Showing 168001 words to 171000 words out of 279257 words

Chapter 57 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34664

language, sai ta girgiza kai ta sauke idonta kasa, ko da wani abun aka yi mata ta ina zata iya fada a gaban idon Namra, ta sake dago kai zulum ta zurma su a idon Captain dake kallonta kamar babu gobe, wannan karon da girar idonsa yake tambayarta.

 Me ya faru?

Ita kuma da yake bata iya munafurci ba sai ta amsa masa da kai cewar babu komai ta kalli Namra ta yi saurin sauke idonta kasa.

 Na dauka zaka ce ya jikina Captain

Namra ta tambaya tana kokarin kawarta abun da idanuwanta suke dauka.

 Baki da lafiya ne?

Ita yake tambaya amman idonsa suna gurin Hurriya dake motsa siraran yatsun hannunta.

 Cizon da kunamu suka min jiya

Sai a lokacin ya kalleta yayin da yake kokarin rage tsawonsa.

 Oh gaba daya na manta Wallahi, hankalina yana gurin yarinyar nan na shigo na ga tana hawaye na dauka wani abun ne ya faru

Namra ta kalleshi irin kallon nan na yadda ya fada mata haka kai tsaye ba tare da tsoro ko jin nauyi ba. Shi kuma be yi hakan da wata manufa fa face gaskiya, domin ya ji duk wani takurawa da suke son su yi ma Hurriya, kuma ya ga wasu a idonsa, jiya ma ya shigo ya tarar tana kokarin kasheta, hakan sai ya kara masa tausayinta da kuma son ya taimaka mata.

 Me yasa kake damuwa da abun da ya shafi Hurriya Captain?

Tambayar ta kutso ta huda makogaronta ta lakanci halshenta ta fito ta bakinta ba tare da ita kanta ta shiryawa hakan ba, sai dan mamakin jin furucin da bata tsammaci jinsa daga bakinsa ba. Sai da ya kalli Hurriya dake kallon Namra sannan ya aika mata da tambaya ba tare da ya amsa tata tambayar ba.

 Saboda Uwata ce. Me ye matsakarki da hakan?

Ta kalli Hurriya har zata yi doguwar magana sai kuma ta takaita ma kanta wahala.

 Babu

Ta mike tsaye ta aje remote din hannunta ta nufi stairs har ta haura ta shige dakinta bata juyo ba. Hurriya na ganin haka ita ma ta mike tsaye domin barin falon kamar daga sama ta ji yana bata umarni.

 Shiga Kitchen ki dauko min ruwa

Ba tare da tace komai ba, ta juya alakar tafiyarta zuwa hanyar Kitchen din gabanta na faduwa, saboda hukuncin da Namra ko Momy za su yi mata na abun da ya faru yau idan Captain baya gidan yana kusantota tu????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
n kamin ta san sakamakonta. Ta bude refrigerator din mai kofa biyu ta dauko ruwan dake gefensa murfin ta dago ta rufe sai ta ga mutum tsaye jikin dayan kofar refrigerator din yana hade hannayensa yana kallonta. Ta dan ja baya kamar ta tsorata sai kuma ta nufi kofar fita daga kitchen din tana rike da gorar ruwan.

 Wa zaki kaiwa ruwan?

Ta juyo ta dawo ta tsaya gabansa ta mika masa ruwan, gaba daya kwarjininsa ya rikitar da ita. Be karba kuma be fasa son sanin dalilin zubar hawayenta ba, ji yake kamar ba shi da natsuwa da sukuni idan be zama silar yayewar damuwarta ba a koyaushe, zuwansa ma a yau na tabbatar da ta ci abinci ne.

 Me kike yi ma kuka?

