Showing 30001 words to 33000 words out of 279257 words

Chapter 11 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34622

nata haka ba sai dan ta takura mata idan kuma ta fadawa Appa wata kila zata iya jawa kanta matsala a gurin Momy. Dakin dan'uwanta ta fara gyarawa sannan ta shiga nata dakin ta fara sharewa. Cikin Woki Hamad ya shigo dakin nata.

 Hurriya za mu je dauko Hajiya yanzu

Ta juyo ta kalleshi da sauri.

 Wace Hajiya

 Hajiyar Appa tace zata zo, Appa ya kira ni yace na zo muje daukota yanzu nan

Hurriya ta daka tsalle tana murna, daga ita har Hamad suna matukar son zuwa gurin Hajiya Binta kuma suna daukin ganinta a gidan ubansu, al'adace ta Alhaji Haruna, duk ranar da mahaifiyarsa zata zo gidansa da kansa yake zuwa ya daukota idan kuma ta tashi tafiya shi zai maidata gidanta, komai yake zai aje ya dauko ko ya kaita gida matukar gidansa zata zo, wannan ya saka tun ana sauran kwana biyu ta zo gidan take sanar masa, shi kuma ya sanar ma matansa a shirya mata tarba mai kyau. Murmushin da murnar da Hurriya ta gani a fuskar dan'uwanta Hamad ya ninka farinciki zuwan Hajiya Binta da take a gidan, domin tun tafiyar Amma bata san wata rana da Hamad ya sake fuska yana far'a kamar yau ba.

 Zan mata wanka mai kyau kin san ta iya tsokana ta tana cewa ban iya wanka mai kyau ba, tufafi zan canja yanzu nan

Da karfi yake maganar, kamar yadda ya saba yi a bangaren Amma idan yana cikin farinciki. Hurriya ta yi saurin yi masa alama.

 Yi a hankali kar Momy ta ji ta fara maka masifa?

 Saboda me?

 Bata son hayaniya kuma tace idan zamu hauro ko sauka stairs mu yi a hankali kar mu yi making sound bata son ana hawa mata da karfi

 Yaushe tace haka?

 An dade, kai ai ba zama kake bangaren ba sai idan zaka kwanta shiyasa baka sani ba

 Sai na fadawa Hajiya duk abun da ake mana a gidan nan

Hurriya ta saki mopper dake hannunta ta nufo kofar dakin gun da Hamad yake tsaye.

 Hamad kar ka yi haka, kasan zata yi ma Appa fada shi kuma zai yi ma Momy, idan aka yi Momy kuma kan mu zai dawo

 Sai na sake fada mata, Appa ma dan ina fushi ne da shi shiyasa ba zan fada masa ba, ni ba zan ma iya zama bangaren nan ba i hate them

Ya saki kofar ya nufi tasa kofar ya bude, Hurriya ta dora hannu daya akai tana jin ina ma ace bata fada ba, tsoro take kar ace daga dawowarta bangaren ta fara hada munafurci, kuma ta san at the end abun gurinta zai dawo. Hamad na canja tufafi ya dauki turare ya saka ya canja shoes ya fito daga dakin ya sauko kasa ya fice daga falon daga Miwan har Namra dake falon be cewa kowa komai ba. Miwan ya bishi da harara

 Yaro nan fa ya raina mutane, idan zai shigo haka zai shigo babu sallama idan ya tashi be iya gaishe da kowa

 Yaya idan ka ce zaka biye ta Hamad za ku yi ta samun matsala ne fa, Amma ma da tana nan fama take da shi balle kuma mu

