Showing 153001 words to 156000 words out of 296192 words
fa, ka kwantar da hankali ina lafiya sosai"
"Ba zan so wani abu ya sami lafiyarki ba, ni wa zai kula da ni?" Ganin yadda yayi maganar yana tsareta da idanunsa ya sanya ta kawar da kanta gefe.
"Meenal" ya kira sunanta.
Ta ɗaga ido ta kalleshi.
"Keep looking at me, akwai wani abu mai tasiri a gareni da yake fitowa daga idanunki"
Jan idanuwan nata tayi ta lunshe, ta sake buɗe su ta ce "Daddy, kaje wurin Khalil please"
"Ai kuma na fasa, sai naga ya naki jikin tukuna"
"Kar ka biye mini, na gama duk ayyukana, kaya kawai zan saka, sai ka saka a kaini".
"Na san abokin nan nasa da na tarar da su tare, zai kai shi Asibiti, shirya mu tafi kawai"
"A'a Daddy, ya fini buƙatarka"
"Ki shirya mu tafi" ya maimaita mata yana tsuke fuska.
Miƙewa tayi ta wuce ɗakinta, ta shiryo tsaf sannan ta sake fitowa, hannunta riƙe da kwalbar turaren da ya taɓa bata tana ɗan ɓata fuska.
Ya dubeta ya ce "Ya dai?"
"Turare na ne ya ƙare"
"Shikenan kin huta"
"Na huta kuma, wai haka zan tafi babu turare"
"Eh mana haka shi ne dai-dai" sai ta sake ɓata fuska, ta tsaya tana kallonsa.
Ya ce "Ya dai mu tafi mana"
"Ni ba zan tafi ina wari ba"
"Waye ya ce kina wari, ba kin yi wanka ba?"
"To idan nayi gumi fa?" Ta faɗa tana sake tura baki gaba.
Ya girgiza kai ya ce "Shikenan, kije ɗakina ki shafa nawa"
Ta juya ta nufi ɗakinsa, sai dai yadda ya tashi daga bacci, haka ya ɗan gyara gadon, sam bai gyaru ba, ga kayansa nan na bacci da ya fito daga wankan a kan gadon a ajiye, kan mudubinsa ma da ya yi kwalliya a nan ya bar komai har da wani comb da brush, da mayuka kala kala, ta tsaya ta fara da gyara masa gadon, ta kwashe kayan da ya fito da su daga wanka, ta ajiye su a toilet, ta fito ta gyara masa kan madubin, wani mai ta gani a tube, ta ɗauka tana dubawa man da ake shafawa gemu ne, dan ya ƙara taushi.
Dariya Amina tayi, ta ce "Su Daddy an girma amma ba a daina gayu ba" ta gama taɓe taɓenta, ta ɗaukar masa turarr ta dinga ɓarnarsa, har da fesawa a jikin jakarta. Sai da ta gama rashin jinta sannan ta fito.
Tana buɗe ƙofar ɗakin ya san ta yi masa aika aikar turaren, saboda yadda falon ya gauraye da ƙamshi.
Ta nufo shi tana "Mu tafi Daddy"
"A ina da ina kika fesa turaren nan ne?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Tsakani da Allah, kawai fesawa nayi"
"Ai na san fesawar kawai kika yi, kin san tsadar turaren nan kuwa? Ai shikenan Meenal, idan ya ƙare sai ki sai mini wani"
Dariya tayi ta ce "Duk in da naji ƙamshin turaren nan na san kaine a wurin" bai ce mata komai ba sai murmushi, ya tashi tsaye yana gyara zaman suit ɗinsa, ta kalli dogon gemunsa da yake ta ƙyalli, kamar wadda mintsuna ta ce "Daddy, kana shafa mai a gemunka dama?"
Nufota yayi gadan gadan, har sai da yaje daf da ita, ta tsaya cak tana wulƙita idanu, ya sunkuyo daidai fuskarta ya ce "Duba da kanki ki gani"
Duk da irin sassanyan ƙamshin turaren da take shi yake yi, amma sai taji wanda yake tashi a jikinsa na musamman ne, ta zama kamar gunki tana kawar da kai.
"Silly girl, da bana taje shi ina shafa masa mai da bai burgeki ba" da sauri ta ɗago ta kalleshi, ya kashe mata ido ɗaya, yayi gaba, ajiyar zuciya ta yi, tabi bayansa da sauri.
Suna tafe a mota, cikin rarrashi tana kuma yi masa nasiha a kan ya duba lamarin Khalil, amma yayi mata shiru sai zuba take.
