Showing 78001 words to 81000 words out of 296192 words

Chapter 27 - GABA DA GABANTA

a tunani, jefa ƙafarta kawai take a cikin falon, tana son ta lalubi ƙofar falon ta buɗe, ba tsammani tayi karo da wani abu, ware baki tayi za tai ihu, amma taji an rufe mata baki. Mutsu mutsu ta fara yi, zata ƙwace jiki ba ƙwari ya ce "Shhh Ahmad ne" yayi Maganar yana sakar mata baki.

"Waye Ahmad kuma?" Ta faɗa bakinta na rawa, duk da ta gane ƙamshin turarensa.
"Daddy" ya faɗa a hankali.

Amina ta dafe ƙirjinta ta ce "Wayyo Allah, na zata aljani ne Wallahi"

"Idan Aljanin ne shikenan, ba zaki addu'a ba sai ihu?"

"Ai wannan tunanin ana yinsa ne idan mutum yana cikin hayyacinsa" tayi maganar tare da ɗan ja da baya, saboda kusancin da ke tsakanin su.

Cikin duhun ya ce "Me kike yanzu baki bacci ba?"

"Baranda zani karatu"

"Ok, yayi kyau" ya furta ya raɓa ya bi gefen in da yake jin alamun tana tsaye.

Amina ta ƙarasa ta buɗe ƙofar, ta fita baranda, hasken lantarki ko ina, ta zauna ta bubbuɗe litatafanta, ta fara duddubawa.

Gani tayi an kunna wutar falon, haske ya gauraye falon.
Tashi Amina tayi ta leƙa falon, taga Alhaji Ahmad ne ke ta zagaya falon.

Ji yayi kamar ana kallonsa, dan haka ya waiwayo, sai ya ga Amina a tsaye tana kallonsa.
Amina ta ce "Jikin ne dai?"
Ya jinjina mata kai yana cigaba da zaga falon.
"Wai me ya sameka, naga kana ta zagayawa?" Tayi tambayar kanta tsaye.

"Suga na ne ya hau, da kuma jinina shima ya hau, ƙafafuwana ne suke zafi da cikina" ya samu kansa da bata amsa, ba tare da shi kansa ya san dalili ba.

Cikin tausayawa Amina ta ce "Allah sarki sannu, dama kana da suga amma komai ma kake ci, ba'a tsara maka Abincin da yakamata ka ci? Naga bakomai masu ciwom suke ci ba fa"
Daddy ya cigaba da aikin zagayensa ba tare da ya kuma cewa komai ba.

"Allah ya baka lafiya" ta faɗa tare da juyawa ta koma wurin karatunta.

Kusan mintuna talatin ta tashi ta kuma leƙawa, ta ganshi a zaune ya mimmiƙe ƙafafuwansa sai lanƙwasa yatsun ƙafarsa yake yi.

"Sannu Daddy, Allah ya baka lafiya" ya jiyo siriryar muryata a kunnensa.
Murmushi kawai ya yi bai amsa ba.

"Haryanzu ƙafar na maka zafi ne?" Ya jinjina mata kai alamar eh, tare da lumshe idanunsa, da ganin yadda yake gumi zaka san yana jin ciwon sosai.

Komawa tayi, mintuna kaɗan ta dawo ta ce "Daddy zo ga ruwa na zuba maka a bokiti, kazo ka sanya ƙafafuwan ko zasu daina"

"To zan zo" ya bata amsa ba tare da ya buɗe idonsa ba.

Ta koma ta cigaba da karatunta, harta fidda ran zai fito, sai gashi ya fito, ta ajiye masa kujerar zama, da bokiti ta zuba ruwa. Ya zauna a kan kujerar, ba tare da ya ce mata komai ba, ya janye jallabiyarsa, ya zura ƙafafuwan a cikin ruwan, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sanyin ruwa ke ratsa shi, yana samar masa da releif, tun daga ƙafafun nasa zuwa ga ilahirin gangar jikinsa.

Amina ta cigaba da rubuce-rubucenta,  a hankali yake samun releif daga zugin da ƙafarsa ke masa, ya buɗe idanunsa ya na kallon Amina, da take ta aikin karatunta. Shi dai Allahn da yayi shi ba mutum ne mai shiga sabgar mata ba, shi ko wasa da yara bai fiye yi ba, dan magana ma bata dame shi ba, amma har cikin ransa yake jin daɗin yadda take nuna damuwarta da shi.

"Naga kin kasa wannan, kawo mu gani" yayi Maganar yana kallon littafin gabanta
Ba musu ta miƙa masa littafin dake hannuta, tare da biron.

