Showing 105001 words to 108000 words out of 296192 words
da ta kasa ɓoyewa Mama, ta faɗa mata kai tsaye, abin ya girmama.
"Yanzu dan kawai kina 'yar talaka shi ne suka je suka yi miki Wannan cin mutuncin?"
Hafsa ta ɗaga mata kai tana kuka.
"Shikenan, share hawayenki, Allah ya kawo miki mafi alkhairi, ita kuma Allah ya ganar da ita, in dai Khalil ne ba shine autan maza ba ai"
Hafsa ta faɗa jikin mama tana kuka, Mama ta rungumeta sosai tana rarrashinta, ganin Hafsa bata ganinta ya sanya ta lunshe idanunta ita ma, hawaye suka shiga kwararo mata, ita ta matsa Hafsa a kan ta yarda da Khalil, sai da ta yadda da shi tayi nisa a son sa wannan matsalar ta kunno kai, Mama ta share hawayenta ba tare da Hafsa ta gani ba ta ce "Ga ruwan wanka can na dafa miki, na kammla girkin dare, idan an yi sallar magariba, sai kiyi wanka ki zo ki ci Abincin dare.
Hafsa jin Mama kawai take, amma Abincin nan ba ciyuwa zai yi ba a wurinta.
Khalil kuwa ya dinga jerawa Hafsa waya, amma ko ɗaya bata ɗauka ba, ta share wayar, ƙarshe ma ta saka wayar a silent, ta jefata bayan katifarta.
Daddy na zaune a kan kujera 3seater, Fadila na kusa dashi, tana ta 'yan ciye-ciyenta tana masa hira irin ta uba da ɗa. Amina kuma na ƙasa a zaune tana kallon tashar da suke kallo.
Fadila ta ce "Ke ɗan jeki ɗakina, ki ɗauko mini wata leda a kan madubina" Amina ta tsani ke ɗin da Fadila kan kirata da shi, ko ita ko Mummy, amma ba yadda ta iya, haka ta tashi, ta nufi ɗakin Fadilan. Ta je ta ɗauko ledar ta kawo, ta miƙawa Fadila, Daddy ya ɗan ƙure Amina da ido, yana mata murmushi.
Amina dai bata nuna ma ta san ita yake yiwa murmushin ba.
Fadila ta ɗauko turarukan da Yazid ya bata ta ce "Daddy, sansana wannan turaren kaji, da ƙamshi?"
Daddy ya ce "Wow, lailatul sahara, na so turaren nan sosai, ina kika samo shi?"
"Wani ɗan ajinmu ne Yazid ya bani, as a birthday gift, but you, you even forget about it, you don't even wish me" tayi maganar cikin shagwaɓa.
"Ohh my dear, ai naga birthday ɗin naki sai gobe in Allah ya kaimu zai cika, kuma ni banga kina mana organising komai ba".
Fadila ta ce "Yusra zata yi mini cake, then just chill with you tonight, mu ci Abinci tare snap pictures together that's all, ba zan haɗa hayaniya ba"
Ya ce "Hmm, alright Allah ya kaimu"
"Ameen Daddy, amma me zaka bani as my birthday gift?"
Ya ce "Mmmm, what do you want?"
"Kome ka bani yayi"
"To shikenan, Dubai or Umrah"
Fadila ta ɗan zaro ido ta ce "Daddy Umrah, ina son komawa Saudiyya"
"Fine, amma ke da Mummyn ki zaku je, idan kun yi hutun makaranta"
"Alhamdilillah, Daddy na gode sosai, Much Love my Hero" tayi maganar tana rungume Daddy tana murmushi.
Amina da ke gefe, ta kwaɓe baki, ganin yadda Fadila ke ta nan nan da babanta, tana zuba taɓara, amma ta iya zagewa ta wulaƙanta wani, ba tare da tunanin yadda take jin son babanta a ranta haka kowama yake ji ba.
"Daddy, ka san Mummy cewa tayi wai turaren nan wari suke yi kar in shafa"
Daddy ya ce "Aikuwa turaruka ne masu kyau"
Fadila ta nuna masa hannunta ta ce"Kalli, har abin hannu ya bani, da turaren nan, Daddy baka ga ƙoƙarinsa ba sai dai Yaizd bai iya turanci ba, kaga yadda yake larabci kamar balarabe"
"Dama ai haka lamarin ilimi yake, kuma turanci yare ne kawai"
Hajara ce ta leƙo falon, ta ga Daddy zaune shi da Fadila suna hira suna kallo, Amina kuma ta kame a ƙasa ita ma kallon take yi.