'Daddy ka ƙi cewa komai fa"
"Ina jinki ai"
"Maganar tawa ba ta da muhimmanci kenan?"
"Ai ke hirar taki ce, wata ina ganewa wata kuma shirirtarki kawai ki ke yi"
A ranta ta ce 'Ai ba zan yi fushi ba, sai burina ya cika'
"To shikenan, ai wannan hirar ba ta shirita ba ce ba, a duba lamarin nan ranka ya daɗe, wasu lokutan ana ɗaukar soyayya wata aba ta shirita musamman ma gamu 'yan zamani, amma soyayya da daɗi aba ce mai tsayawa a rai"
Waiwayowa ya yi ya kalleta ya ce "Kin taɓa yi ne?"
"A'a ji nayi nima ana faɗa ai, kuma ina ji in ana karantawa a littafi, ai kai ka taɓa yi da daɗi ko?"
Kafin ya yi mata magana, wayarsa ta fara ringing ya kalli Amina ya ce "Remain silent, Gimbiya na kirana"
Wani haushi ne ya kama Amina, ta ce "Idan ka ɗaga sai nayi magana" tayi maganar very serious.
Kallonta yayi yaga da gaske take.
"Ina magana kike cewa sai kin yi magana?" shi ma yayi maganar so serious.
Ta mayar da kanta ga kallon window, ya ɗaga wayar ya sa a kunnensa.
"Hello dear, kin tashi ne?"
Amina na iya jiyo muryar Hajiya Zainab ta ce "Na tashi, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, ya Fadila kodayake mun yi waya da ita".
"Haka ne tana lafiya, sun kusa gama exams ma"
"Masha Allah, kina lafiya dai ko?"
"Lafiya lau dear, visa mu ta fito fa, ba zaka dawo muyi sallama ba, da Fadila sun gama exams zamu tafi"
"Ohh, yakamata in dawo in ganki muyi sallama kuwa, dole in tsayar da komai in dawo in ki my dear"
Amina ce ta jiyo ta kalleshi a fusace, gane yinƙurinta da yayi na zata yi Magana, ya sanya cikin hanzari ya janyota jikinsa, ya toshe mata baki.
Ware baki tayi zata yi masa ihu, amma ya kuma danneta a jikinsa, ya toshe mata baki, ta kasa motsi.
Wani Irin Bugu zuciyarsu take a tare, Hajiya Zainab na yi masa magana amma ya kasa amsa mata, saboda halin da suka shiga baki ɗaya.
(TOFA AKWAI JAGWAL FA🤣🤣🤣)
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
50
Lamo Amina tayi a jikinsa, tana cigaba da jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa, shiru yayi ya kasa magana, yana sauraren Hajiya Zainab.
"Hello, ya naji kayi shiru, kana jina kuwa?"
Da ƙyar ya iya harhaɗo kalaman da zai yi Magana da su ya ce "Lafiya lau"
"Amma ya naji muryarka ta sauya, ko akwai wani abu ne?"
"Bakomai, mu cigaba da magana ina jinki"
Ta ce "Nifa so nake da zarar mun dawo daga umara, kaje kayi maganar auren Khalil, dan ba zan bari ya auro mini ƙasƙantacciya a cikin zuri'ata ba"
"My zee, a bar wannan maganar zuwa ku dawo ɗin, sai muga yadda za ayi"
"To zaka zo ɗin kan mu tafi?"
"Gani nan dai, idan na samu chance zan dawo kan ku tafi in sha Allah"
"Shikenan, Allah ya sa ka zo na fara kewarka, zaman nan da kayi ka daɗe a gida, naji ina missing ɗinka"
Yayi murmushi ya ce "Bayan nace ki biyoni nan kin ƙi, kuma ma ai guduna kike kince na tsufa"
Dariya Hajiya Zainab tayi ta ce "Kai da ba zaka canza ba ko? Ko zaka dawo ne, am just missing You"
"Idan kika ce in dawo sai in dawo ai"
Mutsu mustu Amina ta dinga yi, tana son ƙwacewa dan hirar ta su tafi ƙarfin kunnenta, kuma ga hirar ta su wani irin baƙin ciki ta jefata a ciki, gaba ɗaya Amina ta rasa ƙwarin jikinta, dan ba ƙaramin riƙo yayi mata.
Kawai ta ware haƙoranta ta gasa masa cizo a hannunsa da ya toshe mata baki.
