Showing 195001 words to 198000 words out of 279257 words

Chapter 66 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34701

Haruna ba, na yi nadamar wannan aure na kaddara.... 

Da in'in'ina take maganar muryarta na rawa as well as bakinta saboda dadewar da ta yi ba ta yi maganar ba, Twins dinta suka zo a guje suka tsaya suna kallonta, abu ne da ba su tana gani ba, tun da aka haife su suka yi wayo Amma bata tana magana ba, ba su taba jin sautin muryar uwarsu ba, bata taba kiran sunansu sun ji da kunnensu ba.

 Amma... Amma... Ammma. Muryarki ya bude Alhamdulillah Ala kulli halin, Alhamdulillahi hamdam kasiram

Hurriya ta fada tana kuka tana dariya a lokaci daya sai kuma ta rumgume Amma. Gaba daya sai falon ya karade da sautin kuka, Amma kuka, Gwaggo kuka, Rukayya kuka. Su ma Twins sai suka fashe da kuka ganin Amman da Hurriya na kuka.



HAJIYA KALTUME POV.

 Kuma be ce zai dauki wani mataki ba?

Khairy ta girgiza kai.

 Yace zai dauki mataki na wanda ya aikata mata haka, Ya Yasir ma yace zai dauki mataki akai

 Dan'iya daman idan be dauka ba ai be cika Yasir ba, amman na yi mamakin ace Alhaji be mata komai ba, da ada ne Wallahi korarta zai yi

 Kuka ma yayi sosai, Appa ya zubar da hawaye Hajiya kuma yayi tsinuwa akan duk wanda ya aikatawa Hurriya wannan abun...

Khairy ta fada cikin kuka.

 To ke miye naki a ciki? Har da wani kuka ni kowaye ya aikata haka ya biyani Wallahi, dan Allah ni tashi ki ba ni guri zan yi waya

Khairy ta mike tsaye ta fice daga dakin, Hajiya Kaltume kuma ta daga wayarta ta kira Hajiya Fatee. Khairy ta shigo dakinta tana share hawaye ta nufi wayarta dake aje ta dauka ta kira Adam.. Sai da kiran ya kusa yankewa sannan Adam ya daga.

 Adam ka ga abun da ka janyo ko?

 Sai na kasheki Khairy sai na kasheki, ni zaki zaki yi betrayed? Sai na koya miki hankali Khairy

 Ban aikata komai ba, laifin ba nawa ba ne kana ne, kai ka lalata komai Adam... Na yi nadamar saninka a rayuwata

Ta dauke wayar a kunnenta tana kuka.......



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
39

A hankali ya maida fork a plate din kankanar dake gabansa ya kalli mahaifiyarsa wacce ta tsare shi fa ido.

 Na koshi

 Baka wani ci da yawa ba, kuma ka saka na yi cancelled tickets din da na siya, idan na yi magana ka ce ka ji sauki

 Na ji sauki mana Ammy baki gani ba?

 Me kake son ci yanzu? Watermelon din nan kawai ka ci zuwanka gidan nan

Ammy ta fada cikin yanayin damuwa. Ya duba wayarsa da sako ya shigo.

 Good... Ku turo location din gurin da kuka aje shi yanzu

Ya masa reply sannan ya kalli mahaifiyarsa.

 Taliya nake son ci mai zafi sosai, and ke nake son ki girka min

Ta kai hannu ta shafa fuska cikin tsananin so da kauna da kuma tausayinsa.

 Ko wani kake son na girkawa zan girka masa Captain balle kuma kai, zan girka maka yanzu

 Thank You

Ta mike tsaye ta dauke plate din ta fice, binta yayi da kallo sai da ta rufo kofar dakin sannan yayi rejecting kiran Salim dake shigowa wayarsa. Ya mike tsaye ya nufi kofar ya bude ya sauko a hankali ya shiga falon Kakarsa domin ita a kasa aka yi mata nata bangaren saboda kafafuwa da take fama da su, karamin falon ya fara shiga sannan ya karasa bakin kofar dakinta. Daga bakin kofar dakin ya tsaya yana kallonta.

 Nene.. 

Tsohuwar dake rike da carbi ta dube shi da murmushin a fuskarta ta ce.

 Ango ya karfin jiki?

 Alhamdulillah, Nene key motarki zaki ara min

 Ina zaka je? Kai da baka da lafiya?

Yayi mata alama da ta yi shiru.

