Showing 183001 words to 186000 words out of 296192 words
ke masa kallon uba, amma daga baya ha kasa gane wane feelings yake da ita a kanta, ya kan samu wata nutsuwa ta mussman idan yana tare da ita.
Ranar da ya sauketa a hanya kuwa, a kan tayi maganar Hajiya Zainab, ji yayi tamkar ya sauka ya bita su tafi tare, amma yayi hakan ne dan kar alaƙar da kw tsakaninsu ya sanya ta ce zata raina uwar ɗakin nata, dan ba zai iya bari ta koreta daga gidan nan ba.
Sannu a hankali ya dinga tafiya a motar, har zuwa lokacin da ta hau motar Bilal, tun da ta shiga motar Bilal yaji wani irin haushi da kishi ya mamaye masa zuciya.
Kwana biyu a tsakani, yaga Bilala a gidan, ya je wurin Baba suna gaisawa, hakanan hankalinsa ya tashi yaji yana son sanin meye alaƙar dale tsakaninsa da Amina da har zai zo wurin Baba.
Haka nan Alhaji Ahmad ya kasa zane ya kasa tsaye, ya rasa wanda zai tunkara da maganar.
Ya samu wani abokinsa, Alhaji Sambo ya gaya masa komai.
Dariya Alhaji Sambo ya dinga yi masa ya ce "Lallai kana son kunna wuta a gidanka Ahmad"
"Ban fahimce ka ba me kake nufi?"
"Au tanbayata ma kake yi? Son yarinyar nan kake malam"
Daddy ya dafe ƙirji ya ce "Haba dai, yanzu ya zanyi?"
Alhaji Sambo ya ce "Ka yarda son nata kake ko kuwa?"
Daddy ya ɗanyi shiru sannan ya ce "Na yadda da maganar ka, dan bana jin zan iya yarda ta bar gidana, saboda yadda take kula dani, amma na rasa abin yi, ga wani yaro a maƙotana da ya sarƙi zuwa wurin mahaifinta na san bai wuce ya ce Aurenta zai yi ba"
"Ka shirya facing ɗin kowane Challage dan ta zama taka?"
"Kamar dai haka nake ji a jikina"
"Ka fara nemo soyayyarta, sai in gaya maka abu na biyu da za mu yi"
Daddy ya waro ido ya ce "Ta yaya ni Ahmad, Sambo ba ta fi shekaru sha shida ba fa, kalleni sai inje in ce ina sonta?"
Alhaji Sambo ya ce "Kai dalla ware, ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Sweet sixteen kenan ake gaya maka, ita kaɗai ta isa maganin damuwarka, ita waccan matar taka ba ta saka shirme a gaba ba, malam Allah ne ya baka dama kawai kayi abin da ya dace fara samun soyayarta dan ba za ayi mata dole ba"
Daddy ya goge gumin goshinsa ya ce "Ni Ahmad ta ina zan fara wannan taɓarar, na kalli yarinyar da take mini kallon uba nace ina sonta?"
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM
58
Haka suka yi sallama da Alhaji Sambo, Daddy ya koma gida yana cigaba da saƙe saƙen yadda zai ɓullowa lamarin yi wa Amina bayanin abin da yake buƙata, dan yarinta Amina akwai ƙuruciya, ya samu ta karɓi batun ma ya san sai ya sha gwagwarmaya.
Ya cigaba da ƙoƙarin samun kusanci da ita, tare da kyautata mata, yana yi yana lissafin yadda zai yi ya sanar mata da abin da yake zuciyarsa dan ganin abin yake banbarakwai.
Mussaman ya aika aka ɗauko masa ita aka kai masa ita gidansa, ya sakata tayi masa girki, har Kitchen ɗin yaje ya tsaya yana kallonta, amma ya kasa ce mata komai.
Sai da ta kawo masa Abincin, ya fara ci yana ta yi mata santi tana murmushi, ya numfasa ya ɗan tsura nata ido sannan ya ce "Sweetheart Abincin nan yayi daɗi fiye da yadda kike zato, kullum girkinki ƙara daɗi yake"
Waro ido waje tayi ta ce "Sweetheart kuma?"
Ya ce "Eh mana, ai normal ne, ina gayawa mutane na mussaman a wurina, ina gayawa matata da 'ya'yana, kema kuma ta musamman ce"
"To aini 'yar aiki ce" ta faɗa tana ɗan tsuke fuska.
