Showing 69001 words to 72000 words out of 296192 words
suka gama yi mata sanyi kamar ba a jikinta ba, zuwa cikin soron gidansu, wanda duhu ya mamaye, ta durƙusa ta haɗa kanta da gwiwa ta cigaba da rera kukanta.
Sai da Khalil ya tabbatar ta shiga gida, sannan sannu a hankali ya kunna motar ya bar wurin, cikin tsananin tunani da damuwa Khalil ya nufi hanyar gida. Ikon Allah ne kawai ya kai Khalil gida, saboda tuƙi yake sam hankalinsa baya jikinsa, dan lokaci lokaci ya kan daki sitiyarin motar tasa da ƙarfi yana huci.
Amina ta zazzage kayan da Ammin Azima ta bata, har da kayan kwalliya, da wasu dogayen riguna da atamfa, ga kayan ciye-ciye.
"Ohh ni Amina, Allah sarki ashe akwai masu kuɗi masu mutunci, matar nan har da rungumeni kamar 'yar da ta haifa, a gidan nan kuwa bayan hantara da kyara ba abin da suka saka gaba, muma Allah kai mana arziƙi na halal muyi ta jawo 'yan uwa talakawa muna ci tare.
Hafsa kuwa sai da tayi kuka mai isarta, sannan ta share hawayenta ta shiga gida.
Mama ta ce 'Khalil ɗin ya tafi ne?" Jinjinawa Mama kai kawai tayi, ta shiga ƙoƙarin gyara shimfiɗarta ta kwanta.
"Ko dai halin naki na wulaƙanci kika yi masa ne? Naga kin dawo ba walwala jiki duk a sake" Murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo Hafsa tayi ta ce "Haba Mama, ba abin da nayi masa, lafiya ƙalau muka rabu, bacci nake ji ne".
"To shikenan, ba zaki ci Abinci ba zaki kwanta".
"Eh, na ɗumama da safe, cikina ya ɓaci ɗazu"
"To shikenan, Allah ya sawwaƙe"
Hafsa ta nemi wuri ta kwanta, ta shige cikin bargo, ta ɗauko 'yar wayarta ta zuba mata ido, tana tunanin ko Khalil zai kirata a wayar, har ku san sha ɗaya na dare, ta kasa bacci tana dakon saƙon Khalil kamar yadda ya saba, amma shiru nan da nan wata karaya ta zo mata, ta sawa zuciyarta cewa Khalil babu lallai ya cigaba da sonta ko ya aureta, Gashi ta kamu da soyayyarsa ba da wasa ba. A hankali ta sanya hannu ta toshe bakinta, ta lumshe idanunta hawaye suka dinga zuba daga idanunta.
"Hafsa ya naji kamar kina nishi? Ko mura kike?"
"Eh Mama"
"Sannu, daga yanzu idan ya zo ki dinga yi muku shimfiɗa a soro, kinga garin da sanyi sosai, har da wannan iskar ta saki mura"
Hafsa ji tayi tamkar ta ce "Mama ba zai dawo ba' Amma ta ce "To" ta ja bakinta ta tsuke.
Khalil juyi kawai yake a kan gadonsa, ya rasa in da zai sa kansa yaji daɗi, idan aka jima sai ya tashi zaune yayi tagumi ya rirriƙe kansa, idan ya gaji sai ya koma ya kwanta. Tunani daban daban a zuciyarsa, me yasa dangin Mahifin Hafsa suka kasance a haka? Tuna nasu dangin mahaifin yayi, yadda suke nuna musu ƙauna da soyayya, amma sam Mummy ba ta son alaƙar su da su, tabbas da sune suka tsinci kansu a halin da su Hafsa suka tsinta, ya san babu yadda za ayi, dangin mahaifinsu su wulaƙanta su haka.
Gaba daya bacci ya gagari idanun Khalil, saboda damuwa.
Washegari da safe ma haka ya tashi duk babu daɗi, dan haka ya kashe wayoyinsa, dan karma wani ya takura masa.
Har ƙarfe sha biyu na rana ba Khalil babu dalilinsa bai fito ba, balle ya karya kumallo.
Mummy ta kasa jurewa ta tafi sashin Khalil, abin mamaki ta ganshi a ƙudundune a kan gado. Da sauri ta ƙarasa tana kiran sunansa, tare da janye bargon. A hankali ya ware idanunsa a kan Mummy, sai da ta tsorata da yadda taga idanunsa sun yi jawur, jijiyoyin kansa duk sun kumbura.
"Khalil lafiyarka ƙalau kuwa?" A hankali ya gyara kwanciyarsa, ya tashi zaune yana sauke ajiyar zuciya.
