Showing 285001 words to 288000 words out of 296192 words
haka ba zata zo ta ce sai na koma gida"
"Kar ka damu, sai da muka yi wannan yarjejeniyar da Daddy, sannan ya yadda muka zo"
Yazid kuwa duk a tsorace ya ke, kar ya je wani abun yayi wa Fadila bai sani ba take kai ƙararsa.
Khalil ya ce "Baby Hafsat, taho mu tafi yamma ta yi fa".
Fadila ta ce "Sai su Baby, to Baby Hafsat yaushe zaku dawo dan Allah?"
Hafsa ta ce "Ai ni ko cewa kika yi na kwana a nan zan kwana"
Murmushi Fadila ta yi, suka fito suka raka su Hafsa har bakin mota suna ɗaga musu hannu.
Ayshercool
0808101214385
Bayan sun raka su Hafsa sun tafi, suka dawo gida Fadila ta gyara gidan, ta dawo falo ta tarar da Yazid ya zauna yayi shiru yana tunani.
"Zid menene kuma?"
A hankali ya waiwayo ya kalleta ya ce "Fadila bana jin daɗin a duk lokacin da wani daga gidanku ya zo na ga kina kuka, duk sai na shiga damuwa dan Allah idan wani abun nake yi miki da ba kya so, ni ki dinga gaya mini, kar su zata ko ina muzguna miki ne"
Murmushi ta yi, ta zauna a kan cinyarsa ta kalleshi, ta kai hannu ta tallafi fuskarsa ta ce "Allah ne kaɗai ya san irin son da nake yi maka ɗan ustazuna, wani abu ya daina baka tsoro, sai dai ni a halitta ta ne yawan kuka, kuma kaga duk na yi nesa da 'yan uwana da iyayena idan za a zo wurina sai dai a ɓoye, saboda kar Mummy ta sani, shi ne yake sani damuwa, amma ni ba abin da kake mini da zan iya kai ƙararka sai fatan Allah ya biya ka".
Ta ƙarasa maganar tana shafa sajensa, ga wata irin ƙaunarsa da take ji a zuciyarta.
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan,amma dai ina sake baki haƙuri komai zai wuce in Allah ya yarda"
"Haka ne, hira muke yi da matar Yaya Khalil, take ɗan bani labarin rayuwarta, wallahi Zid na ji kunyar ta fiye ds da yadda na ji kunyarka a kan abubuwan da na dinga yi maka. 'yar uwata mace muka sakota a gaba da wulaƙanci saboda talaka ce, har wurin da take sayar da awara fa Mummy ta je ta yi mata wulaƙanci, wallahi zuciyata babu daɗi, kuma sai na ji nauyinta na kasa cewa ta yafe mana wallahi ban kyauta ba abubuwan da na dinga yi"
Ya kwantar da kanta a ƙijinsa, yana wasa d gashin kanta sannan ya ce "Alhamdilillah, tun da har Allah ya sanya kin fuskanci kuskurenki, sai ki yi ta istigfari, sannan ki cigaba da yiwa Mummy ma Addu'a" ta jinjina masa kai alamar to.
"Yarinya ta nutsu, ta auri ɗan shawalwalin ustaz" yayi maganar yana tsokanarta.
Hannu ta saka tana matsa masa Adams apple da yake maƙogwaronsa.
Buge hannunta yayi ya ce "Ba na hana ba"
Ta ƙara kai hannu ta matsa tana dariya.
Hajiya Zainab kuwa dama ladabin da ta yi wa Daddy, dan ya dawo mata da Fadila ne, yanzu kuma ta sako shi gaba, a kan lallai sai ya gaya mata waye mijin da ya aurawa Fadila, kuma a ina yake?
Daddy yayi mursisi ya ce ba zai gaya mata ba, tun da dai ba zata canza hali ba, ya san idan har ya kuskura ya gaya mata sai ta kaso auren nan.
Fadila kuwa ta yi lafiya, ta mayar da hankali sosai a kan karatun da Yazid yake koya mata a gida, ayyukan gida kuwa cikin ikon Allah da taimakon Maryam duk ta iya ayyukan gida ita take kayanta.
Wanki ne dai ba ta yi, iyaka ta wanke undewars ɗinta, sai Yazid ya dawo zai bi dare ya yi musu wanki.
