Showing 18001 words to 21000 words out of 296192 words
ba zan iya ba".
"Aikuwa zaki iya, da kin shiga gidana kin sha jar miya zaki watstsake muyi zaman mu".
"Jar miya a Ina? Da jar miyar a gidan naka ka ke kai yaranka bara wasu suna talla? Ina alamar jar miya a jikinka ko jikin 'ya'yanka, saboda tsabar cuta da zalunci ina kai ina ni, da ƙanan shekaru na ka haɗani a wannan gidanka na gayya, to bari kaji in gaya maka, ko da sarƙa a ka ɗaura Aurena da kai sai na warware shi, kuma ba dai in je gidanka ba sai dai a kai maka gawata".
"Ni kike gayawa wannan miyagun maganganun?" Yayi Maganar yana matsawa kusa da ita, wani azabar warin baki gami da na sigari ya daki hancinta, ga ƙarin rana yana yi, kayan jikinsa ne kawai wankakku, suma sai ƙarnin koren sabulu suke.
Ja da baya ta yi ta ce "Kar ka sake matsowa kusa da ni, na gaya maka ɗin, idan kana da zuciya ka biya ka karɓe kuɗin Aurenka ka fasa Aurena, idan kuwa ba haka ba idan ba a kai maka gawata gidanka ba, sai gidanka ya zama sansanin tashin hankali da bala'i na gaya maka".
"Yaro man kaza, mu zuba mu gani ni da ke shege ka fasa, gidana ne Wallahi sai kin shige shi sai na Aureki".
"Za kuwa mu gani, na bika ta lallalami kaƙi fahimta, zan fahimtar da kai ta hanyar nuna maka ni 'yar zamani ce, tsohon kawai". Saroro ya bi Amina da kallo, bai taɓa zaton za ta iya gasa masa miyagun maganganu haka ba, dan kowa kallon saliha yake mata, ga haƙuri da biyayya, a zatonsa duk irin halin mahaifinta ne da ita zai samu tuɓus, ashe abin ba haka yake ba.
Ita kuwa Amina gida ta shige abinta, Inno na tambayarta yaya aka yi, amma tayi shiru saboda yadda zuciyarta ke tafasa, ko ƙaunar jin sunan Rabi'u Jarmai ba ta yi, balle a kai ga batun Auren su.
Ta haɗa kai da gwiwa ta dinga rusa kuka, Inno kam ta gaji da rarrashin Amina dan haka ta zuba ido.
Baba Hassan kuwa bakinsa ɗauke da Addu'a, ya shiga falon gidan da sallama, a zatonsa ya je daidai lokacin da zai samu Alhaji Ahmad, sai dai kash bai fito ba, sai Hajiya Zainab ya tarar a falo, tana ta bawa Hajara umarni cikin tsawa da wulaƙanci.
Kasancewar abu ne na gaggawa, ya yanke shawarar sanar da Hajiya Zainab, Alfarmar da ya zo nema, ya risuna ya gaida ita cikin girmamawa, ta amsa ba yabo ba fallasa.
"Hajiya dan Allah wata alfarma na zo nema a wurinki".
"Haka dai, Alfarma ba yau ba gobe ina jinka".
Ya gyara zamansa ya ce "Wallahi wani al'amari ne ya taso mini a garinmu cikin gaggawa game da iyalina, nake son dan Allah a bani dama, ko kwana biyu in je in yi in dawo".
Ta ɗago ta kalleshi ta yatsina fuska ta ce "Idan zamu fita ko mun dawo, mu zamu dinga kokowa da ƙofa wurin buɗewa da rufewa kenan?".
"A'a hajiya, ga Hadi nan sai ya riƙa mini kan in dawo".
"Ban lamunta ba, aikin Hadi daban a gidan nan, naka daban dan haka ba in da zaka a yanzu, idan kuwa ka tafi, to ka tafi kenan" Baba Hassan yayi shiru ya rasa abin da yake masa daɗi, ya tashi gwiwa a sanyaye ya bar falon. Idan ya kuskura ya bar aikin gadin nan, tofa rayuwarsa da ta iyalansa za ta shiga wani hali, dan ba shi da wata sana'a da ya iya.
Amina kuwa tun Asuba take amai, ciwo ya ƙi sauƙi kullum sai gaba yake yi, ƙarfe shida da rabi sai ga Kawu Bala da Lawan tare da matansu, da wasu daga cikin yaransu kamar wanda za su je ritsa kwarto, sun shigo suna zazzaga bala'i tun daga hanyar shigowa.