"Magana nake maka fa, baka da lafiya ne?".
"Da ciwon kai na kwana ne"
"Amma shi ne baka gaya mini ba? Kalli yadda duk ka koma wani iri, kwanciyar ce zata yi maka magani? Tashi kayi wanka ka karya, muje in kai ka Asibiti".
Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Mummy ki bari ba sai naje Asibiti ba, zan warke".
"A'a ban yadda ba, tashi kayi wankan, sai in kira Aliyun ya zo gida ya dubaka" haka Khalil ya tashi ya nufi banɗaki, yana jan ƙafa kamar wanda yake maye.
Ko da Mummy ta koma ta tura Amina, taje ta gyarawa Khalil ɗaki ta kai masa Abinci.
Wasa-wasa kan Doctor Aliyu ya zo, wani irin zazzaɓi ya rufe Khalil, ga jiri da yake ɗibansa yana daga kwance.
Nan da nan kowa hankalinsa ya tashi a gidan, suka shiga damuwa Daddy da baya nan ma ya dawo gida, duk suka kewaye Khalil da Mama ta lallaɓo shi, ta dawo da shi falo ta bashi Abinci, shi ma da ƙyar ya ci ya ce ya ƙoshi.
A tambayoyin da Aliyu ya yi masa, ya fuskanci kamar wani abu ne a ransa yake damunsa, amma ganin Khalil na kakkaucewa ya Sanya ya ƙyaleshi, ya rubuta allurai da ruwa ya bayar aka sayo.
Ita Amina har mamaki abin yake bata, murƙusheshen ƙato kamar Khalil, amma dan yana zazzaɓi an kewaye shi, sai sannu suke masa, wanan na shafa kansa wannan na wannan, fuskokinsu duk damuwa.
Suna nan zaune aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, Amina ce ta tashi ta je ta buɗe, Abdul ta gani a tsaye.
Murmushi tayi masa tare da gaishe shi, ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Khalil na ciki ne? Na kira wayarsa a kashe, kuma na zo ɗakinsa tun ɗazu baya nan".
Amina ta ce "Shigo gashi nan bashi da lafiya"
"Subhanallah" shi ne abin da ya furta, ya shiga falon da sauri.
Mummy na tozali da Abdul ta haɗe rai, haka ma Fadila, suka wani tsuke fuska tamkar sun ga kashi.
Abdul ya sha jinin jikinsa, amma ya basar, ya ƙaraso ya gaida Daddy, Daddy ya amsa masa cikin sakin fuska, Mummy kuwa da ƙyar ta amsa masa, ya miƙawa doctor Aliyu hannu suka gaisa.
Abdul ya ce "Daddy meya sameshi haka? Shekaranjiya mun haɗu lafiyarsa ƙalau".
Daddy ya ce "Ka san shi Allah ba yadda ba ya juya lamuransa, yau dai ya tashi jiki babu daɗi, ni ban sani bama, na fita muna shirya wata seminar da za ayi da a Kano.
Khalil ya buɗe idonsa ya kalli inda Abdul yake.
Abdul ya ce "Khalil, sannu ya jikin"
Khalil baya son yin magana, dan haka ya yiwa Abdul alama da ya matso kusa da shi.
Abdul ya matsa kusa da Khalil yana masa sannu.
Ya kamo hannun Abdul, ya ɗora a goshinsa, a hankali ya furta "Abdul kaina kamar zai fashe".
"Sannu zai daina, ya a kai ka kwana babu lafiya baka gayawa kowa ba?"
"Ka bari kawai, ka zauna a nan kusa dani"
"To ina nan kusa da kai"
Haushi ya kama Mummy, Fadila kuwa kallon da Abdul ke mata ne, ya sa ta ja tsaki, tana harare harare.
Doctor Aliyu ya kalli Fadila ya ce "Autar Mummynta, ina abokin nan naki kuwa ya jikin nasa?"
"Ya warke" ta bashi amsa.
"Masha Allah, yana nan dai ƙalau ko? Ko shi ne sirikin Mummy ne?"
Haushi ne ya kama Fadila ta ce "Ban sani ba" ta miƙe ta bar falon, Mummy ta bita da kallo. Ta kalli Aliyu ta ce "Wai a kan wa kake magana ne?"
"Wani abokin karatun ta ta kawo mana Asibiti, bashi da lafiya yana fama da asma, shi ne nake tsokanarta".
Mummy ta ɗan gimtse baki, tana hura hanci.
Abdul yana nan zaune, har ruwan da aka sakawa Khalil ya ƙare, lokacin la'asar tayi, Khalil ya ce masallaci zai tafi.