A ranta zuciyarta ta ce Lallai ma yarinyar nan, ina can ina aiki, kin zo kin zauna a cikin masu gida kina kallo
A fili ta ce "Amina, ko zaki zo ki yanka mini alayahhu muyi mu kammala girkin dare kan Hajiya ta dawo?"
Daddy ya ce "Kallo, take yi, kiyi aikin a hankali ba sai kin yi gaggawa ba, tun da ba yanzu za aci Abincin ba"
Da ɗan mamaki Fadila ta ce "But Daddy, she's also a maid, ai ba kallo ta zo yi ba"
"Yes i know, she's facing her SSCE, yakamata tayi passing, kuma abin da take kalla is educative, bana son yin asarar kuɗin makarantar da nake biya"
Jiki a saɓule, gwiwa a sace Hajara ta koma kitchen, tana masifa tare da mamakin yadda Amina ke abin da taga dama, da wasu abubuwa da ke faruwa, wanda ta kasa gane kan in da suka dosa.
Fadila ta tashi tsaye ta ce "Daddy, zanje in ɗan yi karatu, exams is around the corner"
"Ok Best of luck"
"Thank you" ta nufi ɗakinta.
Sai da ya tabattar Fadila ta bar falon, sannan ya ce "'yar Daddy" shiru Amina tayi ta cigaba da kallonta.
"Amina am talking to you fa" a hankali ta waiwayo ta kalleshi.
"Ya naga kin haɗe rai, any problem?"
"Nothing" ta faɗa a taƙaice.
"Oya kawo mini Apple, da ruwa" ta miƙe ta nufi kitchen, ta tarar Hajara ta cika tayi famm, tana aiki ita kaɗai.
Tana ganin Amina ta ce "Yauwa, ga alayahun nan, kk ɗauka ki yanka"
"Wai baki ji me Daddy ya ce ba? Kallo nake yi, kuma wallahi da nice ba zan takuraki sai kin yi aikin nan ba, duk ni zan abina, amma ke ba damar in ɗan huta sai ki sa mini ido, ke fa wuni kike a gida ni kuma ga makaranta ina zuwa haba.
"Amina rashin kunya zaki mini?".
"Ni ban miki rashin kunya ba, kece ba kya jan girmanki"
Daga haka Amina ta ƙarasa gaban fridge, ta buɗe ta ɗauko Apple, ta ɗora a kan plate da wuƙa ta bar kitchen ɗin, ta bar Hajara da mamakin da tambayoyin da babu mai bata amsarsu.
Ta kawo wa Daddy ta ajiye masa.
"Yanka mini mana 'yar Daddy"
Amina ta zauna ta yanka masa ta miƙa masa, yasa hannu ya karɓa yana ci.
Can Amina ta ce "Daddy, ya sugan naka ya sauka kuwa?".
"Ban duba ba, naji daɗin jikina Yanzu sosai Alhamdilillah"
"To Allah ya raƙa lafiya"
"Ameen 'yar Daddy, anjima ki hau online muyi hira"
Ta ɗan kalleshi ta ce "Karatun fa?"
"Wai ke ba kya hutawa karatun nan ne? Ki dinga hutawa ranki"
"Ai ba iya karatun boko nake ba, bana son haddata ta zube dole sai ina tilawa"
Cike da girmamawa ya kalli Amina ya ce "Masha Allah, 'yar Daddy, kina nufin kina haddar Alqura'ani?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Kai, dole in san abin yi, ban goyi bayan haddar nan ta zube ba, kin haddace duka ne?"
"A'a, ban haddace duka ba"
Daddy ya ce "Matso nan kusa da ni muyi magana"
Amina ta matsa kusa da ƙafafuwan Daddy, ya ajiye ɗan ƙaramin plate ɗin da ta zuba masa Apple a kai, a kusa da ita, sannan ya ce "Na daɗe banga mutum mai ƙwazo kamarki ba, zanga abin da ya dace, yakamata in samo wanda zai cigaba da koya miki a gida ina biyansa"
Amina ta washe baki ta ce "Ai ba sai ka kirawo wani ba, direbanka Zakiru malami ne, ka ce ya dinga koya mini, sai ka dinga biyansa shi"
Daddy yayi murmushi ya ce "To shikenan, zan yi Magana da shi in sha Allah"
"Na gode Daddynmu"
Yayi murmushi ya ce "idan kin yi tilawa, ki dinga yiwa Daddynki Addu'a".
"Me zan roƙa maka?".
