Showing 51001 words to 54000 words out of 296192 words
me kika karanta a kan course ɗin".
Miƙewa tsaye tayi ta ce "Dan Allah malam ni ka ƙyaleni, sai kace dole, ka fita daga harkata kar ka sake zuwa in da nake, bana buƙatar taimakon naka, ni ai bance maka ina son ka koya mini abu ba".
Shima ya miƙe tsaye ya ce "Am sorry, Allah ya baki haƙuri, na yi miki shishshigi, ba zan sake ba insha Allah"
Jakarta ta ɗauka tai gaba, tana cigaba da yadda jikinta ke tsuma kamar wadda tai artabu da aljan.
Cikin ikon Allah su Khalil suka gano in da aka kai Hafsa, tun safen nan ba ta ci komai ba, sai kuka da take yi, kuma taƙi magana, fuskarta duk tayi jawur saboda kuka, an rufeta a ceil.
Su Khalil basu tarar da DPO division ɗin ba, sai yaransa, bayan sun gaisa Aminu ya sanar da su cewar sune wanda suka zo wurin Hafsa.
Ɗansandan ha kallesu ya ce "To mintuna uku kacal zaku yi, dan kotu zamu kaita".
"Wai a kan ta aikata wane laifin?" Khalil ya yi maganar a hargitse.
Abdul yayi saurin dakatar da Khalil ya ce "To Yallaɓai, a bari mu gantan".
Aka fito da Hafsa, idanunta jawur, tana rarraba ido taga Mama, kawai taga Khalil da Abdul, aikuwa tayi sak tana kallonsu, ta ƙaraso gaban teburin ta tsaya tana sunkuyar da kai.
"Hafsat, me kika yi aka kawo ki nan?" Khalil ya yi maganar yana kallonta cikin kulawa.
Fashewa da kuka Hafsat tayi, ta kasa magana.
"Ai na zata faɗa ba, tayi attempting illata mutum, kina mace amma kina abin 'yan daba, ta ƙonawa mutum ƙafa da mai, kuma ta rarumo makami tana nema ta sokawa mutum" cewar wani ɗan sanda mai jajayen idanuwa.
Tsaki Khalil yayi, ya ce "Wanan dalilin ne ya sanya aka kawota nan, wace irin magana ce wannan? Ta yaya zata ɗau makami tace zata illata wani, Yarinyar da ko kuzarin kirki ba ta da shi?"
"Kaga shi mugu fa ba a ido ake ganinsa ba, wanda ya kawo ƙararta ya ce bai yadda da sulhu ba, a kai su kotu a bi masa hakkinsa"
Khalil ya ce "Shi dabban ina ne da zai kai mace kotu ya tsaya a kotu ya ce wai ta ɗau makami zata masa illa? Wace doka ce ma ta bada damar a riƙe mutum tsawon wannan lokaci family ɗinsa ma ba su sani ba, a bani belin ta".
DPO ne ya shigo yana zazzare ido "Yaya, Yaya, meke faruwa nake jin hayaniya haka?"
"Welcome sir, wannan ne ya zo zai mana tsageranci, wai sai an bashi belin wannan 'yar dabar".
"Wallahi ka kuma ce mata 'yar daba, saina ɓata maka rai".
"Kai nutsu, nan station ne, kar kai mana fitsara" Cewar DPO yana zarewa Khalil ido.
Abdul ya ce "Dan Allah Khalil abi komai a sannu".
Khalil ya ce "Wallahi ba zan bi a sannu ba, ya za'a kama yarinya ba bisa ƙa'ida ba, kuma aci zarafinta, sun ajiyeta daga ita sai su a wuri ko danginta basu san in da take ba?"
DPO ya ce "Au rashin kunya zaka mini, kai ku mayar da ita ceil, ba za a bada belin nata ba, sai ta ɗau nauyin maganin wanda ta illata".
Khalil ya ce "Bari in ɓullo muku in da ya dace" kawai ya fita daga cikin station ɗin, kuka Hafsa ta saka, da taga Khalil ya juya ya fita. Abdul ya bi bayansa da sauri.
Mintuna bakwai, DPO ya fito a gigice yana faɗin "Suna ina? Wannan wane irin ɗan tijara ne, maimakon ya tsaya a sasanta sai ya kunno mini wuta daga saman ƙololuwa? Ku kira mini shi mana".
Khalil ne ya shigo ya ce "To zaku bani ita ko kuwa?".
