Showing 162001 words to 165000 words out of 296192 words
ce "Kina son tafiya?" Ta ɗaga masa kai.
"Idan kina son tafiya, dole ki dinga bin umarnina, adadin yadda kike mini biyayya shi zai kusanto da komawarki gida"
"Ai ina maka biyayya"
Ya ce "Kuma kina mini tsiwa ba, da taurin kai ba"
"A'a na daina" tayi maganar seriously.
'A baki ba, amma na san zaki cigaba ai"
"Allah Daddy na daina"
"Kina sane kike yi mini kenan, dan kin raina ni ko?"
"A'a ban rainaka ba"
Ya lumshe idanunsa, ya kamo hannunta ya ɗora a kan gemunsa, Sannan ya ce "Bana jin daɗin ganin kin je school kin dawo, a zo a saka ki aiki, ko kuma in ga ana gaya miki maganar da zata ɓata miki rai, a duk lokacin da na ganki a cikin damuwa bana jin daɗi"
Kamar ba yanzu ya gama yi mata kashedi ba cikin tsiwar ta ce "Eh amma ai kana gani ake mini baka cewa komai, ake mini duk abin da ake minin"
Daddy ya ce "Meenal ba zaki canza ba, Allahn da yayi ki bakinki baya shiru, kamar ba yanzu muka gama yarjejeniya da ke ba"
"Au na manta Yi haƙuri"
"Da anyi magana ki fara ayi haƙuri, matar tawa zan cewa dan me dan ta miki wani abu?, ba 'yar aikinta ce ba ke" ture kansa tayi daga kan cinyarta ta naɗe ƙafafuwanta, tana hararsa.
Dariya yake yi sosai, yana son ya ga ya kunna Amina, tana wannan kumbure kumburen, mussman yadda kishinta baya ɓuya sam.
"Ki cigaba da rashin ji, muna nan da ke like for 6months, in kin daina tsiwa sai ki koma gida, tashi ki shirya mu tafi kar muyi yamma, kinga bamu ci abinci ba"
Tayi masa ƙuri da ido, tana kallonsa cike da ƙuruciya.
Ya ce "Shikenan, bari in zo in shiryaki, sai munfi sauri" da sauri ta tashi tsaye ta ce "A'a zan shirya da kaina, ka tafi zan fito"
"Ni kike kora?"
Ta ɗan rausayar da kai ta ce "A'a ni na isa??"
Ya fice yana mata dariya.
Wajen ƙarfe biyar saura, sannan Amina ta fito cikin shiri, yana zaune a falo yana jiranta, ta gama nuƙu_nuƙunta da ɓaga lokacinta sannan ta fito.
Ya ɗan tsura mata idanu, ya ga tayi masa kyau sosai, ta ƙara girma.
"Me kuma nayi naga kana kallona?"
"Sai kin yi wani abu zan kalleki, kyau kika yi mini sosai"
Ɗan murmushi ta yi ta ce "To turare fa?"
"Ba zaki shafa mini turare ba, idan mun fita zan sai miki naki"
"To kai kana ƙamshi ni bana yi"
"Zaki fara ko?, Dama idan kin saka turaren aini yakamata naji ƙamshin ba wani ba, tun da Karuwar ta wace nikaɗai" yayi maganar yana dariya.
Haɗe rai tayi ta kalleshi ta ce "Nice karuwa?"
"Kefa kika fara faɗa bani ba" haɗe rai ta yi, ta sha kunu ta kawar da kanta gefe.
"Meye na fushin kuma my cartoon, zo kiji" yayi maganar yana jan hannunta, ta fizge hannunta ta naɗe shi a ƙirjinta.
Ɗagata yayi yana juyi da ita a tsakar falon, yana cewa "Smile mana"
Ta rirriƙe shi ta ce "Zan faɗi fa"
A haka ya fito da ita, sai da suka kusa zuwa harabar gidan, sannan ya sauketa ya riƙe hannunta, zuwa mota.
Da kansa yake tuƙin, ya saka hannuna ya riƙe hannunta ɗaya, suna tafe yana mata hira, har ya samu ta ɗan sake daga fushin da take yi.
"Yauwa Daddy ya jikin Khalil kuwa?"
"Khalil ya warke, ya koma aikinsa ma"
Ta ɗan kalleshi ta ce "To ya batun Auren nasa?"
