Showing 39001 words to 42000 words out of 296192 words
masa ƙarar".
Kawu Lawan ya ce "Haba Jarmai, dan Allah kar mu yi haka da kai mana, insha Allah zamu ciko maka sauran kuɗinka, kayi haƙuri".
Jarmai ya gyara wata daƙalƙalalliyar babbar rigarsa ya ce "Ai haƙuri shi ne kawai in ga uwar kuɗina a hannuna".
Kawu Bala ya ce "Insha Allah, zamu cigaba da lalubawa zamu baka sauran kuɗinka" da ƙyar suka lallaɓa Jarmai, ya haƙura bai kai su ƙara ba.
Washegari da Fadila ta koma Makaranta, Captain ya tambayeta ya mai jiki, ta sanar da shi tun a jiyan aka sallame shi ya tafi gida, 'yan aji suna son suyi tsurku su ji yadda abubuwa suka wakana, amma sanin halin Fadila ya sanya ba wanda ya tanka mata.
Ta dinga zuba ido, ta ga ta ina Yazeed zai shigo aji, amma babu Yazeed babu alamar sa, har aka yi lectures ɗin ranar aka gama.
Nan cikin Fadila ya sake ɗurar ruwa, ta san ba zai wuce ace jikin ne ya hana shi zuwa Makaranta ba, nan zuciyarta ta dinga saƙa mata abubuwa daban daban, ciki har da tunanin ko jikin ne ya tayar masa ya mutu? Nan da nan ta yi saurin kawar da wannan tunanin daga ranta.
Da aka tashi daga Makaranta ta samu Captain ta ce "Musa, kun yi waya da gayen nan ne?"
Captain ya ce "Wa kenan?".
"Wanda muka kai Asibiti jiya"
Murmushi ya yi ya ce "Hajiya Fadila ta mu, sunan nasa ne ma ba za a iya faɗa ba. Wallahi tun jiya nake kiran wayarsa, amma ba ta shiga, kuma ina kyautata zaton jikin ne ya hana shi zuwa yau" Fadila ta ce "Ok shikenan"
Daga haka ta wuce ta nufi motarta, tana cigaba da tunani.
A kwanakin nan kowa da abin da ya dame shi a jama'ar gidan, Khalil ya kasa sukuni saboda tunanin Hafsat, gashi ya kuma komawa amma bata nan bai sameta ba.
Fadila kuwa gaba ɗaya tunanin halin da Yazeed yake ciki ne ya dame ta, dan a rayuwarta bata taɓa aikata abin da ya dameta ba kamar abin da ta yiwa Yazeed ba, saboda ta tsorata da irin yanayin ciwonsa. Bata taɓa ganin mutum a mawuyacin yanayi na ciwo kamar Yazeed ba.
Tana zaune a aji, tana ƙoƙarin ɗauko littafi tayi rubutu, ta ga jotter Yazeed, ta ɗauko jotter ta fara bubbuɗewa, rubutunsa a tsare yake kamar musamman yake shirya rubutun, sai dai fahimtar abinda ya rubuta ɗin sai ƙwaro ko kuma shi kansa da ya rubuta abin sa.
Rubutu ne na turanci, jotting ɗin lectures ɗin da ake yi ne, sai yayi sentence ɗaya biyu ya gauraya su da rubutun larabci, ga wasu irin manyan Words na turanci, da bata taɓa jinsu ba.
To ya akai ya iya turanci a rubuce, amma bai iya a baki ba? 'Maybe yana da matsalar public speaking ne' ta bawa kanta amsa.
Bakomai ta iya ganewa a jotting ɗin nasa ba, saboda yadda yake rubutun larabci kamar rubutun yarensa na haihuwa.
Ɗan taɓe baki tayi, ta ajiye jotter, tana fatan Allah ya sa dai ba jikinsa ne ya hana shi zuwa Makaranta ba.
Khalil musamman sai ya shirya ya tafi unguwar su Abdul, yayi shawagi domin kawai ya ga Hafsat, cikin ikon Allah yau yayi sa'a ya tarar da ita a bakin kaskonta bayan magariba, tana ta harhaɗa kayanta ta tashi.
Parking ɗin motarsa ya yi, ya fito da sauri ya ƙarasa in da take. "Sannu dai"
Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce "Yawwa".
"Ba dai har kin tashi ba?"
"Me kaga ina yi?"
"Oh sorry haka ne, na gani haɗa kaya ki ke yi, yanzu ba zan samu ba?".
"Eh ta ƙare".