 Ba ruwana da rashin jinsa ko rashin kunya ni ubansa zanci Wallahi

Ya amsawa Namra yana ayyana yadda zai yi ma Hamad mugun duka idan ya shiga gonarsa. Namra dai bata sake cewa komai ba ta shiga ta jera warmers din da masu aikin Momy ke ajewa a kasan dinning, Hurriya ce ta fito rike da boket din da ta yi mopping da mopper ta nufi hanyar tsakar gidan dake ta cikin falon Momy ta bude kofar baya ta fita ta wanke komai sannan ta dawo cikin falon, a daidai lokacin da aka turo kofar falon aka shigo wata doguwar mace ce tana sanye da bakar abaya da aka kawata da blue stone ta daura dankwalin atamfa saman kanta sannan ta dora mayafin abayar a sama ya sauko mata, hannunta na rike da Gucci bag, tsalle Namra ta saka ta kwala ihu ta nufi matar da alama ta nuna murmushi sai ma sai yayi yaki yake samun mazauni a fuskarta, kallo daya zaka masa ka fahimci ta ninka Momy kasaita da ji da kai.

 Ammy sannu da zuwa

Cewar Namra cikin zumudi tana rumgumeta, Miwan ya mike tsaye yana gyara rigarsa tare da yi mata barka da zuwa.

 Namra...ana gida

Ta fada kamar mai jin wahalar magana.

 Eh Ammy sannu da zuwa, tun safe muke duban hanyarki

 Toh gani na iso, Ina Hajiya Nafisa?

Ta tambaya tana kallon Hurriya da ta yi tsaye da ta fito daga dakin da da ake aje mopper.

 Momy Momy Momy...

Namra ta daga murya tana kiran Momy, Hurriya kuma ta dan risina kamar yadda ta saba ta gaisheta.

 Ina wuni

 Lafiya...

Ta amsa tana binta da kallo tare da dan yamutsa fuska.

 Ita ce .....

 Hurriya

Namra ta karasa mata, sai ta watsawa Hurriya wani kallo daga sama har kasa ta yamutsa fuska kamar wadda ta yi arba da wani abun kyama. Hurriya ta kalli jikinta sannan ta kalli matar da tuni ta kama hanyar stairs gurin Momy dake saukowa da saurinta tana mata lale marhabun. Da alama Namra bata ji dadin abun da matar da take bakuwa a idon Hurriya ta yi ba, sai ta kama hannun Hurriya ta nufi kitchen da ita suna shiga ta rufe kofar kitchen din ta kalli Hurriya da har lokacin mamakin yadda matar ta yi mata kallon wulakanci take, bayan kuma bata da wani abun wulakantawa a jikinta ko suturarta, gashi alama ya nuna ta santa ita kuma bata wayanci wacece matar da Izza ta cikawa ciki har ta bayyana a kamaninta ba.

 Hurriya dan Allah kar abun da ake miki a gidan nan ya dame ki, kin san dai matsayinki a gidan nan, dan haka karki kula komai kin ji?

Hurriya ta amsawa yar'uwar tata da kai.

 Wacece wannan Matar Yaya Namra?

 Big Brother din su Momy to natarsa ce wannan, ba a nan suke ba, a Kaduna suke zaune ta zo duba mahaifiyar mijinta ne da bata jindadi maybe shiyasa ta biyo ta nan saboda suna good time da Momy sosai

Nan ma da kai ta amsa mata sannan ta juya zata fice daga kitchen din.

 Kin ci abinci?

 Aa Hamad ya ce Hajiyar Appa zata zo, ina jiram ta zo ne sai mu ci abinci tare

 Yayi yar gidan Hajiyar Appa

Hurriya ta yi murmushi ta bude kitchen din ta fito tana rike da hannayenta ta nufi upstairs, Miwan ya wurga mata harara yana jin haushin yadda Namra take mata sanyi ko a lokacin da Amma take nan balle kuma yanzu, hakan ya saka suke mata kallon munafukar cikinsu, domin ita halinta dabam da na su, kishi da ya kamata ace tana taya Momy bata yi ta bar musu sai dai su yi. Hurriya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta nufi gadonta ta kwanta ta takure gurin daya kamar wanda aka tsare sai hawaye ya fara saukowa a idonta, tunanin barin gidan da Amma ta yi ya dawo mata sabo.


