Showing 291001 words to 294000 words out of 296192 words

Chapter 98 - GABA DA GABANTA

room ɗin.

Yazid ya zo kanta ya tallafota yana yi mata sannu, tare da yi mata Addu'oi.

Can mai karɓar haihuwar ta cewa Yazid "Kaga rabu da ita, zaka iya zuwa waje ka jiramu, ta kusa haihuwa in sha Allah".

Yazid ya ce to,ya tashi zai fita, ta sake fashewa da kuka tana kiransa.
Ya tsaya cak ya waiwayo yana kallonta cikin tausayawa.

"Dan Allah kar ka tafi, ka dawo ka cigaba da yi mini Addu'a"

Nurse ta ce "Dan Allah ki bar shi ya je ya huta, ga dare kiyi haƙuri mana ki daure".

"Wai ke ina ruwanki da ni ne? Kina ina lokacin da na samu cikin, was he not behind all this am going through?"

Yazid ya buɗe baki, ga kunya ta ishe shi, bakinta ya ƙi mutuwa.

Nurse ta yi murmushi ta ce "Haka ne da gaskiyarki, Allah ya taimaka".

Yazid ya kuma tallafota yana mata sannu, ta tureshi ta ce ya fita ya bata wuri, ba ta son ganinsa ma.
Da taga kuma zai fita sai ta saka kuka "Zid tafiya zaka yi ka barni, baka tausaya mini ko? Dan Allah ka yi haƙuri zo ka tsaya ta nan ka cigaba da yi mini Addu'a"

Mirsisi Fadila ta hana Yazid fita, ta na kuka yana kuka saboda tausayi a haka ta haihu.

"Alhamdilillah barka da arziƙi, gaskiya laborn nan yayi sauri, haihuwar fari?"

Fadila ta ce "Duk uwar wannan wahalar da na sha?"

"Eh mana" matar ta faɗa tana dariya.

Jaririya ce jawur da ita, 4kg Yazid sai Alhamis yake jerawa yana yiwa Fadila sannu.

Aka gyara jaririyar aka bashi, ya ruƙunƙumeta yana yi mata Addu'a, ya fito da ita.

Nurse ta kalli Fadila ta ce "Ke na ce mijinki ya fita, amma kika hana shi, baki san wasu idan suka ga wannan ƙazantar haihuwar suna ƙyamar matan su ba?"

Fadila ta ce "Mijina ba irin saura bane ba"

Hajiya kuwa harda hawayen ta na farinciki ita ma.

Kasancewar cikin dare Fadila ta haihu, Yazid ya turawa Daddy message kawai.

Daddy ya tashi sallar Asuba, ya ga message ɗin, yana gaya wa Amina ta dinga murna, kamar ita ce ta haihu.

Nan da nan Amina ta saka aka ɗora ruwa, tana ta shiri.

Daddy ya ce "Madam ba fa in da zaki je, kina tashin nan da ƙyar ki zauna da ƙyar".

"Dan Allah Daddy Kar mu yi haka da kai, ka barni na je dan Allah".

Yayi murmushi ya ce "Shikenan, shirya mu je uwar iyali" murmushi ta yi ta shiga wanka.


Hafsa kuwa suna samun labarin haihuwar ta kira Yazid.

"Ɗan ustazunta, dan na rigata haihuwa shi ne ta tsokano haihuwa ita ma, to ai shikenan sai mun zo"

Fadila tana gefen Yazid tana karyawa, sai murmushi ta ke, kasancewar tana jin su.

Daddy ne suka yi sallama a ɗakin, Amina na janyo ƙafa da ƙyar suka shigo.

Kallon Amina ta yi da tausayawa, wannan cikin nata kamar zai rinjayeta ta faɗi.


Amina ta zauna da ƙyar, sai sannu ake yi mata.
Yazid ya ce "Sannu Antynmu, a haka kika fito?"


Daddy ya ƙarasa ya rungume Fadila yana faɗin "Congratulations sweetheart"

"Thank you Daddy"

"Hajiya miƙo wa Daddy Innata ya ganta"

Yazid ya ce "Ke ba kya kara ne?"

Murmushi suka yi, aka miƙawa Daddy jaririyar.

Daddy ya shafa kan jaririyar, yana yi mata Addu'a, yarinyarsu kyakykyawar gaske.

Amina ta ce "Daddy baka bani ita ba"

Daddy ya ce "To gata" ya miƙa mata jaririyar.

Amina ta ce "Masha Allah, an haifa mana balarabiya" tayi maganar tana juya 'yar jairiryar da ke ta bacci.

