Showing 75001 words to 78000 words out of 279257 words

Chapter 26 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34707

abubuwan amman sau ta rika furta kalama anyhow.

 Hajiya yanzu laifina na rashin bawa Khairi kyauta ne? Zan je na siye na kai mata shi ke nan

Ta yi kamar bata ji ba har ya mike tsaye ya fara tafiya sai kuma ya juyo yana kallonta domin a lokacin ne wani tunani ya zo masa.

 Hajiya me yasa kika damu da zancen siyawa Khairi gift?

Ya tambaya with little confused domin shi be ma tana jin ta yi maganar birthday Khairi ba sai yau kuma ta nuna damuwarta akai sosai.

 Dalili ba na birthday ne ba kawai, ina ta karkata ha hankalinka ka gagara fahimta, saboda hankalin gaba daya yana can gurin matarka

Ya koma ya zauna yana cigaba da kallonta irin kallon nan dake nuna karin bayani yake nema.

 To me nene dalilin Hajiya?

Ta juyo ta fuskance shi.

 Magana muka yi da Hajiya Kaltume ganin Khairi ta gama makaranta yanzu, kuma ba wani tsayaye take da shi ba zamu hadaku domin aminci na da Hajiya Kaltume ya kamata ace akwai auratayya a tsakaninmu ya kamata ace tarayyar ta wuce abokanta

Wani kalar faduwar gaba ne ya same shi, jin yadda Hajiya Fatee ta gabato masa da maganar aure kai tsaye abun da be yi tsammani ba, domin ba shi da ra'ayin aure mace fiye da daya.

 Amma....Hajiya....

Kamin ya furta ta tari numfashinsa.

 Aha... Ai sai ni ita da yake tana da yar albarka tana mata magana ta amince ita da take mace balle kuma ni da nake da an namiji, amman gashi nan zaka fara musamin gashi nan tun ba aje ko'ina ba zaka fara cewa ba haka ba

Ya saka hannu daya ya shafa kansa gaba daya sai ta ruda masa tunani ya rasa ta ina ma zai bullowa lamarin.

 Ai na sani yanzu zaka fara lissafa min cewar baka da ra'ayin aure mace fiye da daya ko?

Ya dago ya kalleta yana shafa fuskarsa sai dai be ce mata komai ba ya mike tsaye.

 Hajiya zan tafi gida

 Toh a gaishe da sarauniya daman ai karshe na san haka za a rabu

Ya sake kallonta cikin yanayi na damuwa sannan ya fice daga falon. Kamar marar lafiya haka ya isa gurin motarsa ya bude ya shiga, yayi zaman minti goma a ciki sannan ya murza key ya juya motar ya fice daga gidan. Kamar baya son driving haka yake tuka motar a madadin ya karasa gurin aiki sai ya koma gida, domin gaba daya jin yake jikinsa ma babu dadi. Tun daga kofar falon ya jiyo sautin muryar Afrah tana rera karatun qur'ane, a fakin ta zauna kan cushion ya dafa kansa gaba daya Hajiya Fatee ta gama ruda masa tunani, shi ko aure zai kara Khairi bata cikin irin matan da yake so, balle ma ba shi da burin na auren mace fiye da daya. Matarsa tana da duk wasu qualities da yake so a jikin mace, kuma suna zamansu lafiya tana masa biyayya daidai gwargwado gata da addini, why Hajiya zata rikita masa lissafi yanzu da wani zancen aure, sanannen abu ne Hajiya bata son matarsa kuma babu wani abu da zai iya yi akan haka sai hakuri.

 Rabin raina?

Ya dago ya kalleta murmushin da yayi arba da shi a fuskarta ya saka shi jin sanyi, daman a duk lokacin da zuciya ta yi arba da wanda take so, idan ta kalleshi farinciki take ji. Kusa da shi ta zauna ta kai hannu ta shafa kansa zuwa bayansa.

 Yau kuma ta ina aka taba angona? Gurin aikin ne ko friends ko kuma a hanya

 Ba ko daya kawai dai bana jindadi ne

A take hankalinta ya tashi ta saka hannunta cikin rigarsa tana taba jikinsa.

 Me ya same ka? Fever ko headache?

 Ba rashin lafiya ta jiki ba, rai na ne babu dadi

Ta mike tsaye ta cire hijabin dake jikinta ta aje ta nufi kitchen sai ya bi kyakkyawar surarta da kallo, skirt din da ta saka irin wannan ne mai bin jiki gashi Allah ya hore mata baya. Tashi yayi ya bi bayanta tana kokarin dauko ruwa a fridge ta ji ya shafa gurin da ya fi ko'ina daukar hankalinsa.

 Wannan kwalliya haka ai sai ki mantar da ni damuwata ma, ni yanzu kin kwashe min tunani gaba daya kin bar kwakwalwar fanko

Ta saka dariya tare da rufe fridge din.

