Showing 123001 words to 126000 words out of 296192 words
Please"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un"
MASU BUƘATAR SHIGA VIP GROUP, KU TUNTUƁENI TA LAMBAR WAYATA
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
AFUWAN NOT EDITED
42
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, shine abin da Fadila ta dinga maimaitawa, take taji jikinta ya hau rawa bugun zuciyarta ya ƙaru, tana daga kwance amma ta dinga jin kamar jiri na kwasarta. Babu abin da ta hango sai lokacin da Yazid yayi wannan faɗuwar har ta kai shi Asibiti, da ƙyar aka iya ceto ransa.
Da ƙyar taja jikinta ta tashi zaune, ta ciri lambar Captain daga what's app group ɗin, ta kirashi.
Captain na ɗagawa yayi mata sallama "Assalamu alaikum"
"Wa'alaikum salam, Captain Fadila ce"
Captain ya ce "Ahh, babar yarinya ai na ɗauki muryarki"
"Yauwa, naga posting ɗinka a group ne, meya sami Yazid ɗin ne? Kuma yana wani Asibitin?"
Captain ya ce "A gaskiya ban sani ba, dan ke Yakamata mu yiwa wannan tambayar dan fi kowa kusanci da shi, wani abokina ne muka haɗu, muna hira har hirar ta kawo zancen Yazid ya ce mini ko ya sanshi a ina ne na manta, wai yaji ance an kwantar da shi a Asibiti babu lafiya"
Fadila ta ɗan jaa numfashi ta ce "To dan Allah Captain ka ɗan bincika mana, sannan ka turo mini lambarsa"
"Kaii Fadila, kina nufin baki da lambarsa?"
Fadila ta ce "Kai dai ka bar wannan maganar, ka turo mini"
"Shikenan ina zuwa" suka yi sallama, ta zauna tayi shiri tana cigaba da tunanin halin da Yazid ke ciki. Tana nan zaune Captain ya tura mata lambar Yazid, nan da nan tayi saving ta kirashi a wayar, amma wayar a kashe, duk da haka ba ta haƙura ba ta sake gwadawa, amma still a kashe bata shiga. Fadila ta ajiye wayar, tana jin tamkar ita ce bata da lafiyar, dan yana ɗaya daga abin da ya sanya ta fara tausayin Yazid har take sakar masa fuska, tunawa da irin yanayin da yake shiga saboda larurarasa. Ya bata tausyi matuƙa lokacin da ciwon ya tashi.
"Wai ya saunan wannan kwalliyar ne?" Daddy yayi maganar yana kallon Amina.
Murmushi Amina tayi ta ce "Ni ina yi wata kwalliya, kwalli kawai na saka da man leɓe"
"Aikuwa gaki nan kin yi kyau sosai, ko mu tsaya wurin saurayin naki ne ya ga kwalliyar, Bilal yake kowa?"
Amina ta ce "Ba fa saurayina bane, gaisawa kawai muke"
"Au haba?" Daddy yayi maganar cikin sigar bugun cikinta.
"Wallahi da gaske nake maka Daddy"
"Hmm ke baki da saurayi ne?"
"Samarina duk suna ƙauye, kuma na fara yin saurayi a birni, amma kace kar in kuma kawo maka kowa gida, ni yanzu ba ta samari nake ba, karatuna ne ya dameni"
Daddy ya ce"Yauwa yarinyar albarka, your studies supposed to be your first priority, ki mayar da hankali idan mace tayi ilimi tafi daraja".
"Haka ne, tun da Daddy ya tsaya mini, zan yi karatu sosai in Allah ya yarda"
"Yauwa, idan kika gama karatun, da saurayin da mijin ni zan samo miki"
"Kai dama ana haka?"
"Eh mana za kuma ki gani" Amina tayi murmushi tana kawar da kai cike da jin kunya.
Wani katafaren Asibiti suka isa, gini da tsarin Asibitin kamar ba Nigeria ba. Daddy yayi parking suka fito shi da Amina, duk in da suka ratsa manyan mutane ne sai gaisar da Daddy suke yi, alamu suka sake tabattarwa da Amina, ba ƙaramin mutum ne ba Daddy.
Suna zuwa akaa yiwa Daddy iso zuwa wurn babban likitan mamallakin Asibitin, wani ba indiye. Yana ganin Daddy ya faɗaɗa faa'arsa alamu ya nuna dama sun daɗe da sanin juna. Amina ta gaishe shi da harshen turanci, ya amsa mata, sai da suka ɗan taɓa hira da Daddy, sannan Daddyn ya yi masa bayanin abin da yake damunsa.