Mummy ta ce "Ka haƙura kayi salla a gida, saboda jirin".
"A'a Mummy, zan bi Abdul" ba dan Mummy ta so ba, ta ƙyale shi.
Khalil ji yayi kamar ya gayawa Abdul, halin da ake ciki, amma yaji wannan sirrin Hafsa ne, idan ya bayyana bai yi mata adalci ba.
Suka je suka yi salla, Abdul ya ɗau Khalil zuwa wurin da suke zuwa shan fura, dan yaji daɗi, ya bawa Abdul labarin abin da dangin Mahaifin Hafsa suka yi musu, amma ya ɓoye masa batun fyaɗen nan.
Ya ɗora da cewa "Abdul, nayi mamakin jin yadda dangin mahaifinta suka yi musu haka, dangin Daddy nake tunawa, irin karamcinsu da soyayyarsu a garemu, danma Mummy ba ta son alaƙarmu da su".
Abdul ya ce "Khalil, lokaci yayi da yakamta ka cigaba da zumunci da dangin mahaifinka, ko da Mummy ba ta sani ba".
"Ka san wani abu, ina ganin zan shigar da ƙarar yayyane mahaifin Hafsa a ƙwato musu hakkinsu".
Abdul ya ce "A'a Khalil, bakomai ne ake amfani da dukiya ko ƙarfi wurin ƙwatarsa ba, ka mayar da hankali wurin mallakar yarinyar, da kyautata musu, su bar su da Allah kawai, ba abin da dukiyar zata amfana musu, dan ba guminsu bane a banza zasu kaɗar da ita".
"Abdul, ji nake tamkar in nemo yaron nan da ya kai Hafsa wurin 'yan sanda in kashe shi" a razane Abdul ya kalleshi ya ce "Kayi hauka ne kake zancen zaka kashe wani, me yayi maka?"
Taune lips ɗinsa na ƙasa yayi, yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin lugude, kansa na sarawa, yayi shiru bai kuma cewa komai ba.
Ba dan Hafsa na gudun kar Mama ta gane wani abu na faruwa ba, da ba zata fita wurin sana'ara ba ma, haka ta fita wurin sana'ar nan sama sama haka take, loka lokaci tana duba wayarta, ko zata ga kiran wayar Khalil ko saƙonsa, amma shiru ba ta gani ba. Hakan ya ƙara jefata cikin damuwa da karaya, ta saddaƙar Khalil ya rabu da ita kenan, ba zai iya ɗaukar ƙaddarar da Allah ya jarabceta ba. Gashi wani irin son Khalil take ji a ranta.
Khalil ya ɗan samu sauƙi, amma sam ya kasa kunna wayarsa, saboda gaba ɗaya kaɗaici yake so baya son damuwa sam, saboda ciwon kai da yake damunsa haryanzu, duk da tunanin Hafsa da tausayinta sune suka haifar masa da halin da ya tsinci kansa a ciki, yana son ya kirata a waya yaji ya take, amma ganin idan ya kirata bai san me zaice mata ba ya sanya ya fasa kiran nata.
Amina ta lura ƙarfe bakwai saura, Daddy ya ke shiryawa ya fita, ko karyawa ba ya yi.
Ƙarfe shida saura tana kitchen tana aiki, taji motsi a falo, dan haka ta fito falon, Daddy ta gani yayi shirin fita, sai zuba ƙamshi yake.
"Daddy ina kwana" ya ɗaga idonsa ya kalli Amina, dake tsaye tana kallonsa.
"Lafiya ƙalau" ya amsa mata.
"A kawo breakfast ne? Naga zaka fita baka karya ba".
"No, ina daf da makara, ba saina karya ba".
"Ok, bari in kawo maka mota, sai ka tafi da shi".
"Ok, shikenan" Amina ta koma kitchen, ta haɗo Abinci a cikin kwanuka ta saka a kwando, ta kaiwa Daddy mota.
Mama tana banɗaki tana wanka, Hafsa ta saka wayarta a gaba, tana ta gursheƙen kuka, sam ba ta san Mama ta fito daga wanka ba, sai ganin Mama tayi a tsaye a kanta. Da sauri ta wayance ta fara ƙoƙarin goge hawayen.
Mama ta ce "A'a, ai ba sai kin wayance ba, kin san adadin lokacin da na ɗauka atsaye a kanki? Ni dama a kwana biyun nan tun da muka dawo daga Asibiti naga kamar kina cikin damuwa, sai dai bana son takura miki ne, saboda ke idan baki ga dama ba mutum in zai mutu, ba zaki faɗa masa damuwarki ba. Yanzu gaya mini meye dalilin wannan kukan?".