Shima kallonta ya ɗan yi ya ce"Yana nan, mamansa zata yi masa aure da, idan suka daw daga umara zan je in gana da mahaifin yarinyar"
"Wai dama ana yiwa namiji Auren dole ne? Auren nan fa zai iya shafar rayuwarsa gaba ɗaya, tayaya mutum zai rayuwar aure da wanda baya so, ita kanta wadda za a aura masan za a saka rayuwarta a Matsala".
"Ki bari idan muka koma gida, sai ki gaya wa Zeena tun da ita ce mamansa ita ta yanke hukuncin"
Gyara zamanta tayi ta ce "Da ita matar taka, da Khalil ɗin duk a ƙarƙashin ikon ka suke, dan haka kai yakamta ka tsaya ka yiwa kowa adalci ya samu abin da yake so. Wai shikenan a rayuwar anan talaka abin gudu ne? Haba Daddy".
"Naji, yanzu dai ki bar wannan maganar muyi wani lokacin, ki bari muje mu gama abin da ya fito da mu"
Ta ce "Ok, shikenan". Ya cigaba da tuƙinsa.
Yusra tana kwance tana waya, tana ta dariya saboda yadda Abdul ke ta koɗa yadda Cake ɗin nan da Abinci yayi daɗi, da yadda abokansa suka yi ta santi suma.
"Kai Yaya Abdul, ka daina zigani, kaina zai fashe fa"
"Ba ziga bace ƙanwata, ai ke ƙarshe wurin iya girki, mijinki ya huta"
"Kaima ƙarshe ne wurin kirki, ko Abincin bai yi daɗi ba ma dai, gashi ka ɓoye mini kana ta santi"
"Kar ji da wai, abinci yayi fiye da tunaninki, ina ga zan biya in yi joining classes ɗinki, naga kina tallan su a IG, zan joining ina son in ƙware a iya girki kan in yi aure, in dinga taya matata aiki"
Yusra ta ce "Matarka ta huta Yayana ga ka da sauƙin kai, ga barkwanci, ai kai naka class ɗin special za ayi maka"
"To shikenan, zaki fixing mini date in zo a koya mini, sai dai ɗalibin naki baya ja sosai, sai kin yi dagaske sai kin haɗa sa haƙuri. Wataƙila ma sai kin haɗa da bulala tukuna"
Garin dariya sai da ta tashi zaune ta ce "'yar Ƙarama da ni, a ga na saka ƙato a gaba da bulala, abin ai ba kanta"
Yayi murmushi ya ce "To ai malama da ɗalibi ne, duk hukuncin da ta yanke daidai ne"
"Yayana kenan, Allah ya kawo bikinka, ni zan sponsoring duk Abincin da za aci"
Yana zaune a kan gadonsa, ya ɗan yi shiru yana tunani.
"Hello Yaya Abdul, kana jina?"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ina jinki Ƙanwata"
"Shikenan sai anjima, kar in takura maka"
Abdul ya ce "No, baki takura mini ba, ina jin daɗin hirar taki ai, me zaki fara koya mini a girkin?"
"Dafa shayi" ta faɗa tana dariya.
Shima dariyar yayi ya ce "Dafa shayi ƙanwata, ai ko da muna school na iya dafa shayi, kar a kaini playgroup a makarantar taki, a ƙalla zan kai primary 2 a iya girki ai"
Sun daɗe suna waya, barkwancin Abdul ba ƙaramin burgeta yake ba, yayin da shi kuma girmamawarta da karamcinta yake burgeshi.
Alhaji Ahmad kuwa da Amina, wurin cin abinci suka fara zuwa, suka ci, sannan ya kaita wurin shan ice cream, ya zaga da ita wurin liluka, ta dinga hawa tana nishaɗi, taji daɗin fitar sosai, gaba ɗaya ta manta da damuwowin da take ciki. Shi kuma ya dinga kallonta yana nishadi shima, yaji daɗin yadda ta sake, harta ke ta fara'a tana kalle kalle da wasanninta, sai da ya fuskanci ta gaji dan kanta, sannan ya ɗauke ta zuwa wurin sayar da kaya.
A cikin botques ɗin ya dinga zagayawa da ita, ya ce ta ɗauki duk abin da take so, amma yaga kamar tana tsoro. Ya dubeta ya ce "Look, ki zage ki zaɓi duk abin da kike so, waɗan da zaki dinga kwaliya da su. Sanan akwai wurin atamfofi ma sai ki zaɓa in bayar a ɗinka miki, ki dinga mini Kwalliya, ta safe daban ta yamma daban ta other room daban".
