Showing 267001 words to 270000 words out of 279257 words

Chapter 90 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34635

ta yi maka takwara ban yarda ka mutu ba..

Captain ya mika mata waya.

 Cry Cry Baby Ammy zata yi magana dake

Ta karbi wayar ta kara a kunne.

 Hello Ammy ina wuni..?

 Lafiya kalau, ya idon naki?

 Alhamdulillahi ina ta samun sauki

 Ya na ji muryarki wani iri? Ko Captain din ne yayi miki wani abun?

 Aa ba shi ba ne

 Ba shi wayar

Hurriya ta mika masa wayar sai ya zauna kusa da ita ya kara wayar a kunne.

 Ammy

 Wani abun ka yi mata ne? Na ji kamar tana kuka?

 Ban mata komai ba, ya za'ayi na mata wani abu Ammy yaushe muka yi auren ma da za'ace har mun fara samun tsabani?

 To waye be san halin maza ba? me take yi ma kuka?

 Tana tare da dan'uwanta ai na fada miki abun da ya faru, kuma idan suna tattauna labarin baya tana yawan kuka shi ne kawai

 Ayyah ba ka ce gobe za su dawo ba?

 Eh in Sha Allah daman amincewar makaranta Muke jira kuma sun ba mu takardar a rubuce za mu taso gobe da safe da yardar Allah

 Allah kawo ku lafiya, ku kula da kanku

 I will i love you Ammy

Ta gwatsale shi.

 Dan Allah can ko kunya baka ji a gaban matarka da kanenta sai ka ce wani yaro

Yayi dariya ya sauke wayar. Hamad ya kalleshi.

 Kai mutumen kirki ne Captain ka kula da ni yadda ya kamata, Hurriya ta ba ni labarin yadda ka yi mata yaki, amman me yasa ka ce min kowa ya mutu?

 Idan mun je zaka ji

Captain ya juyo da fuskar Hurriya

 Mai tsada me za miki order?

Ta juya ta kalli Hamad.

 Hamad me zaka ci?

 Haba Baby ina lallabaki ki ci abinci ke kuma da wannan gwaskan kike? Babu inda be sani ba a garin Addis Ababa ki daina damun kanki da cinsa

 Ko a gida haka muke, inda har zan ci abinci to zan zuba masa ne ya ci, ka yi hakuri

Yaja hancinta yana murmushi.

 Tsokanarki nake, tambaye me yake so sai na siyo muku

Hamad yayi murmushi yana ganin kamar mafarki ne, wai yayarce da mijinta zaune tare da shi a yau.

 Yayata mai kaunata yar'uwata abar alfaharina

 Ba ka ce ni ba yayarka ba ce?

Ta tambaya tana hawaye shi ma hawayen yake yana murmushi.

 Ada kenan yanzu na bar miki girman

Ta yi murmushi cikin hawaye, Captain ma Murmushi yayi ya tashi ya fita.

Ya sake daukarsu awa biyar da mintuna kamin su iso Nigeria daga babban birnin Ethiopia. A Abuja suka sauka, ba su tsaya komai ba suka sake booking flight from Abuja to Kaduna, Ammy ta yi musu tarba ta musamman tana ta na'am na'am da matar danta kamar daman can babu wani abun da ya taba shiga tsakaninsu. Sai da suka yi wanka suka huta sannan suka hadu a teburin cin abinci da yake gidan. A nan Hurriya ta gane ubanta Alhaji Haruna Mai Yadi karyar arziki yake domin falon Ammy ma ba tile ba ne wani abun ne aka shimfida mai kamar ruwa, ga manyan kujerun da bata taba ganin kalarsu ba a rayuwarta, dinning din ma wani abun kallo ne a gurinta balle kuma dakin da suka sauka. Ko'ina na gidan kyalkyale ni kamar an watsa zinari. Bakauya ta zama a gidan komai ta gani sabo yake zama mata, a nan ta yarda da Momy take ganin kamar bata dace da auren Captain ta bangaren arziki. Masu aikin gidan ma kansu abun kallo ne basa barin komai ya zuba a kasa da zarar an aje abu za su zo da gudu su dauke.

