Showing 207001 words to 210000 words out of 279257 words

Chapter 70 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34654

Yarinyar ido ya rufe mata? Aka tallata tsiraicinta, yarinyar da uwarta ma ga aiki ta yi, talakawa maskakanta, tarin dukiyar Yaya Yau Hurriya ce yarinyar da zata raba a jiki a dukiyar gidanmu, kuma ta bangaren da ya fi gwabi

Daki cinyarta tana jin kamar ta zaga tufafin jikinta, a matukar fucece ta fice daga dakin ta shiga dakin Hurriya ta fara yaye Bedsheets dinta ta jefar tana debo kayanta ta watsarwa abubuwan da ke fashewa kuma tana ta fashe su tana watsar tana kuka.

 Ashe sheri ne ya kawo ki bangaren nan, ashe mugun abu na karba na aje gashi nan kina bibiyata

 Momy lafiya

Namra ta tambaya tana kallon yadda ta watsar da kayan Hurri???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ya ta fasa abubuwa. Momy ta juyo a lokacin da ta kalli Namra sai tausayin yarta ya kamata.

 Yayana ya daureni ya ci amanata Namra, na ci mutunci na ya watsa min kasa a ido, kuma ya nuna min ansa ya fi yar'uwarsa

 Momy dan Allah ki fada min me ya faru?

 Auren Hurriya ya nema a gurin Appanku, Appanku kuma ya amince aka daura auren a cikin gidan nan yanzu nan

Namra ta ji kanta ya dara da karfi.

 Aure abun kamar yar tsana? Ban gane aka daura ba, an taba daura auren haka babu kowa?

 Daga mahaifinku sai Yayana da Yasir aka daura auren

Wani abu ta ji mai sanyi ya ratsa kanta ya sauko har kafafuwanta.

 Momy da gaske...?

 Me zai sa na miki karya.? Yaya yayi min abun da ban yi tsammani ba, da ace wani ne yayi min ba yayana ba zan ji zafi haka ba, amman ba komai kowa yayi mai kyau zai gani kuma Wallahi Hurriya ba zata sake zama bangaren nan ba

Namra ta yi baya baya ta fice daga dakin daman a bakin kofa take tsaye. Dakinta ta shiga ta rufe kofar ta zauna hawaye suka silala mata a hankali.

 Aure?

Ya tambayi kanta abin dai kamar ba zata fahimta ba. Shi ke nan duk wani fata da take da kuma wanda iyayensu suke yi ya tashi a banza yanzu? Hurriya ta shiga tsakaninta da Salim yanzu kuma ta raba ta da Captain ta aureshi? Ta mike tsaye ta isa gaban madubin dakinta ta zauna a stool tana kallon kanta, shi ita bata kai ba ne da Captain be yi hauka a kanta ba? Taya idonsa zai rufe ya tsallake ta ya fada kan yar'uwarta bayan duk abun da ya faru da Hurriya, to da bata aikata ba ai ta yi abin kunya, ta yi abun da cikaken namiji mai aji irin Captain zai guje ta zama matarsa ko dan saboda kunyar duniya. Salim ma ya kusa hauka akanta amman Captain ya goge mata hadda, ta saka hannayenta ta share hawayenta har yanzu jin take kamar dai ba gaske ba ne. Momy ta turo kofar dakin ta shigo ita ma tana kuka.

 Auren nan ba zai je ko'ina ba, Captain da yake da zuciya da saurin fushi kwana biyu ne zata fita ransa, kuma na san Hajiya Turai ba zata yarda anta ya aikata wannan abun kunyar ba, aure ba zai je ko'ina zai lalace

Namra ta mike tsaye da sauri ta shige bandakinta domin bata son Momy ta ga kukanta, ganin take bata cancanci zubar da hawaye akan namiji ba, sai dai wadannan sun zame mata dole ne. Zaunawa ta yi a kasa bayan ta rufe bandakin tana kuka marar sauti. Momy na ganin hakan ta san yar gudaliyar yarta kuka bakinciki take, ita ma sai rauninta ya karu, jikin bandakin ta tsaya tana buga kofar.