"Za a baka, ai ban sai kai waye ba, ashe ɗan gidan controller Ahmad Dutse ne".
Khalil Ya ce "Wannan matsalarku ce, a bani ita kawai".
DPO ya ce "Ai irin haka bayani ake yi, ba bankaɗo mini wita daga sama ba, wadda zata ƙone 'yar kukeear tawa ba, a fito da ita".
Aka fito da Hafsa, DPO ya ce "Amma zaku dawo gobe in Allah ya kaimu, za'a kashe case ɗin da wanda ya shigar da ƙarar".
Aka bawa Khalil wata takarda ya yi rubuce-rubuce, Sannan aka bawa Hafsa damar bin Khalil.
Suna fitowa harabar wurin Khalil ya ce "Babyna ba suyi miki komai ba dai ko?".
Ta jinjinawa Khalil kai. "Ki gaya mini ko sun miki wani abun?"
Ta kuma girgiza masa kai. "To Allah, maza muje mota, Mama na can gida bata san in da ki ke ba".
Ba musu ta bi Khalil, ya buɗe mata bayan motar ta shiga, Khalil ya shiga ɗaya gefen ya zauna, Abdul kuma ya ja motar suka tafi.
A ƙofar gida suka tarar da Mama, tana ta kuka, maƙota sun kewayeta suna ta bata haƙuri suna rarrashinta, amma sai gursheƙen kuka take yi.
Da gudu Hafsa ta fito daga motar ta rungume Mama tana kuka, Khalil da Abdul suka ƙaraso, suka gaida Mama sannan Abdul ya ce bari suje suyi sallar magariba, sai su dawo dan an fara kiran salla.
Maƙota suka dinga shiga yiwa Mutane su Mama jaje, wasu dama zuwa ganin ƙwaƙwaf suke yi.
Bayan sun dawo daga salla, suka koma gidan su Hafsa, Mama tayi mus iso zuwa cikin gidan, ta shimfiɗa musu sallaya suka zauna, yayin da ita da Hafsa suke zaune a kan tabarma, Hafsa tana kusa sa Mama kamar za a ƙwace mata ita. Khalil kuwa sai mamakin ƙanƙantar gidansu Hafsa, kai da gani ba sai an gaya maka ba suna fama da rayuwa, wani irin tausayin Hafsan ya ƙara kama shi.
Suka kuma gaisawa, Mama ta ce "Sai dai ban gane ku ba, ko jami'ansa tsaro ne na farin kaya?".
Abdul ya ce "A'a Mama, ni sunana Abdul, wannan kuma Khalil" nan ya kwashe yadda suka gano Hafsa har suka dawo da ita gida.
Mama ta ce "Allah sarki, yau gani ga Khalil muna gaisawa a waya, ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya jiƙan magabata, idan suna raye Allah ya ja da ransu, yadda kuka faranta mini ubangiji Allah ya faranta muku"
Abdul ya ce "Ameen Mama, bakomai ai yiwa kai ne"
Mama ta mayar da dubanta ga Hafsa ta ce "Hafsa, meya haɗaki faɗa da namiji a wurin sana'arki har ki ɗau makami?".
"Mama wai kin yadda zan ɗau makami in illata wani?" Tayi maganar a raunane.
"To Hafsa meya haɗaki faɗa da wani, har a kai ki wurin hukuma?".
"Mama ni ban nunawa kowa makami ba, Ƙona shi nayi da mai a ƙafa".
Mama ta buɗe baki ta ce "Hafsa wa kika ƙona da Mai?" Cikin kuka ta ce "Mama Najib ne fa, yana zuwa wurin sana'ata ya ci mini mutunci, na kasa jurewa na ɗau wannan matakin"
"Amma Hafsa kin taɓa gaya mini? Sai ki yanke wannan hukuncin haka?"
Khalil ya ce "Mama ayi haƙuri, kinga kamar haryanzu a tsorace take"
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, na gode muku sosai Allah ya jiɓanci lamuranku"
Abdul ya ce "Ameen Mama, gobe in Allah ya kaimu zamu zo muje station ɗin, a rufe case ɗin gaba ɗaya".
"To Allah Ubangiji ya kai mu na gode sosai".
Har ƙofar gida Mama ta rako su Abdul, tana ta cigaba da sa musu albarka. Khalil ya buɗe motar ya ɗauko wata ƙatuwar leda ya ce "Ga Abincinta da muka sai mata a hanya ba ta samu taci ba" da haka suka yi sallama su Abdul suka tafi gida.
