Showing 141001 words to 144000 words out of 296192 words

Chapter 48 - GABA DA GABANTA

da missing ɗina, na san shine punishment ɗin da ba kya so"

"Ba wani missing ɗinka da nake, kawai dai banji daɗi bane"

Ya ɗan ƙura mata ido ya ce "Wannan murnar da kike yi fa dan kin ganni" shiru tayi tana ɗan motsa baki.

"Daddy nan ne gidan abokin naka?" Tayi maganar tana kallon falon.

"Gidana dai" ya bata amsa.

"Kai da waye a gidan to?" Tayi maganar tana waige waige.

"Ni da mata ta" ya bata amsa.

Ta ɗan waro ta tashi ta koma kujerar kusa da shi ta zauna.

"Ya kika tashi"

"Idan ta zo ta ganni a zaune a kusa da kai Allah kaɗai ya san iya zagin da zata yi mini, ni da na san ba gidan abokin naka zan zauna ba, da ba zan zo ba dan na san aiki zata yi ta sakani a nan ɗinma na zan huta ba"

"Da wasa nake miki, nikaɗai ne ba tare muke ba"
Amina ta ɗan yi Jimm sannan ta ce "To yaushe zaka kaini gidan abokin naka?"

"A'a a nan zaki zauna" ƙwalalo idanuwanta waje ta yi ta ce "Wai mu zauna mu biyu kawai a gidan nan?"

"Eh" ya bata amsa kansa tsaye. Ɗan saroro tayi tare da jin nauyin yi masa nuni da rashin dacewar hakan.
Ta zura masa ido tana kallonsa, tana saƙe-saƙe a zuciyarta na yadda zata kawo uzurin da zai sa yasa a mayar da ita in da aka ɗaukota.

"Ya dai, akwai damuwa ne?" Yayi maganar yana nazartar yanayin da ta shiga.

Ya miƙe tsaye ya ce "Muje in nuna miki in da zaki zauna" ya ƙarasa ya janyo Akwatinta, yayi gaba ta bishi a baya a tsorace.

Wani ɗan madaidaicin bedroom ne, mai matuƙar kyau da ban sha'awa, ya kalleta ya ce "Nan yayi miki ko in canza miki ɗaki?"

"Yayi, amma ina jin tsoro ko zaka saka a mayar da ni can wurin 'yan makarantarmu?"

"A nan zaki zauna, kuma da rana tsakar nan me zai kama ki, idan kin huta ki zo ki ci Abinci" yana gama yi mata bayani ya fice ya bata wuri.

Duk da zullumin da take ciki, bai hanata ƙarewa ɗakin kallo ba, tare da jinjina kuɗin da Alhaji Ahmad yake da shi, sai dai da tuna al'umma basa amfana da wannan tarin dukiyar duk sai taji babu daɗi.
Gaban mudubin dake ɗakin taje, taga wata magazine, ta ɗauka ta fara dubawa, babban abin da ya bata mamaki shi ne ganin Alhaji Ahmad ya taɓa riƙe minister, a tattaunawar da aka yi da shi.
Jinjina kai tayi, gaba ɗaya yadda ya saki jiki da ita, har wasu lokutan take wuce makiɗi da rawa ne yake bata mamaki, idan kuwa hakane gaba ɗaya bashi da girman kai, haka ta nustu ta cigaba da dudduba jaridar, sai da ta kammala tsaf ta ajiye. Gaba ɗaya ta gaji da zaman ɗakin, jin ana kiran sallar la'asar ne ya sa ta shiga banɗakin da ke cikin ɗakin tayi alwala, ta dawo tayi salla a kan Carfet ɗin da ke ɗakin.

Ta idar da salla da Adduointa, sai kuma ta ji duk zaman shirun ya isheta, tashi tayi ta bi hanyar da Daddy ya bi da ita, ta koma wannan ƙaton falon, amma baya nan sai TV dake tayi ita kaɗai.
Hakan bata damar sake tsayawa ta kalli abubuwa yadda take so a falon, a hankali kuma ta cigaba da leƙe leƙe tana cigaba da kallon ikon Allah, gidan ba ƙaramin kyau ne da shi ba.

Tuni ta manta da fargabar da take ciki, ta cigaba da buɗe wurare tana leƙawa.

Faluka sun kai uku wanda ta gani, kowanne da kalarsa.
Babu zato ba tsammani ta buɗe wata ƙofa, wani ƙaton ɗaki ne da makeken gado ɗakin shima nasa kalar tsarin daban.
Daddy ne zaune ya saka laptop a gaba, yana nazartar wani abu, daga shi sai dogon wando da vest. Da sauri ta saki ƙofar ta juya zata arta da gudu.