"Abubuwa da yawa, amma ba zan gaya miki ba, kan ki yayi ƙarami ba zai ɗauka ba"
Hajara kuwa tana laɓe ta hanyar shigowa falon, tana hango Amina da Alhaji Ahmad, amma ba ta jin me suke cewa, bata iya hango Alhaji Ahmad, amma tana ganin Amina tana murmushi, Amina ta miƙe, ta ɗau ragowar plate ɗin da Alhaji Ahmad ya gama da shi, ta ɗan tsaya a kan Daddy tana sauraren abin da yake faɗa mata.
Idan ba gizo idanun Hajara suke mata ba, kamar shagwaɓa Amina ke yiwa Daddy, shikuma ya kashingiɗa yana kallonta.
"Na shiga uku ni Hajara, me ake aikatawa a gidan nan ne? Ita ma matar gidan uwar gantali, tana can yawo ana munafurtarta, kai amma wannan an yi tsohon banza, wannan 'yar tamilon 'yar zai tsaya tana masa barikanci yana kallo, yo ko ya aka yi ma ta samu wannan damar oho?"
Amina ta nufi hanyar ƙofar kitchen, sai ga Hajiya Zainab ta turo ƙofar falon, sai da Amina ta ɗan razana, ta tsaya ta zubawa Hajiya Zainab ɗin ido.
"Ke uban me kike kallo, sai kace mayya kin tsaya kin zubo mini ido, ko kin aike ni ne?"
Amina ta girgiza kai, ta nufi barin falon.
"Ki kawo mini ruwa, da exotic ƙishirwa ta isheni" tayi maganar tana ƙarasawa in da Daddy yake.
Hajara na ganin Amina ta ce "Mmm su Amina manya, kina sha'aninki" ko kallon Hajara Amina ba ta yi ba, ta cigaba da sabgarta.
Alhaji Ahmad ya ɗan ɗaga murya ya ce "Sweetheart kin dawo?"
Mummy ta ce "Na dawo, kana gida kenan?"
"Na dawo tun ɗazu, ban sameki ba masu aikinki sun ce mini ba kya nan"
"Eh, fita ce ta sameni da gaggawa"
Ya ce "Ok, sannu da zuwa".
"Yauwa, Fadila ta dawo ne?" Ta faɗa tana zama a kusa da Daddy.
Daddy ya ce "Ta dawo, yanzu ta gama yi mini mita, wai gobe in Allah ya kaimu birthday ɗinta, ban wishing ɗinta ba"
Mummy ta ce "Ƙyaleta rigimammiya"
Daddy ya ce "Nan ta nuna mini turare, wai an bata gift, amma ni ban bata komai ba"
Mummy ta ce "Naji ta ce za'a yi mata girki, ayi hotuna tana ta lissafinta dai".
Daddy ya ce "Na yi mata alƙawarin umara, zaku je ke da ita, maybe idan sun yi hutu"
Mummy ta ce "Inyee 'yar gidan Daddy, to Allah ya kaimu, dama nima ina son zuwa, to Allah ya kaimu"
"Wai ni Khalil ya koma ne?" Daddy yayi maganar da ɗan damuwa.
A daidai nan Amina ta kawowa Hajiya Zainab ruwa da lemo.
Hajiya Zainab ta ce "Mata da wannan yaron, wani halin rashin mutunci ya ɗaukar wa kansa, amma zan yi maganinsa"
Daddy ya ce "No, wani abun yana damunsa ne, idan har yana gidan nan, ba zai ɗauke ƙafa daga shigowa gidan nan ba"
Mummy ta ce "Ka rabu da shi kawai" ta mayar da idonta kan Amina ta ce, "Ki buɗe ki zubamini, kin zo kin tsaya a kanmu kina rarraba ido".
Amina ta tsuke fuska, ta fara ƙoƙarin zuba wa Hajiya Zainab ruwa a kofin, ta zuba zata miƙa mata ruwan, Daddy ya kalli Amina ya kashe mata ido ɗaya.
Aikuwa sai hannunta ya kama rawa, har ta zubawa Hajiya Zainab ruwa a jiki.
"Ke mahaukaciya, ba kya gani ne? Ke wace irin dabba ce, kalli yadda kika zuba mini ruwa a jiki, ba kya gani ne?"
Cikin rawar murya Amina ta ce "Kiyi haƙuri, ba da sani na bane"
Dama Hajiya Zainab har yanzu a ƙule take, duk da sunje sun yiwa Hafsa rashin mutunci, amma bata huce ba, dan haka take ƙoƙarin ƙara hucewa a kan Amina, a hasale ta ce "Dalla ɓace ki bar gabana, dabba kawai"
Hawaye ne suka cika idon Amina, amma Daddy ya shiga girgiza mata kai alamar kar tayi kuka.