 Ba sai kin fada kowa ya ji ba, Ammy zata iya hanani fita kuma abu mai muhimmanci daga office ne

 Ba a aiki da dare ai

 Aikin mu ba shi da hutu, zaki ba ni key din ko na je gurin Hajiyar Maru na karba?

Ta dan yi shiru kamin ta amsa masa.

 Yana nan cikin drawer, amman dai idan turaki ya san ka fita zai yi fada

 Ba za su sani ba

Ya nufi gurin da keys din suke ya dauka ya fice daga dakin, sai da ya fara bude falon ya leka ya ga babu kowa a babban falon sannan ya fito ya rufe kofar ba tare da ya bari ta yi motsi ba, ya fice salin alim, hankalinsa be kwanta ba har sai da ya fice daga gidan. Har ya isa asibitin FMC Salim be daina kiran wayarsa ba, shi kuma be amsa ba kuma ba zai amsa ba domin ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki. Kai tsaye ya nufi ward din da Hurriya take, sai fa ga fara knocked sannan ya tura dakin ya shiga to his greatest surprise sai ya samu wasu ne a dakin ba ita ba, gaishe yayi sannan yayi musu bayanin wanda yake nema.

 Wata kila an sallame ta mu ma yau aka kawo mu

 Okay Allah ya bada lafiya

Ya juyo ya fito, har ya koma motarsa kiran Salim da na wasu new numbers be fasa shigowa wayarsa, sai da ya shiga motarsa sannan ya kashe wayar gaba daya. Daga asibiti ya nufi gidansu Momy, ya san ganin Hurriya a wannan daren a bangaren Momy ba abu ne mai sauki a gareshi ba, bayan sun samu misunderstanding a dazun, and idan tace kar ya shiga dakin Hurriya ko kar a kirata be isa ya ce ba haka ba. Sai dai ya san karfin son ganin Hurriya saboda duba lafiyarta ba zai bar shi ya huta ba har sai ya ganta, shi be ma ga dalilin dauketa daga asibitin a yanzu ba a dawo da ita gida, ko dai daki aka canja mata, wata zuciyar ta hararo. A kokarinsa na neman amsa ya karfafaf kansa guiwa ya bude motar ya fito yana kallon windows din dakin na Hurriya. Tunawa da bata iya ganin komai a yanzu ya saka shi kara jin tausayinta. Hannayesa ya saka a aljhun wandonsa sannan ya taka ya isa gurin kofar dakin ta Momy ya danna door bell. Namra ta bude kofar falon, ganin Captain ya sakata mamaki sosai domin ta san ba shi da lafiya me zai zo yi a gidan by this time. Ta ja baya tana kallonsa without saying anything kamar ta yi arba da wani bako, Momy dake da remote ta aje remote din tana kallonsa.

 Wata fitinar ce kuma ta taso?

Yayi murmushi ya sauke kansa kasa.

 Na je asibiti duba Hurriya ban same ta a can ba

Momy ta dauke kai ta maida gurin Tv kamar bata san abin da ke fitowa daga bakinsa. Namra ta kalli Momy kana ta nufi kujera ta zauna.

 Hurriya bata asibiti if case you didn't know

Ya maimaita yana kallonsu domin zuciyarsa na raya masa, wani abu akan rashin ganinta be yi ba a yanzu.

 She's not here either

Ya kalli Namra gabansa na tsananta faduwa.

 Wani abun ya faru? Mahaifinta ya koreta ko kuma yaya?

 Tana gidan Mahaifiyarta

 Ina ne?

Momy ta kalli Namra dake kallonta sannan ta kalli Captain ta amsa masa.

 Ban san gidan ba

Ya kalleta da kyau sannan yayi murmushi ya ce.

 Zo muje waje ki ji

Momy ta kalleshi cike da fusata ta ce.

 Babu inda zata je, ku fita waje ka tirsasa mata abun da bata sani ba? Ko kuma ka ce zaka daketa?

Yayi murmushi

 Sai da safe Momy

Ya juya ya fice ba tare da ya kara cewa komai ba, Namra ta bishi da kallon mamaki.

