Showing 192001 words to 195000 words out of 296192 words
naje na dawo daga sallar Asuba amma baki tashi ba" Daddy yayi maganar yana mita.
"Wai har Asuba tayi ne? Yanzu fa na kwanta"
"Tashi ko inje in tsomaki a ruwa".
Sai da yaga ta shiga toilet, sannan ya tashi ya bar ɗakin.
Wunin ranar kallon Daddy take, tana son ko sau ɗaya ta gaya masa wata kalma ta soyayya, amma ta kasa kunyarsa take ji, gashi da ta kalleshi sai su haɗa ido, har sai da ya magantu ya ce "Wai me kike son faɗa ne?"
Ta girgiza masa kai ta ce bakomai.
Yana ta shirin tafiyarsu Lagos, ranar da zasu tafi da Safe, Hajiya Maryam ta zo.
Amina taji daɗi sosai da sosai, sai dai tayi farinciki na ganin Amina tsaf da ita, daga ita har gidanta ba datti.
Amina tayi murna da zuwan Hajiya Maryam, lokacin Daddy baya nan.
Hajiya Maryam ta ce "Allah yayi dai nazo, Jiya Baby ya ce mini yau da daddare zaku tafi"
Waro ido Amina tayi ta ce "Wace Babyn?"
Hajiya Maryam tayi dariya ta ce "Mijina mana"
"Shi ne Babyn" Amina ta faɗa tana ganin kamar abun ba tsari.
Hajiya Maryam ta ce "Ke ba kin tsaya ba, baki karanta littafin ba?"
"Na karanta, tun ranar"
"To meye feedback? Kin fara jarrabawa?"
Amina kamar za tayi kuka ta ce "Ni wallahi kunya nake ji"
"Ke ƙaniyarki ke da kunyar, ana nuna miki Annabi kina rintse ido"
Amina dai tayi jimmm.
Hajiya Maryam ta cigaba da yiwa Amina lecture, ta bata wasu irin manyan kwalaban turare, na humra da 'yan ɗuri masu kyau da tsadar gaske.
Ta ce "Idan kinji daɗin turaren nan, in ya ƙare kice ya sai wasu, ni ke sayarwa"
"Wannan kuma, gasu nan sune Auren, ba a zama haka, kiyi duk abin da nace miki, sannan kiyi biyayya. Saura muyi waya kice mini baki yi ba"
Amina ita kunya ce ma ta isheta, ita wannan matar bata jin kunya sam, har da gwada mata yadda zata dinga yiwa Daddyn magana da kwarkwasa take yi.
Hajiya Maryam ta tafi ba daɗewa, Daddy ya dawo.
Ta sanar masa da batun zuwan Hajiya Maryam, ya ce Aikuwa zai kira Hajiya Maryam yayi mata godiya.
Ƙarfe shida na yammaci, Jirginsu ya ɗaga zuwa Lagos, suna cikin jirgi Amina na saƙawa da warwarewa. Ta raya a zuciyarta a Lagos ɗin nan, zata dage ko sau ɗaya ta ce tana son sa taga ya zai ji.
Koda suka sauka a Lagos, Daddy ya ce a ɗaki ɗaya zasu dinga kwana, Amina ta tashi hankalinta, amma take ta ƙoƙarin dannewa, saboda kar ta ɓata masa rai, kuma Anty Maryam ta ce ta daina yi masa musu da jayayayya.
Daddy yana kwance yana waya da Khalil, Amina ta shirya musu kayansu a wardrobe, ta sanya kayanta na bacci, ta shafa turarenta na wurin Anty Maryam, ita kanta ta yaba da ƙamshin turaren Hajiya Maryam.
Ta gama abinda take, ta raɓa ta hau kan gadon, ta koma ƙarshen gadon ta kwanta.
A hankali ya mirgina kusa da ita, ya cigaba da wayar sa. Ya kammala wayar tare da zuba mata ido.
Ta kai hannunta hancinsa ta ce "Kaji turaren nan da ƙamshi?"
"Tun da kika shafa nake jin ƙamshinsa, a ina aka samo mana?"
"Anty Maryam ce ta bani"
"Lallai ta kyauta, na yaba sosai matso inji ƙamshin sosai"
Yayi maganar yana kamo hannunta cikin nasa ya ce " 'yar Babyna?"
"Na'am Baby"
"Meenal, you call me Baby?"
"Eh mana, ko ba ka so?"