 Kai da ba wani nan wayo ne dan kar na tambaye damuwar kuma sai na tambaya

Ya juyo da ita ya rika bayanta yana kankance idonsa.

 To ai na manta, kin taba ganin an bada abun da babu?

Da sauri ta ja baya shi kuma ya cire hannunsa a jikinsa sakamakon jin motsin yaransu da suka yi, ta nufi gurin cups shi kuma ya juya ya tarbeshi yana murmushi.

 Daddy...

Ya daga ta farin din sannan ya daga mai binta ya aje ya sake daga na ukun da yake namiji ya aje.

 Daddy sannu da zuwa

 Yauwa ashe kuna cikin gidan ko? Da na shigo ban ji motsin yarana ba

 Daddy baka duba dakin mu ba da zaka gan mu ai, Aiman ne ya leka windows ya ce Daddy sai muka gano ka dawo

Babbar data fi su wayo ta fada, ya rage tsawo ya shafa kansu yana murmushi.

 Na manta ai ban duba dakin ba, laifin Momy ne ita ce ta dauke min hankali

Ya dago ya kalleta yayinda take mika masa kofin ruwa sai ya kashe mata ido yayi mata alama da bayanta ba tare da yaran sun gani ba. Dariya ta yi

 Allah ya shirya min mijina

Daga yaran har shi suka amsa da Ameen ya ba su hannu suka tana sannan ya sanye ruwan ya rika hannunsu suka fice daga kitchen din.



KHAIRI POV.


Hajiya Kaltume ta sauko da saurinta cike da karfin hali domin har yanzu kafarta ciwo take. Cikin tashin hankali ta kalli Khairi da Yasir ya gama kumbura mata fuska.

 Lafiya wannan kuka kamar an yi mutuwa?

 Da mutuwa da abun da Khairi ta yi yau duk daya Hajiya. Akan wane dalili zata saka tufafi jiki duk a waje da sunan birthday, daman sai da na ce kar ta yi party nan a waje amman kika goya mata baya, gashi nan na je na ga babu kowa a gurin sai tarin yan iska marasa sanin darajar kai, ita kuma ta saka tufafi kamar wata karuwa

 Haba Yasir haba Yasir saboda wannan sai ka nemi raunata nata mata jiki? Idan ma bata yi daidai ba ne kamata ka mata duka har haka ba

Da mugun mamaki Yasir yake kallon Hajiya Kaltume, ganin tana kokarin kare Khairi instead of ta yi mata fada.

 Hajiya kin san abun da wannan abun zai janyo? Idan hotunan birthday nan suka yi yawo mutumcin Appa da naki duk zai zube a idon mutane, wannan abubuwa da Khairi take yi kina kyaleta ba tarbiya ba ne, tun abun nan yana ga kawayen banza har ta kai ita da kanta yanzu ta fara kwaikwayon rayuwarsu

Hajiya Kaltume ta nufi Khairi dake ta kuka ta dagota tana duba fuskarta.

 To sai ka zo ka nuna min yadda zan yi tarbiyar, idan tarbiya ce ban iya ba, kai ya taka take? An fada maka doka na gyara tarbiya ne? Fisabilillahi ko da Khairi ta yi ba daidai ba fada ba zai isa ba sai ka sauya mata fuska haka ko'ina jini kamar mai fada da sa'ansa? Bana goyon bayan ta aikata abun da zai zubar mana da mutumci amman wannan hukuncin naka ba zan lamunta da shi ba, wata kila ma cikin mutane ka rufe ta da dukan

Dubanta yayi irin duban da magana ta makale masa a makoshi yake ganin kamar furta ma ba shi da amfani, ya kalli Khairi da har lokacin take zaune a inda ya wurgar da ita tana kuka ya dauke kai ya fice daga falon.

 Oh ni wannan Yasir sai zuciya ta yi ta dibansa yana kai miki hannu kamar wanda ta kashe masa wani

Cikin kuka Khairi ta ce.

 Hajiya ba laifinsa ba ne, Hurriya ce ta fada masa yana shigowa dakin taron ya hau ni da duka a gaban mutane sannan ya fito da ni ya saka ni a mota yana ta zagina

Hajiya ta zauna a kujera tana hade fuska.