Suka yi murmushi, Fadila ta yi ƙasa da murya ta ce "Daddy, ka gaya wa Mummy na haihu ne?"

Daddy ya ce "Eh na gaya mata kan mu fito".

"To za ta zo?"

Daddy ya ce "Fadila, ku yiwa mahaifiyarku Addu'a kawai, ta yi nisa ba ta jin kira, ta ce ba zata zo ba, tun da kin zaɓi mijinki, amma dan Allah kar ki ɗaga hankalinki, kiyi haƙuri na san ni kike yiwa biyayya, to ba zaki taɓe ba in sha Allah".

Fadila ta Kwantar da kanta a kan kafaɗar Daddy, ta ce "Daddy yanzu za a sallame ni, daga nan zamu tafi gida ku tayani neman afuwar Mummy, haihuwa babu sauƙi Daddy, bai kamata na yiwa Mummy haka ba, amma kai ma dole ne na yi maka biyayya, kuma aurena yana da muhimmanci, mu je ku tayani bata haƙuri, sannan akwai wani abu da nake son ta sani"

Daddy ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, amma ki daina kuka"

Ta jinjina masa kai alamar to.


Likita ya zo ya duba Fadila, ya rubuta mata sallama, da yadda zata kula da ɗinkin da aka yi mata.


Gaba ɗaya suka tafi gida, su Khalil ma can gidan suka bisu.

Suka tarar da Hajiya Zainab ta kame a falo, tana hura hanci, Fadila ta nufi in da Mummy ta ke zaune.

Hajiya Zainab ta tsuke fuska sosai, ta kawar da kanta gefe.




Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YANA IYA TUNTUƁATA A KAN LAMBAR WAYATA.
08081012143
https://youtube.com/@CoolhausaNovels



87


"Mummy ina kwana?" Fadila ta faɗa a sanyaye.

"Lafiya lau" ta amsa mata a taƙaice, Amina ta ja Hajiyar Yazid zuwa sashinta, gudun kar ayi abin kunya a gabanta, dan babu uwar da zata ji daɗin a wulaƙanta mata ɗa a gabanta.

Yazid ma ya ƙarasa gaban Mummy ya durƙusa a gabanta, ya ce "Mummy ina kwana".

Kallon Yazid ta yi ta watsar, ta cigaba da kallon Tv.

Daddy ne ya shigo rungume da jaririyar su Yazid a hannunsa, ya shigo, ya tarar da su Yazid a gabanta, Fadila tana kuka.
Daddy ya ƙarasa ya kamo hannun Fadila, ya miƙar da ita ya kalli Yazid ya ce "Malam Yazid, ta so mana" jiki a sanyaye Yazid ya tashi, Daddy ya janye 'ya'yansa ya wuce da su sashin Amina.

Miƙewa Hajiya Zainab tayi ta bi bayansu da kallo, wasu irin hawaye ne suka zubo mata daga idonta, kenan da gaske Amina ta ƙwace mata miji da 'ya'ya.

Ɗakinta ta nufa, jikinta a sanyaye, ta dafa kanta ta furta "Na shiga uku, komai sai sake kwaɓe mini yake yi".

Tana son ganin abin da Khalil ya haifa, ga na Fadila kuma, babban abin da ya sake jefata a ɓacin rai, butulcin da Fadila ta yi mata, ta zaɓi wannan talakan yaron a kanta. Wai yanzu Fadila ce ta haihu da wannan talakan, Innalillahi wa innalillahi raji'un.
Ta dafe kanta da yake mata tsananin ciwo, ta zauna tana ajiyar zuciya.

A sashin Amina kuwa, ta saka 'yan aiki sai sauke musu kaɓakin alkhairi ake yi na Abinci, aka yi ta kiran 'yan uwa da dangi ana sanar musu da haihuwa.
Fadila dai duk jikinta babu daɗi, saboda rashin samun karɓuwa a wurin mahaifiyarta.
Su Khalil ma suka ƙaraso gidan, suka tare a sashen Amina, sai hada-hada ake.
Yazid da Hajiya suka yi musu sallama a kan zasu je su dawo.
Fadila sai kallon Amina take, sai ƙoƙarin kyautatawa kowa take yi, yanda ta ke karrama Hajiyar Yazid kamar mahaifiyarta.
Hajara ma sai ɗorawa take tana saukewa, ana bawa wanda suka zo barka Abinci.
Da yawa maƙota sai a yanzu suka san an yiwa Fadila aure, su dai sun daina ganinta kawai.
Amina ta yi ta aikawa ana sanar da mutane haihuwar Fadila.

Da magariba sai ga Yusra a gidan, da Hajara ta haɗu a hanyar shiga main falon, ta kalli Hajara ta ce "Wai da gaske Fadila ta haihu Hajara?".