 Namra bude kofar karki saka kanki a damuwa kinji, na san babu dadi amman ki yi hakuri karki wa damuwa kofa dan Allah ki kwantar da hankalinki, ni kaina ba zan bar maganar nan ba ba zan kyale lamarin nan ba

Kalaman na Momy sai suka zama kamar makamashi mai hura wutar bakincikin dake zuciyar Namra, sai dai hakan be saka ta bude kofar ba, har Momy ta gaji da tsayuwa ta fice daga dakin, tana shiga dakinta mayafi ta dauka da key mota ko jaka bata tsaya dauka ba ta nufi family house dinsu.



CAPTAIN JAMAL POV.

A hankali ya fara rankwafa yatsunsa har ya jimke dabinon dake hannunsa yana kallon Daddynsa har lokacin an rasa mai cewa komai. Daddy yayi murmushi yana kallon dansa cike da alfahari kamar yadda Captain din ma yake kallon mahaifinsa ya kasa gasgata kalamansa.

 Da alama dai kuna bukatar na maimaita kaina, abun da nake nufi a nan.... 

Ammy bata bari ya fadi ba ta mike tsaye cikin tsawa da hargagi ta ce.

 No bana bukatar ka maimaita mana sautin da fadij mutuwa ya fi shi dadin ji

Ta tofar da yawu.

 Touf! Allah ya tsare gatari na da saran shuka, har abada ana ya fi karfin wulakantacciya yarinyar yar talaka kuma wanda duniya ta gama ganin tsiraicinta Wallahi

Alhaji Sadiq ya mike tsaye tana dagawa Ammy hannu.

 Hajiya Turai sai dai hakuri amman Wallahi an daura auren Jamal da Hurriya yau, idan baki yarda ba ki kira Nafisa ki tambaye ta

Ammy ta kalli Daddy da sauri tana son kara tabbatarwa. Captain yayi murmushi ya rufe idonsa har lokacin hannunsa na rike da dabinon ya kasa maida hannun kuma ya kasa sauke shi kasa.

 Munafuntata ka yi Captain? Ka ce min ka hakura kuma sai ka juya ka shirya wani abun da mahaifinka?

Cikin kuka Ammy take tambayarsa, sai ya bude idonsa da sauri ya kalleta raunace.

 Wallahi Allah ban san komai akai ba Ammy

Hajiya Turai ta juyar da dubanta gurin Daddy.

 Saboda me? Saboda me zaka aura masa wannan yarinyar? Be fada maka ya hakura ba? Baka duba illar hakan ba a cikin zuri'arka?

Daddy ya daga mata tsaya uku yana nuna mata daya vayan daya.

 Saboda na isa! Saboda yana sonta!! Saboda Allah be haramta ba!!! Kin ga dalilin nan uku su suka saka na je na nemi auren Hurriya a yau, mahaifinta kuma ya bukaci a daura auren a yau

 Ikon Allah abu dai kamar a shirin film?

Cewar Nene, Momy Ikilima ta ce

 A littafi dai wannan ai ya fi karfin shirin film

Ammy da idonsa ya cika da hawaye har wasu za su zubo ta hau masifa.

 Da alama baka yi bincike ba kamin ka aura masa yarinyar nan, mahaifiyarta aikin gida ta yi fa!, ni ba zan iya karbar ta a matsayin suruka ba, ba zan ina nunawa duniya yarinyar nan a matsayin matar Captain ba

Daddy nade babbar rigarsa.