Banbancin tambayar dazun da ta yanzu, furuci kawai, dazun yana mata ne in a code way a yanzu kuma kai tsaye ya tambaya, yana kallon da ya fi kama da an hallito idonsa ne domin kyakkyawar fuskarta. Ta karantu kuma ta haddace cewar baya son maimaita tambayar, baya bada umarni sau biyu, gashi fa saurin bacin rai wata kila ma yar karamar bindigarsa nan tana nan tare da shi, wata kila kuma idan bata amsa masa tambayarsa a wannan karon ba zai barta ta fice daga gurin ba.

 Kawai na jidadin yadda Appa yake kula da twins ne ya dora su a jikinsa yana wasa da su, abu ne da be taba yi ba, Twins ba su taba zuwa gidan nan ba sai jiya, ba su taba rike hannun Appa ba, ba su taba zama a jikinsa sai yau shi ne abun ya saka ni farinciki, har na yi hawaye

_Me yasa ba su taba zuwa gidan ba? Su ba yayansa ba ne? Me yasa be taba wasa da su ba? Me ya faru?_ kusan lokaci daya wadannan tambayoyin suka jero masa, and then he realized be kamata ya tambayeta any of those questions ba, be ma kamata ya wuce gona da iri ba.

 Kwalin dake falo na ki ne ke da twins, kin ci abinci?

Ta daga masa kai, sannan ta juya zata fice har ta isa kofar kitchen din sai kuma ta juyo, tana tunanin da wani suna zata kirashi, yadda Momy da Namra suke kiransa, a gudun bata masa rai ko rage masa girma ya saka ta raba sunan da sunan da take ganin ya dace.

 Yaya Captain...

Ya kalleta yana hade ruwan da ya cika bakinsa da su, be amsa ba be kuma fasa kallon idonta da ta kasa dagowa ta kalleshi ba.

 Removed the last sentence

Ta dago cikin hankali da natsuwa irin nata, ta kalleshi ta cikin gilashin idonta irin kallon dake kashe zuciyar namiji, da muryar dake narkar da zuciyar mai saurarenta ta ce.

 ...Ya... Ya... 

Al'adarsa duk wani wani suna da za a kira shi, idan ya wuce Captain da Jameel kauyanci ne, kalmar Yaya bata masa dadi ko kadan saboda haka ya hana kowa a familynsa yi masa inkiya da Yaya. Sai dai wacan karatun nasa ya kau, dokokin da ya gidanya sun rushe a lokacin da kunnuwansa suka yi kicibus da sautin da ya fito daga bakin Hurriya, she pronounce it so right, so different, so unique, so sweet.

 Say that again

A wani yanayi da ya fi kama da rauni da tausasa halshe ta maimaita.

 ...Ya.. Ya...

In a gentle way ya shigar da lip dinsa na kasa a bakinsa ya jika shi da yawunsa, yadda take furta kalmar YAYA ya san he missed alot, me yasa ba zai so ta kira shi da Yayanba? Ita din ba kamar yar'uwarsa ba ce?

 Repeat it...

 ...Yaya.... 

Ta sake fada da sanyin murya irin mai tsoro aikata kuskure, har tana tambayar kanta ko dai bata furta daidai ba? Ko kuma dai yana son ta yi ta fada ne har ya fusata bayan ta san baya maimaita kansa.

_Miracle_

Ya furta a ransa yana kallon idanuwanta da farin yayi fari kamar watsa ruwan madara a ciki.

 Uhmm mmm

Ya amsa irin amsar dake nuna ta fito ne daga kasan zuciyarsa.

 Ina son na tambayi wani abu...

Wani shaukin kallonta ne ya daukeshi ya lulashi a wata duniyar da ya haddasa bugawar zuciyarsa a mabanbantan dakiku, natsuwarta na neman bukata a gurinsa ya saukar masa nishadi da ya samu kansa da lumshe ido ya bude yana kallonta kamar mai jin bachi.

 Name what ever you want girl...

Ta hade hannayenta biyu guri daya ta rankwafar da kai, a wata murya da ta fi kama da tausayi da shagwaba ta ce.