"Ina so mana, saura kice kina sona kuma"
A ranta ta ce "Laa dama yana son nace masa ina son sa'
Tashi tayi zaune, ta kai bakinta kunnensa ta ce "ان احبك"
Murmushi yayi ya ce "Alhamdilillah, abin da nake son ji kenan?"
Karatun da Daddy ya fara karanta mata ne, ta kasa ganewa, ta so yi masa gardama amma ta tuna abin da Hajiya Maryam ta gaya mata.
Ƙarshe dai a ranar aka rantsar da Amina, daga gigin ƙuruciyar da yake damunta, ya tabbatar da ita a matsayin matar da ya biya sadaki ya auro.
Bai yi zaton Amina ba zata yi masa tijara ba. Duk wannan bakin da tsiwar, da zaƙalƙalewar tayi tsit. Sai share hawaye da take yi.
Ba abinda take sai bin umarnin duk abin da , bayan ya taimaka mata tayi wanka ta dawo ta kwanta, ta toshe baki a cikin bargo tana kuka.
Daddy ya zauna a kusa da ita, ya cirota daga bargon ya ɗan dubeta ya ce "Me kuma ya faru? Haba Babyna"
Ta sake fashewa da kuka, yayi ta rarrashinta sannan ta ce "Bafa haka muka yi da Baba ba, ni yanzu me zance masa?"
"Haba Meenal, yanzu idan ba ke zaki je ki gayawa Baban abin da ya faru ba, ya za ayi ya sani? Dan Allah kiyi haƙuri kuma kiyi shiru da bakinki, kin sai dai Allah ya tsinewa mai tona asirin aurensa".
"Amma Daddy, ka san ban tare ba ai, kuma Baba... Bata ƙarasa ba ta cigaba da kuka.
" To kiyi haƙuri dan Allah, karki gayawa kowa kin ji Sweetheart, wannan ma sirrinmu ne da bai kamata kowa yaji ba, namu ne mu biyu kawai da zai shiga kundin tarihin rayuwar mu" haka yayi ta lallaɓata, yana kwantar mata da hankali, har ta haƙura.
Suka cigaba da rayuwarsu, Amina na cigaba da lallaɓa shi ya shiga lamarin auren Khalil, kuma ya dinga zumunci da danginsa, tana yi masa nasiha dai.
Sai dai abin da yake haɗata da Daddyn, shi ne yadda yayi kunnen uwar shegu da batun Amina bata tare da shi ba, ya cigaba da rayuwar aurensa da ita.
Amina da fari tana yi masa biyayya, daga baya kuwa taga bata kyautawa Baba ba, gashi 'yan makarantarsu tuni sun koma gida, amma banda ita, ida Baba ya samu labari bata san ya zata ji ba.
Dan haka ta uzzura wa Daddy, a kan ita sai ta koma gida, ta sashi a gaba kukan safe daban na dare daban, ya gaji ya biya mata kuɗin jirgi ta koma Kano.
Sai dai tun da ta dawo Kano, ta koma gida, ta fara zazzaɓi da ciwon mara, amma ta basar ta cigaba da sabgoginta.
Tunda taje gidansu Azima, Ammi take kallonta, dan Azima ta sanar da ita 'yan makarantarsu sun dawo amma banda Amina, gaba ɗaya yanayin Amina ya nuna alamun ciki a tare da ita.
Sati guda Amina ta sake komawa gidansu Azima, Ammi tana jinta suna faɗa da Azima, Amina tana cewa bata son ko ganin shinkafa balle ta ci.
Daddy kuwa kasa jurewa yayi, saboda sabon da suka yi da Amina, dan haka ya shirya ya dawo Kano, suka cigaba da rayuwarsu tare, cikin soyayya da kulawa. uwa lokacin da Hajiya Zainab ta dawo.
Lokacin da Amina ta kirashi a waya sanar masa ga abinda ya faru, hankalinsa ya tashi sosai, bai so cikin Amina ya zube ba, saboda yana daga cikin abin da yake ƙauna a rayuwarsa 'ya'ya, tonuwar Asirinsa sam baya gabansa a kan ɓarin da Amina tayi, hankalinsa ya tashi sosai da yaji batun Hajiya Zainab zata kori Amina.
Hankalinsa ya tashi sosai, da ya dawo yaga Amina, ya ɗauke ta ya kaita Asibiti, sai zuba shagwaɓa take son ranta.
