Showing 102001 words to 105000 words out of 296192 words
tashi daga bacci, tayi wanka ta karya, ta cigaba da tunanin ta ina zata ɓullowa lamarin Khalil, yadda zata rabashi da yarinyar nan.
What's app ɗinta ta buɗe, ta duba group ɗin su, da suke ita da Hajiya Salma da Turai, tayi sallama.
Cikin ikon Allah duk suna online, suka amsa mata, suka gagaisa tare da tambayar junansu yara da kasuwanci, Mummy ta tura musu saƙon Voice message.
"Jama'a ku bani shawara yadda zan ɓullowa lamarin yaron nan, haryanzu fa yaƙi rabuwa da ita, jiya har naje ɗakinsa na tsaya a kansa yana waya da ita, bai san na zo ba, har gaya mata yake, wai zai yi mata video na gidanta na Abuja".
Nan da Nan Hajiya Salma ta haɗa group Video call, "Lallai ma Zainab, to wani matakin kika ɗauka?"
"Zage shi nayi tsaf, amma banga alamar zai saduda ba, bina yake kuma yi, wai zai yi mini bayani, na rasa mema yakamata in yi"
Turai ta ce "Ke, ta bayan gida zaki ɓullowa lamarin, Khalil dai ɗanmu ne, ba zaki cigaba da zuba masa ido ba a mallake miki shi a banza ba"
Mummy ta tari numfashinta ta hanyar cewa "Kamar kin san har da maganar tayi masa girki ya ci naji, gaba ɗaya jiya da ƙyar nayi bacci wallahi"
Hajiya Salma ta ce "Kut kinga Zainab bamu ga ta zama ba, ba mun san in da yarinyar take ba, ai mu muka ganota a hanyar zuwa plaza, zuwa za muyi mu kasa mata warning, ko nemi gidansu muje har gidan nasu mu samu uwarta, mu musu wankin babban bargo, idan suna da zuciya zasu rabu da shi, kinga ko ya ƙi Allah ya haƙura"
Mummy ta ce "Amma kamar ƙasƙanci ne, mu wanke ƙafa mu tafi gidan talakawa yawon yi musu warning, gaskiya Khalil ya gama da ni, wai 'yar masu awara a kan kwalta, wannan yaro duk matan garin nan"
Hajiya Salma ta ce "Meye wani ƙasƙanci, biyan buƙata ai yafi dogon buri, da su mallake shi fa, da munyi nasarar raba su, ki nemo masa mata ya aura"
Mummy ta ce "Haka za ayi, bari ƙarfe huɗu bayan sallar la'asar, mu haɗu ku rakani muje"
Turai ya ce "Allah ya kaimu yammar" suka amsa da Amin.
Ganin yau ƙarfe goma babu malamin da ya shigo, ya sanya Fadila tafiya Library, dan Captain ya sanar da cewa malamin ba zai samu shigowa ba, kuma ga exams na gabatowa.
Ta nutsu sosai ta mayar da hankalinta kan littafin da ke gabanta, ba zato ba tsammani taji an ja kujerar da take ta baya, kamar zata faɗi, a razane ta ƙwala wani marayan ihu, saboda ta tsorata sosai da sosai.
Sai da hankalin wasu daga cikin tsirarun ɗaliban da ke cikin libraryn ya dawo kansu, bai saki kujerar ba, ya leƙo fuskarta ta sama yana kallonta yana murmushi.
Ta marairaice kamar zata yi kuka ta ce "Dan Allah ka sauke kujerar nan kar in faɗi"
"Ba zan bari ki faɗo ba ai".
"Dan Allah ka ajiye kujerar, bana so"
"Haka kike shagwaɓaɓiya, faɗi sunana sai in saki kujerar"
"Dan Allah ka bari, zan faɗo fa"
Sake matso da fuskarsa yayi saitin tata ya ce "Sai kin ce Yazid tukuna"
"To ajiyeni sai in faɗa"
"Ni zaki yiwa wayo yarinya, faɗi ko in kai ki ƙasa a kan kujerar" yayi maganar yana sake jan kujerar baya.