 Kai ne ka ba ni wata takardar ranar da Hamad ya bata? Har ka yi min alkawari zaka dawo min da shi?

 Me yasa baki manta ba?

Kwaryar ididonta ya fara tara ruwan da aka sirka da gishiri.

 Har yanzu ziciyata ta kasa amsar cewar Hamad ba zai dawo ba

Ta tako ta matso kusa da ita yana kallonta

 Ni ma zuciyata ta kasa karya alkawarin da na daukar miki...

Ya kara motsawa dap da ita ya rage tsawonsa har tana jin saukar numfashinsa.

 Wata kila zai dawo...!

Zuciyarta da mugun karfi, ta bude baki saboda numfashin dake fita ta hancinta na kokarin karewa.

 Ina fatar haka...

Ta furta muryarta can kasa sosai. Shi ma sai ya bata amsa da muryar mai dadi da ta fi kama da rada ya ce

 Idan wannan ne farincikinki... Ni ma ina fatan haka Hurriya... Duk wani abun da zai yaye miki damuwa ya sakaki a cikin farinciki ina fatan ki same shi

 Kana da kirki kana damuwa da ni, thank you for understanding me

Kamar wata kwarariya haka ta yi masa magana muryarta a kasa fiye da yadda ta muryar shi take a lokacin da yayi mata magana.

 We all need that someone who get us like no one else, a right when we needed the most, you need shoulder to cry on...

hura mata iskar bakinsa mai kamshi a fuskarta, atak, sai ta lumshe ido, murmushi ya fadada fuskarta hawayen bakinciki da suka rikide mata zuwa farinciki suka kawata kyauta. Kamar wanda ta tuna wani abu murmushin fuskarta ya bace bat, sai ta matsa baya da sauri ta bude idonta ta juya da fice daga kitchen din. Murmushi yayi ya taka backwards yana shafa kansa, ya daga gorar ya sha ya aje, sannan ya kai hannunsa saitin da aka aka yi gurbin zuciyarsa.

 Ajiya ce wannan, please ki ba ni hadin kai, saurin fushi breaking up with so many girls wannan duk na yafe miki, karki raba ni da wannan she's special na gane haka from DAY 1 na san ke ma kin san haka... 

Ya rufe idonsa ya sauke dogon numfashi, ya kai ma zuciyarsa duka a hankali yana aje mata sako.

 Idan kika raba ni wannan ni da ke duka zamu cutu, wata kila mu salwanta in one way or the other, so try to be strong please, ki ba ni hadin kai i hope you understand me

Zuciyarsa ta buga da karfi tana raba sakon da yayi aika mata ga sauran sassan jikinsa da suka kasance mukarraban aikinta. Ya bude idon yana murmushi, sai farinciki yake kamar wani sabon ango, ba shi da kwashe kwashen mata, amman idan ya ga wanda hankalinsa ya kwanta da ita ya kan tallata mata soyayyarsa, sau uku ya taba yin haka, sau biyu aka yi nasarar saka ranar aurensa aka fasa saboda rashin hadin kan da zuciyarsa take ba shi. Falo ya fito ya zauna yana kallon tv sai dai gaba daya hankalinsa ba a gurin tv yake ba. Ya kusan minti goma shabiyar da zama sannan Appa ya sauko Momy na bayansa waya a kunnesa.

 Gani nan zuwa

Ya fice tare da twins dinsa, sai jan rigarsa suke. Momy ta zauna tana mamakin ganin Captain domin Appa be fada mata tana da bako ba, ko da yake ba zata kira shi da bako ba a yanzu daman tuni ya zama dan gida. Namra ma da ta haura sama da bacin rai bata fada mata Captain ya zo ba.

 Ban san ka zo ba?

 Saboda Appa yana nan ne, tun dazun na zo ai

 Maa Shaa Allah yau dai na san babu aiki yau Sunday, kuma na ga farinciki a fuskarka a yau fiye da ko yaushe, kana albishir ne?

