Showing 147001 words to 150000 words out of 296192 words

Chapter 50 - GABA DA GABANTA

dawowa a yau shikenan, idan ban samu ba, sai dai mun yi waya" ta ɗau jakarta ta nufi hanyar fita, ta bar Fadla da wani yanayi da ta kasa gane kanta, takaici ne ko mamaki.



Amina tana cikin bacci, tayi mafarkin wata baƙar mage, ta biyota, tana ta gudu tana kiran sunan Allah, amma duk da haka magen tayi tsalle ta kafa haƙoranta a cikin Amina.


"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Daddy ka taimakeni" Daddy da yake banɗaki yana wanka, kansa yayi wata irin sarawa, sai da ya dafa bango, da ƙyar ya iya lalubar towel ya ɗaura ya fito.
A gigice ya ƙarasa gadon da Amina take, wanda gaba ɗaya ya wanke da jini, ga jikinta sai rawa yake, kan ya ƙarasa in da take yaji jiri yana neman kayar da shi.


WANDA KUKE FITAR MINI DA BOOK, NA GODE SOSAI 🙏 ALLAH YA NA KALLONMU DUKA, DAN BA MUYI HAKA DA KU BA.

AYSHERCOOL
08081012143GAB DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL


48

Kallon in da TJ yayi jifa da takardar Yazid da ya duƙunƙune Yazid yayi, yana tunanin laifin me ya yiwa TJ haka.
Tj ya kalli Yazid ya ce ya fita ya bar ajin.
Miƙewa Fadila tayi, ta yi submitting ɗin takardarta, ta ɗauko ta Yazid da aka jefar, ta warware takardar, taje ta ajiye a wurin da ake submitting.

"Ke! Meye haka kika yi?" Tj yayi maganar yana tsareta da ido.

"Yazid bai yi laifin komai ba, ban ga dalilin da zai sanya a yar masa da takarda ba"

Ƙarasowa TJ yayi ya sake ɗaukar takardar Yazid ya jefar.

Yazid bai ce uffan ba, ya fice daga ajin, takardar Fadila ta sake ɗauka tabi bayan Yazid da sauri.

"Yazid" ta ƙwala masa kira, ya tsaya ya waiwayo yana kallonta, karon farko tun sanin ta da Yazid da taga ɓacin rai kwance a kyakkyawar fuskarsa da kullum cikin murmushi ya ke, ko da an yi masa abu da bai yi masa daɗi ba, murmushin nan baya barin fuskarsa, ko ya haɗe rai ba ya ɗaukar lokaci yake sakin fuskarsa.

Amma a wannan karon har idanunsa sun yi jawur, jijiyoyin kansa sun ɗaga ɓacin rai ya bayyana sosai a fuskarsa, sai da Fadila ta tsorata da ganinsa a haka.

Jiki a sanyaye ta ce "Ka zo muje wurin HOD ka gaya masa, na san zai yi wani abu a kai".

Yazid ya girgiza mata kai ya ce "No need" ya juya zai tafi.

Carf ta riƙo hannunsa, ya waiwayo da sauri ya kalleta "Dan Allah ka zo muje, na san Sir TJ yana sane yayi maka wannan abun duk bakinsu ɗaya da Kankiya, dan Allah ka zo muje a san yadda za ayi".

Ya zame hannunsa daga nata ya ce "Kar ki damu, na barwa Allah" yayi maganar yana jan numfashi, alama numfashin ya fara yi masa gardama a sakamakon ɓacin ran da ya shiga.

'yan ajinsu da suka fito suka dinga kumfar baki a kan abin da aka yiwa Yazid, suka ƙaraso in da su Fadila ke tsaye suna ziga Yazid ya kai ƙarar abin da aka yi masa.

Da ƙyar da rarrashi Fadila ta shawo kansa ya amince, suka je wurin HOD, sai dai baya nan sai mataimakinsa, ko da suka gaya masa abin da ya faru, sai ya goyi bayan su Kankiya, wai ai ba za su yiwa Yazid ƙarya ba, meyasa duk ajin ba a yiwa kowa haka ba sai shi, yayi misbehaving a wurin exams. Kankiya kuwa ya ce ta shafi duka 'yan ajin saboda ƙarsrsa da suka kai a kan abin da aka yiwa Yazid.

Ran Yazid ya ɓaci iya ɓaci, duk dakiyar zuciyarsa sai da wata ƙwallar baƙinciki ta taru a idonsa, nan da nan ya fara tari, Asma na neman ta tashi.