Ba laifi Yazid yana samu a kan harkar kanikancin da yake yi, ɓangaren fentin mota ne, duk da gyaran ma ya iya, ga uban gidansa baya yi masa mugunta saboda jajircewasa da gaskiya a kan sana'ar, ga makarantar da yake zuwa koyarwa, suma suna biyansa sun ƙara masa ma albashi, Yazid shi ne har gidan buredi duk in da ya san zai buga ya tashi ya samu halal yana yi, sam ba ya samun isasshen hutu, gashi dare kuma maimakon ya huta, yana tsananta ibada da daddare sosai.
Yana yawan gaya wa Fadila cewar tun da Allah ya sa ya aureta, ƙofofin samu suke ta buɗe masa da kuma alkhairai ta kowace fuska.
Yayin da ita ma take alfahari da samunsa a matsayin mijinta, saboda Yazid mutum ne na gari.
***
Hajiya Zainab duk iya tijararta da bala'inta, Alhaji Ahmad bai yadda ya gaya mata in da Fadila take aure ba, balle ya gaya mata wa ya aura mata, Hajiya Zainab ba ta taɓa sanin yana da wannan uban taurin kan ba sai a yanzu, ashe a baya ƙyaleta kawai ya ke yi take abin da ta ga dama, gashi ba ta san Amina na da ciki ba, sai daga baya ta lura da tsohon cikin da yake jikin Amina, ga takaicin cikin jikin Fadila da ta gani, gaba ɗaya ta rasa in da zata saka kanta.
Su Hajiya Salma na ta banka mata magunguna, wai suna karɓo mata a wurin malamai, wanda zata sake mallake Alhaji Ahmad, ta sha wannan ta jiƙa wancan ta turara wannan amma bata sauya zani ba.
Gaba ɗaya kana ganinta ka san a firgice take, Amina kuwa hankalinta a kwance yake, 'yan ƙauyansu na ta amfana da dukiyar Alhaji Ahmad, ba su ba har danginsa da maƙwabtansu suna morar dukiyar nan.
Sai sunan Hajiya Zainab ya fara ɓata sai na Amina, a matsayin matarsa, haka zalika Amina ba ta manta uwar ɗakinta ba Hajiya Maryam, ga kuma Ammi.
Azima ma an yi bikinta, ta auri abokin ƙanin Ammi an sha biki sosai, Amina ga ciki ga shagalin biki.
Maman Hafsa ita ma Alhamdilillah, ta samu kwanciyar hankali da sauƙin rayuwa, duk da da girmanta ta auri Alhaji Ilyas, amma yana matuƙar ji da ita, mussaman yadda ta rungumi 'ya'yansa ta riƙe kamar nata, ta samu damarmaki a wurinsa, dan har yaran maƙotansu, ta sanya ya dinga samarwa aiki, a tarayya.
Watarana da weekends, Mama tana tare da ƙaramin ɗan Alhaji Ilyas, mai shekaru goma sha biyu tana koya masa karatu, Hafsa ta zo gidan ita da Khalil duk suna tare suka yi baƙi.
Sai da ba ƙaramin mamaki suka yi ba, da ganin suwaye baƙin.
Mahaifiyar Najib ce, da ƙanwarta suka zo, sai ƙarewa gidan kallo suke yi, gida kamar na wani sanata saboda kyau tsaruwa.
Mama ce ta iya ƙarfin halin yi musu sannu da zuwa, suka zauna suna kallon Hafsa da ta haɗe rai.
Kasancewar Khalil bai san su ba ya sanya ya gaishe su, yana ƙoƙarin tashi ya bar falon, amma Mama ta ce yayi zamansa.
Babar Najib ta kalli Hafsa ta ce "Ohh Hafsa aka yi aure amma babu gayyata, to Allah ya sanya alkhairi".
Haushi ne ya kama Hafsa, Mutanen da suka ƙi karɓar mata kuɗin aure ne ke wannan maganar banzan.
Mama ta saka aka kawo musu ruwa da lemuka, suka dirarwa ruwan robar nan kamar ba su ta ɓa sha ba da lemo, suka duma jarka a baki suna kwankwaɗa.
Shi dai Khalil sai mamakin Suwaye wannan yake.
Sai da suka sake nutsuwa, Sannan babar Najib ta ce "Dama alfarma na zo nema wurinki, daga irin arziƙin da Allah ya yi muku ke da 'yar ki".
