Showing 267001 words to 270000 words out of 296192 words
ina ka samu kuɗi?"
"Allah ne ya bani" ya bata amsa.
"A ina?"
"Ai tunda Allah ya sa na aureki, Allah yake buɗe mini ƙofofin arziƙi ya ko ina, kina bacci na je gidan Hajiya, abokin baba ne yayi mana biyan bashi da kuma sauran dukiyar Baba da take hannunsa, aka raba mana aka sako mini nawa ta account, shi ne na sai mana kayan Abinci mu da Hajiya.
Da daddare in Sha Allah zamu je ki sai kayan sawa da na kwalliya wanda zan iya saya. Dan Allah ki ƙara haƙuri kin ji Fadila, komai lokaci ne zai wuce in Sha Allah zan cigaba da ƙoƙarin ganin komai ya tafi dai-dai".
Ɗan shiru ta yi sannan ta ce "Amma tunda kana da takardun karatunka a ƙasa, ka je wurin Daddy ya samo maka aiki mana"
Yazid ya girgiza kai ya ce "Da akwai buƙatar hakan da yayi tun kan ya bani ke, ni dai dan Allah kiyi haƙuri ba sai na je ba komai zai wuce kin ji?"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Zubo mana abincin mu ci" Yazid ya zuzzuba musu, shi yana daga Kitchen, ita kuma tana daga waje suka karya, sai dai tana ankare da yanayin Yazid yau ba ya cikin walwala.
Bayan sun gama, ta tattare kwanukan ta wanke, suka koma falo, kallonsa kawai take yi, tana tunanin wane abu za ta yiwa Yazid wanda zai sa ya ji daɗi, ya rage raɗaɗin abin da yake damunsa a zuciyarsa a tsawon lokaci.
Yana ɗago ido suka yi ido huɗu, murmushi yayi mata ya ce "Meye kika kallona?"
"Me nake kallo?" Ta ɗan yi maganar cikin tsiwa.
"To ni ina na sani, ai ke zan tambaya".
Ta ce "Hmm, ni yaushe zamu je Taraba wurin kakarka?"
Ya ɗan yi murmushi ya ce "Ai bata wani gane mutane sosai, ta tsufa sosai da sosai, zasu zo ne Rano nake son zuwa"
"Ka je kayi me a can?"
"In ga 'yan uwana mana" ya bata amsa. Haushi ne ya kama Fadila ta ce "Me zaka je ka yi musu kuma? Wai kai baka zuciya ne? Kodayake ni ka raina a makaranta da kace bani ba kai kayi fushi" tayi maganar tana tura baki.
Tashi yayi ya matsa kusa da ita, ya rungumeta yana mata magana a kunne "Wancan lokacin ma ina cikin damuwa ne, kuma ina fargabar Kankiya ya rabani da karatuna. Amma na azabtu a wannan lokacin mussaman da nake zuwa ina ganinki kina ganina amma ba zan iya yi miki magana ba. Na kuma zo ina kallonki cikin damuwa na zo ko Abincin kirki bana iya ci, saboda yanayin da nake ganinki.
Mace ta farko da ta shiga zuciyar Yazid, da nake jin idan ba ke ba Yazid, Allah ne ya dubeni ba da dabarata ba, ba da komai ba na sameki ni na san bani da abin da zan iya aurenki da shi Fadila, amma believe me ina sonki sosai da sosai, dan Allah kiyi haƙuri da yanayin da nake ciki na babu amma na san komai lokaci ne" ya ƙarasa maganar yana lumshe idanunsa da suka yi ja, ya ɗora hancinsa a kan nata suna jin numfashin juna.
Gaba ɗaya jikinta ya saki, ta yi shiru tana sauraren Yazid tare da jinta a gajimare.
"Talk please" yayi maganar ba tare da ya buɗe idonsa ba.
Ita dai tayi masa shiru dan bata san me zata ce masa ba.
A hankali ya haɗe bakinsu, yana kissing ɗin ta, ya buɗe idonsa ya kalleta ya ce "yau ba za a wanke bakin ba?" Dariya tayi ta tashi zaune ta ce "Ba zaka fita bane yau?".
Ya ce "Korata ma kike kenan, to ba in da zani, muna gidan nan tare sai Allah ya kaimu yamma zan fita, idan na dawo daga makaranta kuma sai mu fita"
Tare suka wuni a gidan, suka yi girki tare, sai yamma ya shirya zai fita, ita kuma ta tsiri shagwaɓa wai ba zai fita ba.