 Ja'irar yarinya wato ita nan har ta iya munafurci, to yayi kyau zata ko ci ubanta a gidan nan, ke ma kuma da laifinki miye na zuwa ki yi wannan shigar rabin jikinki duk a waje, Fisabilillahi Khairi wani mutumen kwarai ne zai so ganinki haka? Dan Allah ku rika kiyayewa mana muna fa cikin makiya da basa son cigaban mu, abu kadan dariya za'ayi mana a ji dadi

 Wallahi Hajiya ba ni kadai nake jan abun magana ba, Hurriya ma baki ga mutanen da suke mata magana ba a gurin, babu wanda be san Adam ba dan gidan Alhaji Buba Sarauta yaron da yayi kaurin suna gurin iskanci amman haka ta zauna yana ta zuba mata dollars har daukarta yayi suka fita ya dawo da ita, amman da yake makira ce shi ne ta kira Yaya ta fada masa ya zo ya tarwatsa min taro

Ta karasa tana jin wani irin bakinciki ko cake din birthday da ta kashewa kudi mai yawa bata ci ba. Gashi kuma Yayanta ya ci mutuncinta a gaban friends dinta on a special day like this one zai zame mata abun magana.

 To an yi mugun gado, indai shigewa maza ne Hurriya ta fara yi to gurin uwarta ta gado, ba yau aka fara ba a nono ta sha, ba haka ta yi har ta aure min miji ba, ai barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba, kamar kumbo kamar kurensa. Tashi ki saka rufafin kwarai mu tafi asibiti a duba fuskar nan taki kar ta kwana tana miki zogi

Ta tashi daker tana kuka sosai ta nufi stairs sai a lokacin suka lura da Ruma dake tsaye a stairs din tana kallonsu ita bata sauko ba kuma ita bata koma ba.

 Toh lafiya? Kin san yanzu kin zama aljanna ni tsoronki ma nake, kin zama wata halittar ta dabam a cikinmu

Hajiya ta fada tana nuna Ruma da har lokacin bata ce komai ba, sai ma juyawa da ta yi ta koma sama, gaba daya ta canja tun bayan da ta dawo daga hannun masu garkuwa da mutane ta tsani gidan da mutanen cikinsa, ba kasafai zaka ganta a wani abu da kowa yake tarayya ba, wannan dalilin ya hanata zuwa birthday din Khairi kuwa da kusanci na kasancewarta yar'uwarta. Hajiya kamar wata gurguwa haka ta hau sama daker ta shiga nata dakin ta dauko mayafinta da jakarta sannan ta kira direba ta fasa masa ya kunna mota za su fita. Sai da ya shiga dakin Khairi sai ta same ta har lokacin kuka take tana zaune a kasa.

 Ba zaki je ba na tafi? Ba saboda zuwanki ne kadai ba ina son na kai kafar nan a duba min

Cikin kuka Khairi ta kalleta ta ce

 Hajiya ba ki ga wulakanci da Hurriya taja aka yi min ba Wallahi, Yaya ya wulakanta ni gaban friends dina

 Toh ya zaki yi sai ki yi hakuri munafurci daman ai ya cikawa Hurriya ciki, ganewa ne ba a yi sai yanzu amman na san maganinta ai, ke ma kuma fa baki kyauta ba ni Allah yasa dai Fadeel be ganki da wannan shigar ba, abu kamar karuwar Lagos haba Khairi

Ta tashi tana kuka ta nufi gurin da tufafinta suke ta bude, cikin kuka ta canja tufafin sannan ta biyo bayan Hajiya Kaltume da tuni ta sauka kasa.



HURRIYA POV.

Tana tsaye a waje har Yasir ya fito ransa a bace ya sake shiga motarsa da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dan leka bangaren Hajiya Kaltume kamar zata shiga wai dan ta wanke kanta ta fadawa Khairi da Hajiya Kaltume ba ita ta zugo shi ya shigo gurin ba, sanin ba za su kwashe da dadi ba ya saka ta juya ta fice daga bangaren ta nufi bangaren Momy. A hankali ta tura kofar falon ta shiga tsoron dake cikin cikinta ya hanata sallama har ta isa tsakiyar falon.

 Salon labe ne ko kuma rainin wayo? Zaki shigo min falo babu sallama?

 Yi hakuri Momy mantawa na yi

Ta fada da muryarta da bata gama fita ba.

 Daga ina kika?

 Gurin Birthday din Yaya Khairi

Momy ta dauke kai ta cigaba da latsa wayarta, Hurriya na ganin haka ta raba ta haye sama ta shiga dakinta. Sai kusan magariba Namra ta dawo gidan, tufafinta kawai ta cire ta shiga dakin Momy tana bata labarin abun da ya faru ita kanta ta cika da mamaki irin shigar da Khairi ta yi ga kuma wasu watsassun kawayenta da bata san a ina ta samo su ba.

 To ke me kike baki dawo gida da tun dazun ba?

 Momy ina can ina jiran wanda zai dauko ni fa, gaba daya a hargitse aka watse taron saboda Yaya Yasir ni ma ba dan na boya ba Allah kadai ya san kalar dukan da zai min

 Ya dokeki saboda shi ya haifa ki? Ai ba zan dauki wannan ba, ya taba dinka kala daya ya kawo miki? Sai yanzu da girmanki zai ce ya saka miki hannu ya dakeki saboda bikin da kanwarsa ta shirya?

