Showing 243001 words to 246000 words out of 296192 words
ina duhu.
Daddy ya kalleta ya ce "Kwaso akwatunan naki".
Cikin mamaki take bin Daddy da kallo, tare da fatan ba a nan zai barta ba.
Ta kwaso akwatin tana rarraba ido, da jiran ganin me Daddy zai yi.
Kai tsaye Daddy ya nufi ƙofar gidan,
Gidan sai ƙamshin sabon fenti yake.
Wayarsa ya ɗauko, ya ɗan danna ya kara a kunnensa, ya ce "Gamu mun zo".
Mintuna kaɗan sai ga wani ya fito,tana jiyowa wa zata gani? Yazid ne ya fito daga cikin gidan, cikin shadda ash riga da wando yayi kyau sosai. Mamakine ya hana Fadila magana sai kallon Yazid da take yi.
Yazid ya durƙusa har ƙasa, ya gaida Daddy.
Daddy ya amsa sannan ya ce "gamu mun zo".
Yazid ya ce "Bismillah ku shigo" wani irin ƙuntataccen tsakar gida ne, bai wuce kayi taku biyar ba, zaka ƙure shi. Yazid yayi musu jagora wani ɗan mitsitsin falo.
Daddy ya kalli Yazid ya ce "To Alhamdilillah, Malam Yazid ga matarka nan na kawo maka" saroro Fadila tayi ta kasa gane kan maganar da Daddy yake yi.
Daddy ya kalleta ya ce "Ke kuma ga mijinki nan, na ɗaura miki aure da Yazid, bisa gaza cika sharaɗinmu da kika yi, kuma sai da na bincika na ga ya dace da rayuwarki. Idan kin ga dama ki zauna kiyi masa biyayya idan kin ga dama kuma ki bijire masa. Idan kika sake kika taka mini gida ba tare da na neme ki ba, ban yafe miki, idan kika bari Yazid ya kawo mini ƙararki da kina saɓa masa sai na baki mamaki, kiyi masa biyayya kamar yadda kike mini. Yazid ban yadda ka bata waya ba, kar ta kira kowa sai idan ni na neme ta. Idan kin ga dama ki zauna ki riƙe aurenki, in kin ga dama kuma kiyi masa irin halin da ki ka tashi ki ka ga ana yi a gidanku".
A ruɗe ta tashi tana kallon Daddy cikin kuka ta ce 'Daddy, meysa zaka mini auren dole ka kawoni nan, wallahi ba zan iya rayuwa a nan ba, bana son shi wallahi, dan Allah Daddy ka rufa mini asiri".
Daddy ya ce "Fadila kema 'ya ce kamar kowa, dole ki cirewa kanki cewar ke kinfi ƙarfin wani, kuma ki sani ba zan miki zaɓin tunmun dare ba, kamar yadda kuka yi ke da mahaifiyarki da farko ba, ga sadakin nan naira dubu talatin" ya ajiye mata a kan ledar ɗakin da ke falon, da ko kukeru babu sai guda ɗaya.
Fadila ta sake fashewa da kuka, ta yinƙura zata bi Daddy, amma Daddy ya daka mata tsawa, wanda sai da ta razana. A rayuwarta bata tunanin Daddy ya taɓa yi mata irinta.
Daddy ya kalli Yazid ya ce "Allah ya sanya muku albarka" Daddy yayi gaba ya fice, Fadila ta zauna a ƙasa ta dinga wani irin kuka kamar zata shiɗe.
Yazid kallonta yake yi, shi kansa ya san wannan al_amari za a sha gwagwarmaya, sai dai ya san duk abin da ya faru, wani iko ne da tsari na Ubangiji, dan yadda abubuwan suka wakana har ya mallaki Fadila, akwai mamaki.
Cikin tausayawa ya nufi in da Fadila take, ya kwantar da muryarsa ya ce "Dan Allah Fadila kiyi haƙuri, ki Kwantar da hankalinki"
"Dalla rufe mini baki, banza kawai mara imani, wallahi bana ƙaunarka Yazid kuma ba zan zauna a wannan matsiyacin gidan ba, sai na koma gidanmu ba zan zauna a wannan ƙuntatattacen gidan ba"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, naji na kuma yadda, amma dan Allah kiyi haƙuri, kinga dare ne yanzu, ga abinci in zubo miki ki ci?"
"Ba zan ci ba, kana tunanin nayi maka kala da wadda zata karɓi wani abu daga hannunka?".