 Da ada ne zai yi kamar zai tashi gidan nan saboda bacin rai, amman ji yadda ya fita har murmushi yake

 Ai dole yayi murmushi mana saboda ya san ya kulla min bakinciki da bacin rai, ba rantsuwa Hurriya zata yi ba ko kur'ane ta hade ba zai aureta ba

 Amman Momy bata aikata ba fa sheri ne

 Okay wannan ya wadatar dake kenan kin hakura da shi? Fine

Momy ta jefar da remote din ta mike tsaye ta nufi hanyar stairs tana jan tsaki. Namra ya bita da kallo kamar na rashin fahimta kamar mamaki.

Ya dade a cikin motar sannan ya yi mata key ya fice daga gidan yana tunanin yadda za'ayi ya samu ganin Hurriya, da farko yana son na duba lafiyarta ne yanzu kuma yana sso sanin halin da take ciki jin cewar tana gurin mahaifiyarta, korarta mahaifinta yayi ko kuma wani abun ne ya faru...! Ya kunna wayarsa ya duba location din da aka turo masa, kamin ya kashe wayar kiran Ammy ya shigo masa amman ya ki ya daga already ya san dalilin kiran nata. Tafiya yayi mai nisa ta kusan barin garin Gusau sannan ya isa Lalan, ya kutsa cikin wata unguwa dake gurin ya shiga can ciki har ya isa gidan. Horn yayi wani soja ya fito rike da bindigarsa ya duba motar Captain ya sauke gilashin motar Soja ya sara masa sannan ya koma da gudu ya rika gate din shi da wani suka bude. Captain ya fito matarsa suka sake sare masa sannan dayan ya ba shi labarin yadda suka dauko Adam abun da ya motsa asibitin gaba daya domin sun tabka rashin mutunci a kokarinsu na cika umarnin shugaban na su.

 Ina yake?

 Yana ciki gaba daya a firgice yake

Captain ya wuce gaba suka take masa baya, a yayinda ya isa gurin kofar da aka saka Adam kuma sai dayan ya bude masa ya sare masa. Captain ya shiga dakin da shi kadai ne be da haske a duka dakunan da suke gidan. Sojan ya haska Adam dake zaune a kasa daga shi sai gundun wando idonsa daya a kumbure hancinsa na jini sai nishi yake kamar na mutuwa. Captain ya karasa ya duka a gabansa ya karbi wayar ya haska Adam da kyau sannan ya haska kanshi

 Ka gane ni?

Adam ya kalleshi da ido daya ya kasa cewa komai, sai Captain ya kama hannunsa da ya rumgume a shimfida a kasa ya mike tsaye ya daga kafarsa zai taka hannun.

 Dan.... Allah.... Dan Allah.... Karka taka karaya ce a jiki dan Allah ka yi hakuri....

 Na sani ai, ba ni na karya hannun ba? Kuma ga dauri a jiki na gani

Captain ya kai kafarsa ya taka hannun mai karaya na Adam ya murza, sai da Adam ya kwala wani irin ihu ya kwanta a gurin kamar zai mutu. Captain ya dauke kafarsa ya duka saitin da fuskar Adam take yana kallonsa ya ce.

 Soja be san tausayi ga azzalumi ba Adam, wannan kadan ne daga bangaren aikin mu, na ce a aje min kai a nan na tsawon awa goma, kuma a gana maka azaba kala kala, sai dai ka ci albarka na fito duba Hurriya sai na yanke shawarar kawo maka ziyara

 Dan Allah ka yi hakuri... Dan Allah ka yafe min.. Ka yi hakuri... Wayyo Allah mutuwa zan yi

 Mutuwar ai nake son ka yi shiyasa na ce a dauko criminal irinka daga asibiti a kawo ka nan, ka ga babu wanda ya san gurin da kake a yanzu, idan na ga dama zan iya kashe ka a nan, na aje maka bindiga nace tare kake da yan ta'adda, idan na ga dama kuma sai na aje maka bindiga b tare da na kashe ka ba, na ce mum daukoka daga asibiti ne muka kawo ka nan saboda ka nuna mana sauran yan'uwan ta'adancinka, ko a hukunmance babu wanda zai tuhume mu, kaga na lalata maka rayuwa zama gidan kaso kuma ya kama ka, ko da ka fito rayuwa bata da amfani a gurinka

 Me na maka? Me na maka? Ni fa Adam ne Adam Sarauta

 Ni kuma Ni kuma Captain Jamal AA Turaki ne, sai yaya? Wannan be ji wuta ba ku gasa min shi da safe zan dawo

Captain ya mike tsaye, Adam ya yunkuro yana kuka zai rike Captain ya kasa saboda azabar da yake ji a hannunsa.