"Meenalina, Allah ya kawo mai amfani, naji ba daɗi sosai ance mini biyu ne ma"
"Ni baka ta lafiyata sai ka rasa 'ya'ya ko, Daddy na sha wahala sosai"
"Am sorry Meenalina, ina zan so lafiyarki ta taɓu, Allah ya bamu masu amfani"
Bayan nan ya kira Baba a waya, a kan akwai buƙatar ya dawo gida akwai magana, ya kira kawunnansa da suka ɗauro masa aure.
Shine wannan zaman da suke yi yanzu, domin a warwarewa Hajiya Zainab zare da abawa.
Alhaji Ahmad ya kalli in da Hajiya Zainab ke zaune ya ce "Zainab ina mai baki haƙuri, a kan abin da zan gaya miki yanzu, ban yi domin naci zarafinki ba. Na auri Amina 'yar wajen Malam Hassan watannin baya, kuma na ɓoye miki ne zuwa lokacin da Allah zai sa ta tare na sanar miki, sai dai kana nasa Allah yana nasa, Allah yayi yanzu lamarin zai bayyana, dan haka Aure muka yi da ita!!!
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
61
Kawun Alhaji Ahmad, da suke kira da Baba Mamman, yayi gyaran murya ya ce "Haka ne, mune muka je muka nemawa Ahmada Aure, kuma aka ɗauro masa aure, amma batun a sanar miki da auren, wannan shi ke da alhakin yi, mai faruwa dai ta riga ta faru, abin da ya rage kiyi haƙuri ki karɓi ƙaddara, ita ce cikar kowanne musulmi"
Bai ida ba Hajiya Zainab ta miƙe tsaye, fuskarta babu alamar rahama ko sassauci, ta kalli Alhaji Ahmad ta ce "Kayi abin da kake so, nima ka jirayi me zan yi, ka san kayi kaɗan kayi tsararo kayi mini Wannan haukan, wallahi baka isa ba, ko ni ko kai ina nan a Zainab ɗina da ka sanni, zaka ga ƙarshen rashin mutunci, kun goyawa ɗanku baya, ya wulaƙantani ya tozartani ko, mu zuba ni da ku shege ka fasa. Kai kuma tsohon banza munafuki annamimi, zaka ga abin da zan muku, a tarihin zuriyarku nan gaba wani ba zai ƙara marmarin yin cin amana ba, mutumin banza maha'inci"
"Kar ki sake zagar mini uba"
Cikin tsawa Baba ya ce "Amina, ki mini shiru da bakinki"
"Ta dai cigaba, ni haryanzu wannan abar, ba ta kai na kalleta a matsayin kishiya ba ko da kuwa kucakar kishiya, dukkaninku zaku ga abin da zan yi"
Ta juya ranta na mata zafi, ta bar falon.
Baba Mamman ya ce "Ka gani ko Ahmad, abin da muke ta nuna maka kenan, da ka sani ka sanar da ita tun da fari"
Kamar Daddy zai kuka ya ce "Haba Baba, ka san komai ka san halinta, idan har ta san ina neman aure, wallahi ba zata bari ba, ka san abubuwan da suka faru a baya ai"
Baba Mamman ya kalli Amina ya ce "Amina tashi kiyi tafiyarki kin ji" ba Musu Amina ta tashi, ta nufi sashinsu.
Hajara ta gani a tsaye, da alama taji duk abin da aka yi, Amina ta kalleta ta ce "To Hajara, sai ki daina yi mini kallon mutuniyar banza, naje ina kwana ɗaki ɗaya da maigida, har kina zargin ina baki kuɗi ne dan kar ki tona mini asiri, yau kinji abin da ake ciki, mijina ne, kuɗi da nake baki kuma kyautatawa ce, saboda idan na samu sonake kowa ma ya samu, ki daina yiwa mutum hukunci da abinda kika gani kawai a zahiri"
Hajara dai tayi tsuru tsuru, tana jinnkna al'amarin da matuƙar mamakin yadda abubuwa suka wakana haka a ɓoye, hankalin Hajiya Zainab na kan kar ɗanta ya auro mata mai awara, ita kuma an aure mata miji, auren cin amana 'yar aikinta.
Alhaji Ahmad ya ce "Baba Mamman yanzu ba yadda za ayi ku ɗan yi mata nasiha ko zata ji?"
