Showing 195001 words to 198000 words out of 296192 words

Chapter 66 - GABA DA GABANTA

aljani bai san wuta ba, sai ya taka ta"





Amina kuwa tana kwance a kan katifar ɗakinta, saboda haryanzu jikinta babu ƙwari, sai ga kiran Anty Maryam a wayarta. Amina ta ɗaga tana gaisheta.

"Ke Amina yaya ake ciki, Baby ya ce mini wai Hajiya Zainab ta san batun aurenku ya maganar take, tun jiya nake kiran wayarki bata shiga".

"Eh Anty Maryam, ta sani ɗazun nan Babana da su Baba mamman suka tafi, sun zo an yi mata bayani, sai masifa take da kumfar baki wai zan gani"

"Ba wani nan, bawa bai isa ya yiwa kowa komai ba face abin da Allah ya ƙaddara masa".

Amina ta ce "Haka ne, shiyasa ma ni ban tsorata ba, tunda ina Addu'a"

"Yauwa, ki cigaba da Addu'a ki kuma cigaba da kula da shi, ba abin da ta isa tayi miki"

"Haka ne Anty Maryam"

"Yauwa, aure ai ba aibu bane, tun da Allah ya ce ayi, ita ba a auren aka aureta, tun yana ƙoƙarin ƙara auren tana hanawa har ya haƙura saboda tijararta, ni kain nan da kike ji da gani, mu uku ne a wurin mijinmu"

Amina ta zare ido ta ce "Ku uku?"

"Ƙwarai da gaske mu uku, amma mijina yana mutuntani, yana bani girmana a matsayina na Uwargida da aka yi gwagwarmaya tare, kuma gaba ɗaya matan nasa nima girmamani ske yi, abin da nake so shi ake yi, amma nima sai na dubi zatin Allah bana goyon bayan ya cutar da 'yar kowa, nima na kai 'ya'ya ɗaki, kuma ƙannena suna gidan wasu, duk wadda aka wulaƙanta a gidan miji ni aka yiwa, dan haka ban yarda in wulaƙanta 'yar kowa ba dan mijina yana jin maganata. Kuma tsantsar haƙuri da biyayya ce ta sanya yake bani wannan girman. Dan haka ki zauna da shi saboda Allah, idan taga zata zauna da shi shikenan, idan haukan zata cigaba da yi ba ruwan ki da ita, kuma kar ki yadda ki ƙasƙantar da kanki, matsayinku ɗaya yanzu duk matansa ne"

Amina tayi ajiyar zuciya ta ce "Hakane na gode sosai Antyna"

Suka yi sallama, Amina ta ajiye wayar, gaba ɗaya ji tayi gidan ya isheta, so take ta tafi ko gidansu Azima ne ta ɗan sarara.

Baba kuwa har aka kai shi Shanono cikin ɗar-ɗar yake.
Bai san meka iya biyo bayan tahowarsa ya baro Amina ba, ya sna halin Amina a tsaye take, a baya ma yana tausarta ne yana ja mata kunne, balle kuma yanzu da ta san karanta ya kai tsaiko a gidan, ba zata lamunci a cigaba da wulaƙanta ta ba.

Tun da ya koma Inno ta fuskanci yana cikin damuwa, amma yaƙi ce mata komai, har sai da ta gaji, ta magantu ta ce "Nifa ba ka ce mini komai ba"

"A kan me fa?"

"Kace an maka kiran gaggawa can wurin aikin naka, ka dawo gida fuskarka babu daɗi, kuma baka ce mini komai ba, ko wani abu ne ya samu Yarinyar?"

Baba ya ce "Eh to kusan hakan, ɓari tayi"
Zabura Inno tayi ta ce "Wane irin ɓari kuma?"

Baba ya ce "Wane irin ɓari mata suke yi? Na ciki mana"

"A ina Amina ta samu cikin har tayi ɓarinsa" tayi maganar jikinta na rawa.