"Meenalina, ina son na mayar da ke ƙarƙashin inuwata yadda zan baki kulawa yadda yakamata" yayi mata maganar cikin nutsuwa yana kallon fuskarta
"Nifa bana gane magana a dunƙule"
Yayi murmushi ya ce "Ina son ki zama tawa, ki zama cikin kulawata da kariyata"
"In zama taka sai kace wata baiwa, ba zamanin bayi ne ake wannan ba"
Amina kenan duk wani abun serious, sai ta kawo shirmenta a ciki.
"Meenal"
"Na'am Daddy"
"Zaki iya aurena?" Da hankalinta rabi na kansa rabi kuma na kan Tv, dai taji maganar tasa kamar daga cikin tv ta fito, tayi masa ƙuri da ido.
Ya jinjina mata kai ya ce "Yes, i mean it, zaki iya aurena?"
"Taɓ Daddy ka daina wanan wasan dan Allah"
"Kalli idona, ba wasa nake ba, ina son na cigaba da samun kulawa daga gareki. Ki kalli abin da na zo miki da shi a mahanga ta addini, ba a mahangar Al'ada ba, addininmu bai hana hakan ba, amma kiyi tunani a kai, zaki iya aurena?"
Tura baki tayi ta ce "Ni ba zan auri tsoho ba"
Yayi murmushi ya ce "Jarmai kike so kenan?"
"Allah ya kiyaye, Jarmai fa ƙazami ne, gashi masifaffe, ga auri sakin tsiya, gidansa yaransa sun fi Ashirin, ya haɗa kai da su Baffa Lawan, suka sayi gonar Baba da arha, ni bana sonsa".
"To Bilal kike so?"
"To ai ni ban san me ake ji idan ana son mutum ba, Nifa ba soyayya muke da Bilal ɗin bama, kawai mutunci muke yake zuwa gaida Baba".
"Is ok, ina nan ina sauraren amsarki, ba zan takura miki ba, na gaya miki abin da ke zuciyata ne, idan ba kya sona, bakomai zan yi haƙuri in tayaki samun wanda kike so ɗin kinji Meenalina, amma dai Daddy yana son Meenalinsa Sosai, idan Meenal ta auri Daddy zai ririta ta ya bata dukkan kulawar da take buƙata".
Amina ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya, ita wannan abu jinsa take kamar daga sama an yiwa wada ƙwace.
Ganin duk ta takura da maganganunsa, ya sanya ya ce ta tashi ya sauketa a gida. Ba musu ta ɗau jakarta tayi waje.
Suna tafe a mota, taƙi kallon in da yake sai kawar da kai take yi, saboda nauyinsa da take ji.
"Meenal"
"Na'am" ta amsa ba tare da ta waiwayo ba.
"Kalleni mana" taƙi waiwayowa ta kalleshi. Ya ce "kar ki je ki saka maganar nan a ranki ki ƙi sakewa kinji, ba zan takura miki a kan abin da ba kya so ba kinji sweetyna"
A ranta ta ce "Innalillahi, me Daddy ya zama ne?"
Haka yayi ta surutunsa, ita dai ba ta ce masa komai ba suka cigaba da tafiya.
A bakin layin ya ajiyeta, ya ce "Maza daga nan ki wuce gida, kije ki samu ki huta, sai mun yi waya" kai kawai ta ɗaga masa, ta fice daga motar da sauri, ta shiga layin.
Daga nan Kai tsaye wurin Alhaji Sambo ya wuce, ya gaya masa yadda suka yi Amina, Alhaji Sambo ya ce "Shawarar da zan baka ita ce, ka cigaba da lallaɓata sannu a hankali, tunda yarinya ce ƙarama, kar ka nuna zaka yi mata dole, komai zai zo da sauƙi in sha Allah".
Daddy ya ce "Allah ya amince, ina fatan ta amince ɗin, kamar tana sona shirirtarta ce ta dameta shiyasa ba ta gane hakan ba".
Alhaji Sambo yayi dariya ya ce "Ai shirirtar kake yiwa, kawai ka cigaba da wasanka, sai dai kayi taka tsantsan kar wannan masifaffiyar matar taka ta sani, dan wallahi ta sani yarinyar ta shiga uku ne".
"Ai ba zan bari ta sani ba, ina sane da duk abin da nake yi".
Alhaji Sambo ya cigaba da ba shi shawarwari, daga bisani suka yi sallama.