"Wayyo Allah Daddy, Yazid na faɗa ka ajiyeni dan Allah"
"Wow, sake maimaitawa in ji"
"Dan Allah ka bari" tayi maganar tana rirriƙe hannunsa, jin yadda yake kuma baya da kujerar.
"Kar ki saka mutane su juyo suna kallonmu, ke zasu gane ni na da mask a fuskata, sake faɗa"
A hankali ta ce "Ai na faɗa"
"Ki ka ce me?"
"Yazid"
"To daga yau, kar ki sake zuwa ki tsaya a kaina, cikin tsiwa kina wani cewa Ustaz"
"To naji, ajiye ni"
Zuba mata ido yayi, yana kallon bakinta, yadda take motsashi a hankali cikin tsoro.
A hankali ya mayar da kujerar yadda take.
Dafe ƙirji tayi tana sauke ajiyar zuciya, saboda yadda ta tsorata.
Kujerar gabanta ya ja ya zauna, yana kashe mata ido. Wata uwar harara ta watsa masa.
"Da kika samu na saukeki shine ki ke hararata ko" wata harar ta kuma watsa masa tana ta sauke ajiyar zuciya.
Jan littafin gabata yayi ya ce "Kawo mu gani, me kike karantawa"
Janye littafin tayi ta ce "Ina ruwanka da abin da nake karantawa".
"Hmm babu ruwana, me kika ce zan koya miki jiya?"
Cikin tsiwa ta ce "Ai na ce maka na fasa, bana son koyarwar taka"
"Aikuwa karki nuna kin sanni a exam hall"
Hararsa tayi ta saka takalmanta zata tashi.
Ya ce "Haba Besty, zauna muyi karatun mana, tun da kika shigo school ɗin nan nake biye da ke, kika je wurin Yusra, ki ka koma Aji, sannan ki taho nan"
"Wallahi ka takura mini"
Yazid yayi murmushi ya ce "To ya zan yi tun da bani da abokai, ana abota da ni ne saboda abin a za a mora wurina na karatu, ni kuma nafi son ayi abota da ni saboda Allah"
"To ni ina ruwana da wannan bayanan naka?"
Ɗan tsura mata idanu yayi yana nazartar yanayinta, a hankali ya furta "Happy birthday in advance"
Waro idanunta tayi tana kallonsa, "Waye ya gaya maka birthday na?"
Murmushi ya yi ya ce "Password ɗinki na System da kika saka na gane date of birth ɗinki, gobe in Allah ya kaimu shekarunki Ashirin da biyu, Happy birthday 'yar yarinya".
Fadila ta ce "Allah ya hore maka saka ido, da bin ƙwaƙwƙwafi, kai dama ɗan sanda ka zama"
Yayi murmushi ya ciro leda a aljihunsa, cikin fargaba ya miƙa mata.
"Meye wannan?"
A ɗan sanyaye ya ce "Karɓi ki gani, sai dai ban sani ba, ko kina karɓar abin da ya fito daga hannun talaka kamar ni ba, first gift as a brother, and at the same time friend"
Ɗan taɓe baki tayi, ta karɓi ledar ta buɗe, ta fara ciro abin da yake ciki, turaren lailatul sahara da Bushra, da kuma wani abun hannu da zobensa, da gani dai ba mai tsada bane, amma taji kyautar ta kama zuciyarta.
Ɗan murmushi ta yi ta ce "Kai ka mini kyauta ta farko wannan birthday, na gode sosai"
"Da gaske Kin karɓi kyautar da nayi miki?x yayi Maganar da mamaki, dan bai taɓa zaton zata karɓa ba.