"A'a ke kin ji ki wata tambaya, a wurin mijinta mana"

"Malam to ai bata tare ba"

"To, kin san halin Mutanen na zamani, can in da ta tafi birnin tarayya a can suka tare, ni godiyar da nake yiwa Allah shi ne, da ban zafafa a kan maganar auren nan ba, na barwa Allah zaɓinsa aka yi, da ko ba ayi ba idan da rabon zuwan abin cikinta duniya sai ya zo"

"Malam kaga irinta ko, ayi wa yarinya aure tunda wuri kaƙi kai sai tayi boko, ai gashi nan"

Baba ya ce "Ikon Allah, to ai da auren nata dai yanzu ko, a irin tarbiyya da addu'a da muke yiwa Amina ni na san ba zata bani kunya ba, kuma ba albarkacin bokon ta samu mijin da yake ta ɗawainiya da mu ba, har na da na kusa da mu ba? Banda wanda ita ma take aikowa ba, Ai ki gode Allah boko ta yi mana rana. Ni babban abin da ya dameni, yadda matar gidan ta tashi hankalinta, dan kin san bata san an yi auren ba, ina tsoron kar tayi wa uwata wani abu"

A rikice Inno ta ce "Malam kuma ka taho ka barota a can? Idan ta yi mata wani abun fa, da ka sani ka taho da ita"

"Mijinta ya fimi iko da ita, dan haka ba yadda za ayi na ɗaukota, na gaya miki ne dan mu haɗu mu cigaba da yi mata addu'a, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki ba abin da zai faru sai ikon Allah, in sha Allah" yayi ta kwantarwa da Inno hankali.

Amina na nan kwance, mararta na cigaba da ciwo, kaɗan kaɗan, Daddy ya shigo ɗakinta, karo na farko da ya taɓa shiga ɗakinta na aiki.
Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ta tashi zaune ita ma, ba tare da tayi magana ba.

"Sannu my dear, ya jikin?"

Ta ɗan yamutsa fuska kaɗan sannan ta ce "Da sauƙi"

"Yanzu me zaki ci, naje na samo miki?"

"Bakomai, kawai ka kaini gidan Ammi na ɗan huta, ko zuwa dare ne sai ka ɗauko ni"

Ya ɗan gyara zamansa yana kallonta ya ce "Amina dole azo ayi batun tariyar nan, kiyi exms ɗin nan a gidanki, kawai zan saka a sake gyara miki wancan gidan nawa, idan kuma wani kike so sai a saya"
Amina a ranta ta ce 'Anyi ba ayi ba kenan, ai sai Hajiya Zainab ta san bata da wayo tukuna.

Ta ɓata fuska ta ce "Ni gaskiya ka barni a nan, haka kurum taje ta yi mini wani abu a can gidan, gida nika ɗai"

"A'a Meenal, akwai ma'aikata ai a gidan bana son rigima ne, gara na rabaku"

Ta noƙe kafaɗa ta ce "Kawai ka barni a gida, daga ni sai ƙarti suna gadina, a'a gaskiya gara ina nan ɗin, ko wani abun zata yi mini, ai da mutane a gidan nan, balle ba abin da zata yi mini ma, kawai sai na zauna a ɓangaren ka, ni ba ruwana da ita ai"

"Anya kuwa Meenali kin tabatta?" Ta jinjina masa kai.

Ta ce "Sai kuma.."

"Sai kuma me?"

"Sai kuma nima gaskiya kayi mini walima, a san aure muka yi, tunda ba kowa ya san hakan ba, idan na gama Neco sai ayi walimar gama makarantata da tariya"

Daddy ya ce "Sai me kuma?"

Ta kai hannunta fuskarsa ta ce "Sai kuma a maye mini gurbin wannan damuwar da sakin fuska"

"Meenal, dole na shiga damuwa, ban so al'amarin nan ya zo a haka ba"

"Kayi haƙuri, ka kwantar da hankalinka komai na Allah ne, kuma daga gareni ba zaka samu wata matsala ba in Allah ya yarda. Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu, amma dan Allah ka daina wannan damuwar"

Ya ɗan numfasa ya ce "Haka ne, Amen zamu je in kai ki gidan su Aziman ne yanzu?"

"A'a na fasa, ka samu ka ci Abinci ka huta, kar jininka ya hau dan Allah"

"Shikenan, amma ya kike jin jikina naki ba wata matsala ko zamu koma?"

"A'a babu wata mata, naji sauƙi sosai"

"Shikenan bari in tashi, idan da wani abu sai ki kirani kawai a waya"

"To Babyna" ta amsa tana lumshe masa ido.

Murmushi yayi sannan ya tashi ya fita daga ɗakin.

Hajara sai sake jinjina lamarin take.