Miƙewa tayi ta nufi hanyar fita tana kuka, amma Yazid ya miƙe cikin zafin nama, ya sha gabanta ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri ki zauna, da safe in Allah ya kaimu sai mu san abin yi, kinga baki san kan unguwar nan ba, zaki iya ɓata"
Zubewa Fadila tayi a ƙasa ta cigaba da gunjin kuka, Yazid yaje ya kulle ƙofar gidan, ya dawo ya kalleta ya ce "Fadila kin yi salla ko zaki yi? Ki zo na nuna miki in da zaki kwanta"
"Dalla kaga malam ka rabu da ni, ka fita sabgata kan na yi maka rashin mutunci" haka Yazid ya ƙyaleta, ta dinga kuka haka ya zuba mata ido.
Ƙarshe yaje yayi alwala, ya zo ya tada salla, yana kallonta, ta gaji da kukan, ta jingina da akwatunanta, ta yi bacci.
A hankali Yazid ya tashi, ya shiga ɗan ƙaramin bedroom ɗin da ke ɗauke da makekiyar katifa, sak madubi da sip mai biyu, ya ɗauko wani ƙaton bargo, sabo fil ya zo ya lulluɓeta da shi, ya kunna maganin sauro ya koma gefe ya kwanta yana kallon in da take kwance tana bacci tausayinta ya mamaye zuciyarsa tare da tunanin yadda aka yi ya auri Fadila.
Hajiya Zainab kuwa tun da ta dawo, bata bi ta kan komai ba, ta shiga sashinta, tana zuwa ta rage kayan jikinta, ta shiga tayi wanka. Ta dawo falo cikin bada umarni, ta kira Hajara ta sanya ta kawo mata abinci.
Amina kallon Hajiya Zainab kawai take yi, da bata san meke faruwa ba sai auna Abinci take yi a cikinta, tsarguwa tayi da kallon da Amina ke yi mata tayi.
"To mayya, kurwata tafi ƙarfin ki munafuka"
Amina tayi wani irin murmushi ta ce "Ko mayyace ni, bana ci irin kurwarki ba, in ci masifa da jaraba".
"Ai shiyasa nake sake nanata miki, banza 'yar ƙauye".
"Eh na ji na gode sosai, 'yar birni". Ta ƙarasa maganar tana cigaba da yiwa Hajiya Zainab dariya.
Hajiya Zainab bata tashi farga da cewar Fadila bata dawo gida ba, sai magariba.
Sashin Fadilan ta nufa, ta duba amma bata ga Fadila ba.
Ta dawo falo ta ɗau wayarta, ta kira Fadila amma wayarta ta shiga ba a ɗagawa.
Tun tana kiran wayar tana jiran Fadila ta amsa, har ta fara ƙosawa tare da mitar ina Fadila ta ajiye waya bata ɗagawa kuma babu wanda ya san in da ta tafi.
Wasa² har isha'i babu Fadila babu dalilinta, nan hankalinta ya sake tashi, ta kira wayar Yusra ko Yusran ta san in da Fadila take, amma ta ce rabonta da Fadila tun shekaranjiya a online.
Hajiya Zainab fa ta diririce, ta shiga kiran Alhaji Ahmad, amma shima baya ɗaga wayar.
Wajen ƙarfe tara na dare da rabi na dare, sai ga Daddy ya dawo. Sai dai Hajiya Zainab bata san ya dawo ɗin ba.
Amina na ganin Daddy tayi murmushi sannan ta ce "Yallaɓai, ya aka yi ne? Sannu da zuwa".
Daddy ya ce "Alhamdilillah, na kaita sai dai tana ta bori".
Amina ta ce "Bakomai, zata saba ne, ni nayi imani da Allah tana son sa, komai zai zama tarihi in sha Allah, ka kwantar da hankalinka"
Daddy yayi murmushi ya ce "Dama ban ɗaga hankalina ba, na yarda da nagartar yaron".
Hajiya Zainab ce ta banko musu cikin bedroom tana zare ido.
Ya kalleta ya ce "Lafiya?"
"Ai dole ka tambayeni lafiya mana? Tun da baka damu da idan ka dawo ka neme ni ko 'yar ka ba?"
"Meyafaru?"
"Fadila. Bata dawo ba na kira wayarta tana ringing bata ɗagawa, na kiraka a waya amma ka share baka ɗaga ba".
Daddy ya ce "Wayarce a cikin mota, batun Fadila kuma kar ki damu, ki kwantar da hankalinki".