Fadila ta sake gigicewa, ta samo kujera ta bashi ya zauna, ta ɗauko handout tana masa fifita.

Alhaji Ahmad ya shirya tsaf domin tafiya wurin event ɗin su Amina, ita ma ta fito cikin uniform ɗinta, sai wata jaka da ta zuba wasu kayan a ciki ta ratayo.
Tana ganin Daddy tayi murmushi ta ce "Inyee minister an sha kyau"

Ɗan buɗe baki ya ce "Meenal kin raina ni da yawa, ko Zainab idan na haɗe rai nutsuwa ta ke yi, amma naga alama ke kuka zan yi be dameki ba, kin mayar da ni kamar wani kakanki"

"Dan kawai nace kyau?"

"Dame kika kirani?"

Dariya tayi ta ce "Minister mana"

Ya ɗan yi murmushi ya ce "Wanan lokacin ya wuce, yanzu ba harkar siyasa nake ba, kasuwanci nake yi, dan haka ni ba Minister bane"

Amina ta ce "Gaskiya ka cigaba da siyasa, saboda zan tsaya takara fa, sanata zan zama" Sosai Daddy yake dariya ya ce "To Allah ya taimaka, zamu iya tafiya?"

"Eh mu tafi, yauwa idan muka je, yau za muyi debate zagaye na biyu, da wasu 'yan makaranta kayi ta mini Addu'a, idan nayi ƙoƙari ka tafa mini sosai yadda zan jiyo, in samu ƙwarin gwiwa"

"Wancan da ki kayi bana nan ai kin ci, ba abin da tafin zai ƙara miki"

Haɗe rai ta yi ta ce "Ba zaka tafa mini ba kenan?"

"Ke idan mutum ya biyewa rigimarki, sai ayi ta ɓata lokaci, oya let's go"

Kan Amina ta sake Magana, wayarsa ta fara ringing. "Sweet daughter" ya furta a hankali da yaga sunan Fadila a kan screen ɗin wayarsa.

"Hello sweetheart"

"Hello Daddy kana jina?"

"Eh ina jinki, amma ya na jiki kamar a  ruɗe?"

"Daddy akwai matsala"

Ya ce "Subhanallah, nutsu Fadila menene yi mini bayani"

Nan Fadila ta warware wa Daddy komai.

Amina maimaita sunan Yazid tayi a cikin zuciyarta, Fadila na yawan zancensa.

"Fadila meyasa baki mini wannan bayanin ba tuntuni sai yanzu? Meyasa ki ka yi shiru, ban turaki makaranta dan wani malami ya takura miki ba, ki gaya mini idan da wani abu da yayi miki?"

"Ni Daddy babu abin da yayi mini, Issue ɗin Yazid nake so ayi clearing dan Allah, idan aka ɓata masa jarrabawa ba ayi masa adalci ba"

"Shikenan nutsu, kin tabattar babu wani laifi da yayi, kar ki saka in yi magana idan kin san mai laifinsa ne"

"Wallahi Daddy bai yi laifin komai ba, ai nayi maka bayani"

"Shikenan, bani 5minutes"

Amina a ranta ta ce 'Taɓ dama kin san abin da ya dace da wanda bai dace ba?'

Fadila tana nan tana zaman jiran Daddy ya kirata, sai sannu take jerawa Yazid, shi kam Yazid yayi shiru bai cewa komai, sai taron ɗalibai 'yan ajinsu dake tsaye a wajen suna mayar da yadda aka yi.

HOD ɗin su suka gani ya tunkaro in da suke, da shi da wasu malamai guda biyu.

Yana zuwa ya kallesu a ɗan rikice ya ce "Wacce Fadila?"

"Gani"

"Ke ban da abinki, idan kina da wata Matsala ba sai kizo ki mini bayani ba a san yadda za ayi, amma kawai kina nema ki kunno mana wuta daga sama haka ake yi, ina shi wanda aka krɓarwa takarda?"

Yazid ya sauk mask ɗin fuskarsa ya ce "Gani sir"

HOD ya kalleshi ya ce "Yazid kai ne?"

"Eh nine sir"

HOD ya kalli malaman da suka zo tare ya ce "Baku gane wannan yaron ba? Ya taɓa jan sallar juma'a ranar da Imam bai zo ba, Yazid ya aka yi wannan matsalar ta faru, ya aka yi aka kamaka da satar amsa"

"Wallahi sir ban saci amsa ba, ga class mate ɗina nan a tambaya aji?"