"Ai na gaya maka lafiyarka ƙalau, kwanciyar hankali kake buƙata ka cire damuwa ka samu isasshen hutu, sannan ka ƙara kulawa da abincin da zaka ci, shi ma sugan ya sauka, lafiyarka ƙalau"
Daddy ya kalli Amina, ya ɗan marairaice fuska ya ce "Meenalin Daddy, kin ji abin da Doctor ya ce wai lafiyata ƙalau, kin yadda lafiyata ƙalau?"
Amina tayi murmushi ta ce "Tun da Doctor ya faɗa haka ne mana, Allah dai ya ƙara lafiya da nisan kwanax
Shima murmushin ya yi ya ce "To Amin, yanzu meye abin yi?"
Likitan ya gyara zama ya ce "Abin yi dai shine ka kula da shawarwarin da na baka, sanannan ka dinga motsa jiki, ka rage cin daɗi, ka samu isashshen hutu, ka dinga abubuwan da zasu ɗebe maka kewa shikenan, ba zan rubuta maka magunguna da yawa ba"
"To shikenan, na gode sosai, Allah ya sa mu dace"
Amina ta ce "Shikenan, tsalle-tsalle da guje guje sun kama ka, idan naga kana yi ni video zan maka" tayi maganar tana dariya.
"Ai tare zamu dinga tsalle-tsalle da gujegujen, sai kiji daɗin yin video"
Haka suka cigaba da hirarsu cikin nishaɗi, likiya ya sallamesu, suka hau mota suka tafi.
Suna tafe a hanya Daddy ya ce "Ko mu tsaya ki sha ice-cream?" Amina ta girgiza kai ta ce "A'a ni dai mu tafi gida, kar Baba ya dawo bana nan, idan ya tambayeni ina naje ban san me zance masa ba".
"Aminatu, Baba ba zai ce komai ba, kuma har mu koma ba zai dawo ba, bari in sayo miki ice cream"
Da sauri ta ce "A'a Daddy, kaga ba lafiya ce da kai ba, kuma ka bani chocolate da yawa ranar, ina da su kar ka wahalar da kanka" yi yayi kamar bai jita ba, yayi parking a bakin wani wurin sayar da kayan ƙwalam da maƙwalashe, ya sanya facemask ɗinsa, dan ɓatar da kama, ya fita daga motar.
Amina dai kamar a kan ƙaya take, babban burinta kawai ta gansu a gida. Bai wani jima ba ya dawo da wata babbar leda, ya ajiye mata a kan cinyarta.
Ta kalleshi ta kalli ledar za tayi magana ya ce "Shhh, kar in ji komai"
Ta ɗan marairaice ta ce "Amma Daddy..."
Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Nace bana son jin komai fa"
Amina ta gimtse maganar da take shirin yi, ta ɗan kalli Daddy tana murmushi. Shi ma murmushin ya yi mata sannan ya ɗora da cewa "Idan Allah ya kaimu Monday, zan aika a ɗaukeki a kaiki banki, su buɗe miki account, sannan yakamata ke ma ki yi sayayya abubuwa da zaki amfani da su saboda tafiyarku Abuja, musamman kayan sawa, dogayen rigunan nan naga kina san su sosai, kuma suna miki kyau, amma naga Atamfa ma tana miki kyau"
"Daddy"
"Yes" ya amsa tare da kallon wurin da take zaune.
"Idan aka tambayeni waye yake bani wannan abubuwan me zance?"
"Waye zai tanbayeki?"
"Baba mana ko mutan gidan"
"Mutanen gida babu wanda zai tambayeki ina kika samo kaya, Baba ma haka, na baki amsa and keep your mouth shut" haka Amina tayi shiru tana zancen zuci.
Har zuwa bayan sallar magariba, Fadila na dakon wanda zai ce gashi yaje inda Yazid yake duba shi, sai ma ƙorafi da 'yan ajin suka dinga yi a kan cewa babu wanda ya san gidansu, kuma lambar wayarsa ba ta shiga sam.
A layi Daddy ya sauke Amina, dan yana tunanin ko Hajiya Zainab ta dawo, Amina tayi mamakin rashin ganin Baba a bakin gate, a 'yan kwanakin nan tana mamakin in da Baban yake zuwa.
Hajara dake Kitchen taga gilmawar Amina da leda, saura ƙiris ta yanke da wuƙa saboda son ganin ƙwaƙwaf, ta yasar da abin da take tabi bayan Amina tana ƙwala maga kira. "Amina! Amina!!"