Mama ta ce "Ina jinki"
Ta gyara zamanta tana matso hawaye ta ce "Wallahi kinga baban su Hafsan aka kama, bashi ya yi masa yawa, an kai shi kurkuku, hatta gidan da muke ciki, kotu na ƙoƙarin waƙafce shi, ga Najib sai a hankali ba sana'a ba aikin yi, yanzu haka shaye shaye yake yi, Abin da zamu ci ma gararmu yake yi, ki taimaka dan Allah"
Sai yanzu Khalil ya gane in da zancen ya dosa, sannan ya gane ma suwaye.
Aikuwa nan da nan ransa ya ɓaci, dan ba ya ƙaunar ko sunan yaron nan Najib, balle wata alaƙa ta sake haɗasu da su Hafsa, cikin fusata ya ce "Hajiya, nan ba wurin neman taimako bane ba, ko kin manta lokacin da su kuka watsar da su, ko ba dai mijin naki ne wanda aka kawo kuɗin aurenta ya ƙi karɓa ba, yai ta kusheta ba, ba za a taimaka ba ɗin, kuma daga rana mai kamar irin ta yau, kar ku sake zuwa gidan nan".
Babar Najib ta ce "Yaro me yayi zafi haka? Dan Allah ai bai kamata a dinga tuna baya ba, dan Allah ki saka baki komai ya wuce dan Allah"
Mama ba ta taɓa wulaƙanta ɗan Adam ba, amma a wannan karon ji take tamkar ta rufe matar nan da duka, dan ba zata taɓa manta baƙar wahalar da matar nan ta gana mata ba ita da mijinta lokacin tana kishiyarta.
Mama ta duba bayan kujera, ta ɗauko kuɗi dubu biyar, ta ajiye mata ta ce "Suwaiba, dan Allah ga wannan kya hau mota, amma dan Allah dan annabi kar ki sake zuwar mini gida, bana son ɗan abin da yayi saura na mutunci ya ƙarasa zubewa, muddin mijina ya san haryanzu akwai wata alaƙa a tsakaninmu akwai matsala, dan haka dan Allah ki yi haƙuri da wannan dan Allah kar ki sake zuwa".
Ta kalli Mama ta ce "Yanzu wulaƙanta ni zaki yi, dan Allah ya rufa miki Asiri?"
"Lokacin da Allah ya rufa mukun ni ba tone nawa asirin ku ka yi ba?"
Khalil rai a ɓace ya yi mata fata-fata ya koreta, saboda ya tsani matar da duk abin da ya shafi Najib.
Fadila cikinta ya shiga wata na bakwai, amma bata son wanka, wai saboda warin sabulun damunta yake yi, sai Yazid yayi ta lallaɓata tukuna, kan ya tafi makaranta sai ya yi mata wanka, da daddare ma haka, aikin gida ba komai take iya yi ba.
Kwatsam ciwon aljanu ya kuma dawo mata, babu ciwon kai babu komai sai ta yanke jiki ta faɗi, ga ciki, haka kurum kuma sai ta fara zubar da jini, jini sosai, amma da ya kaita Asibiti idan aka yi gwaje gwaje sai ace cikin lafiya ƙalau.
In da Allah ya taimaki Yazid, Daddy ya basu kayan Abinci amma duk kuɗin da ya samu kusan a kan larurar Fadila yake tafiya.
Gashi yayi shiru ba wanda ya gayawa, basa baccin kirki sam, saboda yanayin jikin Fadila.
Idan tana hayyacinta tai ta kuka ta ce "Wallahi Zid ni tunda nake a gidan mu, ban taɓa yin wani aljanu ba, amma ana tsorata ni sosai, kuma ina addu'a"
Yazid ya ce "Dan Allah ki daina kukan nan, ni babban fatana Allah ya rabaki da cikin nan lafiya, ya kuma baki lafiya sai dai ina nan ina Addu'a duk wanda ya yi miki Allah ya mayar masa, tun da ba zai daina ba, dan Allah ki cigaba da Adduoin da na ke baki".
Ya ƙarasa maganar yana share mata hawayen da ya wanke mata fuska.
"Na gode sosai Zid, na san ba kowane miji ne zai iya haƙuri ya zauna da ni, da wannan ciwon ba, kayi haƙuri"
"Haba Fadila, a hannuna fa larurar ta sameki dan me zan guje ki? Allah ya bamu lafiya a daina kuka dan Allah"
Haka yayi ta rarrashinta yana kwantar mata da hankali, lokaci lokaci, Yana kissing ɗin goshinta yana kwantar mata da hankali, dan ita kanta tana cikin damuwa a kan wannan larura da take fama, wasu lokutan ko bata da lafiya sai ta daure ta yi shiru, saboda tausayinsa da take ji sosai.