"Me aka yi miki kike kuka ɗazu?" Yayi tambayar yana kallon littafai da ke hannunsa.

"Wai ni?" Amina ta tambaye shi.

"A'a" ya bata amsa.

Shiru tayi ba ta bashi amsa ba, ta fara wasa da littafin gabanta.

A hankali yake rubutun cikin nutsuwa, mintuna kaɗan ya miƙa mata littafin.
Buɗe baki tayi tana kallonsa, "ya aka yi kayi mini, tun ɗazu nake fama na kasa"

Be ce mata komai ba, ya cigaba da kallonta, ita kuma ta cigaba da bin littafin da kallo tana murmushi.

"Wane course zaki karanta, idan kika kammala sakandare?"

"Ni sakandare kawai nake son nayi, Baba bashi da halin da zai biya mini jami'a".

"Wane course zaki karanta a jami'a idan kin kammala sakandare" ya maimaita mata.

"Bani da zaɓi"

"Meyasa?" Ya faɗa a taƙaice.

"To idan na sakawa raina ga abin da nake so, ai babu me biya mini, shiyasa ni bana tunanin wata jami'a".

"Zaki iya medicine?" Yayi Maganar yana kallonta.

Ƙwalalo ido Amina tayi ta ce "Taɓ, korata za a ayi, bani da ƙoƙari"

"Kina wahal dani, bana son doguwar magana, ke in an tambayeki sai kin yi amfani da different formulas kafin ki amsa".

"To yi haƙuri"

Ya sunkuyo da fuskarsa kunnenta, wanda hakan ya haddasa mata faɗuwar gaba "Gaya mini, me zaki karanta?".

"Kome Allah ya sa na samu, ina so". Ta amsa tana janye jikinta gefe.

"Idan kin yanke shawara ki gaya mini, zan ga abinda zan iya yi a kai"

"You mean zaka barni in cigaba da karatu a gidan nan, naji ance ɗawainiyar jami'a ba kamar na sakandare bane"

"In dai karatun bai fi ƙarfin talaka kamar ni ba, zan yi wani abu a kai Insha Allah, kina da ƙwaƙwalwa bai kamata a barta haka ba ki tsaya iya Sakandire ba"

Daddy ji yake tamkar suka ɗai ne a duniyar, dare ya tsala, ko tunanin wani ya zo wurin baya yi.

Hawaye ne ya wanke fuskar Amina, tana kallon Alhaji Ahmad, amma ta kasa Magana.

"Komai aka yi miki sai kuka?"

"Na gode sosai Daddy, kana da kirki sosai ba kamar.." Sai kuma tayi shiru.

"Ba kamar wa ba? Hmm ko kusa karki bari ta ji kin faɗi wani mummunan abu a kanta, kin san abin da zata iya yi miki, let's keep this as our secret, kar ki gayawa kowa sirrinmu ne, ciki har da Baba, idan kuwa kika bari zancen ya fito, to abinda ya biyo baya ba ruwana, dan ba lallai Zainab ta bari"
Amina ta ɗan kalleshi, yana da zuciyar taimako, amma yana shakkar matarsa.

"Insha Allah ba zan gayawa kowa ba, na rufe bakina, Allah ya baka abin da kake so duniya da lahira"

"Ameen" ya amsa tare da jingina a kujera.

Bacci ne ya ɗauke shi, ƙafafuwansa na cikin bokitin ruwa, Amina ma bacci ne ya kwasheta, ta kife kanta a gefen kujerar ta hau bacci.