Tayi murmushi ta ce "Gashi kuwa kana gani" ta ɓalle abin hannun ta saka, ta zura zoben.
Ta ce "Na karɓi abin hannun Ustazu" tayi maganar tana dariya, tana kallon hannunta.
Yazid yayi mata ƙuri da ido, yana kallon yadda take murmushi, da yake matuƙar burge shi, sai dai ya san cewa abu ne mawuyaci idan ya bayyana mata haƙiƙanin abin da yake zuciyarsa ta yarda da shi ba. Yanzun ma ya aka cika, shirin nasu baya ɗaukan lokaci, suke ɓatawa.
"Ya ka zuba mini ido ne?" Ta miƙa masa greeting card ɗin da yake cikin ledar, wanda rubutun larabci ne a jiki ta ce "Fassara mini wannan"
Ya kalleta ya ce 'Ki karanta mana"
"Amma dai ka san ban iya ba"
"Birthday wishes ne kawai" ta ce ok
Ta jujjuya katin tana kallon adon da ke jikins, ta ɗago ido, taga yadda ya ƙureta da ido.
"Wai kallon me kake mini ne?
"Ba komai, lokacin salla yayi, muje muyi salla" ta jinjina kai ta miƙe, ta ɗau jakarta, da ledar da ya bata suka fita daga libraryn.
Da yamma Fadila ta dawo gida, tana dawowa ta shiga falo ta watsar da jakarta a falo kamar yadda ta saba, ta shilla ɗakinta da gudu, saboda fitsarin da ya matseta.
Daidai lokacin Mummy ta fito cikin shiri, zata je ta ɗauki su Hajiya Turai.
Jakar Fadila da ta gani yashe a tsakar ɗakin ne ya sanya ta gane Fadilan ta dawo gida.
Miƙa hannu tayi zata ɗaukewa Fadilan jakarta, taga leda a ƙasa. Ta ɗau ledar ta buɗe, sai taga turare guda biyu da kati a ciki.
Sansana turaren tayi tana yamutsa fuska, tamkar wadda ta shaƙi warin bola.
Fadila ta fito daga ɗakinta, dan zuwa ɗakin Mummy, amma taga Mummyn tsaye hannunta riƙe da ledar da Yazid ya bata.
"Mummy fita zaki ne?"
"Eh fita zan yi, me kike da wannan a jakarki?" Ta nunawa Fadila turarukan tana yatsune hanci.
"Bani aka yi" Fadila ta bata amsa.
"Waye ya baki wannan tarkacen, turare kamar na 'yan bori"
Fadila ta miƙa hannu ta karɓa tare da faɗin "Wallahi turarukan da ƙamshi, wani ne ya bani"
"Waye wani?"
"Wani ɗan ajinmu ne?"
"Meye haɗinki da shi da zai baki wannan tarkacen ki karɓa?"
"Bani da wani haɗi da shi, muna mutunci ne kawai, and i can't reject it, ba zai ji daɗi ba, kuma bani kaɗai ya bawa ba"
"Shikenan, kar dai ki sake ki shafa wannan turarukan ki shiga jama'a, kowa yaji wannan turaren ya san mai arha ne, wani wari suke kamar na ciyawa, ni zan ɗan fita zan je wata unguwa"
"Ok Mummy, safe journey"
"Thank you" ta amsata ta fice.
Alhaji Ahmad bai tura ɗan aike ba, shi da kansa ya je makarantar ya ɗauko Amina, suna tafe suna hira, ya ajiyeta a ƙofar gida ya shiga da motar ciki, dan ko Baba bai san tare suka dawo ba.
Gaba ɗaya hankalin Hafsa yana kan mutanen da take sallama, tana yi tana iza wutar awararta. Wata danƙareriyar mota ce ƙirar Highlander tayi parking a gefen inda Hafsa take. Sam hankalinta baya kan abin da yake wakana wajen abin da yake gabanta.