Su Khalil kuwa kwanci tashi asarar rai, suka shiga watan haihuwa, ta karɓu maternity leave ta dawo Kano Khalil duk sati biyu sai ya zo gida, wasu lokutan kuma a 'ya'yan Mama ake samun mai zuwa ta zauna da ita.
Amina kuwa na ta yafi na kowa, dan wasu lokutan idan ta zauna sai Daddy ya taimaka mata ta tashi, ƙarshe sai ƙauye Daddy ya je ya ɗauko wa Amina wata tsohuwa 'yar uwar Inno aka kawo mata, take taimaka mata.
Daddy kansa gaba ɗaya Kano ya dawo sa zama, saboda yanayin jikin Amina.
Hafsa ta tashi da matsanancin ciwon mara, sai dai Khalil shi ya fuskanci bta da lafiya, dan miskilancin nan nata yana nan.
Kwana tayi tana fama, da Asuba Khalil ya fuskanta, ya ɗauketa suka tafi Asibiti, suna zuwa Asibiti aka ce haihuwa ce.
Gida Khalil ya koma ya ɗebo kayan Hafsa na haihuwa, ya kira Mama a waya ya sanar mata, ya kira Daddy ma ya ce masa gasu suna Asibiti.
Ya kira Mummy ya sanar mata, amma Mummy ta ce "To ina ruwana, bance kar ka sake sakani a sabgar harkar aurenka ba? Sai ka kira talakawan iyayenta ka sanar musu". Jiki a sanyaye ya kashe wayar, ya kwashi kayan ya tafi kai wa Asibiti.
Khalil ya kasa zama ya kasa tsaye, haka Mama ta zo ta samesu, Amina ma kasa nutsuwa ta yi, tana jin ance Hafsa na Asibiti ta tashi hankalinta, ta ce sai ta bi Daddy Asibiti.
Sai wajen ƙarfe huɗu na yamma tun Asuba, sannan Allah ya sauki Hafsa lafiya, ta haifi sankacecen ɗa namiji mai kama da Khalil sak.
Ana miƙowa Khalil jaririn cikin murna ya rungume shi, yana faɗin Alhamdilillah.
Ya nufi Daddy da jaririn, Daddy ya karɓi Babyn yana faɗin "Alhamdilillah, Congratulations Khalil"
Khalil baki ya ƙi rufuwa, Amina tana daga zaune ta ce "Ni ba za a bani na gan shi ba?"
Khalil ya ce "Anty Amina waya isa ya hana ki jariri" Khalil ya karɓe jariri a hannun Daddy ya miƙawa Amina.
Daddy ya ce "Ikon Allah, shi ne aka ƙwace ɗan daga hannuna".
Khalil ya ce "Yi haƙuri Daddy"
Amina ta karɓi jaririn tana faɗin "Masha Allah, wayyo Allahna beautiful baby boy Allah ya raya mana da imani, ya raya mana bisa tafarkin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam" Amina ta dinga yi masa Addu'a.
Daddy ya ce "To sai ki kawo a bawa kakarsa ma ta gan shi"
Amina ta kalli Mama dake sunkuyar da kai ta ce "Mama zan baki shi, bari na gama ganinsa".
Mama ta ce "Ai ba komai, naku ne"
Wata Nurse ce ta fito ta ce "Zasu iya shiga su ga Hafsa".
Khalil babu ko kunya ya dinga rawar kai, yana lallaɓa Hafsa yana yi mata sannu.
Mama tayi waya gida, 'ya'yan mijinta suka zo da manyan kulolin Abinci, nan da nan Asibiti ya fara ɗaukar harami.
Daddy ne ya kira Yazid a waya, ya sanar masa da cewa Hafsa ta haihu.
Murna Yazid ya dinga yi ya ce gasu nan zuwa.
Fadila na banɗaki, ta fito tana tambayarsa murnar me kake ne?".
"Matar Khalil ce ta haihu" zabura tayi ta ce"Dan Allah? Kirawo mini su a waya"
Yazid ya kunna wayarsa, ya kira wayar Daddy, Yazid ya ce "Daddy ga Fadila"
Fadila ta karɓe wayar ta ce "Daddy ka bawa mai jegon"
Daddy ya ce "Ikon Allah, ba ma da ni ake son ayi magana ba, to shikenan" Daddy ya miƙawa Hafsa waya.
Hafsa ta ce 'Hello Anty Fadila".