Captain da kansa yaja mata kujera ta zauna, sannan ya zauna yana magana da mahaifiyarsa da ta zabi serving din matarsa da kanta ba kamar Momy Ikilima da Mama Rukayya da masu aiki suke zuba musu abinci ba, sai da ta fara ajewa Hurriya plate din abinci sannan ta zubawa Captain ta aje masa warin kwai dake kan salad ya saka shi jin tashi zuciya da sauri ya kawar da fuska yana yunkurin amai.

 Me ya faru wani abu ka gani a abinci?

 No kwan ne na ji shi wani iri, bana son warinsa

Ammy ta dauke plate din ta zuba masa wani abinci babu kwai har ya fara ci sai kuma ya ji baya son abinci kawai wani abun kwadayi yake so.

 To ko dan kun yi tafiya a jirgi ne?

 Ammy karki sa na ji kunya mana, yau na saba hawan jirgi?

Hamad ya kalleshi.

 Ko dai baka da lafiya ne?

 I think so, jikina ma yayi zafi, tun da muka je ba wani lafiya nake ji ba, kawai dai ina daurewa ne saboda akwai abubuwa da yawa a gabana

Ammy ta kalli Hamad.

 Wannan ne yaron? Shi da wanda kake yawan zuwa Ethiopia gurinsa daman? Da zarar ka samu sarari sai ka tsallake ka tafi Ethiopia ashe duk saboda shi ne?

 Wallahi kuwa Ammy

 Bari na kira Family Doctor ya dubaka kamin ku tafi

 Okay

Ammy ta tashi ta bar dinning din, Captain ya kalli daya daga cikin masu aikin gidan ya ce.

 Samo min wani abu mai ruwa ruwa na sha

 To ranka ya dade

Sai da Ammy ta kira likitansu na gida ya zo ya auna Captain ya duba shi ya fada musu fever ne kawai yayi masa allura ya kuma dorashi akan magunguna sannan suka bar garin Kaduna a business flight din Daddy da baya kasar domin ta waya ya gaisa da Hurriya yayi mata maraba da zuwa gidansa kuma ya saka Ammy ta hada mata goma ta arziki a madadinsa.

*A duk lokacin da nake littafi sai an tambaye ni minene POV saboda ina saka shi a duka books dina, POV yana nufin POINT OF VIEW. idan wata ta sake tambayata sai na cire mata hakorin gaba >?t?*

HAJIYA FATEE POV

 Hajiya jikin ne dai?

Fadeel ya tambaya yana taba jikinta cike da damuwa Hajiya Fatee ya dago ta dubi danta, cikin bakinciki da nadama ta ce.

 Ko da jikinki bana bukatar tafiya asibiti yanzu Fadeel, ku bar ni na yi abun kunyana a nan idan ma kasheshi saku yi ku kashe, bayan na tafi

Afrah ta girgiza kai.

 Haba Hajiya ki daina fadar hakan, abun da ya same ki kaddara ce daga Allah, kowa da yadda Allah ya rubuta masa kaddararsa, zai iya samun kowa, Allah ya tsare mu da kashe abun da kika haifa, ko me kika aikata muna son rayuwarki kuma ina sonki a haka saboda kw mahaifiyar Fadeel ce ina son miJina ba zan taba tsanar mahaifiyarsa ba

 Na yi abun kunya, sanar matar ana ina ta ganin kamar kin tare shi daga gareni ashe sheidan ne yake ta min gizo da sake sake, dubi yadda na zama na janyo muku abun kunya

Fadeel ya sauke ajiyar zuciya, tabbas idan har duniya ta san halin da mahaifiyarsa take ciki zai ji kunya ba karami ba, daga lokacin da na gane gaskiyar abun da take boye masa har zuwa lokacin da ta bayyana masa gaskiyar komai da komai be sake walwala ba, ba sake kwantawa bachi ya dauke shi ba, be sake kallon wani abu yayi dariya ba gaba daya farinciki ya kaurace masa.