Suna tafe Khalil na sake jinjina yanayin rayuwa da su Hafsa ke fama da shi.
Hall ɗin exam ya cika ya batse, ɗalibai sun duƙufa suna ta rubuta abin da suka sani. Fadila kuwa abin da ta sani bai kai ya kawo ba, ta ɗaga kai taga yadda Yazeed idaan ya samu dama yake taimakawa na kusa da shi, ga lokaci ya ja, tuni wasu ɗaliban sun fara bayar da tasu jarrabawar suna fita, amma ita tana zaune bata rubuta abin kirki ba, kanta ya ɗau zafi sai gumi take ta goshi.
Cikin sa'a ɗalibai suka ragu daga hall ɗin, invigilator ya mayar da Fadila kusa da Yazeed, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Fadila ba, tana sa ran Yazeed ya taimaka mata. Sai dai taga Yazeed ya yi mursisi ko kallon in da take yaƙi yi. Wankin hula na neman kai Fadila dare, lokaci na ta tafiya, a kowane lokaci za a iya karɓewa, saboda lokaci ya kusa cika.
Bata ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da taga Yazeed yana tattara takardunsa, zai tashi yayi submitting.
TOFA, ZATA BAR YAZEED YYO SUBMITTING, KO KUMA ZATA SAUKE IZZA TA NEMI TAIMAKO?
Domin gyara, sharhi ko shawara
08081012143READ THE CHAPTER 15 AT AREWABOOKS
https://arewabooks.com/chapter?id=6386388f094c9b1220e3fdb9.
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143
P 15
Ganin da gaske Yazeed yana shirin tashi ya tafi ba tare da ta kammala ba, ya sanya a hankali fadila ta ce "Ban gama ba fa"
Wani miskilin murmushi ya yi, ba tare da ya bari Fadila ta gani ba, ya ɗan tsuke fuska ya kalleta ya ce "Magana kike?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Ban ji me kika ce ba?"
"Ban gama ba?" Ta furta a hankali.
"Kina buƙatar taimakona ne?" Ta jinjina kai alamar eh.
Yazeed ya gyara zamansa ya ce "Me kike buƙata?"
Nan ta gaya masa wanda ba tayi ba a tambayoyin. Ya ajiye mata takardarsa ya ce "Gashi nan kwafi".
"Ka karanto mini, bana iya ganowa sosai".
Murmushi Yazeed ya yi, yana karanta mata a hankali.
Invigilator ne ya fita, hakan ya bawa sauran ɗaliban ajin, damar cigaba da taimakawa junansu, tuni Fadila ta manta ta matsa kusa da Yazeed tana wanke takardarsa, jin jikinta ya fara rawa ne ya sanya ta lura tana kusa da shi, dan haka da sauri ta ja da baya, tana sauke numfashi. Kallonta yayi yai murmushi ya ce "Kin gama ne kika matsa?"
"Ban gama ba" ta faɗa a raunane.
"To ƙarasa mana, zan tashi in kai fa".
"To ka karanto mini mana"
"Ki kwafa mana ni na gaji" ya faɗa yana jin daɗin yanayin.
A hankali ta kuma matsawa kaɗan ta cigaba da kwafa, amma tuni gumi ya fara yankomata, tana rubutu hannunta na rawa.
"Ki nutsu mana, lokaci ya kusa ƙurewa kuma sai rawar jiki ki ke, kin kasa rubutun" da ƙyar Fadila ta ƙarasa saboda gaba ɗaya bata iya tantance yanayin da take shiga idan tana kusa da shi, idan yana nesa da ita ne take iya tatala masa rashin mutunci son ranta, amma da sun samu kusanci sai ta rasa nutsuwarta, sai da ta gama sannan Yazeed yaje yayi submitting.
Ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jere, saboda yadda ta sha da ƙyar, bayan ta fito ta hango Yazeed a wurin motarta yana waya, da 'yar ƙaramar wayarsa, ya jingina da jikin motar dan haka ba halin ta buɗe motar.
Tsayawa tayi ya kammala wayar, tana ta tunani a zuciyarta, godiya zata yi masa ko kawai ta share shi? Ya juya harshe sai zuba larabci yake a waya tamkar bai taɓa jin hausa ba, abin ya ƙara bata mamaki, abubuwa da yawa suna bata Mamaki game da Yazeed.