"Wallahi Sir ka san Yazid ba zai yi satar amsa ba, the overaller of the year, ka sani sir" cewar Captain.

HOD ya ce "Naji, kuje za a san abin yi, ke Fadila da kai malam Yazid ku shigo na kira Kankiyar a waya ai"

Captain ya ce "Allah ya ƙara maka lafiya Baba HOD, Allah ya tsare mana kai, wallahi mun yarda in dai Yazid na da laifi a hukunta shi".

"shikenan, kuje za a kula da komai in sha Allah"

Bayan sun shiga Ofishin HOD, Vice ɗinsa sai masifa yake yi, a kan dan me za a goya musu baya, su kai ƙarar malami?.

HOD ya ce "Daga sama aka bada umarnin faɗaɗa bincike, dan haka sai ka ja bakinka kayi shiru".

Fadila da kanta ta janyowa Yazid kujera, ta goge masa ya zauna a hankali.

Ɗaya malamin ya ce "Shi bashi da hannu ne?"

Fadila ta ce "Ba shi da lafiya ne"

"Meya same shi ga mutum garau da shi?"

"An masa aiki ne, kuma yana da Asma, baya son ƙura"

"Lallai kam"

Shi dai Yazid babu abin da ya iya cewa.

Kankiya da yaga kiran HOD, ya gama tsara ƙarairayin da za suyi shi da TJ, bai zaci abin ya girmama ba, sai da ya tarar da Exam officer da student affairs ga kuma Yazid da Fadila, a take ya sha jinin jikinsa. Gaba ma she akwai gabanta.

Suka nemi wuri suka zauna, nan aka shiga bin diddigin abubuwan da ya faru, da har ya sanya aka yi waya daga sama a kan case ɗin.

Nan Fadila ta warware komai, hatta chats ɗin su da Kankiya, da yadda yake takura mata da waya, da warning a kan Yazid, sai data nuna musu da wasu daga recordings ɗin wayar da suke yi.
Shi kansa Kankiya sai a lokacin ya san waye mahaifin Fadila, Yazid kansa yayi sanyi da jin Fadila 'yar waye, bai taɓa zaton hakan ba, kawai dai ya zata 'yar masu kuɗi ce, amma mutumin da ya taɓa riƙe ministan albarkatun ƙasa, kuma sananne bai zai gaza sanun kowace irin alfarma yake nema a ƙasa ba.
Aka koma ɓangaren Kankiya ko yana da abin cewa, da kuma TJ ya bada hujjar cewa Yazid ya saci amsa, amma kowanne ya gaza kare kansa.

Nan aka ce sallami su Fadila, amma Fadila ta ce ya batun jarrabawar Yazid? Ta fito da takrdarsa da aka duƙunƙuna, EO ya karɓa ya ce su tafi an sallamesu.

HOD ya ce "Dan Allah dan gaba idan abu irin wannan ya faru, kan a gayawa father a fara zuwa a samemu muyi maganin abin, ba sai an kunno mana wuta daga sama ba" Murmushi kawai Fadila tayi.

Yazid ya kalli malaman ya ce "Sir na gode sosai da sosai, Allah ya saka muku da Alkhairi ya biyaku da aljanna"

Student affairs ya ce "Kar ka damu, Allah yayi muku albarka"

Suka amsa da Amin.

Yazid ya fito yana ta jera ajiyar zuciya, yana godewa Allah yadda yake tsallakar da shi tarko da sharrin mutane daban daban.

Fadila ta kalleshi ta ce "Nayi farinciki da Allah ya sanya wahalarka ta semester nan bata tafi a banza ba, Allah ya ƙara kiyayewa"

"Amin, na yaba da namijin ƙoƙarin da kika yi a kan ganin ba aci mutuncina ba"

"Kar ka damu, idan na bari aka tozarta ka kamar ni aka yiwa, kuma koma menene ai a kan gaskiyarka ne, bari in kira Daddy in yi masa godiya"

Yazid ya jinjina mata kai. Ta ciro wayarta ta kira Daddy.

"Hello yaya aka yi, komai ya daidaita ko kuwa?"

Ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Daddy komai yayi daidai, an kiramu an warware komai, muna godiya Allah ya saka da alheri"

"Amin, sannan idan na dawo gari zan zo makarantar ta ku, dole ayi miki tsakani da wannan malamin, ba zan lamunci irin haka ba, kuma daga yau kar ki sake ɓoye abu makamancin wannan"

"To Daddy in sha Allah, mun gode sosai"

"Never mind sweetheart, ayi karatu da kyau Allah ya bada sa'a"

"Amin Daddy"

Ta mayar da dubanta kan Yazid ta ce "To yaya, muje in sauke ka ne?"

"A'a, ina jiran Sir Kankiya ya fito ne, zan bashi saƙo"

"Saƙon me?"

"Ki jira zaki gani"

"Ko mu samu wuri ka zauna, saboda jikinka?"

"A'a bakomai, zan iya tsayawa"

Ba su wani ɗau lokaci ba, sai ga Kankiya ya fito fuskarsa babu annuri, ga wani gumi a goshinsa shi da TJ, aka yi sa'a kuwa su biyu ne kawai suka fito.

Yazid ya tari Kankiya ya ce "Sir kayi haƙuri a kan abin da ya faru, ni da a son raina ne, ba zan taɓa yin abin da zai ja maka ɓacin suna ba, sai dai ka sani duk wata halittar ubangiji da ke doron duniya duk talaucinta muninta, kayanta ko arzikinta, ko da kafiri ne Allah yana son halittarsa, ba kuma zai bar zalunci ba, ka tsangwameni ka takurawa rayuwata duk saboda Fadila. Dan Allah Sir idan har kana son Fadila da gaske kaje gidansu ka sami mahaifinta, ka cireni daga wanda ke barazana ga soyayyar ka, ni kawai na ɗauketa a matsayin'yar uwata da muke aji ɗaya. Fadila tana da komai na gata da jin daɗin rayuwa, Amma Bani da komai sai Allah sai karatuna, idan ka durƙusar da ilimina ka durƙusar da rayuwata baki ɗaya, in dai yanke alaƙata da Fadila zai sama maka nutsuwa na yanke duk wata alƙata da ita, zan mayar da hankalina a kan abin da ya kawoni, amma ka dubi Allah ka tausayawa maraya, ka bar ni in samu ilimin da na zo nema cikin kwanciyar hankali" yayi maganar tare da haɗa hannayensa biyu alamar magiya.
Daga haka ya juya ya fara tafiya, Fadila ji tayi kamar ta shaƙe Kankiya ta huta.

Jikin Fadila yayi sanyi, tabi bayan Yazid da kallo, ga wani irin tausayinsa da ya mamaye zuciyarta, ta mayar da kallonta ga Kankiya da ya ƙame a wurin, tayi masa wani mugun kallo ta bar wurin, a can harabar ajinsu suka tarar da ɗalibai a tsaye suna jiran su ji yadda ta kaya game da jarrabawar Yazid.
Yazid ya basu tabbacin cewa komai ya daidaita, na suka dinga yi masa son barka, tare da cewa Fadila ta cika ƙawa ta gari.
Sai dai bai tsaya wani abu ya kuma haɗashi da Fadilan ba ya bar Wurin.

Debate ɗin yau babu Amina a ciki, sai dai a quiz tayi participating, shima cikin ikon Allah makarantarsu Amina tayi nasa zuwa mataki na gaba.
Daddy har mamakin ƙwaƙwalwar Amina yake yi, ta burgeshi matuƙa gaya, a ransa yake jin ko nawa ne zai kashe ya kaita ko ina ne a faɗin duniya tayi karatu, ba zai taɓa barin wannan ƙwazo nata ya tafi a banza ba.

Ana tashi daga quiz ɗin wurin Daddy ta nufa, kan ta ƙaraso ya fara tafa mata, sai da ta rufe fuskarta tana murmushi.

"Gaskiya kin birgeni, ban san yadda zan misalta miki fatincikin da na shiga ba, Allah ya ƙara hazaƙa Allah ya baku nasara"

"Amin Daddy, duk wata nasara dana samu a harkar karatuna, ba zan taɓa mantawa da gudumuwarka ba, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi ya kula da zuriyarka, sai da na zubda hawaye a lokacin da naji nawa kake kashewa a kan harkar karatuna, bani da bakin....

"Ya isa haka, zo mu tafi ai kun gama" ya katseta ba tare da ta gama maganar ba.

"Wai Daddy duk lokacin da ka yi mini abu ba zaka barni nayi maka godiya ba, bana jin daɗin hana.