 Zan tafi na bar muku abun kunya Fadeel, dan Allah ka yafe min kuma ka kula da yar'uwarta, ka fahimtar da ita ban kai aikata aka min cikin nan ba sai dan kaddara ta biyo ta nan

 Karki damu Hajiya, Zainab zata dauko kuma zaki samu sauki ki tashi da yardar Allah, ko ma miya faru mu dai muna son rayuwarki

 Mutuwata tafi rayuwata Fadeel bana fatan rayuwa idan ma na haihu lafiya, idan kuma ban haihu ba, kun huta karku fadawa kowa abun da uwarku ta yi, Afrah ki yafe min dan Alla..

 Na yafe miki Hajiya Wallahi ni ban rike da komai ba

 Allah ya muku albarka... Tashi ka tafi gurin aikinka, ga matarka nan ai ta isa tana kula da ni

 Toh Hajiya

Ya mike tsaye ya fice daga dakin. Kusan tun da gaskiyar cikin ta bayyana shi da yar'uwarsa suka ji cewar ba kari ba ne, cikin shege ne Hajiya Fatee ta yi Zainab ta bar gidan ta koma gidan kanen mahaifinsu kuma ta kasa komawa gidan mijinta saboda uwarta ta yi abun kunya, sai kulawar Hajiya Fatee ta dawo karkashin Matar Fadeel wato Afrah wanda ya maida ita gidansa bayan fasa auren Khairy da yayi daman ba shi da burin auren kawai yana biyayya ga cilastawar mahaifiyarsa ne. Matar da take zagi take cewa ta mallake mata a matar da saboda ita wannan mummunan kaddara ta same ta yau ita ce take kula da komai nata take mata komai kamar yarta, kusan a gidan ta tare ita da yaranta saboda kula da uwar mijinta.
?? A ranar da Hajiya Fatee ta yi ma danta da matarsa wasiya kuma ta roki gafararsu a ranar ta yi musu bankwana, a ranar ita da danta ba su kwana duniya ba, cikin dare nakudar data shekara ashirin da wani abu rabon da ta yi kalarta ta taso mata, idan Fadeel yayi yunkurin kiran wani ko kaita asibiti sai ta hana tana fadin ya barta ta mutu cikin gidanta domin ta san cikin nan ba zai barta ba, daga karshe da ya ga wahalar ta yi yawa sai ya dauko mota kamin ya saka ta ciki ta ce ga garinku ita da danta. Rufin asirin da take rokon Allah yayi mata na mutuwa cikin gida ta samu wannan an karba mata, kamin safe fuskar Fadeel da Afrah ta kumbura sosai saboda kuka. Haka Afrah ta rinka rusa kuka kamar uwarta ce ta mutu tana matukar jin tausayin mijinta da ya rasa uwa da kuma tausayin Hajiya Fateen. Sai yafiyar Allah take roka mata, wani kukan ba tashi a gidan ba sai da yarta Zainab ta zo ta fara nadamar tafiyar da ta yi ta bar mahaifiyarta cikin fushin abun da ta aikata musu ashe ma ba mai dade bace a duniya, a yanzu kam sun zama ba su da kowa daman uban ya dade ta rasuwa yanzu kuma uwa ta bi bayansa. Har aka yi amsar gaisuwa aka kare Hajiya Kaltume bata zo gidan ba, sai da aka kara kwana sannan Yasir ya zo gaisuwa gurin Fadeel Maama kuma ta shiga ciki ta yi ma matan. Yasir ya fada masa halin da Hajiya Kaltume take ciki na rashin lafiya da ba zata ita zuwa gaisuwa ba, sai Fadeel ya tausayawa mata duk da kasancewar Yasir din be fito fili wikiwiki ya fada masa hauka take ba. Sai dai hakan be hana shi tausaya masa ba, domin daga ta shi Hajiyar har Hajiya Kaltume bin bokaye da rashin yarda da kaddara be haifar musu da an mai ido ba.