Amina ta tsaya ta waiwayo ta ce "Lafiya?"
"A'a lafiya lau, ina kuka je ne haka ke da Alhajin, na ganki da uwar leda haka, ina kuka je?"
Amina ta kalli Hajara rai a ɓace ta ce "Yana sashinsa, zaki iya zuwa ki tanbayeshi, zai fi baki amsa yadda yakamata"
Hajara ta haɗe rai ta ce "Ke Amina, kar mini rashin kunya mana"
"Hajara wace irin rashin kunya, da muka fita da mutumin nan kin san ina muka je, ana ta shirin tafiyarmu Abuja ne, kuma Yanzu tare kika ga mun dawo da zaki titsiyeni da wasu maganganu na daban"
Hajara tana jinjina yadda Amina ta ƙware a iya rainin hankali, da sauya zance, amma ta basar ta biye mata ta hanyar cewa "Wannan ledar a makarantar aka baku kenan, bari in zo a kwanceta da ni"
Banza Amina tayi mata tana tunanin yadda za tayi maganin Hajara da saka idonta.
Abdul ya kira wayar Khalil har ya gaji, baya ɗaga wayar, har ya fara tunanin ko wani abun ne ya samu Khalil ɗin.
Ba tsammani yaga kiran Khalil ya shigo wayarsa, ya ɗaga wayar yayi sallama, Khalil ya amsa sannan ya ɗora da cewa "Abdul yakake?"
Abdul ya ce "Dalla ware, kawai ka kashe wayoyinka, na kiraka na kiraka ka ƙi ɗaga wayata".
Khalil ya ce "Yi haƙuri, bani da lafiya ne"
"Ya salam menene ya sameka?"
Khalil yayi ajiyar zuciya sannan ya ce "Bari kawai Abdul, tun da na baro gida da ƙyar na samu Hafsa ta ɗaga wayata sau ɗaya, itama ashe babu lafiya, yarinyar nan ta tubure, da gaske take ba zata aureni ba" ya ƙarasa maganar cike da damuwa.
Abdul ya ce "Dama banda abin ka Khalil, ka sawa ranka salama a kan yarinyar nan, mahaifiyarka bata so. Kuma dan shirme ka koma wurin aiki baka sanar a gida ba, sai da na mayar da motarka sannan suka sani, baka ga faɗan da Mummy tayi mini ba"
"Abdul ba zaka gane bane, gaba ɗaya Mummy bata damu dani ba, ta tatarani ta watsar da ni, ko kiranta nayi na gaisheta sai dai mu ƙare babu daɗi tayi ta mini faɗax.
"To ai haƙuri zaka yi, tun da ta nuna bata son abu kayi haƙuri da shi kawai"
Khalil ya ɗan numfasa sannan ya ce "A zahiri na rabu da Hafsa, amma zuciyata ga kasa Abdul, ka san me ma Mummy ta ce? Wai ba zan zaɓi matar da zan aura ba sai wadda ta zaɓa mini"
"Khalil, ni dai babu abin da zan iya ce maka, sai dai kayi haƙuri, iyayenmu ba zasu taɓa zaɓa mana abin da zai cutar da mu ba, sannan dolenka kayi haƙuri ka cigaba da yi mata biyayya, komai zai wuce in sha Allah"
Khalil ya ce "Kaga ni ba wannan ba, dan Allah so nake kaje ka duba mini ita"
"Khalil, ba zaka haƙura da batun Hafsa ba ko?"
"Ba haka bane ba, ni dai dan Allah kaje ka duba mini ita"
"Shikenan, naji zanje in Allah ya yarda"
Khalil ya ce "Yauwa na gode sosai, dan Allah idan kaje ka haɗani da ita"
Abdul ya ce "Shikenan, zanje in sha Allah".
Sai wuraren ƙarfe tara na dare, sannan Hajiya Zainab ta dawo gida, ta sha hidima duk ta gaji, tayi wanka ta rama sallolin da bata samu yi ba, ta fito falo ta bawa Amina umarnin dafa mata indomie da tea ta kai mata sashin Daddy.
Ganin tun da ta dawo Fadila bata fito ba, kuma rabon da ta ganta tun kan ta fita da ga leƙa taga tana bacci, ya sanya ta tafi ɗakin Fadila.
"Autar ko nemana ma ba kya yi ko?" Fadila data mayar da hankali a kan litattafanta a zahiri, wanda a baɗini tunani ne fal ranta, ta ɗago ta kalli Mummy ta ce "Mummy kin dawo?"