Yazid ji yake kamar ya koma yayi zamansa, gani yake kamar a mafarki, Fadila na ta lallaɓa shi tana bashi kulawa.
Bayan fitar Yazid, Fadila ta ƙara gyara gida, ta ji sallama. Leƙowa tayi daga falo, ta ga Maryam.
Fadila ta ce "Maryam, ina kika shiga kwana biyu?"
Maryam ta ce "Ina nan Anty, ni da 'yan makarantarmu ne na yo gaba na bar su, wai zasu zo su gaisheki"
Fadila ta ce "To Allah ya kawo su" suna cikin maganar kuwa suka ji sallama.
Fadila ta amsa musu ta ce su shigo, zaratan 'yan mata ne su kusan takwas suka shigo, haka nan gaban Fadila ya faɗi da ta gansu.
Ta daka ta basu wurin zama, suka shiga gaisheta, kamar karta amsa amma sai ta tuna alƙawarin da tayi wa kanta na ta daina wulaƙanta ɗan Adam. Dan haka ta sake ta amsa musu.
Ta je Kitchen ta ɗauko musu pure water a plate, ta kawo musu.
Ta ɗora da cewa "Gashi ban san da zuwanku ba, da na yi girki da ku"
"Wallahi bakomai kar ki damu, mun gode sosai hakan ma, a gaida malam"
Suka ajiye mata wata leda suka tashi suka tafi.
Fadila ba ta kula da kayan da suka kawo mata ba, Maryam ta shiga bata labarin ɗaliban da sunansu, har da wadda ta ce tana son Yazid amma shi bai ma sani ba.
Fadila ta kawar da hirar, Maryam ta fara tayata aikin Abincin dare.
Yayar Maryam ce ta zo dan kiran Maryam ɗin ta aiketa, sai a nan nema suka gaisa da Fadila, amma ba dan haka ba ko kalar Fadila Maryam ba ta sani ba, saboda babu wanda ta shiga ta yiwa sallama.
Bayan la'asar sosai sannan Yazid ya dawo, ta kawo masa abinci yana ta mata hira, amma ya ga tana basarwa ta ƙi kulashi, sai yayi shiru ya fara cin abincin, ya kammala ya fita da kwanon da kansa ya dawo ya zauna yana satar kallonta.
"Wai suwa kake koyarwa a makarantar da kake zuwa ne?" Ta jefo masa tambayar unexpected.
Yazid ya kalleta ya ce "Ɗalibai mana"
"Maza ko mata?" Ta tambayeshi tana tsareshi da ido.
"Duk wanda ta kama ina koyarwa amma menene?"
"Ba wani duk wanda ta kama kana koyarwa, 'yan mata kake koyarwa". Ta ƙarasa maganar tana harararsa.
"To Fadila laifi ne dan na koyar da su ɗalibaina ne"
Ta ce "Au sunana ma haka kake faɗa kai tsaye Fadila ko, to ɗaliban naka sun zo har da budurwar ka"
Ya waro ido ya ce 'Ni ɗin, ni ina naga wata budurwa? Wallahi Fadila ɗalibaina ne"
Kicin-kicin tayi da fuska ta ce "Oho maka dai, ga abin da suka kawo can a ajiye maka"
Gaba ɗaya Yazid ya shiga damuwa, ya zauna a gabanta ya riƙe hannunta ya ce "Wallahi Fadila ni bani da wata budurwa, ɗalibai na ne kawai ni bakomai a tsakanin mu" murmushi ta yi ta ce "To shikenan na yarda".
Murmushi yayi ya ce "Meyasa ba kya son nayi budurwa?"
"Au budurwar zaka yi? Wallahi duk ranar da na tabattar da kayi wata budurwa sai dai ka dawo ka tarar bana nan"
Murmushin sa da ya saba yayi ya ce "Babu ma abin da zai kaini, dan Allah Fadila kina sona?" Yayi maganar cikin marairaicewa.
Kallonsa ta yi ta kwashe da dariya, har hularta na cirewa daga kanta.
"Fadila meye ya baki dariya kuma?"
"Bakomai, miƙo ledar nan na ga me 'yan matan naka suka kawo mana"
"Ba zaki daina wannan zancen 'yan matan ba ko?"
Rungumeshi ta yi ta ce "Gwani ɗan Inna"
Lumshe idonsa yayi yana jin daɗin yanayin.