"Kwana biyu na zo ba na ganinki, meyasa ba kya fitowa?"
Hafsa ta ce "Eh da yake ai ba aikin gwamnati nake ba, kuma ba wani ne ya ɗauke ni aiki ba balle a tuhume ni"
Murmushi Khalil ya yi, yana jinjina hali irin na Mai awara, ya ɗan sosa kai ya ce "Haka ne, am sorry"
"Yawwa dama ina nemanka" tai maganar tana saka hannu a jakarta.
Khalil ya ce "Kina nemana kuma? Allah ya sa ba laifi na miki ba"
Ɗari biyar ta miƙo masa tana faɗin "Karɓi canjinka da ka tafi ka bar mini ranar"
"Ai ba bashi bane, kyauta na baki".
"Ai bance maka ina buƙata ba, ka karɓi canjinka".
Khalil ya ce "Ai kyauta na baki, kuma ba kyau mayar da kyauta".
"Meye tsakanina da kai, da haka kurum zaka bani kyautar kuɗi"
"Alkhairi ne tsakanina da ke. Naga kamar gida zaki tafi, ko zamuje in sauke ki?"
"Malam ka karɓi kuɗinka, zan tafi dare nayi"
"Da ban dawo ba ya zaki?".
Ƙoƙarin saƙala masa kuɗinsa take a hannunsa da harɗe a ƙirjinsa. Ja da baya yayi yana kallonta tare da sakin murmushi ya ce "ke dai kin fiye gaddama, dama zuwa na yi in ganki, kuma na sai awara, tun da ban samu awara ba na samu ganinki, shikenan, ki gaida gida" galala ta tsaya tana kallon Ikon Allah, Khalil kuma yayi gaba abin sa yana jin wani nishaɗi da ya rasa na menene.
Yana tafe a mota yana tuna yadda tai kicin-kincin da rai tana bashi kuɗinsa, sam bai gaji da ganinta ba, amma ya lura ba ta son takura, magana kuma na bata wahala, shiyasa ya tafi ya ƙyaleta.
Shiru yayi yana tunanin menene haka yake ji game da yarinyar nan? Wani irin baƙon al'amari yaji yana ratsa zuciyarsa, duk Hafsa daga gaban kaskon wuta ta tashi, ƙamshin turarenta ya haɗe da ƙaurin mai da na hayaƙi, amma a hancin Khalil ƙamshi ya bashi mai daɗin gaske.
Amina kuwa zuwa makaranta ya kankama, dan ta gane hanya, Baba ne yake bata kuɗin mota, ta hau abin hawa ta tafi, idan an tashi ma ta taho gida.
Kullum da kiran sallar farko, Amina idan ta tashi bata komawa, duk wani aiki da zata yi, sai ta tabattar ta yi shi, har karin kumallo sai ta dafa, ta gyara ko ina sannan take shiryawa ta tafi makaranta.
Sati ya shuɗe kusan kwanaki takwas, Yazeed bai dawo Makaranta ba, gaba ɗaya hankalin Fadila a tashe yake, dan ba wanda ya san gidan su Yazeed balle a samo information akan halin da yake ciki, gashi wayarsa ba ta shiga sam.
Fadila Addu'a take, da fatan Allah ya sa ba mutuwa yayi ba, dan da ƙyar in ta tambayi malamai ba a ce tayi azumi sittin ba, saboda abin da ta aikatawa Yazeed, dan da gayya ta balbale shi da hayaƙi da kuma ƙura, duk dan ta muzguna masa.
Yau Saturday, kuma suna gaf da fara exams, dan haka akwai lecturer da ya ce, lallai su shiga Saturday, dan bai yi covering course ɗinsa ba.
Jiki a sanyaye take tafiya dama gashi ta makara, dan ƙarfe goma ya ce aje, yanzu kuma sha ɗaya saura mintuna goma sha biyar, haka ta tunkari ajinsu tana fatan Allah ya sa malamin ya bari ta zauna, tuni har malamin ya fara lectures, Allah ya taimaketa bai koreta ba. Tun da ta shiga ajin ya ƙura mata ido, ɗaga idon da za tai suka yi ido huɗu da Yazeed. Gabanta ne ya faɗi ganin yadda yayi wata muguwar rama, sauke facemask ɗin sa yayi, tare da yi mata murmushi, gaba ɗaya ya rame sosai, sai dogon hancinsa da ya sake fitowa.
Tsuke fuska tayi, ta basar kamar ba ta ganshi ba, ta nemi wani wurin ta zauna, tare da ɗauke kanta da sashen da Yazeed yake.