Rintse idanunsa yayi, saboda yadda zafin cizon ya ratsa shi, amma ya sake riƙeta yana, fesar da iskar bakinsa.
Hajiya Zainab ta ce "To ni dai ya maganar kuɗin, haryanzu baka turo mini ba"
Ya buɗe idonsa ya ce "Anjima zan saka miki in sha Allah"
"Wayyo Allah, na gode sweetheart, sai na jika"
Shi dai direba duk da ba jin hausa yake ba, mamakin Boss ɗin nasa yake yi, ya san shi mutum ne ba mai son hayaniya ba, mai matuƙar tsare gida, sai dai rana tsaka ya ganshi da wata 'ya da bai san alaƙarsu ba sai biye mata yake.
A hankali ya ajiye wayar, ya kalli Amina, da tayi wuƙi wuƙi kamar an kwashewa karya 'ya'ya.
Ya cire hannunsa daga bakinta, aikuwa da sauri ta tashi zaune daga jikinsa tana ɓata rai.
Ya kalleta ya ce "Meyasa kika cijeni?"
Hararsa tayi ta ce "To waye ya ce ka rungumeni?"
"Ba rungumeki ne ya sa kika cijeni ba, kishina kike saboda ina waya da matata, haushin hakan ha saki cizo na"
"Ni ina ruwana da wayarku?"
"Meenal" ya kira sunanta.
Ta ɗago idonta ta kalleshi ya ce "Meyasa kike kishina, kina sona ne?" Yayi maganar yana ƙura mata ido.
Hararsa tayi ta ce "Allah ya kiyaye, me zan yi da tsoho?"
"Tsoho yana da abin da zai yi da ke, kuma na kuma ganin ina waya da mata ta, kina haɗe rai za kiga abin da zan miki"
Haɗe rai tayi, ta kawar da kanta gefe, idanunta har sun yi ja, tana ta ƙoƙarin basarwa amma ta nemi ta kasa. Har suka isa wurin da zasu ajiyeta, ba wanda ya kuma cewa kowa komai, sai da zata sauka sannan ya ce "Ki kula zanje in ga Khalil in dawo"
"Kar ma ka dawo" ta faɗa cikin ƙunƙuni.
"Kar ma na dawo ko Meenal? Na gode" ba tayi zaton zai ji ba.
"Yi haƙuri ba haka nace ba"
"Idan ma hakan kika ce, yaya zan yi da ke?" Sai da ta sauka suka tafi, taga bai dace ta gaya masa haka ba, "Am sorry' ta furta a hankali ta nufi cikin hall ɗin.
Ko da Daddy ya kira Khalil, Khalil ya sanar masa yana gida, yaje ya ɗauke shi ya mayar da shi Asibiti, sai dai an samu cigaba sosai da sosai, jikin Khalil yayi sauƙi sai dai fuskarsa babu walwala sam.
Maganganun Amina ne suka dinga dawowa Daddy, ya ɗan ƙura wa Khalil ido sannan ya ce "Khalil"
"Na'am Daddy"
"Gaba ɗaya baka walwala, ka gaya mini meke damunka ne?"
"Bakomai Daddy, yanayin jikina ne kawai da bana jin daɗi, amma na ji sauƙi sosai Alhamdilillah"
"Khalil, ina son ka dinga sawa ranka salama a kan komai, ba kowane lokaci ne muke samun abin da muke so ba, wasu lokutan sai mun gama saka ranmu a kan abu, kawai sai Allah ya musanya mana da mafi allhairinsa, dan haka ka koyi bawa zuciyarka haƙuri a duk lokacin da ka rasa wani abu" Khalil ya jinjina masa kai alamar to, a ƙasan zuciyarsa kuwa damuwa ce fal, baya son Hafsa ta auri wani ba shi ba, ji yake ko ya roƙi Abdul ya aureta, idan ya so sai ya yi masa bayinin abin da ya faru da ita, ya san Abdul mutumin kirki ne, ya san ƙaddara ba zai cutar sa Hafsa ba, amma sai yayi tunanin idan shi ko kuma Hafsan wani daga cikinsu bai amince ba fa? Haka yayi shiru ya cigaba da laluben menene mafita.
Tun da al'amarin nan na ranar exams ɗin Kankiya ya faru, sai yau suka sake komawa makaranta domin suna da exams, a aji ta tarar da Yazid, amma sai taga ya yi mata kwarjini sosai da sosai, ba tare da tunanin komai ba ta isa wurin da yake.