Suna zuwa suka tarar da Amina a zaune dirshen tana amai.
Ladiyo Uwar gidan Kawu Bala ta ce "Wallahi malam zancen ya tabbata, abin da ake ta gudu, wannan aman ai irin na masu ciki ne".
Inno ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wane irin masu ciki kuma bata da lafiya ne fa".
"Ƙarya kike munafuka, dama ance mini an ganta a tasha wai taje wurin Saminu, dama zuwan da Saminun yake gidan nan kenan, Kuna lalacewa, kafira mai siffar munafukai, har an samu wanda zai rufa miki asiri ya Aureki, amma zaki tozarta mu, ashe dagaske ne kullum sai kin je tasha kin bada jikinki a baki kuɗi, wannan cikin ba zaki haife shi a gidan nan, jibi in Allah ya kaimu idan an sakko daga sallar juma'a za'a ɗaura aurenki da Rabi'u, kuma ba wata bidi'a da za a yi, ɗaurin Aure kawai za ai a kai ki dama da ke da bazawara ba maraba, kin gama tsufa a titi da rabawa maza jikinki".
Wani malolon baƙin ciki ya tokarewa Amina ƙirji, ba ta san lokacin da zafin maganganun wan mahaifin nata suka sanyata jan tsaki a fili ba. Ai kuwa hakan ya tunzura shi, ya nufi dangar kara, ya ciro kara suka rufar mata da duka.
Inno ta dinga kururuwa tana faɗin "Kuyi haƙuri, ba ta da lafiya".
Ladiyo ta ce "Wallahi ku casa ta, ko Allah ya sa cikin jikinta ya zube".
Tun Amina na iya motsi tana kuka, har ta sare sai wata irin ajiyar zuciya take, jikinta duk ya farfashe saboda duka.
Bayan tafiyarsu Inno ta ɗumama ruwa, ta gargasawa Amina jikinta tana faɗin "Kin ga Abin da nake gaya miki ko, shiyasa na gaya miki taurin kai ba shi da rana Amina"
Kwanaki biyun nan, jikin Amina ya ƙara zafi, wai sunan amarya ba kitso ba ƙunshi tana kwace ba lafiya, iyalan su Kawu Bala suka kwashi raftar kayan da suka yiwa Amina aka kai mata gidan Malam Rabi'u.
Ranar Juma'a kiran Sallar farko, Amina ta ɗebi kuɗi, daga kuɗin da ake bawa Inno gudunmuwar Aurenta, dama tun dare ta haɗa kayanta Inno na bacci, kiran sallar farko, ta kwashi kayanta ta fice daga gidan.
Tana tafe a hanya tana kuka ta ce "Babana maganin kukana, na san wataƙila har yanzu saƙona bai riske ka ba, shi yasa baka kawo mini ɗauki ba, duk da ban san wurin da zan sameka a birni ba, amma gara in tafi da tambaya har Allah ya sanya in dace in gano in da kake, dan da in auren nan gara in mutu a hanya".
Arewabooks
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724
GYARA SHARHI KO SHAWARA
08081012143GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
P6
Follow my Arewabooks account
Ayshercool7724
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724
Tafiya take tana ratsa tsakanin gonaki, ga duhu ga babu haske, amma hakan bai dameta ba, babban burinta shine ta ga ta baro cikin ƙauyen nan cikin salama, ba tare da wani ya ganta ba.
Baba Hassan kuwa bacci ma ɓarawo ne ya ɗauke shi, tunanin mafita kawai yake yi, zuciyarsa ta dinga raya masa kawai ya haƙura ya tafi ƙauye, komai zai faru ya faru, idan ya so ya haƙura da aikin, amma gefe guda yana tunanin idan ya bar aikin gadin me zai yi? Wace sana'a zai yi? Wata shawara yake ta jujjuyawa a ransa wadda ba shi da tabaccin zata karɓu.
A haka har garin Allah ya waye, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake gudanar da komai, yana nan zaune a bakin gate yana ta jujjuya yadda zai ɓullowa lamarin, wajen ƙarfe goma Fadila ta fito ta fita, wajen ƙarfe sha ɗaya kuma Alhaji Ahmad ya fito, cikin wani ash ɗin yadi, an fito masa da motar sa da zai fita da ita.