Cikin rashin Fahimta ta ce 'Kamar yaya in kwantar da hankalina ban san in da 'ya ta take ba?"
"Ai na ce ki kwantar da hankalinki, ni na san in da take kar ki damu"
"To ka gaya mini tana ina?"
"Tana nan lafiya" yayi maganar yana cire babbar rigarsa.
"Wai ban gane tana lafiya ba, ina ka kai mini 'ya ta?"
"In da ya dace, kuma bani wuri ina son na huta" ya bata amsa.
"Wallahi ba in da zani, sai ka gaya mini in da ka kaita".
Ya ce "Aikuwa sai ki ta tsayuwa"
Ya rage kayan jikinsa ya shige banɗaki ya barta.
Amina ta kalleta ta ce 'Dan Allah ki ɗan bani wuri, zan cire kaya ina son na kwanta".
A fusace ta ce 'Idan a kan ki nake sai ki sauke ni, tun da wurinki na zo"
Amina tayi mata shiru, ta wuce ta ɗaura towel ta cire kayan jikinta, daga ita sai towel tabi bayan Daddy zuwa toilet.
Buɗe baki Hajiya Zainab tayi, tana ganin salon barikanci da iskanci a wurin Amina, sun ma mayar da ita wata mara amfani a wurin.
Zuciya ce ta kwasheta ta je ƙofar banɗakin tana duka kamar zata ɓalla ƙofar.
"Ka fito ka gaya mini in da 'ya ta take, macuci wanda bai san darajar kansa ba" ta dinga dukan ƙofar iya ƙarfinta.
Banza suka yi mata, har ta gaji da bugun, ta koma gefe ta tsaya tana huci.
Sun ɗauka ta fita suka fito tare shi da Amina, suka tarar da ita a tsaya tana ta kumbura wuya.
Tana ganin sun fito, ta kuma kallon Alhaji Ahmad ta ce "Nace ka gaya mini in da ka kai mini 'ya ta"
Daddy ya ce "Zainab, nace kiyi haƙuri ki Kwantar da hankalinki, amma ki sani Fadla tana cikin kwanciyar hankali, da sannu zaki san in da take"
Amina kuwa wucewa tayi gaban mudubi tayi zamanta, ta fara shafa manta.
Tana jin yadda suka cigaba da fafatawa, tayi kamar ba ta san suna wurin ba, suka gama tashin hankalin su, Hajiya Zainab ta fice daga ɗakin.
Daddy ya tako ya dawo kan gadon da Amina ke kwance, shi ma ya hau ya ce "Am sorry Meenalina, duk an ɓata miki rai ko?"
Ta ce "A'a"
Ya ce "Yauwa, ya maganarmu?"
Amina ta ce "Wace maganar?".
"Maganar zuwa umara, ina son mu kuma komawa duba matar Khalil, ina son mu koma Lagos a gobe in Allah ya kaimu, idan ba haka ba zata sakani a gaba a kan lallai sai ta san in da Fadila take, idan kuwa ta sani ba zata bari ta zauna ba, sai ta san yadda zata kashe mata auren".
Amina ta ce "Amma akwai buƙatar ta san inda take, ka san uwa ce hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba".
Daddy ya ce "A'a, nima na san zata shiga damuwa, amma ba zan bari ta sani yanzu ba, tayar mana da hankali zata cigaba da yi, ki ƙyaleta kawai".
Amina ta ce "Shikenan"
"Yanzu dai gaya mini, suwa kika yanke a biyawa"
Amina tayi murmushi sannan ta ce "Da farko ina son a biyawa Babana, sai Zakiru sai kuma ƙanin mahaifin Hajiya Zainab sai kuma mai gadin Family house ɗin ku, sai kuma ina neman alfarmar ka biyawa mutum uku da suke da buƙata a family ɗinku, ko da maƙotanku ne, tun da na san a familynku babu wani mai ƙaramin ƙarfi da za a biyawa".
Murmushi Daddy yayi, ya ce "Allahu Akbar, abin da yake ƙara mini ƙaunarki rashin son zuciyarki, yanzu har da ƙanin mahaifin Hajiya Zainab a wanda kike so a biyawa, ita da ko da wasa bata taɓa sawa ko biyar na bawa wani nata ba sai dai ƙawaye"
Amina ta ce "To Daddy meye a ciki? Allah dai ya ƙara maka arziƙi da kwanciyar hankali mu ci mu bayar"
"Amin Babyna, ina alfahari da ke masoyiyata ina ƙaunarki sosai da sosai" yayi maganar yana janyota jikinsa.