Ko da taje gida ɗakinta ta wuce, tana tunani tana jujjuya maganar da Daddy yayi mata, ita kaɗai ma a ɗakin sai kunya take ji, tana sake jin abun wani iri.
Da daddare ta gama shirinta, ta zauna ta ɗauko littafinta tana karatu, kawai sai taga wayarta tana ringing, ta duba taga Daddy ne, taƙi ɗagawa ta zubawa wayar ido.
Ya kirata ya kai sau uku, amma taƙi amsa wayar.
Saƙonsa ne ya shigo wayar "Meenali meyasa ba kya ɗaga wayata?"
"Bakomai" ta tura masa dan shirme.
"Wai duk a kan maganar nan ne, dan Allah ki saki ranki, ki ɗaga wayar muyi magana". Yana tura mata saƙon ya kuma kiranta a waya, jiki na rawa ta ɗaga, ji take kamar a gabansa take kunya na sake ratsata.
"Duk dan nace ina sonki shi ne kika ƙi amsa mini waya?" Tayi shiru.
"Meenal, ke ma'abociyar ilimin addini ce, abin da na nema a wurinki, bai saɓawa addini ba, ki kalleshi a ma'aunin Addini ba al'ada ba, kin ji, ni dai fatana ki saurari zuciyarki ki gani idan zaki iya aurena ki zauna da ni, amma idan da wanda kike so ba zan takura miki kinji"
"To"
"Yauwa, na san wataƙila yanzu kina karatu ne, ayi karatu lafiya" ko sallama ba ta yi masa ba ta kashe wayar gaba ɗaya.
Babu wanda ta gayawa abin da ya faru, da abin da Daddy ya ce mata. Sai dai duk abin da zai haɗa su kauce masa take yi, ta koma shiryawa da uwar safiya ta tafi makaranta, idan ta dawo kuwa ba zata bari su haɗu ba, ta wuni a ɗaki. Ta daina kunna wayarta gaba ɗaya, dan karma ya kirata ya sameta.
Ranar wata juma'a, bayan ta dawo daga makaranta, Hajiya Zainab ta tafi yawon bikinta, Fadila kuma na makaranta. zaton Amina Daddy ma baya gida, dan haka ta fito falo tana cin kantu a leda, tana goge goge, ba tsammani ta juya ta ganshi a tsaye yana kallonta. Gaba ɗaya ta rikice ta na neman wurin ɓuya, kamar wadda ta yada zani a gaban siriki.
Yayi murmushi yayi mata alamar ta zo. Ji tayi kamar kar taje, sai kuma taga idan tayi hakan baya kyauta ba, dan haka tabi bayansa.
Bai tsaya a ko ina ba sai a tsakiyar falonsa. Ya kalleta ya ce "''yar Babyna, laifin me nayi miki kuma kike guduna, kika dai na amsa wayata?"
Tayi shiru tana wasa da ledar hannunta.
Ya miƙa mata tafin hannunsa ya ce "Ɗan sanmini abin da kike cin"
Ba musu ta miƙa masa ledar kantun.
Ya ce "Zaki bani abin hannunki amma kina guduna ko, dan Allah ki bar wayarki a kunne muyi magana da daddare kinji?"
Ta amsa da to, ya ce "You can go, ko in zo in tayaki aikin ne"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Hmm to shikenan, sai munyi wayar, jeki ki cigaba da aikin ki" ita dai ba tace masa ƙala ba ta bar falon.
Da daddare da Daddyn ya kirata ma dai, shirun tayi masa yayita kiɗansa yana rawarsa, bata iya ce masa komai, sai ya gama wayar ta ajiye tana dariya.
Suna daf da fara jarrabawa, ta shirya zata tafi makaranta, ta fito falo ta tarar da Baba a durƙushe a gaban Hajiya Zainab, sai banbamin bala'i take yi masa. Cak Amina ta tsaya ta rasa abin da za tayi ko ta ce, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, tana ta ci masa mutunci, Amina ba ta san laifin da Baba yayi mata ba, sai da tayi ta gama ta sallmeshi, sannan Amina tabi bayan Baba.
Cikin sauri ta ƙarasa ta cimmasa "Baba" ya tsaya ya waiwayo ya kalli Amina.
Ƙwalla ta gani kwance a idon Baba, ya dake ya ce "Makarantar zaki ne?"
"Baba me kayi mata take maka wannan rashin mutunci da sassafe"
Baba ya ce "Kar ki damu, Kina da kuɗin makaranta ko na baki?"