 Kin gani Turai ba a daura auren yarinyar da Jamal ba sai da na yi ma mahaifina alkawarin zan rike yarsa da mutunci da amana, kuma a matsayinki na matata idan ba ki taya ki cika alkwarin nan ba, to be kamata ki barar da shi ba, karki zuga kanki da yawa ki kone kanki ta hanyar haramta abun da Allah ya halatta, hargaginki da kumbar baki ba zai saka Jamal ya saki yarinyar nan ba, domin ba je na auro masa yar mutune saboda ya zubar min da mutunci ba, ina ce Alhaji Haruna ma yana da kalar nasa rufin asirin idan kuma kin raina arikin gidansu ne yanzu danki take aure make her a billion naira

 Wayyo Allah na wannan wane irin abun kunya abun bakinciki ne? Kenan duk abun da Jamal yake so sai mu biye masa mu aikata ko da halaka ce? Yarinyar da kare da mage suka maganin siraicinta, ita zaka hannu biyu mu karba a matsayin in-law?

 Wannan kuma anki kike ci ma mutunci a gaban familynsa, ina jiye miki tsoron ranar da zaki yi nadamar nuna son zuciya fiye da abun da danki yake so, ki shirya da wuri karfe biyar jirgina zai tashi

Daddy na kaiwa ya kabe rifarsa ya fice daga falon, Hajiya Turai ta kalli Nene da kowa dake falon tana kuka.

 Nene kina gani? Babu wanda zai ce komai ni za a bari da fadan nan?

 Hajiya Turai me kike son mu ce? Aure ne an riga da an daura, sakawa zamu yi Captain ya sake ta ko kuma mijinki zamu rufe da fada, kowa a nan yayi mamaki amman abun da kaddara ta aiko dole mu karba mu zuba ido mu ga abun da Allah zai yi a gaba

Cewar Alhaji Munzali, kamin ya mike tsaye ya fice daga falon. Alhaji Sadiq ne kadai yake lallabata.

 Ki yi hakuri Hajiya Turai, ki bi abin da danki da mijinki suke so, ki zuba ido ba fata muke ma amman idan akwai illa a cikin lamarin nan za su gani a gaba kuma su gane sun aikata kuskure, Jamal dai shi yake auren yarinya shi yake jin zai iya daukar komai da ya shafe ta to ke mike naki a ciki? Ki yi hakuri a matsayinki na uwa ki danne duk abun da kike ji dan Allah

 Ba zan iya ba Alhaji Sadiq, Engr ya nuna min ba ni da muhimmanci a rayuwarsa da ta dansa, shiyasa be duba shawarata ko ra'ayina ba ya aikata abub da ya aikata

Ta fice daga falon tana kuka, Hajiyar Maru wacce ta kasance abokiyar zaman Nene ta bi bayanta tare da Momy Ikilima, Alhaji Sadiq da Alhaji ya dafa kafadar Captain yace

 Ka dauko wani aiki mai nauyi Jamal, idan baka yi hakuri ka kai zuciya nesa ba ba zaka iya karasa ba, ka bawa kowa hakkinsa matarka da mahaifiyarka, Allah ya bada zaman lafiya ya hada kanku

Ficewa suka yi daga falon sai ya rage daga Captain sai Nene a falon har jikokin Nene yan matan da kanana duk babu ko daya.

 Ka yi hakuri Jamal kowa ya ce zai iya sai an gwada aka ko zai iya dauka saboda haka ka saka kana'a a zuciyar.... 

Sakin baki ta yi tana kallon ikon Allah ba tare da ta karasa maganar ba. Gira Captain yake daga masa ya sumbanci goro da dabino da Daddy ya ba shi, sannan ya zuba shi a alijihu ya bude babban rigarsa yana nufar ina da take da rawa. Nene ta rike baki.

 Ah...ah... Ah... Ja'irin yaro? Wato ni ka raina ko? Kake min rawa me yasa baka yi ba a gaban iyayenka

 Su ai iyayena ne, ke kuma kakata ce my first wife my kalbi

 Tsohon makiri, amman tsaye ka yi a gabansu ba wani murna ba komai kamar wanda aka yi ma auren dole, ashe kana so....

Ya kyalkyale da dariya ya sumbanci kumatunta.

 Nene na godiya da kika haifo min gwarzon namiji kamar Daddy, ba dan shi ba da yanzu na rasa yarinyar nan

Nene ta kai masa duka a fuska.

 ja'irin yaro, amman kai da gaske baka ganin illar abun da yarinyar nan ta yi?