(ALLAH YA SA HAJIYA ZAINAB TA ZO TA KAMA KU🥴)
Ayshercool
08081012143GABA DA GABANTA

AISHA ADAM AYSHERCOOL

26-27




Tsananin sanyin da yaji yana ratsa shi ne ya sanya ya buɗe idanunsa, gari ya ƙara yin duhu baƙi ƙirin, ba kajin motsin komai sai haushin karnuka a waje, ya kalli in da Amina ta dunƙule a wuri ɗaya, ta jingina da kujerar da yake kai tana bacci, da alama tana jin sanyi sosai, amma bacci ne a kanta.
A hankali ya zare ƙafafuwansa daga cikin bokitin ruwan nan, ya tattara litattafanta da ta baza a wurin, bironta ya ɗauka yana shafa mata a fuska, yamutsa fuska ta yi, ta kai hannu ta kori abin da yake bin fuskar tata, amma ya kuma shafa mata.
"Ki tashi kije ki kwanta"
Amina ji take tamkar a kan katifarta take, dan haka tayi wani irin juyi tana ƙoƙarin faɗawa jikinsa ta cigaba da baccinta.
Cike da rashin sabo, da yi mata kallon 'yar cikinsa, ya sanya hannayensa ya ɗagata ya tsayar da ita a kan ƙafafuwanta, ya ɗan girgizata ya ce "Open your eyes" a hankali take buɗe su tana lumshewa, tamkar zata faɗi. Ya danƙamata litattafanta, ya buɗe musu ƙofar falon, ya kunna fitilar wayarsa, ya rakata har bakin part ɗinsu, sannan ya wuce sashen Hajiya Zainab.
Ya tarar da ita ta rashe, sai baccinta take hankali kwance. Ya lallaɓa ya hau kan gadon, cikin ikon Allah, ya rage jin zafin da tafin ƙafarsa ke yi masa sosai.
Ya janyo bargo, ya rufa musu shi da Mummy, ya kwantar da kansa a wuyanta, yana shaƙar ƙamshin turaren da take fitarwa mai daɗin gaske a hancinsa. Tuna halinta ne ya sanya shi sassauta rungumar da yayi mata, dan yanzu sai ta farka ta hau shi da masifa.

Amina bata farka ba sai asuba, dan sai da ta kusa makara, sai da ta farka ta ganta a tsakar ɗaki a kan litattafanta tana bacci, sannan ta tuno abubuwan da suka faru jiya da daddare, gaba ɗaya ta ɗauka mafarki take yi, a hankali ta tashi ta shiga toilet, tayi alwala ta dawo tayi sallar auba.
Bayan ta idar, ko karatun Alqur'ani da azkar ba ta samu yi ba, saboda kanta har wani nauyi yake yi mata, ta haye kan katifarta ta hau aikin bacci.
Hajara tamkar ta tashi Amina, ganin har ƙarfe takwas bata fito ba, sai kuma ta fasa, saboda itama ko ƙarfe nawa zata kai ba ta fito ba, Amina ba ta damuwa balle ta taso ta, aikinta kawai take yi, dan haka taga idan ta ce sai Amina ta taso, to tabbas bata kyauta ba.
  Wasa² har goma saura, Amina baccinta take yi, A lokacin Alhaji Ahmad ya fito karyawa, tare da Hajiya Zainab. Ya tarar da Hajara na ta shirya Abinci a dining ɗin, haka nan yaji yana son ganin Amina, dan galibi ita yake gani tana shirya Abinci, amma har Hajiya Zainab ta zuba masa Abinci, yana son ganin ta ina zai ga Amina, kamar ba raba dare suka yi tare ba jiya.
Ɗanɗanon Abincin kawai ya ci, yaji ya banbanta da nata, ya kalli in da Hajara ke mopping ya ce "Ina wannan Yarinyar take?"

Hajara ta kalleshi ta ce. "Wace yarinyar ranka ya daɗe?"

" Wadda kuke aiki tare?"

"Bata tashi ba" Hajara ta faɗa tana sunkuyar da kai.

"Yau ba taje makaranta ba ne?"

"Ai sun yi hutu" ta bashi amsa, bai ce komai ba ya cigaba da cin Abincin da a bakinsa na Amina yafi daɗi.

Hajiya Zainab ta kalleshi ta ce "Kai meye damuwarka da taje Makaranta ko ba taje ba?".

"Saboda kuɗina nake biya, dan haka yakamata in bibiya"

"Shiyasa tun farko ni ban so ka kaita makarantar kuɗi ba, sai a kaita ta irinsu, amma ka kaita cikin yaran da ba sa'aninta ba a fannin rayuwa da arziki"
Alhaji Ahmad yayi mata shiru ya cigaba da cin Abincinsa.



Ƙarfe goma saura, gaba ɗaya ɗalibai sun tattara hankalinsu a kan malamin da yake tsaye yana kaiwa yana komowa kamar mazari, a ajin yana gabatar da darasi, sai ga Yazid a wahale, kamar an koro shi, cike da fargaba ya fara yinƙurin shiga ajin.

"Hey stop their, ko ɗakin babarka idan zaka shiga sai ka nemi izini, balle aji" cewar malamin da yake yiwa Yazid kallon banza.

"Am sorry sir" ya faɗa cikin ladabi.
Gaba ɗaya ajin suka yi shiru, suka mayar da hankalinsu kan Yazid.

"Yanzu ne lokacin da yakamata ka zo aji? Ni in baro gidana tun bakwai takwas tayi mini a nan, amma ka zo yanzu kuma kai tsaye ka ce zaka shigo mini aji?"