 Ka yo hakuri dan Allah, me na yi?

Captain ya juyo ya kai masa duka a baki.

 Mai tsada ka taba, ba ka ce kai dan'iska ba ne? Zan nuna maka na fika zama shege

 Wallahi Wallahi ban mata komai ba

Captain ya daga gira daya, sannan ya kunna wayarsa ya saka ta a plane mode, ya shiga camera ya kunna video.

 Me saka ka yi min karya to? Me yasa ka ce min tare kuke haduwa?

 Na yi hakan ne saboda kar laifin ya shafe ni kadai

 Ya aka yi hannunka ya kai ga jikinta? Har aka yi muku hotuna?

 Hotunan an dauke su ne a lokacin da Hurriya takw bachi bata cikin hayyacinta, bata san an yi ba

 Saboda me?

 Magani aka saka mata

 Kai ka saka mata maganin kenan?

 Ba ni na saka ba, Khairy ta saka mata, ban san yadda aka yi Khairy ta saka maganin ba, ni dai ta kira ni kawai ta ce min na zo gata nan

 Sai kuma ka zo?

 Eh saboda mun shirya hakan da ita?

 Saboda ka lalatawa Hurriya suna?

 Aa ba dan a bata sunanta ba ne, ni ina son Hurriya ne tun farko, sai dai Khairy ta bata min suna a gurinta da iyayenta shiyasa sai ta ki saurarena, ni kuma na kasa hakura Khairy ce ta kawo shawarar na yi amfani da Hurriya kawai a wuce gurin, ta karbi kudi mai yawa a hannuna saboda ta samonin kan Hurriya, amman ban samu yadda nake so ba, ni kuma na biye mata ne saboda ina ganin kamar wannan ce kadai damar da nake da ita, shiyasa ta hada plan aka zo da Hurriya a gidansu Zuhura ta kira ni tace na zo, ko da na zo har sun cire nata tufafi, ni kwantawa kawai na yi aka yi mana hoto

 Saboda me ka yi hotunan?

 Saboda na yi amfani da su na yi ma Hurriyya barazana ta amince da ni, saboda Khairy ba zata iya kawo min ita na yi amfani da ita ba, tana tsoron ace ta yi hanya ayi ma Hurriya Fyade idan asiri ya tonu zata ji kunya

Captain ya kai masa duka akai kamar wani criminal.

 Ka ji Jarumi yarinya tace bata yinka sai ka koma ta bayan gida kai dole sai ka yi amfani da ita ko? Ashe ma fyade ka tashi yi mata!

 Saboda na rasa yadda zan yi ne, kuma ya nuna min bata so na kirikiri

 Me ya hana ka? Ashe baka kai dan'iska ba

 Babu yadda zan yi na samu kan Hurriya ne saboda bata saurare balle na fita da ita ko na ja ta wani gurin, Khairy kuma tana tsoro, shiyasa ta shirya wannan abun, bayan mun dauki hotunan sai kuma yadda zan yi amfani da su ya zama aiki, saboda Khairy bata son ace da wayar na yi amfani na yi barazana a gurin Hurriya ba, saboda tana jin tsoro

Adam na kuka irin na karti da majina shabe shabe ya ke fadar hakan yana rike da hannunsa mai karaya.

 Nii kuma ba zan iya tunkararta kai tsaye ba, saboda ina tsoron kai ta fada a gidansu, gashi ban samu yadda zan yi magana da Hurriya ba, a lokacin ne na gane kamar wayo Khairy ta yi min, sai fadan ya koma tsakaninmu, na kasa daga nata kafa saboda zan bar kasa na tafi gurin masters sanadin haka mu ka yi fada, washe garin ranar da muka yi fadan na kirata na bata hakuri muka hadu a wani gurin and.... I... Rape her there.... 

Captain be san lokacin da ya bude baki ba.

 Wait... Wa ka yi raping?

 Khairy saboda ta ci kudina kuma ta kasa ba ni abun da nake so, sai fadan min take na yi amfani da hotunan, ni kuma hotunan ba su da amfani a gurina saboda ban samu damar kebewa da Hurriya ba, kuma ban san ya hakan zai faru ba

Captain ya mike tsaye yana jinjina lamarin Ubangiji, bahaushe ya ce wanda Allah ke yi ma fada baya fada, all this plan akan Hurriya amman Allah ya kareta sherin da suka kulla be same ta ba.

 Wacece Khairy ma?

Ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login