Baba Sagir ya ce "Kana gani fa a gabanka ta wulaƙantamu, muna magana ta tashi tayi zage-zage ta wuce, ai wannan kuma aikinka ne, mu kaga yanzu ma tafiya za muyi, Allah ya baka ikon haɗa kansu".
Alhaji Ahmad ya lura da yadda jikin Baba duk yayi sanyi.
Ya ce "Bari muje ɗaya gidan nawa, ku ci Abinci kuyi salla tukuna" suka ce su ba zasu zauna ba, tafiya za suyi, suka yi ta bawa Baba haƙuri a kan irin cin mutuncin da Hajiya Zainab tayi masa.
Ya ce "Kar ku damu, ai idan da sabo ni na saba"
Daddy ya saka Zakiru ya mayar da su Baba Sagir Dutse, ya kawo alheri yayi musu.
Ya koma wurin Baba da duk jikinsa yayi sanyi, "Malam Hassan, na san nayi maka laifi na saɓa yarjejeniyar mu, amma dan Allah dan Annabi kayi haƙuri, na san ban kyauta ba amma kayi haƙuri dan Allah, kuma wallahi ba laifin Amina bane ba, bata da laifi ina dai bak haƙuri"
Cikin dattaku Baba ya ce "A'a bakomai, ai a yanzu kai ke da iko da ita, ni tunani nake yadda Amina zata zauna da kai a gidan nan, a wannan yanayin"
"A'a Baba, babu damuwa komai zai zama daidai in Allah ya yarda, yanzu zan saka a mayar da kai Shanono, zan zo da kaina"
"Amma ina jin tsoron kar wani abu ya sameta"
Daddy ya ce "Ba abin da zai sameta in Allah ya yarda"
Baba ya ce "To amma aikina fa?" Daddy ya lura da tsoron tafiya yake ya bar Amina.
Daddy yayi ta kwantar masa da hankali, shima ya saka a kaishi gida.
Hajiya Zainab kuwa sintiri ta dinga yi a ɗakinta, ji take kamar wuta ce take ci a ƙirjinta, wa zata tunkara da wannan maganar abin kunya da tozarcin da mijinta yayi mata. Gaba ɗaya kanta ya toshe ta rasa wani kalar abu za ta yiwa Alhaji Ahmad da Amina ta huce wannan mummunan baƙin cikin da suka ƙunsa mata, gaba ɗaya kanta ya kulle.
Fadila kuwa da a kunnenta Daddy ya furta cikin Amina nasa ne, kuma ba ta kai ga barin falon ba, taji wai auren Amina ya yi, ta koma ɗakinta da gudu, ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka, Daddy ya gama da su ya tozarta su, ba wanda take tausayi irin Mummy, ta san yadda bata ƙaunar kishiya, amma Daddy ya rafka mata wannan wulaƙanci, ta san Mummy ba zata iya jurewa ba, ashe dan ya samu ya sake ne ya sanya ha tura su umara.
Take taji wani matsanancin haushin mahaifinta ya kamata, dan ta san Abune mai wuya Mummy ta iya jure wannan abu da yayi mata.
Duk da tarin fargabar da ke cikin zuciyarsa, haka ya dake ya tunkari ɗakin Hajiya Zainab, yana shiga ya tarar da ita zaune a gefen gado, tayi jifa da ɗankwalin kanta, sai nishi take yi kamar wadda take naƙuda.
Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya gyara zamansa zai yi Magana, amma cikin ƙaraji ta ce "Ahmad bana son jin komai daga bakinka, kai har kana da ƙwarin gwiwar da zaka tunkari inda nake har ka sanya idonka a nawa zaka yi mini magana? Tsohon munafuki mara imani, Ahmad banda idan auren ne ka auro mini mace da zan goga da ita, amma ka auri ƙasƙantacciya 'yar aikina saboda azzalumi ne kai"
"Zainab ban zalunceki ba, kuma koma menene kece kika janyo shi, kece kika bani dama kika buɗe mini ƙofar aikata koma meye, kuma ki sassauta kalaman da kike amfani da su a kaina, aure nayi ba zina ba! Kuma adddini bai haramta mini yin hakan ba, Zainab da na biye ta taki da yanzu ina nan ina biye biyen matan banza a kwararo.
Zainab kusan shekaru talatin muna tare, kina garani yadda kike so, tun a baya na so in ƙara aure amma sai ki uwa ki makarɓiya ki hana, ki soke abun, kika dinga bin diddigina da kishin tsiya da saka ido, amma baki san ki kula dani ba, ƙawayenki sun fini a wurinki.