**** **** ****

Cikin annashuwa da aukin gani Momy take kallonta.

 Ai har ina cewa maybe ba zaki biyo ba, na ga Yamma ta yi

Matar dake kawar da kai daga barin kallon aikin Momy dake jera mata kayan da aka shirya mata ta kalli Momy.

 Ai kin san halin Captain shi ya fi son tafiyar dare

 Tare da shi kuka zo kenan? Amman be shigo ba?

 Yana waje, waya yake

 Oh Soyyayar da bata karewa, ai dai an kusa auren nan a huta, ke ma ki samu hutawa Ammy

 Toh sai a taya mu da Addu'a Allah ya daidaita tsakaninsu

Tana maganar tare da kai hannu ta dauko plate din grapes din da aka rolling ta cire ledar ta fara ci.

 Tsabani suka samu ne?

Cikin mamaki Momy ta bukaci sani. Kamin ta bata amsa sai da ta juya ta kalli kofar dakin Momy da daya daga cikin masu aikinta taja.

 Wai har cikin daki kike barin masu aikinki suna shigowa?

 Toh ya zan yi Hajiya Turai? Kin san dai ba zan yi aiki da kaina ba, dole su zan saka

 Ai ni iyakacina da mai aiki falo sai kitchen da haraba, har yaushe mai aiki ta yi matsayin shigo min bedroom? Kina gani ai idan kika je gidana, su Larai ke kula min da daki

 Toh ni wa zan saka? Ke ai kina rikon su Larai da Aliya

 Wannan yar mijin na ki da kika fada min ta dawo nan hutu ta zo yi? Idan ma baki sonta sai ki duba a cikin dangi ki dauko wadda zata iya kula miki da daki, amman ba dai masu aiki ba

 Zan duba a dangi, yar miji ina sakata za ace bana kaunarta

Hajiya Turai ta yi murmushi mai sauti tana mamakin sakarcin Momy domin a gurinta abun da Momy take fada ko take gi sakarci ne.

 Ke ma dai ban da abun ki Hajiya Nafisa waya taba son Wa ko ?ar kishiya? Ai ba wani boye boye, ba zan hana ka aure ba amman fa ba zan so matarka da ?a?anta ba

 Ai Wallahi Hajiya Turai ba karamin sa'a kike yi ba, da yayana baya sha'awar aure-aure, ba kamar nawa mijin ba, domin ni ko a yanzu da ya saki Iyami tunani nake ko dai ta dawo ko kuma ya auro wata

 Shi ne banbancin tashi a gidan arziki da kuma cintar arzikin, da ace mijinki ma kamar tashin Engr ne, da ba zai yi wannan aure-aurenba, ai talauci mugun abu ne, da zarar sun ga sun yi kudi sai su ga babu abun da ya dace da su kamar aure, amman Engr kam ai rayuwarta turawace da shi, babu ruwansa da wannan hange-hange

 Wallahi ya huta, da alama ma ana halinsa zai gado

Hajiya Turai ta tabe tana girgiza kai cike da kasaita.

 Hmmm Captain? Ai idan ba Allah ya sauya masa hali ba, da wahala ma ya iya zaman da mata, yanzu ma addu'a muke kar ya ce ya fasa auren, shiyasa na ce ban yarda ya zauna ko'ina ba sai a kusa da ni

Momy ta kasa dariya.