"Ayi mini afuwa malam, insha Allah ba zan sake ba"

"Sorry for yourself malam, ɓace mini daga nan"

Yazid ya yunƙura zai kuma magana, amma malamin ya buga masa tsawa ya kore shi.

Duk iya wulaƙanta mutum da Fadila ta ƙware a kai, taji babu daɗi yadda malamin ya kyari Yazid ya koreshi, ga shi 'yan aji gaba ɗaya sun zuba masa ido, duk da Yazid mai sa'a ne a wasu lokutan, kuma mutum mai haƙuri da ladabi, amma wasu lokutan yana yawan shiga komar malamai su wulaƙanta shi. Duk da Yazid ya bar ajin, hakan bai hana malamin cigaba da ƙananan maganganu, a kan Yazid ba.

Bayan fitar malamin daga ajin, Yazid ya shigo ya samu wuri ya zauna, ba tare da ya kalli kowa ko ya kula wani ba.

"Kowa ya tabattar ya mallaki littafin da Sir Bello ya ce a saya, dan da alama wani abun yake shirya mana a kan littafin nan, zai iya kada mutum idan ba shi da shi a jarrabawa, dubu uku ne, ga takadda nan ta na zagawa, duk mai so ya rubuta sunansa, na bada aron kuɗina naje kasuwa na sayo mana, duk mai so sai ya bada kuɗinsa in bashi" Cewar Captain dake tsaye a gaban ajin, yana bayani daki-daki kamar me koyar da karatu.
Tana hangen Yazid daga in da take zaune, kamar mara lafiya, sai ya kifa kansa a kan benci, sai kuma ya tashi yana ɗan lumshe idanunsa yana buɗewa, idanun duk sun yi ja, sai tayi tunanin ko duk dan saboda abin da lecturer yayi masa ne.

Aka miƙawa Yazid takarda, ya rubuta sunansa in zai sai littafi, amma ya girgiza kansa, ya mayar da kansa ya kifa kamar yadda yake da farko.

Da takardar ta zo kan Fadila, sai ta sayi kwafi biyu a take, ɗaya nata ɗaya na Yazid, amma tana jinjina yadda zata bashi littafin, dan bata son yawan shiga sabgarsa.
Tana nan zaune taga ya tashi ya fita, ita ma ta tashi ta bi bayansa, tana biye da shi, ba tare da ya sani ba, taga ya shiga wani aji da babu kowa, 'yan ajin suna wurin excursion, mutanen da ke ajin 'yan tsirari ne, wasu na cin abinci wasu na abin da ya damesu.
Wuri ya samu can ƙarshen ajin, ya je ya samu wuri ya zauna ya kifa kansa.
Ta tsaya daga bakin ƙofa tana saƙawa da warwarewa, daga bisani ta yanke shawarar shiga.
Har taje inda yake bai ɗago ba, ta saka hannu ta ɗan daddaki ka bencin da yake kai. A hankali ya ɗago ya kalleta, idanunsa sun yi jawur, ta kalli ƙafarsa tayi futu futu, kamar wanda yayi tafiya a sahara.
Sauke mask ɗin fuskarsa yayi, tare da sakar mata murmushin ƙarfin hali "Ya aka yi kika san ina nan?"

Ɗan taɓe baki tayi, ta saka hannu a jakarta, ta ɗauko littafin da ta saya masa da handout ta ajiye masa "Gashi nan, kuma ya rarraba group a aji, ya bada assignment za'a yi presentation next week in Allah ya kaimu, na saka sunanka, sai kaje ka dudduba handout ɗin"
Zuba mata idanunsa yayi gaba ɗaya amma ya kasa magana, sai kallonta kawai da yake yi.
"Magana fa nake maka, amma ka zuba mini ido".
A hankali ya ce "Yi haƙuri zan yi magana, numfashina ne yayi mini nauyi"
A ɗan tsorace ta kalleshi "Jikin ne?"
Lumshe idanunsa yayi, ina ma yana da damar gayamata abin da yake damunsa, rabonsa da Abinci tun kunun jiya da safe, Ulcer ta riƙe masa ciki da ƙirji har bayansa, haka ya lallaɓa ya taso ya taho Makaranta da wuri, saboda saurin da yake yi, yaji numfashinsa yana isa huhunsa da ƙyar, a wahale ya ƙaraso makarantar.

"Yazid" ta kira sunansa, karo na farko da yaji sunansa a harshen Fadila, wanda kiran sunan nasa ba ƙaramin tasiri yayi a zuciyarsa ba, ya haifar masa da wata nustuwa ta mussaman ba.

"Kaje Asibiti ne?"

"Eh na sha magani" ya bata amsa da ƙyar, dan baya son yin ƙarya ko kaɗan.