Ya kammala wayar sannan ya waiwayo ya ce "Am sorry na tsayar da ke".
"Never mind" ta faɗa a sanyaye.
"Za muyi karatu ne ko yau ma tafiya za ayi?" Yayi Maganar yana tsareta da idanunsa.
"Ni yunwa nake ji, kuma na gaji sosai".
انت جميل ياحببتي
Ya faɗa yana lumshe idanunsa. Kallonsa ta yi dan bata gane me yake nufi ba.
"Yunwa ki ke ji, kuma ke kin gaji, kar ki nuna kin san Yazeed gobe in Allah y kaimu a exam hall".
"Eh ai nima ba daƙiƙiya ba ce, yau ɗin ma dai kawai na kakare ne" tai maganar cikin tsiwa tana masa kallon up and down.
"Ni a ina nace miki daƙiƙiya ukhti? kalen faɗa ne dai kike yi, kuma ba zaki yi dani ba, aje gida a ci Abinci lafiya". Ɗan taɓe baki tayi, ta hau motarta ta kunna ta ja ta bar wurin.
Ƙarfe goma na safe, Su Khalil suka je suka ɗauko su Mama, Khalil sai kallon Hafsa yake yi, amma tun da ta gaishe shi bata sake ce masa uffan ba, sai hira da suke da Mama jefi jefi.
Goma da rabi suna station ɗin da aka karɓo Hafsa, suka isa wurin, DPO sai haba haba yake da su, har da yiwa Hafsa wasa, wai "Hajiya Hafsa babu gaisuwa ne?" Wata uwar harara ta watsa masa ta kauda kanta.
Suna nan zaune sai ga Najeeb ya ƙaraso da shi da wasu matasa guda biyu.
Mama na ganinsa ta haɗe rai, taƙi ko kallon in da yake, ya shigo yana ɗingisa ƙafa. Shima wani banzan kallo ya yiwa su Hafsan sannan ya ƙarasa ciki ya zauna, suka gaisa da DPO ya maida idonsa kan Khalil da Abdul dake wurin, yana mamakin su kuma wannan daga ina?.
DPO ya ce "Yauwa Najeeb, ga wanda suka zo suka yi belin Hafsat a jiya, dama na gayyace ku ne gaba ɗaya a zo a zauna a teburin sulhu, tun da dai shi sulhu alkhairi ne".
"Kamar yaya aka bada ita beli, haba DPO haka muka yi da kai? Yarinyar da ta nemi ta halakani".
"Dama kai ne kasa aka kamata? Har kake iƙrarin dan me aka bada belinta?, kai ko kunya baka ji, wannan ce zata halaka ka garjejen ƙato da kai?" Khalil yayi Maganar yana zaro ido.
Najib ya ce "Kai kuma awa? Me ya kawo ka cikin wannan case ɗin, abu ne na family issues 'yar uwata ce ina ruwanka?".
"Wallahi ni ba ɗan uwan bane, babu wata alaƙa tsakani da shi, dan Allah Yallaɓai ka mini tsakani da shi kar ya sake zuwa in da nake, ba ruwanshi dani, dan Allah" Hafsa tayi maganar tana kuka.
DPO ya ce "Wai dama ka santa ne?" Ya tambayi Najib.
"Yallaɓai 'yar uwata ce, wani misunderstanding ne kawai ya gifta ake samun wannan akasin"
Duk da sanyin hali irin na Mama, amma nan da nan fuskarta ta sauya, ta ce "Kar ka ƙara danganta kanka da 'yata, baku da wata alaƙa da mu".
Najib ya ce "Ai dama ba dake na ce ba, bani da wata alaƙa da ke, amma ina da ita da Hafsa".
"Shut up malam" Khalil yayi masa tsawa.
"Wallahi kai mana rashin hankali a nan, sai na saka an samaka sarƙa, mahaukaci kawai".
DPO ya ce "Dan Allah ya isa haka, wannan hayaniyar duk ba mafita bace. Ke Hafsa meye haɗinki da shi, da har kika ƙona shi?".
Hafsa ta share hawaye ta ce "Karo kusan uku kenan, yana zuwa wurin sana'ata yana ci mini mutunci yana zagina a gaban mutane, ni kuma na gaji na rasa yadda zan yi kawai na zuba masa mai a ƙafa, kuma ina da shedu a gaban mutane yake zuwa kaina yana ci mini mutunci".