Hajara ta ce "Eh, tana sashin Amina".
Yusra ta ce "Amina kuma?" Da sauri ta shiga cikin gidan.

Saboda rabonta da Fadila watanni tara kenan ko a waya.

Fadila na ganin Yusra, suka saka ihu suka rungume juna, har da hawayensu na farinciki.

Yusra ta ce "Girl, dama da gaske auren aka yi miki? Mummy ta gaya mini amma na yi mamaki".

Fadila ta ce "Ke dai bari, nan da mutane sosai, zo mu je ɗakina"

Yusra ta ce "Ina abin da kika haifa ɗin?"

Fadila ta ce "Zo muje, kya dawo ki ganta daga baya".

Suka wuce ɗakin Fadila, suka nemi wuri suka zauna.

Yusra ta ce "Girl auren nan ya karɓeki, kinga yadda ki ka yi ƙiba kuwa? Amma ban so aurenki ya zo mana a haka ba, bani labari ya aka yi abubuwa suka zo a haka?"

Hawaye ne ya gangaro da ga idon Fadila, ta gyara zamanta da ƙyar, ta bawa Yusra labarin komai har zuwa yanzu.

Yusra ta waro ido ta ce "You mean Yazid Daddy ya aura miki? Ya aka yi ya san shi?".

"Amina ce ta saka ya aura mini shi, Yusra ina son Yazid sosai, faɗar irin alkhairinsa gareni ba zai faɗu ba, haihuwar nan tawa fa, leshin suna kawai na dubu Ashirin ya saya mini, 'yar nan da na haifa, baki ga kayan da ya saya mata ba, Yazid yana wahalta mini duk da ba shi da shi"

Yusra cikin mamaki ta gyara zama ta ce 'You mean Yazid dai shi ne mijinki Fadila?"

Fadila ta jinjina mata kai ta ce "Yazid ne mijina".

"Amma Fadila mun sha haɗuwa da Yazid, amma bai taɓa gaya mini kuna tare ba".

Fadila ta yi murmushi ta ce 'Ni na hana shi ya gaya miki, saboda Daddy ya ce kar mu sake wani ya san shi ne mijina, saboda kar Mummy ta sani, Yusra ina son mijina, amna Mummy ta ƙi karɓata ya juya mini baya".

Sosai Fadila ta ke kuka, Yusra tayi ta rarrashinta, Yusra ta dubi Fadila ta ce "Fadila na yi miki murnar auren Yazid, mutum ne nagartacce, mai kirki, Allah dai ya ƙaddara sai kun yi aure".

"Haka ne, ina laulayin cikin nan har wurinki na aiko shi, ya sai mini cake kika bamu kyauta"

Yusra ta ce "Allah sarki, ya ƙi gaya mini kuna tare, na sha kuka sosai rashinki bestyna".

Fadila ta dafata ta ce "Matar Abdul, yaushe ne bikin?"

Jiki a ɗan sanyaye Yusra ta ce "Wallahi tun muna tare nake jin nauyin sanar miki Abdul zan aura Fadila, saura sati biyu bikinmu".

Fadila ta ce "Kar ki damu Yusra, ai kin san ni ba son Abdul nake ba, amma na tayaki murna, dan halayensu na yanayi da na Yazid, Allah ya kaimu lokacin".

"Amin Fadila, wai abin har ya kai sai dai kiyi jegon a sashin Amina?"

Fadila ta rausayar da kai ta ce "Gashi kina gani, ko abin da na haifa ba ta gani ba, Yusra na yadda da zancen Amina, wallahi su Hajiya Turai suna ziga Mummy ne kawai suna cutarta"

Yusra ta ce "Kin san na daɗe da fuskantar hakan, magana me kawai ban yi ba dan kar ki ji haushi, wallahi Fadila yakamata ki ajiye duk wani kishi da tashin hankali, ki saka a ranki auren Daddy da Amina ta yi, Allah ya riga ya rubuta hakan, amma wallahi mai ƙaunarku ce, kuma abubuwanta ba ganin ido bane ba, kalli halin da take ciki, amma sai ɗawainiya ta ke yi da ke, dan Allah ki daina gaba da ita"

Fadila ta ɗan murza zoben hannunta ta ce "Nima na yi wannan tunanin, ba dan su Hajiya Turai ba da wasu abubuwan basu faru ba. Yusra a baya Jahilci ne yayi mini katutu na ƙarancim ilimin addini, zamana da Yazid ya sanya na gano abubuwa da yawa. Yusra baki ji labarin Yazid ba abin tausayi, amma nima na zo na dinga muzguna masa a makaranta, ba tare da tunanin ya zai ji a ransa ba.
Matar Yaya Khalil, ita ma baki ji nata labarin ba, amma ita ma muka sakata a gaba da wulaƙanci ina dana sani sosai a kan wasu abubuwan"