Alhaji Ahmad yana ƙoƙarin shiga mota, Baba Hassan ya cin masa, cikin girmamawa ya gaisheshi, Alhaji Ahmad ya amsa cikin mutuntawa.
Baba Hassan ya duƙa ya ce "Yallaɓai dan Allah alfarma nake nema".
Alhaji Ahmad ya gyara tsayuwa ya ce "Ina jinka".
Baba Hassan ya ce "Dama Yallaɓai game da 'yar wajena ce, jarrabawar nan ba a samu damar yin ta ba"
"Subhanallah, garin yaya?"
"Kuɗin aka kai a ƙurarraren lokaci, to yarinyar tawa tana son ta yi karatu sosai da sosai, to ka san mutanenmu na karkara, 'yan uwana ba son karatun nata suke ba, to rashin samun damar rubuta jarrabawar ya sanya suna ƙoƙarin su Aurar mini da ita. Shi ne nace dan Allah tun da dama Asabe ta tafi, a taimaka mini a ɗauki yarinyar tawa ta maye gurbin Asabe, idan ya so kuɗin aikin nata sai a sakata a makarantar boko, a dinga biya mata kuɗin makarantar".
Alhaji Ahmad ya ce "Malam Hassan wannan ai ba wani abun damuwa bane, bakomai ka kawota ai ilimi ga 'ya mace abin so ne, idan na dawo an jima ka tuna mini zan yiwa mutan gidan magana, ka kawota".
Wata ƙwallar farinciki ta cikawa Baba Hassan ido, ya zube ƙasa yana faɗin "Na gode, Na gode Allah ya jiƙan magabata ya yauƙaƙa Arziki, Allah ya biya maka buƙatunka na Alkhairi duniya da lahira, yadda ka Sanya farinciki a cikin zuciyata da ceto 'yata ubangiji Allah ya faranta maka, yayi maka tukuici na Alkhairi".
Alhaji Ahmad ya ce "Haba Malam Hassan, kar ka damu dan Allah wannan ai ba wani abin damuwa bane, Allah yayi wa yaranmu albarka baki ɗaya".
"Ameen Yallaɓai godiya nake".
Baba Hassan ji yake kamar an yaye masa damuwar da yake ciki, dan yana zuwa ɗakinsa yayi sujudu shukur, ya lalubo wayarsa ya kira Saminu.
Sai da ta kusa tsinkewa Sannan Saminu ya ɗaga, suka gaisa Baba Hassan ya ce "Saminu, dan Allah idan ka tashi tahowa, duk yadda zaka yi ka taho mini da Amina garin nan, ko a tasha ka ajiyeta sai ka kirani in zo in tafi da ita".
Saminu ya ce "To shikenan, amma ba zan taho yau ba gaskiya, sai dai gobe in Allah ya kaimu"
"Bakomai, amma dan Allah kar ka bari su farga su san da ita zaka taho, idan kuka taho daga baya nazo in musu bayani, idan suka san zaka kawo mini ita ba zasu bari ba".
Saminu ya ce "ba komai, kar ka damu Baba insha Allah zan kawo maka ita lafiya".
"To shikenan Saminu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"
************
Yau Juma'a dan haka wankan hijjabi ta yi, pink tun daga sama har ƙasa, ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, ta shigo tana rataye da jakarta pink, hannunta riƙe da robar ruwa da mukullin motarta, bai san yadda aka yi ya shagala da kallonta ba, tayi kyau ƙarshe, ga wani irin sassanyan ƙamshi da take yi. Sai dai ta yi missing ɗin lectures ɗin farko da aka yi, dan suna takun saƙa da malamin, dan haka yau ba ta yi attending darasin sa ba, kuma darasin da yayi da lissafi a ciki, kuma ko da kai aka yi lissafin a ajin, abu ne mawuyaci mutum ya fahimta saboda yayi tsauri da yawa.
"Kai lafiya kar ka cinye ni dalla" tayi masa maganar cikin tsawa.
Sunkuyar da kansa ya yi daga kallonta, ya koma kallon wani wurin daban.
Class rep ne yayi dariya ya ce "Kai Fadila wannan tsawar haka?"
"To ya sani a gaba da kallo, sai na faɗi tukuna aikin banza".
Dariya ƙawayenta suka din ga yi, wata wadda ake cewa Amra ta ce "Kyau ki ka yi masa ko ustaz?"
Tsaki Fadila ta ja ta ce kwaji da shi.