"Amina zo nan" taji muryarsa. Tsayawa tayi a waje, amma ta kasa dawowa.

"Karki bari in taso, ki zo nace" ya faɗa a ɗan kausashe.

Kamar munafuka haka ta shiho kanta a ƙasa.

"Me kike nema ne?" Yayi maganar da dukkanin attention ɗin sa a kanta.

"Bakomai"

"Ki gaya mini menene?"

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Bakomai".

"Kin ci Abincin ne?"

"A'a na ƙoshi" gaba ɗaya ya lura a tsorace take.

"Ko kin gaji da zaman ke kaɗai ne?" Ta ɗaga masa kai da sauri.

"Ok, taho ki zauna a nan muyi hira"

Ta girgiza kai ta ce "A'a, zan koma ɗakina"

"Kamar a takure kike, bari in zo muje a kaimu yawo, zaki?" Ta ɗaga masa kai da sauri.

Ya miƙe ya zura riga, ya sanya facemask da hula, ita dai tana gefe tana kauda kai gefe.

Kasancewar sanye take da hijjabi, ya sanya suka fita.

Yadda ake ta giramama Daddy abin har mamaki yake bata, ba a masa wannan girmamawar a Kano.

Suka shiga bayan mota ita da shi, direba ya ja su suka fita.

Suna tafe yana mata hira yana nuna mata gari, har ya samu ta saki jikinta, ya saka aka kaisu wuraren shaƙatawa, Amina har da hawa liluka tayi ta nuna halin ƙuruciya da yarinta, Daddy bai hanata ba, sai da ya tabbatar da ta samu nutsuwa ta saki jikinta, sannan suka koma wancan gidan.

Da daddare bai tsareta da doguwar hira ba, ya bata umarnin tafiya ta kwanta, shima ya tafi nasa wuri,Amina bata da tabbacin a in da ya kwana, ko a gidan ne ko ba a gidan bane ba bata sani ba, kawai dai ya saka ta shiga ɗakin ta kulle ta ciki sannan ya tafi.

Da ƙyar Amina ta iya bacci, saboda tsoron da take ji, haka ta kwana da hasken ƙwan lantarki saboda tsoron da take ji.

Bata kuma ganin Daddy ba sai washegari ƙarfe tara na safe, ya kirata a waya ya ce ta fito ta karya.

Dama a shirye take ta daɗe da tashi, ta saka hijjabi ta fito falon, "Good morning" ta gaishe shi cikin girmamawa.

"Morning, kin tashi lafiya?"

Ta amsa da "Lafiya lau Alhamdilillah"

Ta kalli kayan tea da flask ɗin Abinci da ke gaban Daddy, ta kalleshi ta ce "Waye yayi girki?"

"Kawo mana nasa aka yi, serve us"

Ta haɗa musu tea, ta zubawa kowa nasa, ta miƙa masa nasa ta ɗau nata ta koma bayan kujera, ita ba zata ci Abinci a gabansa ba.
Murmushi kawai yayi, ya yi Bismillah ya fara cin Abincinsa.

Sai da ta gama cin nata, ta tashi ta haɗe kwanukan wuri guda.

Kamar an tsikareta ta ce "Yauwa, Daddy dama kai minister ne?"

Ya ce "In ji wa?"

"A ɗakina na gani, ashe ka taɓa riƙe minister"

Ya girgiza kai ya ce "Bani bane gaskiya, wa zai bawa talaka almajiri Minister a Nigeria?"

"Waye talakan?" Tayi maganar seriously.

"Ni mana"

"Taɓ, Ashe mu sai dai a ce mana faƙirai, kalli gidajenka da motocinka, amma kake cewa kanka talaka wallahi Daddy ka dinga cewa Alhamdilillah"

"To Anty Meenal"

"Anty kuma?"

"Eh mana, gashi kin sani a gaba kina mini faɗa a kan zancen da ban san shi ba, ban san a ina kika samo wannan labarin ba"

"Bari in ɗauko maka jaridar ka gani" ta tashi ta tafi ɗakin da ta kwana.

Murmushi kawai yayi ya girgiza kai.

Ta dawo riƙe da jaridar, ta buɗo shafin da ta karanta hirar da aka yi da shi da kuma hotonsa ta ce "Kaga fa"

Ha kalli jaridar ya ce "Ikon Allah, me kama dani"

"Baga sunanka a nan ba, Ahmad Musa dutse gaka nan a zaune"


"Wane sunan kika ce?"