Yayi murmushi shi kansa ya san fitowarsa daga kitchen zuwa zamansa a falon nan ya banbanta da kullum, and baya bukatar wani ya fada masa yana farinciki ya fahimci haka tun a lokacin da sexy voice din Hurriya ya huda kuunnesa har ya karya dokokinsa, ga kuma numfashinta da ke masa yawo a saman hanci har yanzu.

 Wata kila nan gaba kadan na yi albishir, farincikin kuma ina fatan ya daure har abada

 Allah ya tabbatar maka da shi

 Ameen Momyna that's why i love you kina son farincikina

 Kai dan gatan family mu ne Captain, idan wani be so farincikinka ba, to be so Familynmu ba

Ya bude baki ya rufe yana murmushin gefen baki. Daga bisani ya kalli Momy ya aika mata da tambayar abin da ya tsaya masa a rai.

 Momy me yasa kannen Hurriya ba su taba zuwa gidan nan ba sai yau?

Momy ta dan tabe baki.

 Alhaji ya juya musu baya tun da aka haifesu, ni kaina na yi mamakin yadda yau ya shigo min da su dakina ya dorasu har kan gadona yana wasa da su

 Why?

 To Allah masani Captain, wata kila shiga tsakani ne

 Kuma mahaifiyarsu ba ta yi tunanin ta kawo su ba?

 Ta ina? Ka manta na fada maka bata da lafiya? Aiko hannu bata iya dagawa, bata magana bata iya komai nan gaba kadan ma wata kila bara zata koma, domin dai ance duk abun da take da shi ya kare, daman talakawa talas shiyasa kwadayi ya ja ta auri Alhaji, yanzu kuma ta auren ya kare sai ta koma babu komai, ita fa wannan Hurriya kaskantacci ne uwarta ga aiki ta yi, ta zo gidan ta bangare Kaltume daga aiki ta aure Alhaji shiyasa Kaltume bata kaunarsu ko kadan ai, kara ni ina da zuciyar imani ina ragama mata amman can ba ta sha da dadi ai

 Mahaifinta mai kudi ne i guess to me ya kawo zancen kaskanci?

 Ai wannan talauci da uwarta take ciki ba zai taba gogewa ba a ido, kuma ba zai taba barin mutane irina su ga kimarta ba, ba gashi nan ta koma a kwance ba, da ynzu tana da arziki zata tsaya jinya haka ne? Shekara hudu yanzu ana fama da abu daya, ko Kaduna ba su taba kaita ba balle a fitar da ita, kuma wani lokacin da tana da kudi ai ba za'ayi ma yarta ko ita ba, yanzu ka hada ta ni? Ko ka hada Hurriya da Namra? Ai ba za su tana haduwa ba har abada, ka ga fa gidan nan kowa yana karatu wasu sun kare amman ita tun da ta gama SSCE ubanta ya aje ta gefe ko kallonta baya son yi, ya ki sakata makaranta da uwar tana da kudi ai ba za a yi ma yarta haka ba, ko kuma ta dauki matakin shari'a ta karbe yarta ta saka ta makaranta mai kyau

Jawabin da Momy ta kora masa, be kara masa komai ba sai tausayin Hurriya, bayan kalubalen da take fuskanta a gidan ga damuwa na rashin uwa da dan'uwa a kusa, ga kuma rashin lafiyar ido, yanzu kuma ya kara jin halin da mahaifiyarta take ciki, talaucin da ya hana su ganin kimarta a gidan, ya kara mata martaba da tausayi a idonsa.


HURRIYA POV.