Duk yadda Mama tayi da Hafsa, a kan ta daure ta ci Abinci, ƙi tayi, tana sallar isha'i, ta kwanta, ta zubawa wayarta ido, tana kallon yadda kiran wayar Khalil da saƙonninsa ke shigowa babu ƙaƙƙautawa, amma bata ɗaga ko guda ba.
Ƙarshe ta saka wayar a flight mode, ta shiga gallery, tana kallon hotunan Khalil da ke wayarta, da Videos ɗin da yake haɗa musu, na hotunansu shi da ita.
Wata irin soyayyarsa ce take sake fizgarta, tana jinta wani iri iya awannin data kwashe daga fitarta zuwa wurin sana'a zuwa yanzu da ba suyi waya ba, ta san yana can cikin damuwar rashin ɗaga wayarsa da ba ta yi ba.
Ta ƙanƙame wayar a ƙirjinta, ta toshe bakinta, ta cigaba da kuka, dan tun a yanzu ta fara jin kewarsa, tana matuƙar ƙaunar Khalil har cikin ranta.
Fadila ce tsaye a gaban mudubi, sanye cikin doguwar rigar abaya, ta ɗan gyar fuskarta, ta ɗauki turaren wurin Yazid ta shafa, ta ɗaura abin hannun, sannan ta ɗauki wasu turarukan ta shafa, ta ɗauki jakarta ta jefa mukullin motarta a jaka, ta tafi ɗakin Mummy.
Bata tarar da ita a falon ba, dan haka ta wuce ɗakin Daddy.
A can ta tarar da su a falon Daddy, a tare ta gaishe su suka amsa.
Daddy ya ce "Har kin shirya?"
"Eh Daddy, and karku manta, tonight in Allah ya kaimu, za muyi party"
Daddy ya ce "To Allah ya kaimu"
Ta ce "Amin" ta ɗau jakarta ta fito falo, a falo ta haɗu da Amina, ta kalli Amina ta ce "Yauwa, idan kin dawo daga school, zan ɗan yi mini party na birthday na, dan haka a gyara ko ina, zamu zo ni da Yusra, za ayi decorations a falon nan"
Amina ta ce "To, Allah ya kaimu"
Fadila ta fice, ba tare da ta amsawa Amina ba.
A ƙofar ajinsu taga Yazid, kamar me jiran wani abu.
Tun daga nesa yake mata murmushi, har ta ƙaraso.
Tana ƙarasowa ta tsaya tana kallonsa ta ce "Wa kake jira ne? Naga kana ta fara'a kamar an maka kyautar wani abu"
"Ke kawai nake jira, in ga kwalliyar ranar birthday, kin yi kyau sosai".
Ta ce "Ikon Allah, ba zaka daina sa ido ba ko?"
"Ai ke kaɗai nake sawa ido, bayan ke bana sawa kowa" ba ta kuma cewa komai ba ta shiga aji.
Yazid kuwa murmushi ya yi, ganin abin hannunta da ya bata, da kuma tashin ƙamshin turaren lailatul sahara a jikinta.
Lectures ɗaya tayi attending, ta tafi gidansu Yusra, ita Yusra basu da lectures.
Ta tarar Yusra ta gama haɗa mata cake ɗin ta da duk wani snacks da za tayi amfani da shi, suka rankaya tare zuwa gidansu Fadila.
Kusan wuni suka yi, suna decorating ɗin falon, Amina na taimaka musu da wasu abubuwan, yayin da ta zuba ido tana ganin yadda suke gudanar da komai.
Khalil ya kasa jurewa, ya shiga damuwa da tashin hankalin rashin sanin dalilin da ya sanya Hafsa bata ɗaukar wayarsa, dan haka da yamma ya shirya ya tafi wurin sana'arta, dan ya san a daidai wannan lokacin ba zai sameta a gida ba, ta fito sayar da awara.
Sai dai tun daga nesa ya ga wurin nata ba kowa. Ya ƙarasa ya yi parking ɗin motar, ya sauko ya nufi wurin, ya shiga wurin mai shayi, suka gaisa da Khalil.
Khalil ya ce "Hafsa ba ta shigo bane?"
"Eh, ba ta zo ba yau, ai wasu mata ne suka zo wurin nan jiya, suka watsar mata da komai na kayan sana'arta, suka yi mata zagin tsamar nama suka tafi"
A firgice Khalil ya ce "Tsaya, ban gane ba me tayi musu?"