"Kai ka san shi, shi other room ɗin"
"Eh dama ni na san shi mana, kema kin san shi ai" gaba tayi ta bar shi a baya, ya biyota shima ya sai abubuwan da yake buƙata sanan suka wuce gida.
Wannan yawon da suka yi, duk ta gaji, ana yin sallar isha'i, ta nemi wuri ta kwanta.
Gaba ɗaya Hajara ba ta gane Amina ba ƙaramin rana take da shi a gidan nan ba, sai da tayi tafiyar nan, aiki kamar zai kasheta san bata da hutu, tayi aikin gida tayi na Hajiya Zainab, sannan tayi na Fadila kuma abin takaicin ma idan tayi ba sannu ko san barka, sai wulaƙanci da cin zarafi da uwar kyara kamar wadda suka sayo baiwa.
Baba Hassan kuwa yana ta dako da lissafin ranar dawowar Amina, ya samu kiran wayar Alhaji Ahmad, jiki na rawa Baba Hassan ya ɗaga wayar yayi sallama tare da risunawa yana gayar da Alhaji Ahmad, Kamar yana gabansa.
"Malam Hassan, dama nace game da batun Amina ne"
Baba ya ƙara nustuwa ya ce "To meyafaru da ita?"
"Eh, ba wani abu bane ba, nayi magana da malamansu ne, basu gama abin da suke yi ba, dan haka akwai yiwuwar su ƙara lokaci kan su dawo"
Jikin Baba ya ɗan yi sanyi, amma ya maze ya ce "To shikenan, babu laifi, amma bana samunta a waya, sun gaya maka tana dai lafiya ko?"
Daddy ya ce "Tana lafiya lau, sun haɗani mun yi magana har wurin taron nasu naje, wayarce ta samu matsala".
Baba ya ce "To babu laifi, Allah ya dawo da su lafiya".
Daddy ya amsa da Amin.
Washegari, Kamar yadda da Daddy ya faɗa, ba tayi zaton da gaske bane ba, da daddy yake gaya mata ta shirya da wuri, tara da rabi jirginsu na Lagos zai tashi, ta ɗauka da wasa yake mata, ba ta yi zaton tafiya Lagos ɗin nan da gaske yake ba, dan haka ta shantake ta na baccinta.
A lokacin da ya gama shirinsa ƙarfe tara yaje ɗakinta, tana dunƙule a bargo, tana bacci.
"Meenali, mu da zamu tafi 10 amma kina nan kina bacci?" Ya saka hannu ya janye bargon, ta buɗe idonta a hankali.
Haushi ya kama shi, ya ɗagata zaune ya dubeta ya ce "Ban gaya miki zamuyi tafiya ba?"
Ta ɗan mruje idanunta ta ce "Nifa na zata da wasa kake mini"
"Nine nake miki wasan? Oya tashi ki saka kaya"
"Daddy ban fa yi wanka ba".
"Idan mun je can kya yi" haka ya azalzaleta, ta shirya ba ta koyi wanka ba, ya tattara mata sauran kayanta a Akwatinta suka fito, Joseph ya ɗauke su zuwa airport.
Duk da Amina bata taɓa hawa jirgi ba, amma ta kasa farinciki a lokacin da ya zamana wannan ne karonta na farko da ta hau jirgi, saboda tarin damuwar da take ciki. Shi kansa Daddy ya lura da yadda gaba ɗaya jikinta yake a sanyaye, amma bai matsa sai ya tanka mata ba, saboda karata dame shi da rigima, dan da alama ƙiris take jira.
'Meenalina, nan gaba zaki gane gata nake miki, a duk wannan abun da nake yi' yayi maganar a cikin ransa.
Kasa jurewa ya yai, ya ce "Meenalina ya ne?" Ta girgiza masa kai alamar bakomai.
Ya matso da ita jikinsa, ya riƙo hannunsa a nata, yana matsa yatsun hannunta a hankali, tayi lamo a kan kafaɗarsa ba tare da wani ya tankawa wani ba.
Su kuwa malamansu da sauran ɗaliban da suka zo tare, tuni suka shirya a ranar suka nufo Kano, Amina tana ta tunani a ranta, da tuni har da ita amma an mata fin ƙarfi babu yadda ta iya.
Bata taɓa zaton Daddy babban mutum ne haka ba, sai da suka sauka a Lagos, yadda ake girmamashi, ana risuna masa abin har mamaki ya bata, ashe normal yake rayuwarsa a Kano, kamar ba shi da wata damuwa.
Ko a garin Abuja ba taga ana masa haka ba sai da yazo Lagos.