***? ?? ***? ?? ***

Lokacin da Captain ya kira Appa ya fada masa sun kusa shigowa garin Gusau, sai Appa ya fadawa Amma ita kuma ta kira mutanen gidansu ta fada musu sai duk suka taru a gidan na Appa a bangaren Amma. Shi kan shi Appa sai ya dawo gida da wuri, kamin su iso, Amma ta kasa zama ta kasa tsayuwa sai safe da marwa take ta kagara ta ga anta shi din ne ko waninsa. Suna Haka Hajiya Binta ta iso daman tun da Appa ya fada mata take ta mamaki kuma take daukin ganin jikan nata.

Duk yadda Appa ya so ta natsu sai ta kasa saboda abun da yake gabanta ma son ganin Yarta da anta. Daga Hurriya har Mama Rukayya babu wanda ya san da daurin auren Alhaji Haruna da Iyami da aka sake daurawa bayan dawowarta saudi balle tarewar Amma a gidan Appa sai da suka dira a gidan.

Motarsu na tsayawa Amma ta fito da sauri tana sanye da Hijab. Hindu, Gwaggo da Inna Uwani suna bayanta Appa tare da Alhaji Musa da Malam Zakiyyu kanensa da Hajiya Binta duk suna tare da shi, Yasir ma da a lokacin ya iso gidan ya fito motarsa da sauri yana kallon Hamad da Hurriya da suka fito motar. Amma ta durkushe a kasa tana rufe baki tana kuka, tabbas danta ne amman kamaninsa sun sauya yanzu girma ne yake kamashi ya zama ba kamar lokacin da aka dauke shi ba, banbancin wacan ranar da Ruma ta fito mota tana fada mata Hamad ya mutu da wannan shi ne wannan yana a raye ne, amman kukan kusan daya ne, Appa ma hawaye yake kusan kowa kuka yake har shi kan shi Hamad ne.

Amma ta dubi Hurriya dake kallonta garau tana gani babu gilashi ga kuma Hamad sai ta juya baya tana kuka tana godiya a gurin Allah. Hamad ya nufi inda take da gudunsa yana kuka kamar za a cire masa rai irin kukan da ya fi kama da rashi. Ya rumgume Amma yana kiran sunanta jikinsa na rawa muryarsa na rawa Amma ma ta rumgumeta danta tana kuka sosai. Hurriya ma kuka take Hajiya Binta, Rukayya Yasir kusan kowa sai da yayi hawaye a gurin saboda tausayi. Amma ta taba fuskarsa ta taba kunnesa ta lalaba jikinta ta shafa bayansa kamar wanda ta rude.

 Hamad... Hamad... Hamad.. Hamad... Allahu Akbar.. Hamad.. Da gaske ne ashe Hurriya gaskiya ta fada maka mutu ba...

Hamad ya dago ya rumgume Appa yana kuka.

 Na yi marmarinku Appa na yi kewarku, rayuwar da babu iyaye babu dadi no matter what mutum zai samu a duniyar nan

 Mun yi bakinciki rashinka Hamad ashe kana raye, Alhamdulillahi

Appa ya share hawayensa sannan ya kalli yarsa yana murmushi.

 Hurriya an samu lafiya Alhamdulillahi

Hurriya ta nufi mahaifinta ta rumgumeshi tana kuka.

 Kukan ya isa haka ku shiga ciki mana

Hajiya Binta ta fada, sai da Hamad ya rumgume kowa a gurin sannan ya daga kansa yana kallon gidan ta ko'ina.