Ba tare da tayi tunanin komai ba ta ke nuna masa "Gashi Ahmad Musa dutse, gaka nan kaine fa a jiki"

Yayi murmushi ya ce "Wow, sake faɗar Ahmad ɗin in ji"

Kallonsa tayi a shagwaɓe ta ce "Daddy ni gaba ɗaya ka mayar da ni wata 'yar yarinya"

"To meye idan ba 'yar yarinyar ba? Sai sha ɗaya zaku fara event ɗin yau ko?"

"Eh, zaka je ne?"

"Ya na iya, saboda ke ai na zo garin nan"

"Yauwa Daddyna na gode, zan fi samun confidence idan muna tare".



A yau su Fadila zasu zana jarrabawar Kankiya, gaba ɗaya a tsorace take, Saboda warning ɗin da Kankiya ya yi mata, saboda ta ƙi zuwa kiran da ya yi mata.
Ƙarfe takwas na safe tuni ɗaliban sun gama settling a aji, sun mayar da hankali wurin rubuta jarrabawarsu ciki har da Yazid.

Wajen ƙarfe tara da rabi, Kankiya ya yi dirar mikiya a ajin, kai tsaye Ya dubi Yazid cikin son ya tozarta shi ya ce "Me kake yi a zaman jarrabawata na yau, tashi ka fita ka bar mini aji, ai na gaya maka no 75percent attendance no exams come and leave you have automatical carry over"

Malamin nan dai na jiya ne yau ma tare da TJ suke invigilating. "Kankiya ina roƙa masa alfarma, yaron nan ba shi da lafiya ne dan Allah a bar shi yayi jarrabawar nan na roƙa masa arziƙi"

Kankiya ya ce "A'a ba zai zana jarrabawar nan ba, ya tashi ya fita"

Yazid ya kalli Sir Kankiya ya ce "I never miss your attendance sir"

"Ni kake gayawa You never miss my attendance, ƙarya zan yi maka, ka kalli tsabar idona ka ƙaryatani, ga Attendence sheet ɗin a hannuna"

"Sir ba ƙartayaka nake ba, ina da Attendence ɗin ka full"

Ganin Yadda Kankiya ya harzuƙa, ya sanya malam Sani cewa ya ɗauko Attendence ɗin a duba"

Kankiya ya ɗauko takardar Attendence, yana ta kumfar baki, sai dai ko da aka duba lambar Yazid he never missed it.

Mamakine ya cika Kankiya, saboda yadda yake tsaurarawa wurin yin attendance, kuma ya san Yazid baya zuwa ajin, amma complete Yazid yana da Attendence.
Lumshe ido Fadila tayi tana murmushi.

Abin da Kankiya bai sani ba shine, tun lokacin da Yazid yayi ta sintirin zuwa ya amsa kiran da Kankiya yake masa baya samunsa, har sakatariyar Kankiya sai da ta fara jin tausayin Yazid, bayan Kankiya ya hana shi shiga aji, Fadila ta je wurin Sakatariyar Kankiya, ta bawa sakatariyar kuɗi ta ce tana son idan Kankiya baya Office, ta dinga duba Attendence ɗin 'yan ajinsu tana yiwa Yazid.
Aikuwa sakatariya ta amshe kuɗi, ta dinga yiwa Yazid attendance ba tare da sanin Kankiya ba.

A lokacin ba su samu saɓani da Yazid ba, tayi ta kwantar masa da hankali a kan babu abin da zai hana yayi jarrabawar Kankiya, za a dinga yi masa Attendence, amma bata gaya masa me tayi ba, shi dai yaje ya cigaba da Addu'a ne, kuma ya yarda Allah ya karɓa.

Abun ba ƙaramin ɗaurewa Kankiya kai yayi ba, haka ya haƙura da batun hana Yazid jarrabawa.
Sai dai duk da hakan bai haƙura ba, ya cigaba da neman hanyar da zai soke jarrabawar Yazid.

Yazid hamdala ya dinga yi a ransa, ya kammala jarrabawarsa, ya tashi zai je yayi submitting, bironsa ya faɗi ƙasa, ya durƙua ya ɗau biro kawai TJ ya ce "Kai me kake yi haka?"

Ya nuna masa biro ya ɗauka, TJ yana zuwa ya duƙunƙuna takardar Yazid yayi jifa da ita.