 Haba dai Hajiya Turai

 Hajiya Nafisa kin manta halin an naki? Wannan mugun fushi da bakar zuciyar ta Captain tsoro take ba ni, komai aka yi masa a duniya ba a masa daidai, ko kallonsa kika yi zai iya cewa kallon ya wuce kima ya fara masifa ko ma ya ce hararasa kika yi, yadda kika san shaidan aka nade aka saka masa a zuciya haka, abu kadan sai masifa sai fushi baya iya controlling kansa, ga zafin hannu a family babu wanda be san halinsa ba, ita kanta yarinyar da zai aura yanzu, ba dan tana hakuri da shi ba da yanzu rabu da ita, da inda abun ya zo da sauki ita mai sanyi hali ce kuma tana gudun zuciyarsa

 Toh ai sai a kiyaye, haka Allah yake son ganin kayansa, Captain murdaden mutum ne iya masa sai Allah

 Ina ta addu'a dai Allah ya sauke masa wannan mugun fushi da bakar zuciyar, idan ba haka ba zaman auren ba zai jima ba, kuma ya fada min idan yayi wannan auren ba zai sake yi ba har abada, wai ko matarsa mutuwa ta yi ko suka rabu a haka zai zauna har karshen rayuwarsa, ni kuwa ba fatan haka nake ba,?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ni da nake son na yi ta ganin jikoki a makwafin ?a?an da Allah be ba ni ba

 Gaskiya kam, muma muna son gani ai balle kuma ke da shi kadai kika haifa...

Hajiya Turai na taba kayan marmarin suna hira da Momy har time ya fara ja, hakan kuma be saka sun yanke hirar ba har sai da Namra ta shigo turo kofar dakin ta shigo.

 Momy Hajiya ta iso

Momy ta yatsina fuska domin ta san wace
Hajiyar ake magana, wato Hajiyar Binta surukarta uwar da ta haifi mijinta.

 Toh shi ne kuma sai an fada min? Kin san ai ba nan take fara zuwa ba sai ta gama da ko'ina take lekowa nan, to miye damuwata da ita, je ki fadawa masu aiki su kai mata abinci

"Okay

Ta juya ta fita. Momy ta yi tsargi da fuska.

 Idan ban je na gaisheta ba, sai ki ga ya shigo yana ta bala'i, alhalin ba so take ba, idan ta zo bata sauka bangaren kowa sai na Iyami, kuma sai ta fara shiga bangaren Kaltume sannan take leko nan

 ikon Allah haka take ita kuma! Allah kyauta rayuwarku sai ku Hajiya Nafisa

Cewar Hajiya Turai da kamar gatse tana jin ita duk ba zata iya daukar wannan ba, domin kowa yana da yancinsa. Namra na fitowa bedroom din Momy ta nufi dakin Hurriya ta tura kofar dakin, Hurriya na ji an taba kofar ta yi saurin juya fuskarsa ta boye kukanta.

 Hurriya Hajiyarki ta iso, Appa ya aiko Ya Musib ya fadawa Momy

Hurriya ta share hawayenta da sauri ta juyo, sai gata ta sauko daga saman gadon bata ko kula Namra ba ta ratsa gefenta ta fice da gudu, duk wata dokar sauka ko hawa stairs na Momy manta su Hurriya ta yi a lokacin saboda zumudin zuwan Kakarta Hajiya Binta a gidan, kamar yau ne zata fara ganinta a gidan haka Hurriya ta ji. Da sauri ta bude kofar fita falon Momy bata kula komai ba ta saka kai zata fice, da mugun karfi ta ji kanta ya daki wani abu mai karfi har sai da ta yi baya kamar zata fadi. Dagowar da zata yi ta duba me ta buga domin be yi mata kama da karfe ko icce ba, ta ji an wanke mata fuska da lafiyayen marin da ya haddasa mata ganin wadansu kananan taurari, gilashin da yake mafaka ne a idonta ya fadi kasa, sai hudu da buji suka mamaye ilahirin idanuwanta. Sai ta tsaya cak irin tsayin da ta saba yi a duk lokacin da wani bakon al'amari ya ziyarceta.