"Mama bakomai".
"Bakomai Hafsa, ba zaki gaya mini ba kenan, me kike kallo ko kike jira a wayar da kika sata a gaba kina kallo?".
Bata san lokacin da ta sake rushewa da kuka ba, tare da faɗin "Mama Khalil".
Mama ta zauna kusa da ita ta ce "Meyafaru da Khalil ɗin?".
"Mama na gaya masa, be sake kirana ba, ina ga ba zai iya aurena a haka ba, Mama ba zan taɓa yafewa dangin mahaifina ba, sun mini mugun tabo, ba kowa zai yadda da ni ba"
Jikin Mama yayi sanyi ƙalau, ta rungomo Hafsa a jikinta, ta runtse idanunta hawayen tausayin Hafsa na tsiyaya daga idanunta.
"Taki ƙaddarar kenan Hafsa, a haka Allah zai baki wanda zai so ki a haka, ki daina kukan nan" ƙanƙame Mama Hafsa tayi, ta cigaba da rusa kuka tamkar wadda uwarta ta mutu.
Sai bayan la'asar Sannan Alhaji Ahmad ya dawo gida, da Amina ya fara tozali, tana kunna wa falo turaren wuta, tana sanye da doguwar rigar atamfa, ta ɗaura ɗankwalin atamfar.
"Sannu da zuwa" ta faɗa cikin girmamawa.
Ya amsa mata da cewa "Yauwa sannu, ga kwanukan ki can a mota, kije ki ɗauko na gode sosai".
"To Daddy, bari in gama kunna turaren zan ɗauko" ta cigaba da zaga falon, dan ko ina ya samu ƙamshin turaren, ya nufi sashinsa kai tsaye.
Sai da Khalil ya kwana uku, sannan ya samu ya rabu da wannan matsanancin ciwon kan, ya ɗan ji ƙwarin jikinsa, yaji ba abin da yake buri banda ya ga Hafsa.
Da magariba ya shirya cikin ƙanan kaya, ya sha turare bai ko tsaya yiwa Mummy sallama ba, saboda baya son ta tutsiye shi da tambayar ina za shi?.
Fadila na ɗakinta, tana game a waya, Mummy ta shigo tana ɗan tsareta da ido.
"Mummy ya dai?"
"Wace maganar na ji doctor Aliyu yana yi ɗazu?"
"Wace magana kenan Mummy?"
"Wa kika kai Asibiti?"
Fadila ta ce "Ba wani bane, wannan Yazeed ɗin ne da nake baki labari"
"To meye haɗinki da shi da zaki kai shi Asibiti? Nifa bana son jaye-jaye me haɗin kanwa da kuka?"
"Mummy, bani da wata alaƙa da shi, bani da wani zaɓin da ya wuce in kai shi Asibiti Mummy, na taimaka masa ne saboda..
"Saboda me? Wanene ɗinki shi?"
"Mummy matsalata da ke saurin ɗaukar zafi, ki tsaya ki saurareni Mummy, da ban yi hakan ba da tuni ina nan ina rama azumi sittin".
Mummy ta ce "Kamar yaya?"
Nan ta warwarewa Mummy abin da ya faru, ta ɗora da cewa "Shi ne saboda son gulma yake wani tambayata a gabanki, ni babu wata alaƙa tsakani na da Yazid".
"To ai shikenan, duk da haka a dai kiyaye, dan ba zan amince a kawaso mini gayyar tsiya cikin zuriya ba".
Fadila tayi murmushi ta ce "Mummy kenan, ki sha kuruminki, ai nima na san ni ba kalar talaka ba ce"
"Ƙwarai kuwa, ai mun tattauna da Hajiya Turai, akwai ƙaninta da ya taɓa ganin hotonki ya ce mata yana sonki, a U.K yake aiki, ina jiran ya dawo ne tukua kan in sanar da ke, sai kuma Allah ya kawo hira na ke gaya miki"
Yamutsa fuska Fadila ta yi, taƙi magana.
"Ya kika yi shiru?"
"To Mummy me zance? Ni dai in bai mini ba, ba ruwana da wata U.K"
"Ke dalla can, zai ma yi miki"
Fadila ta ɗan taɓe baki, sai dai kawai taga fuskar Yazeed na mata gizo. Har Mummy ta ƙarasa surutanta ta fita daga ɗakin, ba wani gane me take faɗa take ba.
Wayarta ta miƙa hannu ta ɗauko, ta ci karo da saƙon Kankiya, da yake addabarta da su. Wani uban tsaki ta ja, ta kashe wayar, maganar Yazeed na ƙoƙarin zamowa gaskiya, Sir Kankiya sonta yake yi.