 Momy dan baki ga bikin ba ne, bari na nuna miki dress din Khairi kamar ba yar gidan nan ba

Ta shiga gallery wayarta ta kama hotunan da ta yi ma Khairi tana nunawa Momy.

 Momy kalli fa, ni ma raina ya bace da abun da ta yi Wallahi, ai na jidadi da Hurriya ta fadawa Yaya Yasir ya zo ya watse taron nan

 Au Hurriyar ce ma ta fada masa abun da ake yi? Ina ta ganshi to?

 Oho mu ma kamar daga sama muka ganshi ina ganin ya fada jibgar Khairi na boya ban bari na ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?gan ni ba

page 10

 Ikon Allah yaushe kuma Hurriya ta fara zama munafuka? Hada yaya da kanwa? Wannan kam ba shi da kyau ai, ko bata fada masa ba ai ya san kanwarsa zata aikata yadda take jin ita sa'ar kowa ce kawaye babu na albarka ai dole ma ta aikata, kuma Alhaji ba zai ce komai ba duk abun da Kaltume ta yi ai shi ne daidai a gidan nan ita da yaranta yanzu basa laifi

 Gaskiya Momy kawayenta gaba daya babu na gari, wani dayan frind dinta ya zo yana yi ma Hurriya liki da dollars

 Rawa ta yi

 Aa Momy kin san ai ba zata yi rawa ba, Momy kin san shi ma Adam ne fa, dan gidan Sarauta

 Ba dai dan Hajiya Nana ba?

 Shi fa, yaron nan yana wasa da kudi

 A ina ta san shi?

 Ni ma ban sani ba, bari ma na tafi na tambayeta

Ta tashi da saurinta ta bar wayar a gurin ta fice daga dakin Momy bata zame ko'ina ba sai dakin Hurriya. Cikin natsuwa irin na masu son gulma ta tura kofar dakin ta shiga, Hurriya na tsaye jikin windows, dan kwalin abayarta ya sauko saman wuyanta hannunta kuma yana wuyanta tana shafawa zuciyarta kuma ta tafi wata duniyar karatu.

 Hurriya...

Ta juyo ta kalli yayarta, Namra ta maida kofar ta rufe ta nufi gurin da Hurriya take tsaye.

 Me kike yi

 Ba komai kawai ina tunanin Hamad ne

Ta fada tana sauke idonta kasa.

 Ke dai kin saka Hamad a ranki Hurriya, idan yana raye Allah ya bayyana shi idan kuma ya mutu Allah ya jikansa da Rahma

 Amin

Hawaye ya sauko mata.

 Da ace yana nan kusa da mu, wata kila da yanzu muna son junanmu ba kamar baya ba, wani lokacin ina jin bukatar abokin tattaunawa, har yanzu na kasa sabawa da rashinsa ina jin kadaici sosai

 Ki yi ta addu'a abun zai cire miki In Shaa Allah, amman shiga damuwar da kike ina tunanin shi ne silar daya kara jefa Amma cikin damuwa

 Ina kokari Yaya Namra bana bari ta gane ina cikin damuwa

 Haka na da kyau, yauwa Hurriya kin san wannan wanda yayi miki karin kudi dazu?

Ta share hawayenta da gefen hannun rigar abayar.

 Aa ban san shi ba, dazun ne ma na fara ganinsa

 Toh amman kuma yake miki karin kudin haka nan kawai?

 Ni ma abun ya ba ni mamaki sunana ma ban san inda ya ji ba

 Maybe ko ya sanki wani gurin ke ce baki san shi ba

 Ni da ba fita nake ba, amman ni ma mamaki nake

 Toh ki yi hankali da shi yaron nan dan shaye shaye ne

Ta amsa mata kai kamin ta ce.

 Yaya Namra dan Allah zaki taimaka min na fadawa Hajiya ba ni na kira Ya Yasir ya shiga ciki ba?

 To waya kira shi?

 Ni amman na ce masa ya zo ya dauke ni ne kawai saboda wannan saurayin ya takura min kuma ba ni da wanda zai kai ni gida, amman WallahI ban ce ya shiga ciki ba

 To ai ke kika yi kuskuren Hurriya kema kin san dole zai shiga ai, kuma yanzu babu mai wanke ki a gurin Hajiya

 Ba Hajiya kadai nake tsoro ba, har da Yaya Khairi na san ni zata dorawa laifin

 To kije ki ba su hakuri mana

 Zan yi haka

Ta fada cikin yanayin damuwa wasu hawayen na kara cika idonta. Namra ta fice tare da ja mata kofa. Hurriya ta kai hannu ta taba hancinta kamin ta dago ta sake juyawa top side view ta rumgume hannayenta.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login