 Bata aikata ba sheri aka yi mata, kuma asiri zai tonu nan ba da jimawa ba, kowa be wuce kaddara ba hakan zai iya faruwa da ni, ko da wani a cikin jikokinki sheri ne aka yi mata saboda a lalata sunanta

 Haka ne, abun kam babu dadin ji babu dadin fadi, amman na tausaya mata matuka

Captain ya daga hannayensa sama fafaren hakoransa na bayyana yayi ma Allah godiya.

 Allah ka ba ni ikon kyautata ma yarinyar da daukar nauyinta yadda ya dace, ka ba ni ikon faranta mata, ka taimaka min gurin tarbiyarta da na yaran da zamu haifa Allah, ya Allah ka karkato da zuciyar mahaifiyata da hankalinta ta fahimce kuma ta so abun da nake so, Allah ya ba mu zaman lafiya ka kawar da shaidan da mahassada a wannan aure

 Ameen

Nene ta amsa masa tana kallonsa cike da burgewa.

 Kana da hankali matuka Jamal, ba dan kana jikana ba hakika wannan yarinyar ta yi dacen miji, matukar ba zata fusata ka ba to zaku zauna lafiya da ita

 In shaa Allah Nene

Ya kara taka mata rawar sai a lokacin yake jin wani kalar farin ciki da be san a muhalin da zai aje shi ba, a lokacin ne wani shaukin auren da annashuwa da zumudi suka same shi. Hanyar da dakinsa yake ya nufa yana tafe yana gyara babbar rigar abun ka da wanda be saba saka manya kaya irin wannan ba. Agaban madubi ya zauna yana shafa fuskarsa ya dauki ragowar tutaren ya feshe a jikinsa, wani irin yanayi yake jin kansa da be taba samun kansa a ciki ba, yanayi ne dabam da yake zuwa sau daya a rayuwar ko wane saurayi fa budurwa, yanayin da kan canja yanayin ango da Amarya tun daga yanayin gari har zuwa na hallita da mu'amala da kuma na iskar da aka shaka. Hoton da ya dauka na Hurriya ya kama a wayarsa yana kallo yana shafa screen din da hannunsa.

 You're the only thing i want touch.... Kin kawo ni a wata duniya da ban yi mafarkin zuwanta a kusa ba, kin haska min abubuwa da yawa da duhun watan soyayyarki bata bari na gani ba, zan baki kyauta duniyar dake cike da haske da farinciki sai na dawo miki da abubuwan da kika rasa, bakinciki da kike ciki zan maye miki gurbinsa da farinciki, zan canja shafin rayuwarki har ki bata damuwa baya, zaki gode Allah ki yi alfahari da ya baki ni a matsayin miji.... QURRATUL AYN (meaning
Delights Of The Eye, Darling, sanyin idaniya...)

Ya sumbanci hoton sannan ya dorashi a kirjinsa ya rumgume ya lumshe ido yana murmushi, a zuciyarsa yake ayyana Hurriya tsaye a gabansa tana kallonsa da murmushi a fuskarsa fararen tufafi sanye a jikinta.

 Ya... Ya... Ya... Na.. 

Ya ji yana fitowa between her soft lips tana motsa halshenta a hankali.

 Uhmmm..... 

Ya bude ido yana amsawa, a nan ya gane imagination ne yake ba gaskiya ba, murmushi yayi mai sauti ya cige bakinsa ya maida idonsa ya rufe yana jin kamar ace yana da damar ganin Hurriya a yanzu.


HAJIYA KALTUME POV.

 Hurriya fa ka ce Yasir ko dai zolayata kake?

 Taya zan zolaye ki Hajiya? Ga abun da yake zahiri, goro da dabino suna waje, idan baki yarda ba ki tambayi Appa ki ji

Hajiya Kaltume ta juyo ta kalli Khairy da ke kallon sarkar kamar wanda ta yi arba da wani abun tashin hankali.