Ɓangaren Hafsa kuwa, wunin da tayi koke koke ita ma ya sanya, ciwon kai ya kamata, dan ko wurin sana'ar ba ta fita ba, ta kasa cin abinci sai aikin rarrashi da Mama take yi.
Wayarta ce ta ɗan yi vibrating, ta miƙa hannu ta duba.
Message ne. "Ina waje"
Da sauri ta tashi zaune ta ce "Mama, Khalil ne wai yana waje"
Mama ta ce "Alhamdilillah" da sauri Hafsa ta tashi zata zari hijjabi.
"Haba ke kuwa, kije ki wanke wannan kumburarriyar fuskar ta ki, ki canza wasu kayan mana"
Cikin azama Hafsa ta je ta wanke fuskarta, jiki na rawa ta fara neman kayan da zata sauya.
Tausayin Hafsa ya kamata, tabbas Hafsa ta kamu da son Khalil sosai.
Ta ɗau dadduma ta nufi hanyar fita har da tuntuɓe.
Yana tsaye a jikin motarsa tana ganinsa ta tsaya cak, tana kallonsa.
"Shi ne kika shanya ni, da juyawa zan yi in koma ai" Kawai ta fashe da kuka.
Khalil ya ce "Subhanallah, Kuka kuma? Me nayi?"
Kuka take sosai, ta kasa cewa komai.
Ya karɓi sallayar hannunta, ya shimfiɗa a kan dakalin gidan, sannan ya zaunar da ita, ya fuskanceta "Am sorry, na tafi ban kuma kiranki ba, bani da lafiya ne, baki ga na rame ba?"
"Na zata ba zaka dawo ba" ta faɗa cikin kuka.
"Baby me zai hana ni dawowa?"
Magana take son yi, amma ta kasa.
Khalil ya gyara zamansa ya ƙara matsawa kusa da ita ya ce "Ya isa haka dan Allah, so kike ki kuma sani a damuwa? Ki daina Please" da ƙyar ya samu ta sassauta kukan da take ta ce "Na zata ka daina sona ba zaka dawo ba, saboda abin da na gaya maka, ko kana ganin ƙarya nake yi".
"Haba Hafsa, Wallahi ba haka bane, labarinki ya tsma zuciyata to the extent tun da na bar wurinki bani da lafiya, sai yau na samu sauƙi. Ina da ƙanwa mace, mai rawar kan tsiya da tsiwa, sai dai idan makamanciyar ƙaddara irin taki ta sameta wani ya muzanta ta yaƙi aurenta, ko ya ce ƙarya ne abin da ya sameta bai mini adalci ba, Saboda na fi kowa sanin halinta, duk rashin jinta, tana da kamae mutuncinta, kwatankwacin yadda kike.
Meyasa zan ƙi dawowa gareki, dan wani abu da kika rasa a sanadin ƙaddara wanda ko ni ɗin ne na karɓe shi, iya na lokaci ɗaya ne, kyawawan ɗabi'unki da halayarki da su zan rayu tsawon rayuwata?.
Matasa da yawa bama yiwa kanmu adalci, wurin zubar da mutunci da ƙimarmu kan mallakar abin da Allah ya halarta mana na aure. Sai dai akwai tsautsayi da ƙaddara, abin da kika gaya mini na yarda ɗari bisa ɗari, kuma ni banji cewar zan iya rabuwa da ke saboda haka ba, ina son ki Hafsa, kuma ni aurenki zan yi, dan Allah ki daina wannan kukan"
"Dan Allah haryanzu kana sona?" Tayi maganar tana kallonsa.
Yayi mata murmushi ya ce "Ina sonki mana, kema kina sona?"
Murmushi take haɗe da hawaye ta ce "Na zata ba zaka dawo ba ka daina sona, shiyasa nayi ta kuka"
"Allah sarki Sweetheart ɗina, ni damuwa ce ta sani rashin lafiya, na kashe wayoyina, amma kina zuciyata am sorry for not hearing from me"
Hannayenta biyu ta haɗa a fuskarta ta cigaba da kuka.
"Babu ya isa haka mana, ki daina kukan nan mana"
"Kukan farinciki nake ka ƙyaleni"
Murmushi yayi ya ce "Dole ki kuka, Allah ya azurta ki da ɗan shawalwalin saurayi kamata, ɗan beauty da ni"
Murmushi tayi, duk da akwai hawaye kwance a fuskarta.
"Yanzu gaya mini, kina sona?"
"Sai nayi shawara" ta faɗa tana dariya,