Yusra ta sharewa Fadila hawaye ta ce "Kiyi haƙuri, ai Allah mai afuwa ne, mu cigaba da yi wa Mummy Addu'a kawai"

Haka suka yi ta hira, sannan suka koma sashin Amina, Yusra ta ga jaririyar su Fadila.
Sai dai Fadila ta roƙi Yusra a kan kar ta gaya wa kowa a makarantar cewar ta auri Yazid.



Sosai mutane suka cika gidan Alhaji Ahmad, mutanen Dutse 'yan garin su Amina, duk suka cika gidan.
Sai dai duk wannan budurin, Hajiya Zainab bata ko fitowa, balle ta ga me Fadila ta haifa, hakan ya sake jefa Fadila cikin tsananin damuwa, tana farinciki idan ta ga mutanen da suka taru dominta, amma ta rasa kulawar mahaifiya, a kan abin da bai taka kara ya karya ba.

Hajiya Zainab, bayan damuwar da take ciki, ciwo sai gaba yake yi, da ƙyar take iya fitsari, ga ciwon ciki da na baya.


Tun da Inno ta zo, ita ke yiwa jaririyar nan wanka, ta haɗa wa Fadila ruwan wankan jego, tamkar jikarta haka take kula da ita, hakan ya sanya jikin Fadila ya yi sanyi, da irin rashin mutuncin da ta ke yiwa Amina, duba da yadda mahaifiyar Amina ke ta mutunta ta da son 'yar ta.

Ga shi Hajiyar Yazid kullum idan zata zo, sai ta zo da Abinci fal nama, ta kawo wa Fadila, duk da ta san gidansu akwai.
Idan Amina ta yi magana, sai Hajiya ta ce "Ƙyaleta kuɗin mijinta ne".

Ranar suna ana ta shiri, Daddy ya kama musu babban hall da za ayi taron suna.
Kuma Yazid daidai gwargwado yayi ƙoƙari, iya ƙarfinsa.

Amina ce ta ga Fadila ta ɓuya tana kuka, babu komai a ran Amina ta dafa Fadila ta ce "Fadila kukan me kike yi?"

Fadila ta girgiza kai ta ce "Ba komai".

Amina ta ce "Na san ba zai wuce a kan abin da yake tsakaninki da mahaifiyarki ba, amma kiyi haƙuri mai wucewa ne, duk tsananin fushin da ta yi zata huce. Ki cigaba da yi mata Addu'a"

Cikin kuka Fadila ta ce "Cewa fa ta yi babu ni babu ita".

"Faɗa kawai take yi, amma zata sakko, ai tsakanin ɗa da uwa sai Allah"

Khalil ma yayi yinƙurin zuwa ya samu Mummy, a kan ta yi haƙuri ta sassauta fushin da take yi da su.
Amma ta ci mutuncinsa ta koreshi.

Ranar suna an ci an sha, aka sakawa yarinyar suna Khadija ana kiranta Hidaya, sai dai zancen duniya ba ya ɓuya, da yawa mutane sun samu labarin rashin saurarar 'ya'yanta da Hajiya Zainab ta yi saboda sun auri talaka, hakan ya sanya fa yawa mutane suka dinga Allah wadai da halinta ciki har da 'yan uwanta da suka zo suna.


Bayan suna jama'a suka watse, sai Fadila da Amina, da Dattijuwar da take yi mata wanka.
Amina tana daga zaune, har wanka take yiwa Hidaya.


Hajiya Zainab na zaune, a babban falo, jikinta babu daɗi su Hajiya Turai sun zo dubata, sai ga Fadila ta fito ita da Yazid, sai Khalil da Hafsa.

Fadila na ganin Mummy, jikinta yayi sanyi, ta nufi in da Mummy take hannunta riƙe da jaririyarta. Sai dai tana ƙarasawa ta yi wata uwar ƙara ta saki Yarinyar a ƙasa, ita ma ta faɗi ganin Hajiya Salma ta rikiɗe ta zama wata ƙatuwar mage.

Ƙarar da tayi sai da Daddy ya fito shi da Amina, saboda iya ƙarfinta ta yi, jarirriyar ta fashe da kuka.
Khalil ne ya ɗauki Hidaya, yana faɗin Innalillahi wa innalillahi raji'un.
Hatta su Hajara sai da suka fito a gigice.