Aka zo aka ɗauke su daga airport zuwa residents ɗinsa na Lagos, wani irin gida ne na alfarma, kai baka ce za a mutu ba.
A wani irin katafaren bedroom suka yi birki, in da suka tarar an ajiye musu kayansu da suka zo da su.
Daddy ya nemi wuri ya zauna a gefen gado, yana cire neck tie ɗinsa.
Ƙarshen gadon ta samu ta zauna ita ma, sannan ta ce "Ni ina nawa ɗakin, a ina zan zauna?"
"A nan babu wannan, we are sharing the same bedroom, the same bed and pillow together"
Cikin rashin fahimta ta ce "Saboda me? Naga kamar gidan da ɗakuna ai, meyasa zamu zauna a bedroom ɗaya"
"Saboda gidana ne, kuma dokata ce haka nake son ayi"
Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Ai dama bance gidana ne ba, amma ni gaskiya ba zan zauna ɗaki ɗaya da kai ba"
Ya miƙe tsaye ya ce "Kinga kenan a maimakon kwanakin da zaki yi tare da ni, ki cigaba da gardama da taurin kai, su zama watanni".
Jan bakinta tayi tai shiru.
"Idan kin huta ga toilet nan, ki shiga kiyi wankan, a cikin wardrobe ɗin nan akwai towel"
A ɗan shagwaɓe ta ce "Ai na fa sa yin wankan"
"A haka zaki zauna?"
"Eh, idan ka fita nayi"
Ya ce "As you wish"
Ya zagaya bayanta, ya kwanta a kan makeken gadon, yana lumshe ido.
A ranta tayi ta tunanin ko iya adadin yaushe zata kwashe a gidan nan oho.
Fadila suna ta shirin tafiya umara, amma gaba ɗaya hankalinta na kan yadda zata samo Yazid.
Tana falo tana kallo, Hajara na kaiwa tana komowa tana gyarawa, Hajiya Zainab na gefenta da system a kan cinyarta.
"Fadila kinga yaron nan ko?"
Ko ba ayi wa Fadila dogon bayani ba, ta san maganar ba zata wuce a kan Khalil ba.
"Mummy what again?"
"Muna ta shirye shirye zamu yi tafiyar nan, amma dan wulaƙanci ko ya zo garin nan, gaba ɗaya yama ɗauke ƙafarsa daga zuwa"
"Amma ai kamar bai san zamu yi tafiya ba fa"
"Au baki gaya masa ba?"
Fadila ta ce "Ina nake ganinsa online balle na gaya masa, ba fa kulani yake yi ba"
Ta ɗan jinjina kai ta ce "Anya Fadila yarinyar nan ba Asiri suka yiwa Khalil ba? Duk nacin Khalil da gida, amma shi ne ya shafe wannan lokaci bai ko waiwayo mu ba, ya nesanta kansa da mu?"
"I don't know"
Hajiya Zainab ta ɗauki wayarta da ke gefenta, ta nemo lambar Khalil.
Sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga tare da yin sallama.
"Anya Khalil kana son ka gama da duniya lafiya kuwa?" Gaban Khalil ya faɗi ya ce "Subhanallah, Mummy me ya kawo wannan maganar kuma?"
"Ban sani ba, shikenan ka daina zuwa gida kenan? Ga tafiya za muyi umara, babu ma alamar zaka zo gidan nan balle muyi sallama ko Khalil, duk saboda masu awara sun yi tsafi sun baka ka ci"
Khalil ya fesar da wata iska, ya ce "Mummy, dan Allah kiyi haƙuri, ban san zaku yi tafiya ba wallahi, rashin lafiya nayi na sha wahala, sai da Daddy ya zo ya kaini Asibiti"
Ɗan shiru tayi sannan ta ce "Ban gane ya zo ya kai ka Asibiti ba, shi da yake Lagos kana Abuja, ya aka yi ya je ya kai ka Asibiti?"
"Mun yi waya da shi ne, ya ce mini ya shigo Abuja, shi ne yaje in da nake, sai da aka yi tayi mini ƙarin ruwa da allurai"
"Eh lallai, har ka gayawa mahaifinka baka da lafiya, amma ni ban sani ba, duk dan saboda masu awara ko?"
Fadila ta fara tausayin ɗan uwanta, Mummy akwai nanata zance, abu baya wucewa a wurinta, ta saka Khalil a gaba da zancen nan.
Nan ma ta ƙare masa ta tas ta kashe wayarta.