"Dan Allah ko sau ɗaya Fadila, bana son na cigaba da zama da ke ina takura miki ba kya sona"
Miƙa masa hannunta ta yi ta ce "Biyani sai in gaya maka ina sonka ko bana sonka"
Gani ta yi jikinsa yayi sanyi, yana cigaba da kallonta.
Ta kai hannunta fuskarsa tana cigaba da murmushi.
"Fadila da kin san matsayin da kike da shi a wurina kuwa, da kin san matsayin da kike da shi a nan da baki ɗau maganata wasa kina dariya ba" yayi maganar yana nuna saitin zuciyarsa.
"Meye a nan ɗin da ka nuna" tayi maganar tana dariya.
Yazid ya ce "Irin abin da yake cikin ƙirjinki"
"A'a gaskiya da banbanci ƙirjina da naka ba ɗaya bane, kenan bani da maraba da maza" a tare suka yi dariya yana cewa Allah ya shiryeki.
Yau ko makaranta bai je ba, Ya sa Fadila ta shirya suka fara zuwa gidan Hajiya, sannan suka wuce titi ya samar musu napep, wani store suka shiga, Fadila ta ɗan sai abin da take buƙata, suka wuce ya sai musu Abinci sannan suka dawo gida.
Fadila ta ji daɗin fitar da suka yi,haka kurum ta tsinci kanta cikin nishaɗi. Sai da suka dawo suka ci Abincin dare sannan ta bi ta kan kayan da ɗaliban Yazid suka kawo mat, turaren wuta ne suka kawo mata, fal da humra.
Ta turawa Yazid gabansa ta ce "Ga abin da 'yan matanka suka kawo wa matarka"
"Ai ke suka kawowa bani ba"
"Ai sai ka yi musu godiya, idan ma dai 'yan matanka ne ba damuwa fa, da na ƙara gaba sai ka yi aurenka".
Shiru yayi mata, duk sai da ta ɗan gane bai ji daɗin abin da ta ce ba.
Ya ƙi kulata, ta shirya kwanciya ta kwanta, shi kuma yayi zamansa ya buɗe Alqur'ani ya fara tilawa.
Kusan awa biyu, amma ba shi da niyyar tashi. Dan haka ta fito daga net ɗin ta dawo kusa da shi ta zauna.
Miƙa hannu ta yi ta rufe Alqur'anin, amma ya shareta ya cigaba da yi da ka.
"Ka shiga time ɗina fa sir" ta faɗa tana riƙe masa hanci.
Yazid ya ce "Ke, sai kin ƙarasani tukuna? Ke da ba kya so na wane time ɗin naki na shiga?"
"Ni zaka yiwa wayo, fushi kake da ni ko?"
Ya ce "Ni na isa na yi fushi da ke?"
Ta ɗan sauke numfashi ta ce "Zid ina gane wa idan abu bai maka daɗi ba, amma sai ka danne fushi da murmushi, shikenan dai mu je ka kwanta"
Kamar ƙaramin yaro ya noƙe mata kafaɗa.
"To ƙaddara ina sonka, shikenan"
"Ba shikenan ba, anjima kuma sai ki ce ba kya so na"
Murmushi Fadila ta yi ta ce "Bayan ka gama tofeni da Addu'a cikin dare, kana sa mini hannu a riga ai ina jinka wataran".
"Sharri zaki mini"
"To ka ce ba ayi ba mana, kana ta tofeni da Addu'a, ka mallekeni"
Yace "Ni addu'a kawai nake miki ta kariya, ni ban san zancen da kika gama ba"
haka suka kwanta Yazid yana jin farincikin ganin Fadila na nuna masa kulawa da soyayya.
Sannu a hankali ta gama sakin jiki da shi, ta rungumi rayuwa a yadda ta zo mata, ta rungumi Yazid da sai a yanzu ta gano yadda take mutuwar son sa.
Sai da Amina suka yi wata da sati uku, da tafiyarsu Lagos zuwa umara, sannan suka dawo Kano.
Tun da suka dawo Daddy yake fargaba, dan ya san halin Zainab sarai.
Jin labarin su Amina sun dawo, ya sanya maƙwabta suka dinga shigowa sannu da zuwa suna yi wa Amina sannu da zuwa.
Zakiru da Hajara kuwa duk garuruwansu suka wuce, domin suma su samu su ɗan huta sannan su dawo bakin aiki.