"Sannu ya jiki kuma?" Ya ɗaga kansa ya kalleta ya ce "'Jiki Alhamdilillah, na ji sauƙi"
"Kaji sauƙi, ko kuma ka warke?"
"Da sauƙi dai" ya bata amsa yana ɗauke kansa daa gareta, saboda wani abu da yake fuzgarsa game da ita, idan har zai yi tozali da ita sai ya nemi ya rasa nutsuwarsa, yana matuƙar jinta a ransa, amma idan har ya na son ya zauna lafiya a makarantar nan, ya zama wajibi ya nisanceta, idan ba haka ba zai ta shan wahala ne a banza.
Ta ɗan jingina da jikin bencin da yake ta ce "Wannan karon da baka zuwa, akwai abubuwa da yawa da ban iya ba, kawai dai nayi karatu ne ina fatan Allah ya sa na tsallake".
"Just feel like you never knew me before, ki fuskanci karatun zaki iya ko babu ni"
"Kamar yaya kenan, ni bana gane irin wannan hausar da ake yi a dunƙule"
"Fadila, kar ki saka a kuma jefar mini da takarda, na riga na sanarwa da Kankiya babu ni babu ke, ban sani ba ko bayan Kankiya akwai wani malamin ma da yake sonki, kar yawan ganinmi tare ya kuma janyo mini wata matsalar, idan na rasa karatuna komai nawa zai koma baya ne"
Jiki a sanyaye ta ce "You mean i should leave?" Ya jinjina mata kai.
Miƙewa tayi tsam ta bar wurin, ji yayi kamar ya kirata, yana missing ɗinta sosai, daure zuciyarsa kawai yake yi, amma babu yadda ya iya, tun da ruwa ba sa'an kwando bane ba.
Ɓangaren Hafsa kuwa, Mama jiki na nema ya kuna rikicewa, saboda ganin halin da Hafsa ke ciki, duk da Hafsan na ƙoƙarin ɓoyewa, amma Mama ta kan gane wasu lokutan idan tayi kuka, wasu lokutan kuwa sai cikin dare take jin sheshsheƙar Hafsan tana kuka, Mama bata ga laifin Hafsa ba, saboda ta daɗe ba taga mutumin da Hafsan ta bawa yarda ɗari bisa ɗari kamar Khalil ba, zata iya wuni ba ta zauna ta yi hira sosai da Mama ba, sai abin da ba a rasa ba, saboda ɗabi'arta ce haka, amma da zarar Khalil ya kirata a waya, sai dai Maman ta dinga jiyo dariyarta, yana bi da ita a yadda take da halinta, yayi faɗi tashi sosai kan ya samu kanta.
Hafsa na iya ƙoƙarinta, dan kar Mama ta gane, amma yanayin ya kasa ɓoyuwa baki ɗaya, lokaci loka idan suka zauna, Mama na yiwa Hafsan nasiha, gami da rarrashinta, da bata shawarar ta dage da Addu'a.
Sai dai ita ma Maman dakewa kawai take yi, har zuciyarta tana son Auren Hafsa sa Khalil, tana jin yaron a ranta, yadda yake girmamata da yadda yake bawa Hafsan kulwa daa hausawa sun ce mai ɗa wawa, ya siye zuciyar Mama da soyayyar da yake wa 'yar ta, sai dai mahaifiyar Khalil ta rushe burin da suke da shi na son kasancewa da juna.
Khalil na kwance a gadon asibiti, ana cigaba da ƙara masa ruwa, Daddy kuma ya yi masa sallama ya tafi, ya rintse idanunsa, babu abin da yake hangowa, sai Hafsa a kusa da shi, ko muryarta yana ƙishirwar ya ji, zuciyarsa ta dinga raya masa ya koma Kano, ko ya samu ya ganta, amma yana matuƙar jin nauyin Maman Hafsa bisa ga abin da Mummy tayi musu, baya jin ko ido zai iya haɗawa da ita, ga furucin Hafsan ita ma da tayi.
Lumshe idanunsa yayi, yana tariyo al'amuran masu wuyat gushewa a zukatan masoya da ya faru tsakaninsa da Hafsan, abubuwan da suke burgeshi da ita, na kamewarta, miskilancinta murushinta da yawan tsokanarsa da ta kan yi, uwa uba kyauta da bashi Adduoi na tsari, da jaddada masa ya riƙe Addu'a.
"Am missing You so badly Hafsa" ya furta yana jan numfashi da ƙyar.