Babu jimawa wani lecturer ya shigo, wanda ya basu class work ya ce su yi da waya, nan ya dinga yi musu mita ya ce "Ace gaba ɗaya ajin nan babu wanda ya fahimci tambayar da na yi sai mutum ɗaya, ina sane nace ku duba waya, dan na san idan har baku fahimci tambayar ba, babu yadda za ayi ku samo amsar. Waye Yazeed Hashim Shareef?".
"Sir" ya faɗa tare da ɗaga hannunsa sama.
Gaba ɗaya idanun mutan ajin suka dawo kansa.
"Wow, dama na gaya muku ustazan nan sune ƙwarin ajin, Malam Yazeed fito ka mana bayanin yadda ka fuskanci tambayar da na yi, har ka samu damar amsawa"
Yazeed ya fita gaban aji, ya ce "Sir zan iya yi da Hausa?".
"Yi da duk yaren da kafi iyawa"
Yazeed na haɗa ido da Fadeela ta ƙunshe baki tana sinne dariya, ta ɗan ɗaga murya ta ce "Sir gara yayi mana da hausar dai, da turancin nan bama ganewa"
Malamin bai kawo komai a ransa ba, ya yin da 'yan ajin suka gane me Fadila take nufi da faɗar hakan, su kai ta yi masa dariya.
Tun a nan ya rasa karsashin da zai yi bayanin, duk ya ji jikinsa yayi sanyi, amma ya daure ya aro jarumta, ya daidaita nutsuwarsa, cikin kamalarsa ta zance da iya sarrafa harshe, yayi bayanin yadda ya fuskanci tambayar da yadda ya bi amsa tambayar.
Malamin da kansa ya tafawa Yazeed ya ce "Weldone Ustaz, you are genius man, ka burgeni ƙwarai mutane masu sharp brain irinka ba su da yawa, Allah ya ƙara basira"
Yazeed ya ce "Thank you sir".
Malamin ya ce "Gaskiya duk ajin nan babu wanda ya amsa daidai sai Malam Yazeed, dan haka kowa yaje ya sake faɗaɗa bincike a kan bayanin da yayi, zan yi test a kansa, idan kuma kuna buƙata ku tuntuɓe shi yayi muku bayani sosai".
"Gaskiya mu dai Sir kai mana bayanin da kan ka" cewar Fadila.
"Meye baki gane ba a bayanin da yayi?".
"Ni ban gane komai ba" ta faɗa cike da rainin hankali.
"Well, zaki iya zuwa ki same shi ya yi miki bayani".
"A'a Sir gaskiya gara ka yi mana da kanka".
"Ba zan ba" ya bata amsa.
Tura baki tayi cike tsiwa da harare-harare.
"Leave my class" malamin ya faɗa yana nuna mata hanyar fita.
Kamar kullum, ta saɓi jakarta ta fice, tana fita ya kalli 'yan ajin ya ce "A ciro takarda, kowa ya rubuta attendence, attendance 30 marks, test 10 marks.
Takardar attendence ta fara zagawa, har ta zo kan Yazeed, ya kalli takardar attendance ya kalli wurin zaman Fadila, ya rubuta sunansa sannan ya rubuta Fadila Ahmad Musa.
Bayan kammala lectures, malamin ya ƙirga ɗaliban ajin, ya ga mutum ɗaya ya hau kai, aikuwa ransa ya ɓaci, ya ce "Waye ya rubutawa wani attendance? Kowaye ya faɗa kafin in binciko shi da kaina".
Yazeed ya miƙe tsaye cikin jin kunya ya ce "Ni ne Sir".
"Wa ka rubutawa?" Yayi shiru.
Malamin ya kalli Attendance ɗin ya ɗago ya kalli Yazeed ya ce "Yazeed Hashim Sharif, Faidla Ahmad Musa, da kai da ita kun rasa wannan 30mrks ɗin".
Tana ƙarasawa ƙaramar tashar garinsu, ta tarar an fara lodi, kasancewar fuskarta sanye da niƙabi ne, babu wanda ya gane wacece, ta samu wuri ta shimfiɗa ɗankwalinta ta yi sallar asuba, daga nan ta shiga motar da za ta kai ta babbar tashar ƙaramar hukumar su.
Gari da sauran duhu, haka suka ɗauko hanyar barin ƙauyensu, babu abin da Amina take a zuciyarta sai Addu'a, da fatan Allah ya kaita lafiya ba tare da kowa ya ganta ba.