Fadila da ƙyar ta iya rarrashin Mummy, ta nemi wuri ta kwanta, ita kuma ta koma ɗakinta, tana cigaba da tunanin wace shawara zata bawa Mummy. Ita kanta ta dasa a wani muhallin da zata ajiye abin da Daddy ya aikata.
Wasu hawayen takaici suka shiga zubo mata, saboda ita kanta a ganinta wulaƙanci ne da cin zarafi ga mahaifiyarsu.

Wayarta ta ɗauko tana kuka ta kira Khalil a waya, tayi sa'a wayar na fara ringing ya ɗaga, yayi mata sallama.
Kasa Magana Fadila tayi sai uban kuka da ta fashe da shi.

A rikice Khalil ya ce "Fadila menene? Meyafaru?"

"Daddy ne Khalil"

"Me ya sami Daddyn?"

Ta share hawaywnta ta ce "Khalil Daddy ne yayi aure"

Khalil yayi tsaki ya ce "Shine zaki ɗaga mini hankali, wallahi na zata wani abin ne ya same shi"

"Khalil, baka yi tunanin wani hali Mummy zata shiga ba? Ka san wa ya aura ne? 'yar aikin nan Amina 'yar gidan mai gadi fa, could you imagine?"

Khalil ya ce "To kuma shine kike wannan kukan kamar ance Daddy ya mutu? Ni duk kin tayar mini da hankali"

Fadila ta ce "Khalil, baka damu da halin da Mummy zata shiga ba ne? 'yar aikinta fa ya aura?"

"Fadila aure fa kika ce, Aure yayi ba wani abu ba dan Allah karki tayar mata da hankali da wannan kukan da kike yi"

"Amma Khalil ka bani mamaki fa, ka manta yadda Mummy bata son kishiya? Wato ko a jikinka ko?"

"Ba haka bane ba Fadila, yanzu ace mahaifinmu ya nemi 'yar wani a waje fa? Na san zuciyar Mummy babu daɗi, na san ba a kyauta mata ba, amma kamata yayi ki kwantar mata da hankali, ba ki zauna kina kuka ba, ta sake shiga cikin damuwa ba. In Allah ya yarda zan shigo a satin nan, amma karki bari Mummy ta ce zata yi wani abu da zai janyo mata dana sani a nan gaba"

Gaba ɗaya haushi ne ya kama Fadila, saboda gaba ɗaya ji tayi kamar Khalil bai damu ba sam.

Kashe wayar tayi, ta ajiye, ta fito domin ta koma wurin Mummy.

Tana fitowa falo ta ga Amina ma ta fito, tana ta share share, tana gyara falo.

"Ke!" Fadila ta dakawa Amina tsawa.

Amina ta ɗago kai ta kalli Fadila.

"Baƙar munafuka algunguma, saboda munafurci shine ki auri mahaifina kinga kuɗi jiki na rawa kika shiga kika fita kika aureshi, to wallahi kin kawo kanki kabarinki, sai kin bar gidan nan da ƙafarki, baƙauyiya dabba kawai mayyar abin duniya".

"Fadila kenan, duk abin da zaki gaya mini, ma riga na gama da ke, tun da na haɗa shimfiɗa da babanki. Daga ke har mahaifiyar ki zan baku shawara, ba ruwanku da ni, kuyi rayuwarku nayi tawa mu zauna lafiya, idan ba haka ba yanzu na fara baku mamaki, a cikin gidan nan ku kiyayeni!!!




AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL



62


Murus bakin Fadila ya mutu, ba abin da take sai bin Amin da kallo, ga kalaman na Amina ba ƙaramin baƙantawa Fadila rai suka yi ba, wai har ita Daddy zai ce a yiwa warning a kan wannan Yarinyar da take yiwa kallon ƙasƙanci. Amina ta bata mamaki ƙwarai da gaske.
Amina kuwa ta cigaba da aikinta, ta share Fadila da ke tsaye tana binta da ido.

Kasa jurewa Hajiya Zainab tayi, ta ɗau wayarta ta kira Hajiya Salma, har ta kusa katsewa Hajiya Salma ta ɗaga, suka gaisa Hajiya Salma ta ce "Ya naji muryar taki ƙasa-ƙasa ko baki da lafiya ne?"

"Hajiya Salma ba gara ace kwance nake ba lafiya ba, idan likita ya dubani wataƙila na warke ba, a kan masifar da nake ciki a yanzu"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyafaru ne?"