Sai dai lokaci lokaci ta kan kalleshi, tare da sake tabattarwa da kanta yayi rashin lafiya sosai.
Haka aka gudanar da lectures ɗin aka gama, aka yi Attendance.
Da yawa ɗaliban zasu zauna ne a school, suyi karatu, saboda gabatowar exams, wanda ita ma Fadilan ta yanke shawarar ta zauna ta yi karatu, dan idan taje gida bacci zata yi, sai dai kafin nan akwai buƙatar ta ɗan samo abun motsa baki, da zai ɗebe mata kewa yayin karatu.
Bayan tafiyar malamin daga aji, akai ta yiwa Yazeed ya jiki.
Fadila tana ta hanzari ta tunkari motarta, ta saka key tana ƙoƙarin buɗewa ta ji an kira sunanta "Fadila" waiwayawa tayi, taga Yazeed a bayanta.
Cikin murmushinsa da ya zame masa ɗabi' ya ce "Kina lafiya?"
Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Lafiya ƙalau".
"Dama na ce bari in zo in sake yin godiya ne, game da taimakon da ki ka yi mini, na gode sosai Allah ya bar zumunci" Wata uwar harara ta watsa masa, ta buɗe ƙofar motar.
"Au ashe fa ni mai laifi ne, na manta a ranar na ɓata miki rai, kiyi haƙuri dan Allah, naga baki ji daɗin abin da nayi ba".
"Ashe kana sane kai min abin da kayi mini ko?" Tayi maganar tana hararasa.
"Ai nace kiyi haƙuri ban kyauta ba"
"Kaji da shi" tayi maganar tana ƙoƙarin shiga mota.
Cikin harshen larabci Yazeed ya ce
"هل يمكنني الحصول على jotter الخاص بي"
(*Can i have my jotter*)
Kallonsa ta yi saroro, ba tare da ta gane me yake faɗa ba.
Ya kuma maimaita mata abin da ya faɗa. Tsaki tayi ta ce "Malam speak what I can understand".
Wani irin ƙasaitaccen murmushi Yazeed ya yi ya ce "Ni kuma gashi ban iya turanci ba, amma dai ina roƙon ki bani jotter ta ne, zan ɗan kwafi lectures da na yi missing, ance mini suna wurinki"
Tura baki tayi, tana wani basarwa, ta fara duba jakarta, ta zaro jottersa da bironsa ta miƙa masa.
Sansana jotter ya yi ya ce
رائحته جميلة
(
*It smells nicely*)
Ƙaramin tsaki ta ja tana kuma ƙoƙarin shiga mota.
Riƙe ƙofar motar yayi ya ce "Malama kayana da saura" kamar ba shi yayi Maganar ba, ya wani basar, dan ba zaka taɓa cewa yana magana haka ba.
"Ban gane ba" ta faɗa tana kallonsa.
"Ina kuɗina?" Ya faɗa ransa a haɗe.
"Hamsin ɗin?" Ta faɗa a wulaƙance.
Yazeed ya ce "Eh ai tawa ce ko?"
Tsaki tayi ta saka hannu a jakarta ta ɗauko ɗari biyar ta ce "Ungo".
"Ni tawa nake so, amma dai shikenan na bar miki, ki zo muje muyi karatu tare, ki koya mini abin da aka yi bana nan, sannan baki mini ya jiki bama, kin kusa halaka ɗan marayan Allah, ni yakamata ma ki gaya mini laifin da na yi miki kika tsane ni haka".
"Dan Allah ka bani wuri in tafi, ka tsayar da ni kana ta mini surutan banza".
"Subhanallah, yi haƙuri na takura miki, shikenan ki gaida gida" ya matsa ya bata wuri, ta shige motar ta, ta sauke glashin ta ce "Ka matsa kar in tada ƙura ka kama sumewa mutane".
"Idan na suma ma in dai kina nan ai ba damuwa" hararsa tayi, ta bawa motarta wuta ta wuce ta bar wurin.
Shi kansa Yazeed bai san yadda aka yi ya tsinci kansa, da ƙoƙarin tsawaita hira da Fadila ba, dan a rayuwarsa kusan shi mutum ne mai tsoron duk wani abu da zai haɗa shi da mata.
Sake shanshana jotter yayi, sai ƙamashin turaren Fadila take, ya fara bubbuɗewa, kawai ya ci karo da rubutun da ba nasa ba, kusan duk lectures ɗin da aka yi baya nan, ta rubuta masa a ciki.