Ita ma murmushi tayi, ta ce "Nima ina sonka sosai Sweetheart".
Washegari da safe, Amina tare da Hajara, suka shiga Kitchen yin girki, sam Amina bata nunawa Hajara ƙyama saboda tana matar gidan, sai ma kyautatawa da take nuna musu, domin bayan aurenta da Daddy yayi, har ƙarin albashi ta sanya yayi musu.
Ta dafa abin da zasu karya, da kuma abin da zasu kai wa su Hafsa Asibiti.
A dining Amina taje ta shirya abinci, ta koma sashinta da nufin tayi wanka ta tashi Daddy, su karya su tafi dubiyar, saboda da Yamma zasu bar gari.
Sai dai me tana zuwa bedroom ɗin nata ta tarar da Hajiya Zainab tana ta zazzagawa Daddy masifa.
A fusace Amina ta ce "Nifa gaskiya na gaji da shigo mini ɗaki da kike yi kai tsaye, ki tafi can ki dinga jiransa idan ya zo wurinki kuyi wadda zaku yi, ni ba zan iya jure in kallonki kina cin mutuncin mijina a gabana ba"
Hajiya Zainab ta kalleta ta ce 'Ki ka ce mijinki?".
Amina ta murguɗa baki ta ce "Eh mana, ko baki ji bane ba, mijinmu ko ma in ce mijina, tun da dai ke kin sallama mini shi".
Kallon banza Hajiya Zainab tayi mata ta ce 'Eh kece mayyar namiji, in dai shi ne kije kiyi tayi, a fito mini da 'ya ta kawai, yauwa".
Daddy ya ce "Zainab na gaji da wannan rashin mutuncin naki da wulaƙanci".
Mummy ta ce "Ai rashin mutunci da wulaƙanci, da kanka kayi cinikinsa ka saya, dan haka dole ka jure shi, ka gaya mini in da 'ya ta take".
Daddy ya ce "Ki je, zan yi wanka na karya, Dutse na kaita zanje na ɗaukota idan na gama shirina"
Wata masifar ta dira da bala'i, a kan me za a kai mata 'ya Dutse. Saboda ta ƙyaleshi, ya lallaɓata ya ce yanzu zaije ya taho da ita.
Amina ta daɗe ba taga azababbiyar mata kamar Hajiya Zainab ba.
Bayan yayi wanka ya karya, ya shirya shi da Amina, suka fice.
Asibiti suka fara zuwa wurin Hafsa, Khalil ne ya kwana tare da ita, yana jiran Maman Hafsa ta zo, shi kuma ya koma gida. Yana ta kula da ita kamar ya mayar da ita ciki.
Yanzun ma yana zaune a gefen gadonta, yana rungume da ita, yana shafa gashin kanta yana mata hira, hannunta kuma ɗauke da drip.
Su Daddy na shigowa Hafsa tayi sauri ta rabu da jikin Khalil.
Murmushi Daddy yayi ya zauna, suka gaisa yana mata sannu.
Amina ma sannun ta shiga yi mata tana yi mata ya jiki.
Hafsa ta amsa mata da sauƙi, so take ma a sallame su.
Khalil ya ce 'Babu mai sallamarki, sai kin warke".
Amina ta miƙo musu fulas, ta ce xGa abinci nan na kawo muku".
Khalil yayi murmushi ya ce "Mun gode sosai Anty Amina".
A nan Daddy yake gaya masa batun tafiya umara, da kuma waɗanda ya biyawa.
Khalil ya ce "Gaskiya Daddy kayi dabara, mussaman biyawa ƙanin babnsu Mummy shi ma, zai ji daɗi wallahi".
Daddy ya ce "Ai Antynku ce tayi wannan tunanin, har da Zakiru duk zamu tafi, albarkacin haka har ita Hajara zamu tafi, sun daɗe suna maana aiki a gidan nan, yakamata a mutuntadu, kai kuma idan kuka gama jinyar ka nutsu ka biya muku kai da matarka. sai dai Lagos zamu tafi mu anjima, kai zan bawa gabarar sanar da wanda za a biyawa, da kuma biya musu saboda wani dalili nawa".
Amina ta ce "To waye ya ce kace nina ce a biya musu"
Daddy ya ce 'Ai yabon gwani ya zama dole Aminatu'.
Khalil ya ce "Daddy godiya suke, Anty Amina Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana"
Amina tayi murmushi ta ce "Amin"
Daddy ya ja Khalil suka fice daga ɗakin, Amina kuma ta zauna suka cigaba da hira da Hafsa.