(WHAT DO YOU THINK GUYS, ZAMAN DADDY DA AMINA A GIDA ƊAYA SU BIYU IS IT SAFE? GA KANKIYA GA FADILA GA KUMA YAZID DA KANKIYA KE SON GANIN YA KAI SHI ƘASA, AYI HASASHE LAFIYA SANAN AYI HUTUN ƘARSREN MAKO LAFIYA)




AYSHERCOOL
08081012143LITTAFINA NA KUƊI NE, ₦500 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
AISHA ADAM
JAIZ BANK
KO KU DUBA AREWABOOKS.



Har Amina zata rufe flask ɗin ta juya, ta kuma tsayawa tana kallon naman, sam bata kawo Hajiya Zainab ce ta dafa ba, ta zaci Hajara ce ta tashi ta kammala aiki da wuri ko akwai in da take son zuwa.
Amina ta ɗauki spoon, ta ɗan ɗiba ta saka a bakinta. Ya ji spices sai ƙamshi yake, duk da akwai wani ɗan ɗaci da tayi zaton kawai bakinta ne.

Amina ta sake ɗiba ta ci, taji yayi mata daɗi sosai da sosai.
Jan kujera tayi ta zauna, ta dinga tsamar naman nan tana ci, kan kace meye wannan ta ci ya kai rabi.

Hajiya Zainab kuwa sai lallaɓa Daddy take yi, tana yi masa kwarkwasar da sai zai bata kuɗi yake ganinta.

Ta sha uwar kwalliya, sai ƙamshi take tayi masa jagora zuwa falo, sai hira take yi masa.

Turus tayi lokacin da suka ƙaraso dining, taga Amina zaune da spoon a hannunta tana cin naman da ta tanada saboda Alhaji Ahmad.

"Ke, wani irin wulaƙanci ne wannan da rainin hankali, na girka wa Mijina abun ki zo ki zauna kina ci?" Ɗan saroro Amina tayi sannan ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, wallahi ban zaci ke kika dafa masa ba, nayi zaton Hajara ce......

"Ko kuma uwar Hajara ba, saboda tsabar rashin mutunci ko Hajarar ce ta dafa ba kya bari a baki iznin ci ba, zaki zauna na yiwa mijina girki ki cinye"

Amina ta ce "Ya salam, amma nace kiyi haƙuri ni wallahi ban san ke kika girka ba, saboda ban taɓa ganin kin yi ba, raina ne ya biya amma ba damuwa ai sai na girka masa wani".

A cikin tsananin fushi Hajiya Zainab ta kalli Daddy ta ce "Wallahi tun wuri ka taka wa Yarinyar nan burki, wannan wane irin iskanci ne da rashin mutunci,? Yaya za ayi na dafa abu saboda kai ta zauna ta na ci, yanzu nayi magana ace na fiye kishi da neman rigima ita kuma wannan me tayi?"

Daddy ya kalli Amina ya ce "Meenal, meyasa ki ka ci bayan kin san ba ke kika ajiye ba, kin san fa bana son neman magana"

"Wallahi Daddy ban san naka ne ta ajiye maka ba, ji nayi ina son ci shiyasa"

"Eh tunda gaki mayya ba, dangin mayu kinga nama idan baki ci ba mutuwa zaki yi".

Amina ta ce "Ni ba mayya bace, danginmu kuma babu mayu, dan hak.... Ba ta ƙarasa ba Daddy ya ce "Ya isa haka, ki bata haƙuri kawai a wuce wurin"

"Amma Daddy tunda kuka fito fa nake bata haƙuri, me kuma take so nace mata?"

A ɗan hasale ya ce "Ki bata haƙuri nace, bana son gardama"

Amina ta sunkuyar da kanta ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ban san ke kika girka ba"

Daɗi ne ya kama Hajiya Zainab, ganin yadda Daddy ya fara acting, ya sanya taji a ranta ai maganinta ya fara ciksa, dan ma bai ci wannan naman ba, in da Allah ya taimaketa akwai sauran maganin.

Ta haɗe rai ta ce "Gaskiya dai ka sake ja mata kunne, kar ta sake yi mini irin haka, idan kuma ta kuma komai nayi mata ita ta saya"

Daddy ya ce "Kiyi haƙuri, ba zata sake ba in Sha Allah, kuma in dai nine kar ki damu, na karya haka na gode sosai da kulawa"
Amina kuwa miƙewa tayi, ranta babu daɗi garin ta bar wurin, ta kifar da sauran naman ya zube a ƙasa.

Daddy ya kalleta ya ce "Ina zaki? Ba zaki zauna ki karya ba?"