Zubawa Jotter ido yayi, a hankali ya ce "Allah ya sa ki fara jin abin da nake ji a kanki" can kuma ya ce "Subhanallah, ba ajina bace" shikaɗai yake wannan surutan, daga baya kuma ya ja jiki ya nufi masallaci.
Amina ta gama aikinta tsaf, ta zauna a falo tana karatu, Hajiya Zainab bata nan, Hajara kuma ta tafi yin sayayya.
Turo ƙofar falon aka yi, Amina ta waiwaya, taga baƙuwar fuskar da bata saba ganinta ba.
Yusra ta ce "Ina mutan gidan kuwa, naji kamar ba kowa?"
"Sun je Islamiyya a koya musu sallama, da yiwa wanda suka tarar sannu" Amina ta bata amsa.
"Ke, wacece ke kika gaya mini wannan maganar?"
"Ahh musulma mana Hajiya, ai a koyarwar addinin musulunci idan ka zo wuri da sallama kake farawa, kuma ka yiwa na zaune sallama, amma kawai kya shigo kanki tsaye ki hau Magana. Bisimillah shigo amma dai nan gaba ba a haka" saroro Yusra ta bi Amina da kallo, dan ba su taɓa haɗuwa ba sai yau.
Ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon Yusra take, amma Amina ta miƙe ta ce "Hajiya ba fa banɗaki zaki shiga ba, ya zaki shigo mana da takalmi falo, ciresu a nan wurin ki ƙaraso" Yusra cire takalman tayi tana kallon Ikon Allah wurin Amina, dan ba ta san matsayinta a gidan ba.
Yusra ta zauna, Amina kuma ta wuce kitchen, ta haɗowa Yusra ruwa da lemo, ta kawo gabanta ta ajiye mata ta ce "Ga ruwa ki sha, 'yan gidan basa nan, idan kuma zaki ci Abinci ne ki faɗi wanne zan dafa miki? Dan an cinye na rana, na ɗan gidan nan ne kawai ya yi ragowa"
Sai yanzu Yusra ta gane matsayin Amina, a ranta ta ce 'Ina Mummy ta samo wannan tantiryar mara mutuncin 'yar aiki? Ka rashin kunya ga karrama mutane'.
"Ba Abinci na zo ci ba, ai ban miki kama da mai jin yunwa ba"
Dariya Amina ta yi ta ce "Haba Yayata,. Idan a jiki ake gane yunwa ko rashinta, ai cewa za ai baki taɓa cin abinci ba ma" ai gaba ɗaya Amina ta kashewa Yusra bakin Magana.
Ƙamshin turaren da ya karaɗe falon ne, ya sanar musu da zuwan Khalil, sai dai tun kan ya shigo, Yusra ta rasa nutsuwarta.
Kansa tsaye ya shigo, da sallama iya wuyansa wadda shika ɗai yaji kayarsa, jiki na rawa Yusra ta risuna tana gaishe shi. Amma ya amsa ba yabo ba fallasa, haka ya shigo falon da takalmansa, sai da yaje dining ya ajiye takalman a kan step ɗin dining ɗin.
Amina kuwa ta ƙulu, saboda yadda ya biyo har ta kan carfet da takalmansa, a fusace ta miƙe taje ta kwaso takalman Khalil ta je ta watsa su waje tana mita cike da tsiwa "Ai ni ba baiwarku ba ce da zan dinga aiki kuna takawa, sai na sake!"
SHARE PLEASEGABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143
P12
Sai da ta watsa takalman waje ta dawo falo, ta lura da yadda duk suka bita da kallo, mussaman Khalil da ya ke mata Wani irin mugun kallo, sai a lokacin ta sha jinin jikinta ta gano ta yi wauta.
Ɗan marairaicewa ta yi ta ce "Dan Allah kayi haƙuri ba dan halina ba, na gaji ne sosai yau na sha aiki, bayana har ciwo yake, na canza wancan carfet ɗin na bayar wanki, na saka sabo wankakke kuma ka taka mini da takalimi ai kaga ba zan ji daɗi ba, aikin da wahala, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba".
Rai a haɗe ya ce "Ke na fuskanci ba ki da kunya ko? Tun ranar farko da na fara ganinki a gidan nan na fuskanci haka".