Zainab yaushe rabonki da shimfiɗata a matsayinki na matata, idan nayi magana sai ki ce mini wai na girmi haka, ta yaya? Bayan kinfi kowa sanin ba haka bane, ko kin manta a baya lokacin da sai na biyaki zaki zo in da nake, duk kin manta wannan ashe ban yi haƙuri da ke ba.
Buƙatuna Abincina, da makamancinsu duk sai dai masu aiki suyi mini, da masu tsafta sa akasin haka, na nemi ki bini wurin aikin kika ƙi saboda ƙawayenki, shikenan ni ban san ciwon kaina ba, ba zan yi farinciki ba sai abin da kike so, wace irin zuciya ce da ke haka mara adalci, ki......
"Dalla rufe mini baki, wannan bai isa ya zama dalilin da zaka auro wannan matsiyaciyar yarinyar ba, duk ina matan da suka amsa sunansu mata a garin nan, ba wadda zaka aura sai ita? Talaka 'yar ƙauye da ta zo cin arziƙi"
"Duk a matan garin nan, babu wadda tayi mini sai ita, ban haifeta ba ban aureta ba amma tana mini biyayya, ta na zaɓar farincikima a kan nata, ita kuwa zuciya tana son mai kyautata mata, na zo da niyyar in rarrasheki, in baki baki, amma tunda haka ne abin, kiyi abin da kike so, amma ki sani wallahi muddin wani abu ya samu matata, Sabo da kaza baya hana a yankata, sai na ɗau mataki a kanki kuma ki jawa Fadila kunne, ba ruwanta da matata, dan kune silar ɓarim da tayi" yana gama yi mata kashedin ya fice daga bedroom ɗin.
Zama tayi dirshen a ƙasa, ta ɗora hannu a ka tana "Wayyo Allah na na shiga uku, na lalace Ahmad ni zaka wulaƙanta har ka fara nuna ta fini, wannan kucakar ƙazama 'yar talakawa, wallahi sai nayi maganinka sai kayi dana sanin abin da kayi mini.
Fadila kuwa kasa jurewa tayi, ta tashi ta nufi ɗakin Mummy, ta ɗan tsaya a ƙofar bedroom ɗinta, taji alamar Daddy baya ciki, sai surutan Mummy, ta shiga ɗakik da sallama.
Tausayin Mummy ya kamata, ganin yadda tayi zaman dirshen a tsakar ɗaki tana kuna, lokaci ɗaya har ta fita hayyacinta.
Fadila ta ƙarasa gabanta, ta zauna ta dafa kafaɗarta ta ce "Haba Mummy, ya da saurin karaya haka? Ban sanki da haka ba dan Allah ki kwantar da hankalinki"
Hajiya Zainab ta ɗago jajayen idanuwanta ta kalli Fadila ta ce "Fadila kinga abin da mahaifinki yayi mini ko?"
"Na gani Mummy, amma dan Allah kiyi haƙuri ki danne zuciyarki ki daina kukan nan, kar a ga gazawarki"
"Nayi ƙoƙarin yin hakan, amma na kasa dole na nunawa mahaifinku kuskurensa a kan abin da yayi mini, sai na sanya yayi dana sanin abin da ya aikata, Fadila yayi aure wata uku ban sani ba yanzu ban da wannan tsautsayin ya gifta sai dai na tsinci Yarinyar zata haihu a lokacin ne zan san ya aureta, 'yar aikin fa Fadila. Meye abin so sa burgewa a tare da ita?"
"Dan Allah Mummy, ki daina wannan kukan, bari naji na samo miki wani abu ki ɗan ci ki kwanta ki huta, amma yarinyar nan ko da me take yawo sai ta bar gidan nan"
Mummy ta yiwa Fadila wani irin kallo mai cike da takaici ta ce "Ni da ya bani saƙon cewar, in sanar da ke bake ba matarsa idan kika kuma yi mata wani abu, zai ɗau mataki a kan ki"
Waro ido Fadila tayi ta ce "Daddyn?"
"Zan yi miki ƙarya ne?"
Fadila ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, 'yar aiki ta zame mana annoba".
"Ta zamewa kanta dai, ai aljani bai san wuta ba sai ya taka, shiyasa ba kunya ba tsoro ta kalli tsabar idona take gaya mini Gaba ma akwai gabanta, to nima zan gwada mata