Ƙiri ƙiri ya basar da zancen ya ce "mu tafi ko" ba yadda ta iya haka tayi shiru ta fito suka tafi.



Gaba ɗaya jiki babu ƙwari haka Fadila ta koma gida, haka nan ta rasa abun da yake mata daɗi.
Ba dan tana jin daɗin komai ba, tayi wanka ta ci Abinci ta fara karatunta.

Wajen ƙarfe biyar na yamma sai ga Mummy ta dawo, ta tarar da Fadila tana zaune tana duba litafinta.

"Ashe kin dawo"

Fadila ta ce "Eh na dawo, ai exams muke a school"

"Yayi kyau, ke Albishirinki?"

Fadila ta ɗan kallk Mummy sannan ta ce "Mummy duk wannan fara'ar ta mecece?"

"Ke dai ki amsa mana, ai dole kiga farinciki a fuskata"

Fadila ta rufe littafin, ta tattara dukkan nutsuwarta a kan Mummy ta ce "Goro"

"Ina kyautata zaton, na kusa yin sirukai very soon, na yiwa Daddynku maganar Kursum, ya ce mini in bari mu dawo daga umara, zai zauna da mahaifinta, and finally ɗa gidan Hajiya Salma yana iya dawowa a kowane lokaci, dan yana ta bada saƙon gaisuwa a baki, da ya takura ma a bashi lambarki amma ta hana, ta ce kar ya ɗauke miki hankali kina karatu ne yanzu, ya bari ya dawo tukuna, dan har ta yiwa mahaifinsa magana"

Fadila gaba ɗaya zancen bai mata ba, ta ce "Ohhh my Goodness, yanzu a kan wannn maganar ne kike ta wannan murnar for God sake, Mummy ko ganinsa fa ban taɓa yi ba, har ya yiwa babansa magana, dan Allah a ajiye wannan maganar aside"

Ɗan tsuke fuska Hajiya Zainab ta yi ta ce "Ban gane a ajiye maganar nan aside ba, am trying to make your tomorrow better ke da ɗan uwanki, yadda ko bayan ba ranmu na san na kafaku abokan rayuwarku ba zasu zame muku liability ba, ba ruwansu da abin da kuka mallaka, ta nuna mini hoton yaron ba shi da wani aibu, kuma already yana da sana'arsa a can in da yake karatu, idan kun yi aure can zaku tafi gaba ɗaya"

Tura baki Fadila tayi ta ce 'Ni gaskiya Mummy am not going anywhere, karatuna fa?"

"To karatun dama ba a waje muke yi burin kiyi ba, amma mahaifinki ya hana ba yanzu ga dama ta samu, ba sai kije ki cigaba da karatun a can ba"

Sake tura baki Fadila tayi tana noƙe kafaɗa, dan tun bata ga gayen ba taji lamarin bai yi mata ba sam.

Mummy ta kwantar da murya ta ce "Haba autar, am sure you will like that guy, yaron yana da hankali ba zaki shiga wahala ba zaki huta sosai, Please don't disappoint your mum, na san type ɗin mijin da kike so, I know you are classic that's why I chose him for you"

Fadila ta tashi tsaye ta ɗau littafinta ta ce "Mummy, we should discuss it later, let me first concentrate on this one" tayi maganar tana nuna wa Mummy littafin hannunta.

"Ok dear, good luck"

Fadila ta amsa da thank you ta bar wurin.





"Minister" Amina ta faɗa tana leƙa fuskar Daddy, dan taga reaction ɗinsa.
Shareta yayi ya cigaba da kallon tagar mota.

"Minister am talking fa"

"Kinga ki kiyayeni tom"

Murmushi tayi ta ce "Ka san me nake sha'awar ci kuwa?"

"A'a, ki faɗi ko meye kan mu isa gida sai mu tsaya a nema a hanya"

"A'a ni ba na sayarwa ba, wainar fulawa zan soya in ci"

Ya waiwayo ya kalleta ya ce "Ina kika ga kayan wainar fulawa a gidan?"

"Ban gansu ba amma sai a nemo"

Daddy ya ɗan ƙura mata ido ya ce "Ni ne zan nemo"?

"A'a ni na isa in ce haka, wace ni ranka ya daɗe, dan Allah ka saka a samo mini kayan yi, ni zan yi da kaina"

"Sai dai a ajiye ki, ke kije ki nemo"

"Idan na ɓata fa, ko wanan karnukan suka cinyeni a hanya"

Ya kasingiɗa da jikin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login