"Hajiya Salma na ƙara yadda, namiji ƙanin ajali ne, tsawon shekarun da muka yi tare, a wannan karon ya gwada mini halin nasu"

"Zainab, dan Allah ki warware mini ki daina yi mini magana kwan gaba kwan baya, me yayi miki?"

Ta  ɗan numfasa sannan ta ce "Aure yayi"

"Shi wa?"

"Ahmad mana Salma, aure yayi ban sani ba yau watanni kusan uku da ɗaura masa aure, sai jiya Allah ya toni asirinsa, kin san abin baƙin ciki kin san wa ya aura?"

"Bala'i, wace 'yar hau ɗin mai tsautsayin masifar ya aura?"

"Salma 'yar aikina, 'yar wurin maigadi"

"Laila ha illalahu Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam, dan Allah Zainab kice mini da wasa kike yi mana"

Cikin karaya Hajiya Zainab ta ce "Na taɓa yi miki irin wannan wasan ne?"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, amma Ahmad ya cika mara mutunci, shi duk matan duniya ya rasa wadda zai aura sai wannan? Amma Zainab kina me har alaƙa ta shiga tsakaninsu suka yi aure baki sani ba"

"Hmm, Salma munafuncin ɗa namiji ya wuce lissafinki da tunaninki, ko da wasa bai taɓa nuna wata alama na yana son Yarinyar nan ba, Rashin kunya tayi mini, Fadila ta tureta ta faɗi sai jini ya ɓalle, na kira Doctor Aliyu aka dubata sai ga ciki, na kira shi nace zan koreta ya ce in jira ya dawo, ashe wai ya aureta wata Uku kenan, wai idan ta gama jarrabawa zata tare, sannan ya gaya mini, Ashe abin competition da ta tafi Abuja suna tare, Salma na rasa yadda zan yi da raina, ji nake tamkar na balbala fetur na ƙonemu duka a gidan, kaina ya toshe na rasa mafita".

Hajiya Salma ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai ba zamu so kiyi abin da za ayi mutuwar kasko ba, ubansu zamu ci sai ta fita ta bar gidan nan ko tsirara ne, shi kuma zai gane bashi da wayo, zan yiwa Turai magana zamu zo"

"To shikenan Salma, sai anjima"

"Dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar kiyi musu wani abu da zaki illatasu, abu ya kwaɓe miki, ki bari dai mu zo"

"In Sha Allah, ba abin da zan yi sai kun zo ɗin" suka yi sallama ta kashe wayar.

Amina jin ta ɗan ji sauƙi ya sanya, ta ware ta cigaba da aikinta, amma hankalinta na kan Daddy, tunda ya fita bai dawo ba, ta san yana tsoron dawowa saboda Hajiya Zainab zata rikita masa lissafi. 'Aikuwa ba zan abri hakan ta faru ba, idan ita bata son sa ni ina so, ba zata katse mini walwalarsa ba, wadda ita ce tsanin farinciki na ba'

Kitchen ta shiga tana gaganiyar ɗora Abinci, Hajara ta shigo Kitchen ɗin tana ganin Amina, da sauri ta ce "Amina ai kinfi ƙarfin wannan aikin yanzu, ga baki da lafiya ga shi kin zama matar gida, ai wannan aikin sa mu".

Amina tayi murmushi ta ce "Ni ɗin wace da ba zan aiki ba, in naɗe sai dai ayi mini komai, ladan da zan samu fa. Manta kawai zan yi aikina, kya tayani da abin da ba a rasa ba".

Hajara ta ce "A'a Amina, idan Allah ya ce ka huta ai sai ka huta, ke ina ke ina wannan aikin yanzu, yanzu fa daidai kike da masu gida, ke ma matar gidan ce, dan kije ki huta nayi aikina"

"Hmm, lallai Hajara gani kike da wasa nake" Amina ta cigaba da ayyukanta.

Sai da ta kammala, Hajara na tayata suna hira, amma Amina ba ta bari Hajara tayi mata tambayar rainin hankali ba, ko bin diddigin taji yadda abubuwa suka gudana ba.

Ƙarfe takwas na dare, Amina ta gama komai ta cewa Hajara, ta je ta sanarwa da su Hajiha Zainab, an gama girki su fito suyi dinner.
Ita kuma ta wuce ɗakinta, ta ɗau waya ta kira Daddy.