Mummy ta ce "Eh mana na dawo, amma ko kizo ki mini sannu da zuwa"
Fadila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Mummy karatun exams nake ne, mun kusa farawa"
"Amma dai dan kizo ki ganni kawai, shikenan Allah ya bada sa"a ya karatun?"
"Alhamdilillah"
"Fadila na so kin rakani wurin bikin nan, mates ɗinmu duk da yaransu wasu suka je, gwanin sha'awa ke kuwa ba kya son shiga mutane sam, sai kace daddawar sata kullum kina ƙule a ɗaki"
"Mummy, ni kin san bana son abin hayaniya ne gaba ɗaya, gara in zauna a gida in karatuna"
"Aishikenan, amma dai ai gara ki dinga shiga mutane, da haka ake sabawa, wai ni ya na ganki duk wani iri ne, meke damunki?"
"Mummy me kika gani?"
"Kamar ya me na gani, gaba ɗaya mood ɗinki ya canza yayi wani iri"
Fadila ta ce "Kawai gajiya ce Mummy"
"To ki dinga hutawa kanki dai, bari inje in ci Abinci" ta tashi ta tafi sashin Alhaji Ahmad, ta tarar da shi yana aiki a system.
"Sannu da gida" ta faɗa tana zama a kusa da shi.
"Yauwa sannu da zuwa ya hanya?"
"Lafiya lau, ya jikina naka?"
Ya ɗan kalleta ya ce "Ina ruwanki da ya jikina, da kika iya ficewarki kika barni"
Tsuke fuska tayi ta ce "Zaka fara ko?, Yanzun da naje na dawo meye ya sameka nifa bana son neman rigima daga dawowata Yanzu"
Girgiza kai kawai yai ya ce "Ba zaki camza ba Zainab"
"Eh ba zan canza ba ɗin, yauwa ni dama ina son muyi magana, ina son ka ƙara mini jari ne"
Banza yayi mata ya cigaba da aikinsa.
"Sweetheart magana fa nake maka" tayi maganar tana kashe murya.
Still bai kulata ba, ta sanya hannu ta saƙalo kafaɗarsa ta ce "Talk mana"
Amina tayi sallama hannuta riƙe da kular Abinci da teaflask.
Gabanta ne ya faɗi da taga Daddy tare da Hajiya Zainab, wani abu taji yana ƙoƙarin taso mata. Innalillahi wa innalillahi raji'un tai ta maimaitawa a ranta.
Ta ajiye ta ce "Bari in kawo miki kofi da plate" tayi maganar muryarta har sarƙewa take yi, ta juya ta bar ɗakin.
Murmushi Alhaji Ahmad ya yi, dan ya lura da halin da Amina ta shiga.
"Wai ya naga kana murmushi ni kuma kaƙi kulani?"
Ya ce "To ba ina jinki ba"
"To kayi Magana"
"Me kike son ince miki, wato bani da wani amfani a wurinki sai lokacin da kike buƙatar kuɗi ko wani abu a wurina ko?"
"Haba dai, ba haka bane taimakawa zaka yi Please Baban Khalil" tayi maganar tana sake shigewa jikinsa.
Amina ce ta kuma dawowa, yanzu ma kanta a ƙasa har da tuntuɓenta.
Alhaji Ahmad na ganin haka ya rungumo Hajiya Zainab ya ce "Nawa kike so?"
Gyar zama tayi tana murmushi cike da duniyanci ta ce "Ni ko million uku ce, wasu sarƙoƙi zan order da takalma"
Ganin Amina taƙi kallonsu, kuma tana ƙoƙarin tashi ta tafi, ya sanya Daddy ya ce "Buɗe fridge ki bani coc"
Kallon Daddy tayi da sauri, dan daga dokokinsa da aka saka masa an hana shi shan lemukan nan. Yana ganin ta kalleshi, ya kashe mata ido yana kuna rungume Hajiya Zainab, Amina bata san lokacin da ta watsa masa wata uwar harara, ta nufi fridge ɗin, maimakon ta ɗauko masa coc sai ta ɗauko masa ruwa.
Daddy ya ce wa Hajiya Zainab "Zan duba inga nawa zan baki, amma ba wannan watan ba"
"A'a gaskiya ni yanzu nake so"
Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Bafa na son rigima"
Ko da Amina ta kawo ruwan dire masa tayi a wurin, ta fice daga falon, Ba tare da ta kuma ko kallonsu ba.