Hawaye Amina ta fara yi, wani irin tausayin Baba ya sake kamata.
Saura ƙiris hawayen idonsa ya zubo, amma ya dake ya ce "Yi maza ki tafi kar ki makara"
Haka Amina ta tafi makaranta tana kuka, gaba ɗaya haka taje makarantar bata walwala.
Azima tai ta tambayarta meke damunta, amma taƙi gayamata sai kukanta kawai take.
Da aka tashi daga makaranta, sun fito zasu tafi, Amina ta ce "Azima kinga sabon dabino, muje na sayawa Baba yana son sabon dabino sosai"
Azima ta raka Amina, suka sai dabino, Azima ba ƙaramin burgeta Amina take ba, saboda alaƙarta da Babanta, dan ita nata mahaifin ya daɗe da rasuwa.
Amina ta kalli Azima ta ce "Azima wannan dabinon sai dai kiyi haƙuri, na Baba ne, dan haka ni da ke ba mai ci"
Azima tayi murmushi, ta ce "Ai nima mai saya ce in baki ki kai wa Baba. Amina ina fatan ubangiji Allah ya baki miji nagari a garin nan, wanda zai riƙeki amana ya raba Baba da wannan aiki a ƙarƙashin mutanen gidan nan naku marasa mutunci"
Shiru Amina tayi tana nazartar maganganun Azima, kamar ta tunatar da ita wani abu mai matuƙar muhimmanci, da sauri Amina ta ce "Azima na gode, sai Allah ya kaimu gobe" ta nufi titi tana cigaba da juya maganar Azima a ranta.
Baba yayi murna da dabinon da Amina ta kawo masa, Yayi ta yi mata addu'a.
Amina da taje ɗakinta, tayi salla ta dinga tunanin maganar Azima, Allah ya bata miji nagari wanda zai raba Baba da aikin gadi.
"What if na Auri Alhaji Ahmad, kenan Allah ma ya riga ya bani ban ankare ba" tayi maganar tana murmushi.
Amina ta wuni ta na nazarin maganar Azima.
Kamar kullum da daddare, Amina na tsaka da karatu, Daddy ya kirata, yau ba jan aji ta ɗaga wayar.
"Hello 'yar Babyna"
"Daddyna" ita kanta da ta faɗi hakan sai da kunya ta kama ta.
"Wow, amma naji daɗi sosai, ya school ɗin 'yar Babyna?"
"Alhamdilillah, ya aiki?"
"Aiki kam akwai shi, kin bani aikin tunaninki Sweetheart, ina cikin damuwa, duk na rame".
Cikin kulawa ta ce "Daddy damuwar me kuma?"
"Kin ƙi bani amsa zaki aureni, kince ba kya sona"
Amina ta ce "Ka tambayi Baba duk abin da yace maka shikenan"
"Kina nufin idan Baba ya amince zaki aureni?"
A kunyace ta ce "Mmm, amma kar kace masa ni nace ka tambayeshi"
Wani lumshe ido yayi yana murmushi ya ce "Thank you Meenalina, idan har Baba ya amince na aureki, zan baki farinciki da kulawa iya yina"
"Hmm sai anjima"
"Au ba zaki tsaya muyi hirar ba, a haka za mu yi auren Babyn, Ahmad yana sonki sosai fa"
Kashe wayar Amina tayi, ta dafe ƙirji tana murmushi ta ce "Daddy dama haka kake? Sai kunya yake bani, innalillahi wa yaga na auri Daddy".
Ta shiga what's app ɗinta, ta duba hotunansa da yake turo mata.
"Wayyo Allah na, masha Allah Daddy fa yana da kyau, ga shi da gemu ga gayu. Yana aura ta zan saka Baba ya bar aikin gadi a gidan nan, kuma duk wani mai rabo sai yaci arziƙin da ake wulaƙanta mu a kansa, wayyo zuciyata". Tayi maganar tana tsalle a kan katifarta
Daddy kuwa jinsa yake tamkar ya taka rawa, saboda tsabar farinciki da jin daɗi, washegari da safe Alhaji Ahmad ya koma wurin Alhaji Sambo, ya sanar masa.
Alhaji Sambo ya ce "Alhamdilillah, yanzu abin da ya rage kan ka tambayi mahaifin nata aurenta, zan fara zuwa garinsu, nayi maka bincike a kansu tukuna dan ko ba komai yakamta ka san wa zaka aura, Daddy ya ce hakane.