Fadila ta ce 'Ba wata Anty, shi ne kika rigani haihuwa ko? Ashe ma haihuwar ba wuya, har kin haihu"
Hafsa ta yi murmushi ta ce "Hmm zaki yi bayani ne, yaushe zaku zo?".
"Ai yanzn nan makuwa, sannu gamu nan zuwa, da wa yake kama jaririn ko jaririyar?"
Hafsa ta ce 'Namiji ne da yake kama kuma"
Fadila baki har kunne ta ce "Shikenan gamu nan"
Shaf-shaf ta shirya, ta saka Yazid a gaba, suka tafi Asibiti.
Ai tuni Asibiti ya ɗau harami, ya cika da mutane masu zuwa barka.
Rungume Hafsa ta je tayi tana faɗin "Sannu dan Allah"
Amina kuwa mamaki ne ma ya kamata, yaushe Fadila har suka daidaita da Hafsa haka, lallai ta yi hankali yanzu.
Fadila ta karɓi jaririn nan tana wow Masha Allah, su Yaya Khalil an zama Father, dama nima na haihu kan mu bar Asibitin nan".
Sosai ta basu dariya, saboda ba ta san ya abin yake ba, ta tashi ta kaiwa Yazid jaririn tana cewa "Zid Allah ya kawo mana namu muma kamar haka"
Daddy ya ce "Wai ke wace irin mara kunya ce haka ne?"
Sai kuma da Daddy yayi maganar sannan ta sunkuyar da kai ta ji kunya.
Sai da magariba aka sallami Hafsa, suka ɗunguma zuwa gidansu na Kano.
Da ƙyar Yazid ya ja Fadila, suka tafi gida saboda da ƙyar take yadda a ɗauki ɗan nan.
Ko da Hajiya Zainab ta samu labarin haihuwar matar Khalil ta bakin Daddy, kawai sai ta ji daɗi, ta samu jika sai dai ba ta in da ta so samu ba, saboda abubuwa sun yi mata yawan da ta manta da sabgar Khalil da yi masa aure.
Sai dai ba ta iya yanke hukunci ita kaɗai ba, ta kira su Hajiya Turai ta sanar musu, Hajiya Salma ta ce "To ke ina ruwanki? Ki ƙyale su su yi sabgarsu"
Hajiya Turai ta ce "A'a ba a haka, jikan fari ai ko da ba kya son ta ɗanki ne fa uban yaron, dan Allah ki shirya ki je ki ga yaron jikan fari fa"
Hajiya Salma ta ce "Ke Turai meye haka ne? Tayaya za ta je bayan ba ƙaunar yarinyar ta ke yi ba, ai kuwa da ajinta ya zube".
Hajiya Turai ta ce "Albarkacin zuwan da zaki yi ma, wataƙila ki sake ganin Fadila, ko ki ji labarin in da take, kawai ki shirya ki je".
Zuciyar Mummy ta fi karkata da ta je ɗin, dan haka ta amince zata je.
Tuni Mutanen Dutse ma suka samu labari, suka dinga murna Alhaji Ahmad ya ɗau jika.
Kasancewar Yazid ya gaya wa HakiyaWashegari da safe Hajiya ta shirya ta ce su tafi tare ta je ta yi barka, Fadila ta gama duk aikinta da wuri, suka tafi gidan Khalil.
Hafsa kuwa da Mama sun mutunta Hajiya sosai, bayan ta yi musu barka ta tashi ta tafi gida.
Yazid ma tafiya ya yi, ya bar Fadila, can Amina ma ta zo, duk da haushinta da take ji, amma tausayi take bata, ga cikin yayi ƙasa sosai, gashi har rinjyarta yake yi saboda girma.
Fadila dai cikinta baya hanata harkokin ta, amma na Amina ko salla a zaune take yi.
Hafsa kamar ya da ƙanwa ita da Fadila, Fadila kamar ita ce uwar ɗan, sai hada-hada ake yi.
Da yamma Yazid ya zo zai tafi da Fadila, Khalil ya ce sai Yazid ya shigo ya sake ganin jariri kuma ya ci Abinci.
Suka haɗu a falo suna ta surutu, dan Mama bar musu falon ta yi, Amina tana gefe sai ana hira sai su Fadila su sauya yare zuwa larabci.
Khalil ya ce 'Nifa bana son haka, wannan wane irin abune ana magana ku wani dinga sauya yare, Anty Amina ce kawai take jin me kuke cewa, madam ko ke kina ji?"