Tun Amina na zaman ɗari ɗari da Alhaji Ahmad, a hankali har ta saki jiki da shi, ko girki tayi ba zata ci ba sai ya dawo, gashi tana ta kula da Abincinsa, cikin ikon Allah sugansa ya sauka zuwa normal range, ga exercise da yake yi a gida, gaba ɗaya Amina ta mayar da shi kamar dai-dai da shekarunta, har tseren keke suke yi tare a gidan. Babu yadda za ayi ka zo gidan kace ba matarsa bace ba.
Shima yana ƙoƙarin faranta mata, yana kaita wurare daban daban na buɗe ido da sanya nishaɗi, idan yana gida tare suke gabatar da wasu ayyukan.
Tana kwance a kan gado tana cin cheese, duk ta ɓata gadon da cheese, ya bata wayarsa tana game, shi kuma yana gefe ya saka system har biyu a gaba, ya dannan wannan ya koma ya danna waccan, ga ruwa da lemo mai sanyi a kusa da shi yana ta aikinsa.
"Daddy"
"Na'am" ya amsa mata.
"Wai dan Allah aikin me kake yi ne? Ranar kace mini sayar da kuɗi ka ke yi, Yanzu kullum kana ce mini kaje wurin aiki, amma ban san aikin da kake yi ba"
Ya ɗan waiwayo ya kalleta yana murmushi ya ce "Ai nace miki sayar da kuɗi nake"
"Ai ba a sayar da kuɗi"
"A na yi mana" ya bata amsa.
Ɗan matsawa tayi, tana leƙa computer da ke gabansa, ɗaya calculation yake yi da ita, ɗaya kuma kamar zane yake yi, ba ta gama fahimta ba.
"To wai wannan ɗin meye kake yi?"
"Meenal, sai ɓatar da ni da kike yi fa, ni da na sani ma ɗakin karatuna na tafi"
Ta ce "Au nan ma kana da ɗakin karatu, aikuwa da sai na bika"
"Ki zauna ki cigaba da game ɗinki"
Ta noƙe kafaɗa ta ce "Ni na gaji da game ɗin, i just wanna disturb you"
"Ina aikin zaki disturbing ɗina?"
"Eh, ni ka ajiye aikin ka kulani" tayi maganar a shagwaɓe tana jan hancinsa.
Murmushi ya cigaba da yi, yana aikinsa.
Ta koma ɗaukar cheese tana saka masa a baki, duk cikin son ta addaba masa ta hana shi aikin da yake yi.
Wayarsa ce take ringing a jikinta, ta duba ta ga hayatee da emojis na luv, ta san Hajiya Zainab ce, amma ta basar ta ajiye wayar.
"Miƙo mini wayar mana"
Ta saka idonta a nasa ta ce "Na hana"
"Meyasa?"
"Tun ɗazu nake maka Magana ka ƙi kulani, amma tana bugo waya shi ne zaka ɗauka, ban bayarwa" tayi maganar tana haɗe rai.
"Bani wayata, bana son ɓacin ran matata"
Kicin kicin tayi da rai, ta hana shi wayar.
"Allah ya shiryi cartoon da rigima da tsagwaron kishi, idan muka koma gida ya zaki yi ne?"
Tayi shiru tana kallonsa ta gefen ido.
Wayar tayi ringing ta gaji ta katse.
Hamma ta fara yi ta kalleshi ta ce "Tun da ba zaka gaya mini aikin da kake ba, ka zo ka rarrasheni bacci nake ji"
Girgiza kai kawai yayi, ya kashe system ɗin, aikin da yake yi ɗin ne a yanzu bata so, shine take ta ƙaƙalo abubuwa.
Ya nemi wuri ya kwanta, ita kuma ta kwanta a jikinsa, ya rufe su da bargo, daga nan ya fara gaya mata aikin da yake yi.
"Akwai wani abokin mahaifina, babban ɗan siyasa ne, a zamanin wancan shugaban ƙasan na hannun daman shugaban ƙasar ne, dan kusan shuhaban ƙasar yaronsa ne. Bayan an yi Election yaron nasa ya ci zaɓe, ni kuma a lokacin ina da master's a kan Civil engeenering, nayi aiki da kamfanoni daban daban na Chinese da 'yan Turkiyya. Abokin mahaifina ya sanya aka yi mini ministern ayyuka. Na fuskanci ƙalubale daban daban, kasancewar ana ganin akwai waɗanda suka fini cancanta, kuma ni ba ɗan siyasa