasarmu ba

 Shikenan za'ayi haka, zan kira ka duk yadda ake ciki

 Na gode Appa...

Ya sauke wayar ya kalli Hamad.

 Hawayenka su suke saka yar'uwarka kuka kuma kasan yadda idonta yake

Hamad ya kalleta sai ya mike tsaye da sauri Hurriya ta rike hannunsa ganin take kamar idan ya fita ba zai sake dawowa ba.

 Dan Allah karka tafi..

 Hurriyana sake ki babu inda zai je tare zamu koma nigeria, na yi magana da Appa zai yi magana da jami'an tsaron can a matsayinsa na Mahaifin Hamad sai su aiko da takarda zuwa ga Ambassador Nigeria da yake nan shi kuma zai yi magana da makaranta su ba mu aron Hamad mu tafi tare da shi a can za a warware komai

Ta sake shi ba dan ta gamsu zai dawo ba idan ya fita sai dan babu yadda ta iya.

 Bana son ya sake tafiya ya bar ni..

 As long as you're with me you're not alone, you will never be, babu sauran damuwa Hamad ba zai sake tafiya ba..

Captain ya fada mata yana kokarin kwantar mata da hankali. Hamad ya share hawayensa ya ce.

 Idan ace Hajiya bata mutu ba, sai na kashe ta da hannuna...

 Baka bukatar yin haka, jami'an tsaro da kotu zasu yi aikinsu

Captain ya fada sannan ya karasa ya zauna kusa da matarsa ya kama hannunta ya rike sai ta kwantar da kanta jikinsa.

 Da gaske wai Hamad din ne dai? Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'u, wannan wane irin abu ne? Hamad...

Mama Rukayya ta fada sannan ta nufe shi ta rumgume tana kuka sosai shi ma kuka yake yana kewar kanwar mahaifiyarshi...

Sai da suka sake yin two days a garin saboda processing din da Appa ya bi na ganin an samu dawowa tare da Hamad ba tare da wata matsala ba, a tsawon kwanan biyun nan kullum Hurriya tana tare da Hamad sai idan ya bar hotel din zuwa school, idan ya dawo Hurriya tana tare da shi tsawon wunin ranar tana labarta masa abubuwa da suka faru bayan baya nan yadda rayuwa ta zame mata a gidan Appa bayan tafiyarsa har zuwa aurenta da sherin da aka yi mata. Duk abun da suke Captain sai da yayi ta kallonsu gwanin sha'awa domin shi dai be san dadin dan'uwa ba.

 Na yi kewarki sosai Hurriya na fi jin kewarki fiye da kowa, saboda ina yawan dukanki ina zalintarki, da Captain ya fada min cewar bani da kowa a yanzu, sai na tuna abubuwa da nake miki na ji kamar na akashe kaina abun yana ta damuna...

Hurriya tana hawaye ta ce.

 Yanzu duk mun girma Hamad, daman can kurciya ce, kana da zafin zuciya ni kuma bana iya raba kaina da kai, shiyasa har Amma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login