Amina kamar zata fashe da kuka ta ce
"To ai na ce kayi haƙuri, ba zan sake ba insha Allah, kuma rashin kunya ba halina ba ne, ba zan sake ba kayi haƙuri"
"Rufe mini baki malama, ki ɓace mini daga nan wurin 'yar ƙauye mara kunya kawai"
Amina ta juya baya ta murguɗa masa baki, tana yatsina baki a ranta ta ce "Ko ba komai, na faɗi abin da ke raina, ba zaku mayar da ni baiwarku ba"
Yusra ta jinjina hali irin na Amina, yarinyar akwai iya nuƙufurci, yanzu za ta maka laifi, kuma ta nemo abin da zata goge laifin nata.
Ta ɗan ƙurawa Khalil ido da yake zaune yana cin Abinci, cikin son lallai sai ya kulata ta ce "Yaya Khalil ita ma wannan maid ɗin Mummy ce?" Ba tare da ya kalli in da Yusra take ba ya ce "Me ya hana ki tambayeta tun tana nan?"
Yusra ta ji haushin amsar da ya bata, amma ta haɗiye ta tsuke bakinta, tana cigaba da satar kallonsa.
Yusra gajiya tayi da zaman Jiran Fadila, ta kirata a waya amma taƙi shiga, gashi Khalil ko kallon in da take ya ƙiyi, gasjiya tayi ta tashi ta kalli in da Khalil yake ta ce "Na tafi sai anjima, na kira lambar Fadila ba ta shiga".
"Ok ki gaida gida"
Yusra ta fito gwiwa a saɓule, a harabar gidan ta ci karo da Abdul, a jikin motarsa, yana ƙoƙarin kiran waya.
Murmushi Abdul ya yi ya ce "Wata sabon gani, Yusra dama kina nan?".
"Ina nan Yaya Abdul, ya kake ya gida?".
"Lafiya ƙalau Yusra, yaushe rabon da na ganki, ya school?".
Yusra ta ce "School Alhamdilillah".
Abdul ya ce "Masha Allah, kin zo wurin ƙawar taki ne?"
"Eh, na tarar ma ba ta nan, ta je school wai za suyi lectures yau".
"Allah sarki, to shikenan, ki gaida gida"
"Yauwa gida ya ji, na gode".
Abdul ya kira wayar Khalil, "Gani a cikin gida, naga baka part ɗinka"
"Shigo falo, ina cikin gida" Abdul ya ɗan yi jimm, ya ce "To bari in shigo".
Ya nufi cikin gidan, yana fargabar karɓar da zai samu a wurin matar gidan.
Da sallama ya shiga falon, ya hangi Khalil a kan dining, yana cin Abinci.
"Ashe kana nan kana kintsa cikinka".
Khalil ya ce "Ai sai da kintsa cikin, ƙaraso mu ci".
"Ni bana jin yunwa, na ji gidan shiru ko ba kowa ne?" Abdul ya yi maganar yana zama a kan ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin.
"Eh basa nan, Fadila tana Makaranta, Mummy kuma ba ta nan".
"Allah sarki, na so inga Fadila ko ba zata kulani ba, ai yau na ga ƙawar nan ta ta Yusra, rabona da ita ina ga tun kan mu tafi karatu".
Khalil ya ce "Hmm ka san wani abin takaici kuwa?"
"A'a sai ka faɗa"
"Wai wannan yarinyar Yusra ce, suka haɗa kai da Fadila wai sona take".
Dariya Abdul ya yi ya ce "Amma ta taimaki ƙaton tuzuru, to kai ya ake ciki? Yarinyar ai ba laifi".
Khalil ya yi tsaki ya ce "Ƙawar ƙanwar tawa, dan rainin hankali ni sa'anta ne?"
Abdul ya ce "Ji wani zancen banza, dan sa'ar ƙanwarka ce shi ne ba zaka aureta ba, ai masoyi abin a kula da shi ne, meye dan ta ce tana sonka?".
"Dalla, bana son raini, kuma ni bana son ramammiyar mace, na fi son in ga mace a cike"
Abdul ya ce "Banda cin fuska dai malam"
"Kaji da shi, ni idan an yi sallar magariba, zamu je ka rakani wani wuri, in nuna maka wani abu"
Khalil ya ce "Me zan gani?"
"Kai dai ka bari, idan muka je ka gani"
"Ni ina Amina 'yar Makaranta ne?".
Wani dogon tsaki Khalil yayi ya ce "Sai ka tashi ka tafi nemanta ai".
"Wai kai kowacce magana akai maka sai ka kushe" banza Khalil ya yiwa Abdul, ya kammala cin abincin sa, ya dawo ya zauna a falo, suka kunna tv suka cigaba