"Oho ina na sani, biyu ɗima-ɗima, ɗaya sirirya a wata ƙatuwar mota, haka suka zo suka yi rashin albarka suka tafi, dama da ganinsu kaga 'yan duniya, na rasa a in da Hafsa ke zuwa tana kwaso rigima, rannan sun yi da wannan ɗan iskan, jiya kuma da waɗa nan mata" Khalil dana fahimtar me mai shayi yake faɗa masa yai, ya juya da hanzari a koma wurin da motarsa take, ya shiga ya rufe, ya bar wurin.
A bakin layin su Hafsa ya yi parking, ya sauka ya taka da ƙafafuwansa, zuwa ƙofar gidansu, ya samu wani yaro a ƙofar gidan, ya aika shi ya kira masa ita.
A ƙalla ya shafe mintuna Ashirin a tsaye a ƙofar gidan bata fito ba, ba wai taƙi fitowa bane, dan ta muzguna masa, sai dai tunanin halin da su biyun ka iya shiga, ta daɗe tana kuka, da ƙyar Mama ta rarrasheta ta fito.
Ko da ta fito, bata ƙarasa in da Khalil ya ke ba, a bakin soron gidansu ta tsaya.
Kallo ɗaya ya yi mata yaga yadda ta rame, idanunta sun yi jawur alamun tayi kuka har ta gaji.
Da sauri ya nufi bakin soron, ya tsaya cikin damuwa ya kalleta ya ce "Hafsa baki da lafiya ne? Ina ta kiran waya ba kya amsawa, kalli yadda duk kika fita hayyacinki, meke faruwa ne?"
Duk yadda ta so dakewa, sai da hawaye suka zubo mata, ta miƙa masa wata babbar jaka, ta ajiye a gabansa, sannan ta kalleshi ta ce "Khalil, jiya na maka text, ka turo mini kuɗi, ka bani ninkin abin da na nema, na nemi kuɗin nan ne dan mayar da asarar da aka yi mini, na kayan sana'ata, Khalil daga rana mai kamar irin ta yau, ka sa a zuciyarka baka taɓa saɓnin wata mai kama da ni bama, balle tuna mun yi soyayya.
Jiya mahaifiyarka ta zo ita da wasu, sun yi mini kashedin babu ni babu kai.
Tabbas sun yi gaskiya, zaren ba kalar yadin bane, ni da kai bamu dace ba, kyautatawarka a garrni ta ruɗeni na fara sonka, ba tare da na kalli banbancin matsayinmu ba.
Ga shi nan duk wani abu daka bani, na tataro na dawo maka da su, zoben nan ne kawai ba zan iya dawo maka da shi ba, saboda kana cikin mutane masu muhimmanci da suka shigo rayuwata, na san ba zan taɓa iya mantawa da kai ba, Na gode Khalil Allah ya haɗa kowa da rabonsa" ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye, ta juya ta shiga cikin soron.
Cikin zafin nama Khalil ya bita, ya riƙota ya juyo da ita tana fuskantar sa.
Kamar zai fashe da kuka ya ce "Haba Hafsa, ina duk alƙawarin da kika yi mini na kasancewa da ni, duk ƙalibalen da ka iya tasowa kuwa, dan Allah karki ce zaki rabu da ni ba, dan Allah kar ki mini haka, in dai Mummy ce zan yi mata bayani, zata fuskance ni kuma, dan Allah Hafsa, muna son junanmu karki yanke wannan hukuncin"
"Bakin Alƙalami ya riga ya bushe Khalil, idan na ce bana sonka nayi maka ƙarya, amma duk wani abu da za ayi iyaye ba sa so ba zai taɓa yin albarka ba, banga alamar Mummy zata fahimceka har ta bari muyi aure ba, dan Allah Khalil kar ka sake shigowa rayuwata, Allah ya haɗa kowa da rabonsa"
Ta zame hannunta daga cikin nasa da ya riƙe, ta shige cikin gidan tana kuka.
Contact me for the VIP group
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
PAGE 38
Wani abu me mai nauyi ya tokarewa Khalil ƙirji, bai taɓa tunanin Mummy zata aikata abin da ta aikata ba, na zuwa ta ci mutuncin Hafsa a gaban mutane.
Tamkar wanda aka zare wa lakar jiki, haka ya ja jikinsa ya buɗe motar, ya shiga ya zauna, ya kifa kansa a kan sitiyarin motar, ya rasa abin da