Kamar yadda Daddy ya tsammata, haka Hajiya Zainab taje ta titsiye shi, cikin faɗa da tashin hankali, a kan lallai ya gaya mata in da Fadila take, amma still ba ta samu wata gamshashiyar amsa daga gareshi ba, hakan ya ƙara tunzarata, tayi masa cin mutunci san ranta ta koma sashinta ta zauna ta dinga kuka kamar ƙaramar yarinya.
Washegari da sassafe Hajiya Zainab ta shirya ta nufi Dutse,bata tsaya ko ina ba, sai gidan kawun Alhaji Ahmad, gaba ɗaya mutan gidan bin ta ska dinga yi da kallo, dan rabon da ta tako taje Dutse har sun manta, balle ta je gidansu, amma yau suka ganta a gidan.
Ta sanar musu da wurin Kawu ta zo, suka je suka yi mata iso a wurnsa.
Shi kansa mamakine ya kama shi, tare da tambayarta ko lafiya?
Fashewa da kuka Mummy ta yi ta ce 'ƙarar Ahmad na kawo maka, yau an kusa shiga wata na uku, ya ɗauke mini Fadla ya kaita in da ban sani ba, nayi-nayi ya ƙi gaya mini in da take"
Kawu ya ce "Ke Zainab ban da abinki wannan ai abin da zaku iya sasanta kanku nex.
"Nifa na yi iya yina, amma yaƙi saurarata ni dai ku saka baki ya gaya mini in da 'ya ta take".
Kawu ya ce "Shikenan, zamu zo gidan naki in sha Allah, ki koma gida" jin ya bata tabbacin zai zo ya saka Alhaji Ahmad a gaba ya gayamata in da Fadila take, hankalinta ya ɗan kwanta, ta fito ta fice.
Tana ƙofar gida tana shirin kunna mota, sai ga wata ƙanwarta, tana ganinta ta ce "Laa Anty Zainab, dama kin shigo Dutse Baba Auwalu ya dawo daga umara mun ji abin arziƙi Allah ya saka"
Ko saurarata ba tayi ba, ta ja motarta ta bar wurin, dan ga san ta tsaya ne ta gaya mata Baba Auwalu ya dawo dan gulma, tunda sun san kishiya ce ta saka aka biya masa.
Fadila kuwa ta kwantar da hankalinta, tana rayuwarta sannu a hankali da Yazid, wata irin soyayya suke yi kamar su cinye juna take, ji take yi Allahn da ya haɗata da Yazid ne kawai zai iya rabata da shi, saboda yadda yake kulawa da ita ne da yake da biye mata da yake yi, ya sanya take taɓararta son ranta.
Tana matuƙar tausaya masa saboda labarin rayuwarsa da ta ji, yayin da shi ma yake tausaya mata na wannan sauyin da ta samu lokaci guda.
Yau ma suna kwance ya gama yi mata ƙarin Alqur'ani, da litattafan Addini.
Fadila ta fuskanci cewar ƙarancin ilimin addini ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu, da ya sanya suke aikata wasu abubuwan.
Suna kwance Fadila ta ɗora masa ƙafafuwanta a jikinsa. Yana jinta tana neman magana amma yayi mata shiru.
Can ya kira sunanta "Matar"
"Mmmm"
"So nake muje Rano" Yazid yayi maganar yana murginawa kusa da ita.
Fadila ta ce "Mu je mu yi me?"
Yazid ya ce "Muje kiga 'yan uwana da dangina mana, idan Allah ya bamu haihuwa ma kinga kin san in da dangina suke"
Fadila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Waye zai haihun?"
"Ke mana Habibty"
Fadila ta ce "Taɓ, gaskiya na yi ƙanƙanta da wata haihuwa"
Yazid ya ce "Au Ba zaki haihu ba amma kin iya zuwa ki sakani gaba kina a baki time ɗinki ko kina lallaɓani?" Yayi maganar cikin zolaya.
Dariya Fadila ta yi ta ce "Nake lallaɓaka ayi me? Ka jika har da sharri abin naka, to amma dai ka san ba a haka aka kawo maka amanata ba ko? Saliha ce ni ba abin da na sani"
"Mhmm shiyasa idan na zauna kusa da mutum a makaranta yake rawar jiki ko?"
Buɗe baki tayi ta ce "Laaa wai haka ka iya sharri Zid?".
"Kice ba ayi haka ba? Kullum kina liƙe da ni, ni matsa ki bani wuri na yi bacci" rasa me zata yiwa Yazid ta huce tayi ta ɗau pillonta tana kwaɗa masa.