 Da wannan sarkar aka biya sadakin Hurriya? Wanene? Be san abun da yake yawo a gari ba ne Yaya?

 Ba za su rasa sani ba, wata kila ma shi ne dalilin da yasa suka zo neman auren a yanzu, kuma zai iya yiyu ba su sani ba din ko ma dai minene an riga da an daura fatan mu Allah ya bada zama lafiya

Ya karasa yama dauko wayarsa daya dake aljihu ya amsa kiran Appa.

 Hello Appa... Eh tana hannuna okay gani nan zuwa

Ya mike tsaye ya rufe sarkar.

 Appa yake kirana, yace ma kawo masa sarkar

Ya nufi kofa, Hajiya da Khairy suka bi shi da kallo kamar wasu kauyawa. Hajiya Kaltume ta kalli Khairy

 Anya Nafisa ta sani kuwa? Sadaki da sarkar zinari?

 Abun kamar hankali ba zai dauka ba Hajiya, duk wannan cecekucen da ake akan Hurriya ace wani ya zo ya aureta a rana daya kuma ya biya sadaki mai yawa haka?

 To ni ma mamakin abun nake, abun dai kamar a mafarki

 Kuma Wallahi idan wanda nake zargi ne dan Alhaji Turaki Hurriya ta warke Hajiya, kin san yan'uwan Momy babu talaka balle kuma AA Turaki

 Shin waye be san ubansa a kasar nan ba? Wai ko mafarki na ke dai

Ta mari kanta baren dama ta koma hagu ta mari kanta ya mursa idonta ta hade yawu.

 Kuma fa ta makance kuma ya yarda zai aureta ko dai asiri aka masa?

Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta dauki dankwalinta a hannu, ta nufi sama. A gurin da wayarta take aje ta dauka ta kira number Hajiya Fatee.

 Sallamu Alaikum

 Ba sai na amsa sallamarki ba balle gaisuwa, Hajiya Fatee duniyar nan fa tana shirin rikice min, wai ashe motocin da kika gani dazun sun shiga bangaren Nafisa neman auren Hurriya aka zo?

 Hurriya? Ko dai Namra?

 Hurriya dai da kika sani yar wajen Iyami... Kuma Alhaji ya ba su ba su bar gidan ba sai da aka daura auren

 Ina na taba jin abu haka? A bada aure kuma a daura a take? Anya mutanen kwarai ne kuwa ko da yake Mahaifinta yana neman a raba shi da abun kunya ba dole ya amince ba

 Ba auren ne abun mamaki ba, wanda ta aura ne da kuma wanda ya zo nemam auren ne abun mamaki

 Toh... Wata kila dan fashi ne ko ko kuma masu yankan kai, domin su ne kadai za su iya runtse ido su auri Hurriya a yanzu, ganin manyan motoci ba shi ke nuna mai daraja zata aura ba wata kila ma ba zai wuce mai sharar gidan masu arziki, ya walkilta mai gidansa nema masa aurenta

 Alhaji Aliyu Turaki ne fa Hajiya Fatee, Yayan Nafisa, ya zo neman aurenta.

 Oh... To... Wata kila yaron gidansa ya yi ma kara ko kuma ubanta ya nemo mai raba shi da abun kunya ayi hadaka, ke waya sani ma ko tsoho ne za a hada ta saboda su basa kunyar auren ko wace mace Sugar daddys din nan da kike ji da gani

 Wannan saurayi ne sabo dal a cikin kwali, an Alhaji Aliyu Turaki ne wanda yake zuwa gurin Nafisa, ina kare miki zance da zinari aka yi sadakinta na naira na gugar naira har naira miliyan hansi....

Hajiya Fatee ta amsa da karfi.

 Ke.... Hajiya Kaltume... Hurriyar? Har kin sa cikina ya murda

 Ai ni fitsari kubce min suka yi, yar Iyami? Sauran yaran gida ba a musu ba sai ita da duniya ta gama wulakantawa? Zama be gan ni ba Hajiya Fatee wannan yakin ba na uwar Hurriya kadai ba ne har

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login