Ya jingina da teburin, ya lumshe idanunsa, ita kuma ta tsaya a tsaye, ita bata zauna ba ita bata tafi ba tana kallonsa.

Kamar wadda aka yiwa dole, ita a lallai bata damu da shi ba ta ce "Ko zaka tafi gida ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Zan ji sauƙi yanzu insha Allah, ganinki ɗin nan ma kawai ya sanya mini nutsuwa da jin na warke" tsuke fuska tayi ta harare shi, tare da ɗan hura hanci.

"Allah ya sawwaƙe, ni na tafi" ta juya ta nufi hanyar ficewa, ta bar masa handout ɗin da littafin ya zubawa bayanta ido, har ta bar ajin.


Ɓangaren Amina kuwa, bayan tayi wanka ta nemi abin da za ta ci taci, bayan ta tabattar da an kaiwa Baba nasa Abincin, ta koma ɗakinta ta ɗora da rubutun Alqur'ani da take yi.
Sai wajen azahar sannan Amina ta fito, ta haɗa wanke wanke tayi, tare da gyara duk in da aka ɓata, duk da Hajara taji haushin yadda yau Amina taƙi kataɓus ta sha baccinta, haka ta jure ta danne fushinta, saboda ita ma Aminan ba ta mata ƙorafi.
  Yau Alhaji Ahmad a gida ya wuni, sai ƙarfe huɗu sannan ya shirya zai fita, yau ba da Zakiru direba zai fita ba, shikaɗai zai fita, ya shiga motar, yana ƙoƙarin kunnawa, ya hango Amina a wurin Baba, riƙe da littafi, tana ta aikin nata na surutu, tana yi tana kallon littafin hannunta, Baba kuma yana ta ɓare gyaɗa yana miƙa mata, tana karɓa tana ci.
Ya ɗan jima a zaune a cikin motar yana kallonsu, gwanin sha'awa, ita 'ya mace duk in da Allah ya baka ita, ya baka Sarauniya ko da kuwa kai ba sarkin bane, Alhaji Ahmad yana son yaga ana tattala mace,baya son ya gansu a wulaƙance, shiyasa yake matuƙar ji da Fadila, shi namji duk in da yake zai iya kula da kansa, amma mace tana buƙatar kafaɗar da zata jingina.
Sai karɓe gyaɗa take daga hannun Baba tana ci, tana nunawa Baba littafinta, duk da Baba mutumin karkara ne, kuma ba wanda yayi ilimin zamani ba, amma wasu lokutan yadda yake gudanar da rayuwarsa a waye, ba girman kai ba hayaniya.
A hankali ya fara jan motar, zuwa wurin gate, daidai in da suke ya tsaya da motar, Baba ya taso da sauri, ya tsaya jikin motar ya risuna yana gaida Alhaji Ahmad, Ya amsawa Baba cikin sakin fuska, Amina ta wani basar, kamar bata san da wanzuwarsa a wurin ba.
"Aminatu ina wuni" Alhaji Ahmad ya faɗa lokacin da ta ɗago suka haɗa ido, tana ƙoƙarin mazewa ta kau da kanta.

Baba ya ce "Ja'ira ke wace irin Yarinya ce Uwata, baki iya gaisuwa ba?"

"Yi haƙuri, ina wuni?" Ta faɗa a kunyace.

"Ƙyaleta malam Hassan, tun da bata gaisheni ba, ai gara ni in gaisheta, tawa gaisuwar zaki amsa"
Amina tayi shiru cike da kunya, dan ta san bata kyauta ba sam.

"Zo" yayi Maganar yana kallonta.

Ta tashi daga kan bencin, ta matsa jikin motar.

"Meyasa baki je lesson ba yau?"

"A makarantar aka ce mu huta yau" ta bashi amsa tana kallon ƙasa.

"Kina gane karatun dai ko?" Ta ɗaga kai alamar eh.

Alhaji Ahmad ya kalli Baba ya ce "Buɗe mini gate ɗin"
Baba ya amsa da to, ya tafi buɗe gate.

Ya sake mayar da dubansa gareta ya ce "Me zaku dafa yau da daddare?"

"Hajiya ta ce, a dafa kuskus da miyar ganye" ta bashi amsa tana kallon ƙasa

Alhaji Ahmad ya ce "Likita ya sanya mini ƙa'idoji, saboda sugar na da ya hau, ki dafa mini faten dankalin turawa, da alayyahu, zan yi dinner da shi, yau zaki karatun dare ne?"

"Eh insha Allah"

"Idan na dawo, zan miki magana ki kawo mini"

Ta jinjina

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login