Dariya yake yi, ya ja hancinta ya ce "Ki kwanta kar mu kasa tashi gobe in Allah ya kaimu".
Fadila ta tura baki ta ce "Wallahi zan rama, dani kake zancen" ya rungumeta yana murmushi.
Wuta aka kawo, haske ya gauraye ɗakin Fadila ta ɗan rintse idanunta ta ce "Dama baka kashe fitila ba"
"Eh, tashi ki kashe mana"
"Naƙi ɗin" ta faɗa tana lumshe idanunsa.
Gani yayi ta zabura ta tashi da sauri, shima ya tashi zaune ya ce "Wifey menene?".
"Zid kaina ne ya fara yi mini irin wannan ciwon da na kwanta a asibiti"
A gigice ya ce "Subhanallah ko jinin naki ne ya hau?"
Ta girgiza masa kai ta ce "Zid kaina zai fashe, duhu fa nake gani".
Take ya gigice "Fadila menene?" Yayi maganar yana riƙeta.
Fizge-fizge ta dinga yi tana neman ta fita hayyacinta.
Yazid ne ya fara yi mata addu'a yana tofa mata, amma sai mimmiƙewa take tana wani irin numfashi.
"Bana ganinka fa Zid, duhu nake gani kaina zai rabe biyu, bana gani fa"
Sosai ya rungumeta a jikinsa, ya ɗora hannunsa a kanta yana karanto mata addu'a.
Su Kawu ne zaune a falon gidan Alhaji Ahmad, ga Hajiya Zainab duk suna zaune a falo.
Kawu Hamza ne da Kawu Ali ƙannen mahaifin Alhaji Ahmad, da suka yi wancan zaman tare da su lokacin da za a gaya mata auren Alhaji Ahmad.
Kawu Hamza ya ce "Ahmad, kar kace mini ba tare da saninta ka yanke hukunci da ka yanke ba, ace tsawon wannan lokaci ba ta san in da ka kai mata 'ya ba?"
Daddy ya ce "Kawu ban yi mata haka ba dan na wulaƙanta ta, sai dan sanin cewa idan na gaya mata zata iya ɓata komai"
A fusace fuska duk hawaye ta ce "Ni bana son wani dogon jawabi, ka gaya mini in da 'ya ta take, saboda rashin tausayi da imani ka ɗauke mini 'ya ka kaita wani wurin, kuma ka ɗau matarka kayi tafiyarka ka barni ko na mutu ko na rayu ba ka damu ba, ina ka kai mini 'ya ta?"
Daddy ya ce "Na aurar da Fadila ne ha mutumin da ya dace da rayuwarta"
Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"
"Kamar yadda nake gaya miki, Fadila na ɗakin mijinta yanzu haka"
Kawu Hamza ya ce "Haka ne, a Dutse aka ɗaurawa Fadila aure, sai dai mu bamu san ne gaya miki ba!!!
Ayshercool
08081012143LITTAFIN KUƊI NE, MAI BUƘATA YA TUNTUƁENI A KAN LAMBAR WAYATA.
81
"Ahmad kana cikin hayyacinka kuwa? Ko dai ka sha wani abun ne?"
Daddy ya ce "Tun da nake da ke na taɓa shaye shaye ne?"
Cikin ƙunar rai ta ce "Zata iya yiwuwa ka fara a 'yan tsukin kwanakin nan, wace irin maganar banza ce haka kake yin ta? ta yaya zaka yiwa Fadila aure babu sani na, aure ba shiri bakomai kamar auren dabbobi"
Daddy ya ce 'Ai dama nine nake da alhakin aurar da ita ga mutumin da ya dace ba ke ba. Da fari kin kawo naki zaɓin kun dawo kun janye, kun zubar mini da mutuncina a idon a duniya, dan haka na aurata ga wanda na ga ya dace"
Ta kalli Daddy ta ce 'Ahmad so kake ka ga na haukace ina bin bola saboda baƙin cikinka ko? To da ikon Allah, sai dai kaga haka a kanka, kuma na baka nan da awa ashirin da huɗu duk in da 'ya ta take ka fito mini da ita, idan ba haka ba wallahi kotu zan kai ka azzalumi mara imani Ahmad ka kasheni ka huta kawai mana"
Kawu Ali ya ce "A'a Zainab ba a haka, bai kamata kiyi haka ba uban 'ya'yanki ne fa, dan