"Amma me yasa baki yi wannan bayanin jiya ba, da muka tambayeki?".
Khalil ya ce "Amma duk ba kuyi wannan binciken ba, kuke iƙrarin zaku kaisu kotu, anya makuwa ka san aikinka?"
DPO ya ce "Wannan abu dai duk kuskure ne an riga anyi shi, saboda shi abin da ya zo ya gaya mana daban, ita kuma taƙi Magana, amma insha Allah yanzu za a rufe case komai ya wuce".
"Eh, a rufe case amma ba komai zai wuce ba, idan aka rufe wannan case ɗin ni kuma zan shigar da ƙararsa a kan cin mutuncin da yayi mata, kuma Wallahi CID zan kai shi, ba dai abun wa ka sani wa ya sanka bane? Zan masa abinda ya yi".
Abokan Najib da suka rako shi wanda ba suyi magana ba tunda suka zo, ɗaya daga cikin su ya ce "Dan Allah dai kayi haƙuri komai ya wuce, kuskure ne an yi, ayi haƙuri".
"Dalla rufe mini baki, waye ya sa da kaiz' ba dai kuna ƙaryar rashin mutunci ba, kawai ya sa aka kama yarinya aka rufe, bayan laifinsa ne, ba zaku bar nan wurin ba zan waya azo a tafi da shi, koma a haɗa da ku duka" yayi Maganar yana zaro wayarsa daga aljihu, aka dinga bawa Khalil haƙuri,ƙarshe sai da Mama ta saka baki ta ce "Bakomai Khalil, wannan taimakon da ka yi mana ma mun gode, bana son wani abu ya sake shiga tsakaninsa da 'ya ta, kawai ka sa a musu iyaka, kar ya kuma zuwa wurin da take".
Da ƙyar Khalil ya haƙura aka rufe case ɗin nan, dan sai da Abdallah shima ya saka baki, sannan aka rufe case ɗin, suka ɗau su Hafsa a mota suka tafi mayar da su gida.
Najib kuwa mamaki ya dinga yi, waye Khalil a ina su Hafsa suka samo wanda ya tsaya musu haka? A iya saninsa basu da kowa basu da Komai, amma ya akai Khalil ya shigo rayuwarsu, ya so ya kuma amfani da damrsa ya wulaƙanta Hafsa son ransa, daga ita har Mama, amma ya lura wannan Khalil ɗin yafi shi zafin kai da masu gidan rana, idan ya matsa shi ne zai kwana a ciki.
Khalil ya so yaji alaƙar dake tsakanin su Mama da Najib, amma ganin kamar basa son zancen ya sanya shi yin shiru.
Yau ma har gida suka kai su Hafsa, Mama nata musu godiya da sa albarka, Mama ta nufi gida, Hafsa ma ta biyo ta. Mama ta kalli Hafsa ta ce "Ke wace irin Yarinya ce mara lissafi? Har a miki wannan abin Arziƙi amma ba zaki tsaya ki sake masa godiya ba? Maza koma kije ki kuma yi masa godiya".
Cikin sanyin jiki ta koma inda su Khalil ke ƙoƙarin tafiya, taje ta tsaya ba tare da ta ce uffan ba. Khalil ya sauke glashin motar, ya kalleta ya ce "In zo ne?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya buɗe motar ya fito, ya tsaya a gabanta ya ce "Gani ranki ya daɗe".
Ta ɗan yi turus, Sannan ta ce "Dama, ce maka za yi Na gode sosai da taimakon da kayi mini, Allah ya saka da alkhairi".
Khalil ya yi murmushi ya ce "Meye abin godiya, dan mutum ya yiwa matarsa abin daya dace?" Da sauri ta ɗago ta waro masa manyan idanunta.
"Kin san wani abu Hafsat?" Ta girgiza kai.
"Ina kishinki da yawa, bana son zaman da kike a titin nan, dan Allah ni dai ki daina".
"Idan ban zauna a titi na yi sana'a ba, da me zamu rayu?".
"Ba zai gagara ba Hafsa, ni dai dan Allah ki daina, kuma very soon nake son ayi zancen aurenmu".
"Na gode sosai da taimakon da ka mini, amma ni ba zan aureka ba, ka ƙyaleni a yadda ka ganni kawai"
"Amma Hafsa saboda me?"
Ƙwalla ta taru a idanunta ta ce "Dan Allah kar kayi