Ƙarfe bakwai suka isa babbar tasha, ta shiga tambayar direbobin nan Saminu, tare da yi musu kwatancen sa, wasu suka ce ba su gane shi ba, wasu kuma suka ce sun gane shi, amma ya kwan biyu bai shigo tashar ba, ganin gari na cigaba da haske, ya sanya ta fara tsoron kar a biyo sawunta, dan haka ta shiga motar da ake lodin Kano!.
Haka tayi ta rarraba ido, kamar agola a rabon gado, tana kallon hanya, tare da mamakin manyan gine gine da tituna da ababan more rayuwa da suke shimfiɗe a maraya, yayin da ƙauyuka ko oho, banda yau da Allah ya sa ta fito maraya ta gani da idanunta, da sai ta ce ƙaryane a garin Kano babu irin wannan manyan ababan more rayuwar, duba da yadda rayuwar karkara take da wahala, saboda rashin isar da ayyuka yadda yakamata har karkarkara.
Sai da suka yi kusan tafiyar awanni biyu cir a mota, sannan suka iso babbar tashar mota ta kabuga da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.
Ware idanunta tayi a kan manyan motocin da ke shiga suna fita a cikin tashar, wadda ta sha banban da tashar su ta ƙauye, sai a yanzu ta gane tayi wauta, ta ina zata fara neman Inda Baba yake? Ga Saminu ya ce mata yana Ikko, amma yau zai ƙaraso, to idan ya ƙaraso ina za shi? Nan Kano ko can gida? Gaba ɗaya ta rasa abin yi, ga jikinta babu daɗi, cikinta sai hautsunawa yake, saboda yunwa da kuma doguwar tafiyar da suka yi ta mota wadda ba ta saba ba. Ta samu can wani wuri a ƙarƙashin wata bishiya, ta rungume kayanta tayi zamanta tana kalle kalle.
Saminu kuwa cikin dare suka sauka, dan haka washegari da safe baccinsa ya kwanta ya sha hankali kwance saboda gajiyar tafiya. Sai wajen sha biyu saura ya tashi yayi wanka kasancewar juma'a ce, ya shirya dan ya fara biyawa ta gidansu Amina, ya sanar mata da saƙon Baba sannan ya ce ta shirya su haɗu a tasha washegari da safe, ba tare da sanin a ranar za a ɗaurawa Aminan Aure ba.
Ko da yaje gidansu Amina, sahsensu ya nufa ya tsaya a bakin ƙofa yayi salama, aka amsa masa tare da bashi izinin shiga. Sai dai yana shiga yayi tozali da Inno a zaune, idanunta sun yi jawur sun kumbura, sai ajiyar zuciya take yi, ga mata duk a zazzaune a kusa da ita.
Saminu ya ce "Subhanallah, babar Amina lafiya kuwa? Aminan ce ta rasu ko kuwa mai ya faru?".
Aikuwa Inno ta sake fashewa da kuka,maƙwabciyar su Inno ce ta iya cewa "Ka san yau za'a ɗaurawa Amina aure, har kafi anje an yi an gama komai yau ɗaurin Aure, an wayi gari an nemeta an rasa".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, an nemeta an rasa kamar yaya? Ba sai wani satin ɗaurin Auren ba?".
"A'a an dawo da shi yau, sai wayar gari aka yi babu Amina babu dalilinta a garin nan".
Saminu ya girgiza kai ya ce "Ta ina zan fara gayawa mahaifinta wannan mummunan labarin haka? Kunga illar Auren dole kenan".
"Wallahi Hanne ba ki isa ba, duk in da yarinyar nan ta shiga garin nan kin sani, Wallahi sai kin nemota dan ba zaki mayar da mu ƙananan mutane ba, yau ɗaurin Aurenta ace an nemeta an rasa, duk mun zagaye garin nan kowa yace bai ganta ba" Kawu Bala kenan, har wani irin yawu ne yake tsartuwa daga bakinsa, saboda azabar masifa da jaraba.
Inno kuwa ta sake fashewa da kuka, ita ba batun Auren ne ya dameta ba sanin in da Amina ta tafi ne ga bata da lafiya shi ne babban damuwata.
"Wallahi yau duk in da yarinyar nan take sai an nemota, ko gawarta aka tsinto a gidan Jarmai za a mata sutura, Wallahi Hanne ko ki