 Ashe zan dawo na yi rayuwa a nan

Ya fada yana tuna ranar da Amma ta shirya kayanta zata bar gidan, tana boye musu sakin da Appa yayi mata, shi kuma a lokacin ya gama fahimtar komai saboda ya fi Hurriya wayo da fahimtar abubuwa. Yasir kallonsa yake yana jin tausayin mahaifiyarsa ita kawai yake tunawa halin da take ciki? yanzu da kuma wanda zata shiga a nan gaba.
A falon Amma suka zauna gaba dayansu, Hurriya na ganin yadda aka kawata falon aka saka furniture da komai ta fahimci Mahaifiyarta ta dawo sai farinciki ya lullube ta daman abun da take da burin gani tuntuni kenan dawowar mahaifiyarta a gidan.

Sai da suka yi sallah suka dan huta sannan suka sake haduwa a bangaren Appa har Momy da yaranta Hamad ya ba su labarin yadda aka daukeshi zuwa lokacin da suka buga masa karfe a kai suka fita da shi daga dakin be sake sanin inda yake ba sai da ya farka ya ganshi a wata kasar tare da wasu mutanen da ba yarensa ba kabilarsa ba.

 A haka na yi ta rayuwa a cikinsu, sun suna min kauna sosai sun dauke ni kamar ansu ba su tana muna min banbanci ba, saboda mahaifiyar Salim mace ce mai son mutane, musamman ni, tana yawan cewa tana ganina kamar anta Salim ne, tun daga lokacin da Captain ya fada min cewar ba ni da kowa a duniyar nan, sai na rike su a matsayin yan'uwa da iyaye amman babu daren da bana kewarku...

Captain yaja numfashi ya sauke har lokacin yana jin fever dake tare da shi ya kwadayin son abu mai ruwa be fita jikinsa ba.

 Wannan dalilin ne kadai ya saka na dagawa Salim kafa, ta bangaren nan yayi min hallaci kuma mahaifiyarsa ta cancanci ko wane kalar tukuici daga gareni

 Me yasa ka ce min kowa ya mutu?

Hamad ya tambaya, sai dai Captain be kula tambayarsa ba ya dauko zaren labarin tun daga tushe.

 A ranar da na zo gidan nan, na shiga bangaren Momy na samu Hurriya tana kuka ta fada min cewar an dauke dan'uwanta, kamin ita Namra ta ba ni labarin abun da ya faru saboda tana saka ran ko akwai hannuna a ciki ne saboda fasa min tayun mota da Hamad yayi da kuma kyautar da na yi ma Hurriya a lokacin ta gilashi sai ta ki ta karba, na ce mata sai na dauki mataki, a yanayin yadda aka ba ni labarin ma sai na fahimci ba Hamad aka zo dauka ba Hurriya aka so sacewa da ba sameta ba ne aka dauke Hamad, a ranar Hurriya ta roke ni wata alfarma ta tambayi sunana na ce mata ni Soja ne sai tace Malam soja ka nemo min dan'uwana dan Allah, ni kuma na mata alkawarin zan nemo mata shi har na yi mata rubuta a takardar na ranar da na dauki alkawarin da sign na bata, tun daga lokacin sai na baza mutane na neman yaron sai dai ba a same shi ba sai after an yi sanarwar cewar ya mutu a nan, sojojin da suke aiki a hanyar sokoto suka samu gawarsa a cikin wata gona shi ma kuma saboda sun za su shiga cikin kauyen dake gurin ne gurin kai farmaki, a take suka sanar da da headquarters Mu cewar sun samu gawar yaron da na ba da cigiya na shigar da report akansa, su kuma suka sanar min, a take na shirya ni da kaina na tafi gurin tare da wasu soldiers daga headquarter saboda bincikar yadda komai ya faru, sai muka samu har lokacin yana zubar da jini fresh blood ba daskarare ba irin na wanda ya mutu, kuma da na taba shi sai na samu yana da rai amman baya numfashi, a take muka dauki gawarsa zuwa asibitin tureta dake sokoto muka saka likitan gurin ya duba shi sai ya fada mana cewar alama sun nuna yana raye, amman yayi nisan da abu ne mai wahala ya iya tashi saboda

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login