Gafen fuskarta ya hau zugi yayi ja, idanuwanta suka masa tantance mutunen da ke tsaye a gabanta, fafadane ta ga hakan a cikin hudun idanuwanta, dogo ne irin tsayin da ta tsaya iyakar kirjinsa. A hankali ta sulale ta kai kasa ta saka hannayenta tana lalaben gilashinta hawaye na kwankwaso mata kofa. Lalabe ta yi ta yi amman ta kasa jin gilashin, kamar yadda ta duka haka ta mike tsaye a hankali ta juya ta lalabi kofar falon ta fara tafiya.

 Hurriya... Me ya same ki

Namra ta tambaya tana nufota da sauri ta kama hannayenta ta rike domin hawaye take kamar an bude kofar fanfo.

 Ya... Ya... Namra... Gilashi... Na...

Namra bata tsaya komai ba ta rika hannunta ta juya da ita suka fita tana janye da hannunta, har lokacin Mutumen da ya mareta yana a gurin tsaye ko yatsansa be motsa ba. Namra ta kalleshi kamin ta sako hannun Hurriya ta fara duba gilashin, can gefe ta hango shi ta nufi gurin da sauri ta dauko mata.

 Har gefen ido daya ya fashe daga sama, me ya faru Hurriya

Ta saka mata gilashin da kanta, lokaci daya ganinta ya dawo fashewar da gilashin yayi ba irin wadda zai hanata gani ba ne, daga sama ne ya fashe shi ma kuma kadan. Hurriya ta daga ido ta kalli mutumen da be mata uzuri ba ya wanke fuskarta mai tsada da mari. Hawaye be daina mata zuba ba, hakan kuma be hana idanuwanta ganin mutumen da kyau, dubansa ta yi ta dube shi, ta sake dubansa sannan ta sauke idonta kasa ta ratsa gefensa ta fara sauka kasa. Slowly ya juya ya kalleta kamar mai son gasgata wani abu ko karyatawa.

 Bata gani sai da gilashi, me ya faru Yaya?

Ya juyo ya kalli Namra a fusace.

 Aza min bindiga sai na fada miki

Jinin jikinta ta sha ta kauce ta ba shi hanya ya shiga ciki, ita kuma ta ja kofar sannan ta bi bayan Hurriya domin gaishe da Hajiya Binta, kamar yadda Appa ya sabarwa kowa a gidan ko baka cikin gidan idan mahaifiyarsa ta zo matukar kana cikin garin sai ka zo ka gaisheta...


[10/18, 5:16 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?

Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


5???5???5???5??? 1?? 3??

Da kallo ya bi Hurriya da Hamad har suka fice sannan ya kalli Hajiya Kaltume ya dauke kai ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa abun da ya fara yi shi ne duba gurin da ya aje gilasan Hurriya, amman be ga ko daya ba, a nan ya fara tunanin ko ya canja musu gurin ajiya ya manta, haka ya bi komai na dakin ya duba ba gilasan babu alamarsu, fitowar yayi mamaki duk ya cika fuskarsa ya sauka kasa sai ya samu mahaifiyarsa a gurin da ya barta zaune sai dai wannan karon waya take amsawa, gefenta ya zauna a hannu kujera har sai da ta gama wayar sannan ya tambaye ko ta dauka.

 Me zan yi da gilasai kuma? Komai dai ni, ubanka ya dora min laifi matan ubanka su adabe ni kai kuma yanzu ka zarge ni da satar gilasan Hurriya saboda ga Kaltume makiyiyarta ko?

Maganar Hajiya bata masa dadi ba kuma ya san duk wani kalami da zai dora bayan nata a yanzu ba zai fahimtar da ita. Dan haka ya tashi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi dakin yan'uwa daya bayan daya ya bi yana tambayarsu kowacce tace masa bata dauka ba, Khairi har da hadawa da rantsuwa saboda ta fi kowa rashin tsoron Allah.

 Toh ko Hurriya ta zo ta dauka ko Hamad ban sani

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login