Alhaji Sambo da kansa ya je Shanono, yin bincike a kan dangin su Amina, ya samu kyawawan bayanai a kan mahaifinta, sai dai sai da aka gaya masa batun guduwa da Amina tayi daga garin za ayi mata aure.
Da Alhaji Sambo ya dawo wa da Alhaji Ahmad da sakamakon binciken sa, Alhaji Ahmad ya ce Bakomai, da ta gudun ai wurin Baba ta taho nan gidansa, hakan ya ƙara bawa Alhaji Ahmad ƙwarin gwiwar zuwa ya tunkari Baba Hassan.
Malam Hassan yayi mamakin ganin Alhaji Ahmad a ɗakinsa na gadi.
Suka gaisa da Baba, gaba ɗaya jikin Baba yayi sanyi, saboda tsananin mamaki har tsoro yake kar wani laifin yayi.
Alhaji Ahmad ya duni Baba cikin nutsuwa ya ce "Malam Hassan, na san zaka yi mamakin ganina a daidai wannan lokaci, sai dai na zo ne domin wata muhimmiyar magana sosai da sosai, amma ina son ka kalli maganata a mahangar addini, wata alfarma na zo nema a wurinka, ban sani ba ko zaka iya yi mini"
Baba ya ɗan yi shiru yana tunanin wace irin alfarma ce haka, ya numfasa ya ce "In dai bata fi ƙarfina ba, kuma bai saɓawa addini ba in Allah ya yarda zan maka"
Alhaji Ahmad ya ce "Masha Allah, abu ne na alkhairi, da nake saka ran ya zame mana alkhairi a tsakaninmu. Malam Hassan ba wata alfarma ba ce ba, Auren Amina nake son ka bani, ina son zan aureta idan ka amince"
Jimmm Baba yayi, yaji maganar daga sama, wani banbarakwai.
"Malam Hassan, ba takura maka zan yi kayi mini abin da baka yi niyya ba, ba takura muku zanyi ba, idan kana ganin babau damuwa ina son ka bani aurenta, ta zama a ƙarƙashin kulawata"
Baba yayi shiru sannan ya ce "Amma Yallaɓai, wannan lamari da ka zo da shi yayi girma da yawa, al'umma za suyi mana kallon butulallu, daga zuwa cin arziƙi, shikenan kuma sai ka auri 'ya ta"
"Malam Hassan kar ka damu da wannan, ai addininmu bai hana ba, idan kana ganin babu damuwa ina neman wannan alfarmar, amma zan baka dama kayi shawara tukuna"
Malam Hassan ya ce "To shikenan, Allah ya wuce mana gaba".
Bayan kwana da biyu da yin maganar, Baba ya dage yana Addu'a a kan lamarin, baya son yayi jayayya a kan lamarin, saboda ya lura da tun kan Alhaji Ahmad ya gaya masa, Ya lura da yadda kusancin Alhaji Ahmad da Amina yayi yawa.
Dan gaba ɗaya ta daina jin nauyinsa, ƙarewa ita ma Daddy take ce masa, baya son ya zaƙe ya zo yaji kunya daga baya.
Amina ta kai masa Abincin dare, ya tsayar da ita, ya ce "Uwata magana za muyi"
Ta ce "To Baba".
"Maigidan nan ya zo mini da wani zance na cewar wai yana sonki, zai aureki, duk da dai alamu sun nuna kun gama fahimtar juna kan maganar ta iso gareni"
Nan Amina ta tubure a kan cewar ita bata san zancen ba.
Baba yayi murmushi ya ce "Hmm koma dai mene, ki je kiyi ta addu'a, sannan idan kina son mutumin nan zaki aureshi, ki aure shi saboda Allah ba wani abu ba, kuma abu na gaba ina jinjina yadda zaki da iyalansa, sannan kuma ga batun karatunki bana son karatunki ya tsaya".
"Ai ya ce saina gama karatu x
Baba ya ce "Kuma ki ka ce baki san zancen ba" da sauri Amina ta shiga taitayinta, ta tuno katoɓarar da tayi.
Baba ya ce "Tashi kije, ki cigaba da Addu'ax
Amina ta tashi ta tafi.
Baba ya duƙufa yana ta Addu'a a kan lamarin, saboda ya lura da yadda ita kanta Amina ke da rawar kai, kuma ya fuskanci tana son Alhaji Ahmad ɗin.
Alhaji Ahmad kuwa ya cigaba da lallaɓa Amina, yana kyautata mata