Gaba ɗaya haka Amina ta dinga jin ranta babu daɗi, musamman da Amina ta lura da gayya yayi, dan ya bata haushi.
"To ma ni ina ruwana" ta faɗa cike da basarwa.
Abu kamar wasa Yazid ya kwashi kusan kwanaki bakwai bai zo makaranta ba, kuma babu wanda taji ya ce gashi ya san ga a halin da Yazid yake, ta san ba ƙaramin abu ne zai hana shi, zuwa makaranta ba, ta so tayi zancen da Yusra amma ta san halin Yusran, yanzun nan zata fara kawo mata wasu zantukan na banza da zasu ɓata mata rai.
Gefe guda ga Kankiya ya addabi rayuwarta, ta so ta yiwa Mummy zancensa, but she knows what she can do, Mummy bata ɗaukar al'amura irin wannan da sauƙi, ba ta ƙi ta rufe kanta taje ta sameshi ta yi masa tatas ba a kan Fadilan, koma ta kunno masa wutar da ba zai iya kashewa ba, wanda ita kuma Fadila ba ta son hakan, dan haka ta sak duk lambobinsa a blacklist, yadda ba zai iya samun damar kiranta b, amma ya canza lamba ya cigab da uzzura mata.
Gaba ɗaya Fadila a yanayin Activities ɗinta zaka gane cewar tana cikin damuwa, amma ta ƙi gayawa kowa meke damunta.
Amina tana kallon saƙonnin Daddy, yana mata magana amma ta shareshi, dan haka kurum haushinsa take ji.
Kamar yadda Khalil ya buƙata, Abdul ya je gidansu Hafsa domin dubata, sai dai ya tausaya mata, ta rame tayi zuru-zuru, suka gaisa cikin mutuntawa, Sannan ya ce "Dama Khalil ne ya ce in zo in duba masa ke, wayarki ta daina shiga gaba ɗaya"
Hafsa ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Yaya Abdul, dan Allah ka dinga gayawa Khalil gaskiya, ka nuna masa muhimmancin yiwa iyaye biyayya, mahaifiyarsa ta nuna ba ta son alaƙarmu, har wurin sana'ata suka ,o ita da wasu, a kan in rabu da shi mai zai sa ya cigaba da dagewa a kan lallai sai mun cigaba da alaƙa?"
Abdul ya numfasa ya ce "Haka ne Hafsa, kuma nima kaina ina gaya masa, sai dai kiyi masa uzuri tun da na san Khalil ban taɓa ganin macen da Khalil ya nuna ya ce ga budurwarsa ba sai ke, duk da ana nuna ana son sa, a kanki ya fara cewa wannan mace ce da tayi mini nake son na aura, dan haka abin zai masa wuya rabuwa da ke lokaci ɗaya, shima yana can ba shi da lafiya, amma Hafsa ku cigaba da addu'a, idan da Alkhairi sai kiga kun yi auren"
"Anya Yaya Abdul? Kamar yadda mahaifiyarsa ta faɗa ni ba tsarsr aurensa bace, haka ne ni ɗin ban dace da shi ba, ko ya aureni ba zanji daɗin zama cikin family ɗinsu ba"
Abdul ya ce "Ai shi lamarin Allah, ba ruwansa da wani yana so wani baya so, idan ya ƙaddara abu zai yiwu sai ya yiwu, ki cigaba da Addu'a, Amma Khalil ma yana cikin wani hali, kiyi masa Addu'a"
Jiki a sanyaye ta ce "Allah sarki Khalil, mutumin kirki ne zan cigaba da yi masa da Addu'a".
Abdul ya ce "Bari in kirashi ku gaisa" tayi saurin girgiza masa kai ta ce "A'a na samu nutsuwa kwana biyu, idan muka yi waya zan kuma shiga damuwa" tayi maganar idonta fal hawaye.
Wani irin tausayin su ne ya kama Abdul, sun shaƙu da juna, Mummyn Khalil ba ta da tausayi kanta kawai ta sani.
Abdul ya cigaba da rarrashin Hafsa, ya shiga har gida ya gaida Maman Hafsa, yayi musu alheri sai dai da ƙyar ya samu suka karɓa ya tafi.
Amina tana ta shirya kayanta da wuri, saboda tana ɗokin zuwa ganin gida, ranar Litinin da safe, bayan Daddy ya idar da sallar asuba bai dawo gida ba sai ƙarfe shida saura, saboda ya tabattar a wannan lokacin zai ga Amina, tana aikin gida saboda zata tafi