Yanayin yadda ya amsa wayar kawai, ya isa ya nuna maka yana cikin damuwa.

"Hello My dear kana ina ne?"

A ɗan rikice ya ce "Lafiya, wani abin ne yafaru? Ko wani abun tayi miki?"

"A'a ni ba abin da tayi mini"

"To jikin ne?"

"A'a fa duk ka kwantar da hankalinka, naga haryanzu baka dawo bane ba, nayi maka girki ka dawo kaci Abinci ka kwanta ka huta mana"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Zan dawo in sha Allah"

"Yauwa dan Allah ka dawo yanzu kaji My"

"Shikenan Meenali, gani nan" ta katse kiran, ta ajiye wayar ta shiga wanka.

Hajara kuwa koda taje ta sanar da Fadila an gama girki, wata irin tsawa ta daka mata, ta koreta daga ɗakinta, saboda shirme kuma, sai ta tafi ɗakin Hajiya Zainab, wai ko ita zata ci.

Wata ashariya da Hajiya Zainab ta bankawa Hajara, bayan ta gama sanar mata da batun an gama abinci, sai da Hajara ta rikice.
"Munafuka kema kin san komai, dake aka haɗa kai, ki ƙulle kayanki sai kin bar mini gida kema, gayyar tsiya gayya jaraba matsiyatan banza da na wofi, zaki fita ki bar mini ɗaki ko saina taka wuyanki, algungumai zuriyar tsiya" sum sum Hajara ta baro ɗakin Hajiya Zainab, ta tafi wurin Amina.
Ta tarar da Amina a zaune, tana ta shafa turare.
Amina ta kalli Hajara da take kamar a razanae ta ce 'Lafiya kuwa?"

"Sunce ba sa ci, ni wata uwar ashar da aka yi mini, tunda nake ban taɓa jin irinta ba, dama ace mini matsiyaciya na saba, amma wannan ashar tayi mini zafi, wai kuma nima ta koreni barin gidan nan zan yi" Hajara ta ƙarasa maganar kamar tayi kuka.

Amina ta ɗan jinjina kai ta ce "Kiyi haƙuri, ba in da zaki in sha Allah"


Da ta gama shirinta ta windown kitchen taje ta leƙa, taga Alhaji Ahmad ya dawo.

Ta shirya ta tafi sashinsa, da kayan Abincinsa na dare.

Da sallama ta shiga, ya amsa mata yana zaune yayi shiru, alama yana cikin damuwa.
Ta zauna a kusa da shi ta ce "Sannu da zuwa"

"Yauwa Meenal, ya jikin?"

"Jiki Alhamdilillah na warware, ga abinci nayi ta so ka ci"

Daddy ya kalleta ya ce "Baki da lafiya kika yi girki?"

"Idan ban yi ba kai me zaka ci, me mutanen gidan za su ci? Naji sauƙin jikina ne, ta so ka ci"

"Meenal bar abincin nan kawai"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka ci, ga yunwa ga damuwa da wanne zaka ji"
Ganin duk ta damu ya sanya shi haƙura, ya ci Abincin da kanta ta dinga ba shi tana yi masa hira, har ya ɗan saki ransa.

"Daddy, nayi girki naga mutan gidan sun ƙi ci, duk da na san haushina suke ji, amma ni ba zan daina ayyukan da nake na gidan nan ba, daga girki gyaran part ɗinka kan na tare, gyaran ko ina ma, sashensu ne kawai Hajara ta dinga gyara musu, kuma ni zan zauna da su tsakani da Allah babu ruwana da su, ni dai fatana kawai Allah ya baka ikon yi mana adalci"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Meenal kenan, naji daɗin maganarki Allah ya dafa mana"

Ta amsa da "Amin" sai da ya gama ci, ta tashi tana masa sallama ya ce "Ba zaki kwana a nan ba?"

"Saboda me zan kwana a nan?"

"Ba zaki buƙaci wani abun ba? kije ki kwana ke kaɗai keda baki da lafiya"

"Ba abin da zai faru da ni in sha Allah, good night" tayi kissing ɗin lips ɗinsa.

Bayan tafiyar Amina, ya sake komawa wurin Hajiya Zainab, saboda yana matuƙar jin tausayinta, ya san kishi shi ne weak point ɗinta, bata ƙaunar taga wata ta raɓe shi, amma lokaci guda ya shammaceta haka.


Ko da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login