Yazid ne ya ƙaraso gareta cikin damuwa, ya ɗagota yana kiran sunanta.

Ruƙunƙume Yazid ta yi, tana wani irin kuka, sai karta masa farce take a wuyansa ta ce "Zid ka yi mini Addu'a zan mutu, Wata ƙatuwar mage nake gani fa".

A gigice Daddy ya yo kan su yana faɗin, Me ya sameta?"

Hajiya Zainab kanta saukowa ta yi daga kan kujera ta yo kan Fadila.

Yazid ya ɗaga kai ya ƙurawa su Hajiya Turai ido, sai jikin Turai ya fara rawa, ya kalli Hajiya Salma ya ce "Hajiya Salma ko?"

Da mamaki ta kalli Yazid ta ce "Lafiya, a ina ka sanni?"

Yazid ya ce "Ban sanki ba, amma kamar yadda na bada saƙo a gaya miki, kika yi burus yau Allah ya kawo ƙarshen ku, da abin da kuke yi"

Daddy ya ce "Yazid menene? Kayi mana bayani" Fadila dai sai tura kanta take a ƙirjin Yazid, jikinta na rawa.

Yazid ya ɗan zame rigarsa, ya nunawa Daddy wuyansa zuwa kafaɗarsa, wurin tamkar an tsatsaga masa da reza.
Ya ce "Daddy, tun bayan aurena da Fadila, baifi da watanni uku ba, kusan bama bacci da daddare, kwana nake yi mata Addu'a, wannan raunin na jikina duk ita take yi mini.
Duk da zancen aljani mafi yawa ƙarya ne, amma sun tabattar da Hajiya Salma ce ta turo mata su".

Salati suka ɗauka, Hajiya Salma ta fara kumfar bakin za ayi mata sharri.

Yazid ya kalli Hajiya Turai ya ce "Ƙarya na yi?" Ta sunkuyar da kai ta ce "A'a, tabbas muna yiwa Hajiya Zainab asiri. Tun bayan haɗuwarmu da ita, duk mijinta yafi namu kuɗi, muka fara koya mata bin bokaye, dan ta mallake shi.
Sai dai tana da rowar tsiya, dan haka ita ma muka fara kai sunanta wurin malamai, aka bamu wata laya aka jefa a tsohuwar rijiya, ya zamana ba ta jin maganar kowa sai ta mu, kuma duk abin da muke so ta bamu zata nemo ta bamu.
Ana haka aurena ya mutu, na yi ta ƙoƙarin na samu na auri mijinta, amma ya ƙi, ba asirin da ban yi masa ba, amma abu bai yiwu ba, na koma zaman Saudiyya.
Hajiya Salma ma ba yadda ba tayi ba, a kan ta samu ya auri ƙnawarta ba nan ma ba nasara.
Sai daga baya na haƙura mijina ya mayar da ni.
Bayan Alhaji Ahmad yayi aure, muka yi amfani da wannan damar, muna kaita karɓo asiri, ana kuma asirce mana ita. Aka karɓo maganin da za a zubar da cikin abokiyar zamanta Amina, amma mu idan cikin ya zube, za a sadaukar wa da wani aljani jinin yayi mana namu aikin.
Sau biyu muka yi nasara kawai, bokan ya sanar mana, Amina ba zata taɓu ba sai dai ayi ta amfani da makirci a kanta.
Muka ɓullo da batun haɗa Khalil aure da 'yar ƙanwar Hajiya Salma, da nufin idan suka haihu, sai a kashe Khalil, amma Abin bai yiwu ba.

Muka bijiro da zancen, auren Fadila da ɗan Hajiya Salma, shima duk dan muyi yadda zamu yi mu tatsi kuɗi sosai a hannunku, muka dinga zuwa muna yin asiri a kan ta so Salim, amma abu ya ƙi ci, ƙarshe muna tsaka da wani aikin a kanta, sai ji muka yi an aurar da ita.

Muka dinga yi mata turen aljanu a kan duk in da take ta dawo, ta bijire akan lallai sai ta auri Salim, amma abu ya gagara.
Bokaye suka ce babu aure a tsakanin ta da Salim.
Kasancewar Hajiya Zainab, bata da abin so kamar Fadila, sai muka zaɓi haukata Fadila, saboda mu ƙuntata mata, dan har ga Allah muna hassada da ni'imar da ta fi mu.
Shine muke ta tura mata aljanu, idan aka ce an ƙona wasu sai mu sake biya a tura wasu, kuma galibin kuɗin da muke bayarwar, a hannun Hajiya Zainab muke karɓarsu. Dan Allah ku yafe

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login