Ta rufe fuskarta da tafi hannayenta har lokacin kamshin iskar bakin Captain da ya hura mata be bar hancinta ba, bata taba samun kanta a yanayi kamamancin wannan ba, murmushi take kamar wata sabuwar mahaukaciya a rufaffun idanuwanta bata ganin komai sai fuskar Captain, all the good things da yayi mata suna ta dawo mata, bata da wani abun fada akansa sai khairy yana da kyakkyawar zuciya da tausayi ba kamar yadda ta ke tunani a baya ba. Bude ido ta yi ta sauko kasa ta zauna ta bude kwalin da ta dauko a falo tana duba abubuwan ciki, chocolate ne da sweet candy mai dadin nan, sai kuma gasashen kifi dake ta kamshi, tashi ta yi ta wanke hannunta sannan ta dawo ta zauna ta bude kifin ta fara ci. Bata fito dakin ba sai da dare shi ma saboda Yayanta Yasir ya shigo dakin ne ya bukaci ta fito su tafi kai Twins gida saboda Rukkaya ta matsa masa ya kawo yaran Gwaggo ma sai da ta kira da kanta, tsoronta duk be wuce na irin wulakanci da musgunawar da za'ayi ma yaran a gidan ba, ta fito tana sanye da green hijab dinta ta kama hannun yaran dake falo ta fice da su. Sai da suka isa bangaren Hajiya Kaltume sannan suka shiga motar Yasir yayi mata key ya fice daga gidan suka dauki hanyar gidan Gwaggo.

 Hurriya

 Na'am

 Dan Allah ki bawa Rukayya hakuri, kuma ki lallaba Gwaggo kar ta yo fushi, ni kaina ban jidadin abun da ya faru ba, gaba daya na rasa gane abun da ke min dadi gidan nan ya rikice, mun rasa Salma, Hajiya ba zata karbi soyayya ta Rukayya ba, Hajiya kuma tana asibiti yanzu haka? Gaba dayana rasa ina zan saka kaina na ji sanyi

 Asibiti bata da lafiya?

 Suma ta yi, amman da sauki gobe ma Appa yace ba za'ayi zaman gaisuwa ba, shiyasa aka yi addu'a uku a yau

An yi addu'an uku kuma bata sani ba? Ta tambayi kanta.

 Ban san an yi ba, kuma ban san an kai Hajiya asibiti ba

 Kina cikin daki koda yaushe Hurriya ya za'ayi ki sani, kin zaman dabam

 Bana jindadin shiga cikin mutane ne, wani lokacin ina tsarguwa

Ta dora hannunsa biyu a sitiyarin motar.

 I understand your situation now...

Daga haka be kara cewa komai ba, har suka isa gidan.

 Ki aje su ki dawo na maida ke

 Toh

Ta amsa sai a lokacin ta tuna da siyayyar da Captain yayi musu bata ba su ba, kuma bata isa tace Yasir ya koma su dauko ba. Haka ta shiga cikin gidan tare da yaran ta mika su hannun Gwaggo tana fada mata abun da Appa yayi musu a jiya, Amma ta kalleta yanayin fuskarta ya nuna akwai damuwa da magana mai yawa a tare da ita amman babu bakin fada.

 A da yardar Allah komai zai warware, sai ta ga Iyami ta tashi da idonta, amman zaman aure kam ko da ya dawo yace zai maida Iyami ba zan yarda ba, aure ya kare kenan Allah ya bata na gari, wannan wahala da ta sha ta isa haka, amman wai duk wannan abun Rukayya bata gani ba saboda rashin hankali da tunani take kokarin daukar kanta ta jefa a gurin Kaltume? Me ake da Kaltume me ake da jininta? Har abada ko ba ni da rayuwa Rukayya ba zaki auri Yasir ba, sai dai ki mutu babu aure, na Iyami ma kaddara ce da ba mu isa mu kauce mata ba

Rukayya ta mike tsaye ta fice daga falon gudun hawayen da suka tarar mata kar su zubar mata a gaban Gwaggo ta sha fada, daman tun jiya take mata masifa har yau da dare. Hurriya ta kalli Gwaggo cikin yanayin rashin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login