Babban abin da yake tsoro shi ne, kar ya koma Kano yaje gidansu Hafsan, wani ya gayawa Mummy ya ƙara janyo masa wani tashin hankalin.
Ya dafe kansa da yake yi masa wani irin ciwo kamar zai tsage.
Hafsa tana tsakar gida tana ta shara, Mama tayi baƙuwa wata maƙociyarsu da take layinsu Alawiyya, ta shigo sayen kuka da maggi ta tsaya tana ta zuba.
"Ni kuwa Maman Hafsa ina sirikinmu ne?"
Cikin rashin fahimta Mama ta ce "Wane sirikin kenan?"
"Wannan ɗin nan da yake zuwa wurin Hafsa mana mai mota, muna ta jira muji abin arziki ace ya fito, kar dai ace irin samarin shahon nan ne?"
Mama ta ce "A a, baya gari ne ba a nan yake nema ba"
Alawiyya ta ce "Au, ai na zata shima guduwa yayi, kin san samarin nan na zamani, da ance su fito suke guduwa dama wasu 'yan rage dare ne, ina tayi muku murna wallahi, Allah ya tabattar da Alkhairi".
Mama ta amsa da"Ameen"
Maimakon Alawiyya ta tafi, sai ga ɗora da cewa "Wallahi ku yi ta addu'a, Allah ya riƙe musu shi kuna kwa huta, kin san halin mufuncin 'yan unguwar nan, za a iya zagewa aje ace masa 'yar mace ce ba ta da uba, ba a taɓa ganin wani naku ya zo ba. Kwanaki zancen nan yayi ta yawo a unguwa, wani babban mutum ya saka direbansa ya biyota ya ga gidans, kan ya zo ya sa aka ɗan yi masa bincike a kanku, saboda Aurenta zai yi, amma aka samu munafukan da suka gaya masa wannan Magana, na san babu lallai ku san an yi, amma zance ya cika gari"
Mama ta ce "Aishikenan kowa yayi na gari kansa" Alawiyya ta gama soki burutsunta ta fita.
Hafsa ta duƙufa tana wanke-wanke, hawaye na ɗiga cikin ruwan wanke wankeen nata, tayi zurfi a cikin tunani, kawai taji an dafa kafaɗarta, ta ɗago ta kalli Mama da ke tsaye a kanta.
Mama ta durƙuso ta dafa ta ta ce "Dan Allah, ba danni ba Hafsa ki kwantar da hankalinki, ki daina wannan kukan, duk abin da yake rabonki ne, duk surutun mutane sai Allah ya kawo miki shi, kuma a jikina ina ji cewar Addu'ata ta karɓu a wurin ubangiji komai zai zo ƙarshe" ta gyaɗawa Mama kai tana ƙoƙarin cigaba da wanke kwanukan.
"Dan Allah ki daina kin ji Hafsana" mama tayi maganar a sigar rarrashi.
"Na daina Mama"
"Yauwa, Allah yayi miki albarka ya yanke mana wannan wahalar haka"
"Amin Mama" a gaggauce Hafsa ta gama wanke kwanukan, ta gyara wurin ta nufi banɗaki, ta shiga ta kulle ƙofar tayi kukanta mai isarta, sannan ta wanke fuskarta ta fito.
Sam Amina ba ta san Daddy ya zo ba, a wannan karon ma sun yi nasara, makarantarsu taje semi final both a debate da Quiz, sai murna suke yi ɗaukacin ɗaliban da malamansu.
Kamar yadda aka tsara aka yiwa su Amina shigar fulani na shuɗin saƙi, da kwalliya, wasu kuma shigar hausawa, suka fito suka yi presentation a kan Al'adu na fulani da Hausawa, da abubuwan burgewa game da Al'adun nasu. Ciki har da rawa irin ta Fulani.
Wani daga cikin manyan baƙin da aka gayyato, wani Christian mai babban muƙami, ya tashi yayi musu tafi tare da jawabin jinjina ga matasan yaran, har yake cewa Amina zai zo Kano a bashi Auren ba fulatana"
Cikin murmushi Amina ta ce "Zamu baka, bayan Auren bafaulatana har da saniya zamu haɗa maka, Auratayya da abota a tsakanin mabanbantan ƙabilu na ƙara kawo ƙauna da zaman lafiya da kuma cigaban tattalin arzikin ƙasa" tafi aka sake ɗauka a hall ɗin, Amina ta burge mutane sosai da sosai ba ga da tsoro sam idan ta fito gaban mutane, akwai confidence ga iya Magana