A nan Amina ta bata labarin abin da yafaru na aurar da Fadila da Daddy yayi ba wanda ya sani, sannan ta ce wa Hafsa ko Khalil karta gayawa.
Daddy kuwa a waje ya sanar da Khalil cewa da zarar Hafsa ta warke, sannan ya gama abin da ya sa shi ɗauki Hafsa su koma Abuja tare, kar ya kuma barinta ita kaɗai, idan ya so su zane a gidansa na Abuja zuwa ya kammala nasa.
Khalil ya amince, suna nan Maman Hafsa ta zo, suka gaisa tayi musu godiya sannan suka yi musu sallama suka tafi.
Yazid kuwa tun Asuba ya tashi Fadila, amma tayi mursisi taƙi tashi, ba ita ta tashi ba sai shida saura, lokacin ma Yazid bai dawo daga masallaci ba, ga wata irin yunwa da take tatalar cikinta, dan rabonta da Abinci, tun Fruit ɗin da ta ci jiya. Tashi tayi a hankali, ta nufi hanyar fita daga gidan, sai dai ta tarar da ƙofar a rufe.
Ta koma falon ta zauna ta takure jikinta, cikinta na cigaba da ƙugi.
Bakwai saura Yazid ya shigo gidan da sallama. Banza tayi masa bata amsa ba, ya shigo falon ya zauna a kusa da ita ya kalleta ya ce "Ina kwana?"
Tsaki tayi ta kawar da kanta gefe.
"Hmm, me kike so ki ci?"
A fusace ta ce "Ban sani ba, kaga malam ka tashi ka mayar da ni gidanmu"
Yazid ya ce "Meyasa?"
"Ban gane meyasa ba? Saboda ba zan zauna da kai ba, nafi ƙarfinka nafi ƙarfin na zauna da kai, ni ba matarka bace, ka tashi ka mayar da ni gidamu, ko ni na tafi".
Yazid ya kwantar da muryarsa ya ce "Kiyi haƙuri Fadila, yanzu idan kika fita zaki iya ɓata a unguwar nan, kuma ga furucin da mahaifinki yayi a kan barinki gidan nan ki koma gidanku, kiyi haƙuri ki zauna in cigaba da bashi haƙuri idan ya huce sai muje gidan naku"
Cikin kuka Fadila ta ce "Ni ba zan zauna da kai ba, ba ruwanka da furicin da yayi, kasai ka sakeni, ba zan zauna ba".
Ya ce "To shikenan, ki bari ki karya tukuna, sai muyi magana"
"Babu wata magana da zan yi da kai, kawai k mayar da ni gidanmu, wallahi baka yi mini adalci ba, dan meyasa zaka aureni, ni bana ƙaunarka ban taɓa sonka ba, kuma ban yake maka ba"
Shiru Yazid yayi ya dafe kansa, dan ya san an rina an saci zanin mahaukaciya.
Suna cikin wannan mujadalar ne, aka yi sallama da ji ka san muryar babbar mace ce.
Yazid ya miƙe yana faɗin Hajiya sannu da zuwa shigo.
Matar ta sake yin sallama sannan ta shigo falon, da fulas ɗin shayi a hannunta da wani ƙaramin foodflask, ta ajiye tana cewa "Amarya sannu ko, ga kayan kari na kawo muku".
Yazid ya ce "Fadila ga Hajiyata, ita ce mariƙiyata uwa ce a wurina" ko kallon in da matar take ba tayi ba, balle ta gaisheta ta kawar da kanta gefe.
Yazid bai ji daɗin abin da Fadilan tayi ba, Hajiya ta tashi ta ce 'In dai kuwa wannan ce matar, to Allah ya sauwaƙe ya tayaka riƙo, shiyasa ni sam ban murna da wannan auren ba, yaran masu kuɗi zama da su sai dole".
Miƙewa Yazid yayi yana lallaɓa Hajiya dan tayi shiru amma ta ƙi.
Fadila kuwa bayan matar ta bi da harara.
Haka dai Yazid yayi ta bawa Hajiya haƙuri, ta gama mitarta ta tafi.
Ya koma ya cigaba da rarrashin Fadila ta ci Abinci.
Hajiya Zainab gajiya tayi da zaman jiran Alhaji Ahmad ya dawo mata da Fadila, ta kira wayar Fadila tun tana shiga har ta daina.
Gajiya