Hajiya Zainab ta ce "No, bana buƙatarta a nan, daga ni sai kai nake son muyi breakfast, ta samo dai abu ta gyara wannan abin da ta zubar" ko sauraransu Amina ba tayi ba, tai musu banza tayi tafiyarta.

Ɗaki ta koma ta nemi wuri ta kwanta, taji yadda naman da taci yake taso mata, ga shi taji kamar tana ƙaurin hayaƙin nan da ta fito ta tarar ya turnuƙe falo.
Guntun tsaki ta ja ta na juyi a kan gadonta, daga bisani wani irin bacci yayi awon gaba da ita.

A cikin baccin nata ne, taji yadda cikinta yake murɗawa, ta farka ta tashi zaune, abu kamar wasa cikinta ya dinga murɗawa, ta dinga juyi a kan gadon nan, daga baya kuma sai amai. Tun tana iya tashi daga kan gadon ta tafi toilet, har ta nemi wuri ta zauna a toilet ɗin, ta dinga kwara aman nan ba ƙaƙƙautawa, duk ta fita hayyacinta kamar wadda tayi cholera.

Babban abin da ya bata haushi bai wuce yadda Daddy ko ya leƙo yayi mata sallama kan ya fita ba, alhalin idan yana wurinta, sai ya je yaga Hajiya Zainab koda kuwa zata ci masa mutunci ne.

Bayan fitar Daddy, Hajiya Zainab ta ɗau waya take bawa su Turai labarin abin da ya faru a group. Suka tayata murna saboda alamu ya nuna kamar maganin ya fara aiki, amma Hajiya Turai ta ce "A gaskiya naji haushin cin naman nan da wannan shegiyar 'yar tayi, Allah ya sa shi ne ajalinta"

Salma ta ce "Amin dai, sai ki sake dafa masa wani, amma ki tabattar daga ke sai shi a ɗaki, ki bashi ya ci".

"Haka za ayi, na fara na turaren nan ma, ni na naman na damu ya ci, kuma shi yafi son kifi fa a kan nama, saboda hawan jini"

Turai ta ce "Haka nan zaki lallaɓa shi, sai yaci, mu dai fatanmu buƙatar mu ta biya"

Ta ce "Haka ne, in Allah ya yarda zan duk mai yiwuwa, naga na bashi ya ci, sonake naga ya kori Yarinyar nan korar wulaƙanci a gidan nan"

"Kar ki da mu, ke dai ki civaba6da gwada maganin" suka cigaba da zigata da baga shawarwarin yadda zata ɓullowa al'amuran.



Khalil kuwa ya dage sai shiri yake, yana narka kuɗi a gininsa, kamar wanda zai auro 'yar wani gwamna ko sarki, sannan yana turawa Hajiya Maryam kuɗi domin yi masa sayayar kayan lefe.
Sunata cigaba da tsara yadda biki zai kasance.
Abdul ya ga yakamata ya sanar da Khalil batun soyayyarsa da Yusra, kar ya zo yaji a wani wurin yaji babu daɗi.
Dan haka bayan sun gama hirar yadda abubuwa zasu kasance a bikin Khalil, sai Abdul ya fara sako masa nasa zancen ta hanyar cewa "Malam nima fa na kusa kai kuɗin Auren nan". Khalil ya ce "Are You serious?"

"Da gaske nake maka"

"Amma gayen nan baka da kirki, amma baka taɓa gaya mini ba, ko ka haɗani da ita mu gaisa ba"

Abdul ya ce "Ai ba wata bace a nesa, ta gida ce"

"Ok, wacece?"

Abdul ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Yusra ce, ƙawar Fadila".

Khalil ya ce "Ohhh Allah, Allah mai yadda ya so, lallai zaka sha iyayi da rawar kai, ka rasa Fadila amma kusan halinsu ɗaya Allah ya baka wuyanka ɗauka"

"Amin na gode da fatan alkhairi"

"Ahh haba bakomai, amma gaskiya ku bari a fara nawa sai ayi naku"

Abdul ya ce "Saboda wayo, to ban yadda ba"

Gaba ɗaya Abdul bai yi zaton Khalil zai ɗau abin so simple haka ba, a zatonsa zai nuna bai ji daɗi ba, saboda a baya ƙanwarsa ya nuna yana so.


Yazid kuwa ya kuma haɗuwa da Fadila a makaranta, sai dai fuskar nam babu yabo ba fallasa, da fara'arsa ya ƙarasa gareta yana mata murmushi.
"Alhamdilillah, naji daɗi da ban ganki kina kuka ba, amma ya aka yi kwana biyu baki shigo school

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login