"Ke!" Taji an yi shouting a kanta.
Cikin ɗabi'arta ta ta miskilanci, ko ɗaga kanta ba ta yi ba, ta cigaba da sallamar mutane, dan ba ta kawo ma da ita ake ba, saboda yanayin yadda aka yi maganar cikin isa da gadara.
"Ke da ke nake magana, nayi magana kika mini banaza" Jin an dunguri kanta ne ya sanya ta ɗaga kai, ta kalli Hajiya Turai dak zazzaro mata ido, amma ba ta ce uffan ba.
"Wai ba da ke nake ba? Ko bayan talauci kuma naksashiya ce ba kya ji ne?" Cewar Hajiya Salma.
Kamar ba za tayi Magana ba kuma sai ta ce "Me nayi miki ne?" Tayi maganar cikin rauni.
"Uwarki ki ka yi mini? Ina magana kina jina dan iskanci kika shareni?"
"Uwata ta gode" Hafsa ta sunkuyar da kai, tana fifita wuta.
Saboda rashin girma, da iya duniyanci, Hajiya Turai ta saka ƙafa tayi fatali da awarar da Hafsa ta riga ta tsame, ta kuma yi ball da wadda take cikin bokiti tana soyawa.
A gigice Hafsa ta miƙe tsaye ta kallesu "Baiwar lafiya,me nayi miki zaki zo wurin san'ata kina watsar mini da kaya? Ni ban sanku ba ban taɓa ganinku ba balle in ce ko wani laifin nayi muku"
Hajiya Turai ta ce "Ashe ƙaramar fitsararriya ce, yanzu da na zubar da wannan tsiyar, ai gashi kin bani dukkan hankalinki, dana ɓarar da tsiyar da kuka dogara da ita, ba kece Hafsa ba? Kin samu yaro kin asirce shi, yana muku bauta, 'yar matsiyata ce, ni na zata ma wata haɗaɗiyar yarinya zan gani, kalleki kalli kayan kayan jikinki, Khalil ya miki kama da sa'an Aurenki?"
Sai yanzu Hafsa ta gane ina suka dosa, kuma a kan me suke mata wannan tijarar, da tuni mutane suka fara taruwa suna kallon abin da ke faruwa.
Hajiya Salma ta kalli Hafsa a wulaƙance ta ce "Ɗanmu ba tsarar aurenki bane, ki duba cikin kwararon matalauciyar unguwarku, ba zaki rasa Irinki ki aura ba, ko kuma 'ya'yan kwalta lalatattu irinki, da babu yarinyar kirkin da zata zo bakin titi tana kasa kaya, tana cakuɗeɗeniya da maza, ka ce ta kirki ce, ki nemi irinki daidai ke ki aura, Khalil ba sa'an yinki bane"
Turai ta kalli wasu almajirai ta ce "Kai zo ku ƙarasa zubar mini da wannan kayan ƙazantar, zan biyaku, idan na karya jarin in ga uban da zai ɗorasu, matsiyata gayyar yunwa an samu mai kuɗi ana rawar jikin bin malamai a asirce shi aci dukiya"
Hafsa zuba musu id tayi tana kallon ikon Allah, tana kallon yadda ake cigaba da yi mata watsi da kaya, bayan ta kwashi zagi da cin mutumci a bainar nasi, Hafsa a yau tayi dana sanin sanin Khalil da tayi, dan haka ta yunƙura tayi wani abu wanda daga shi, zata yanke alaƙar ta da Khalil.
Ta ɗauko wayarta ta fara dannawa, zuciyarta na mata wani irin zafi, amma ta dake taƙi yin hawayen, ta shiga neman lambar Khalil.
Hajiya Turai ta yiwa Hajiya Zainab alama da ta fito.
Hajiya Zainab ta buɗe motar, ta fito ta nufo in da suke a tsaye da cincirindon mutane.
Gaban Hafsa ya faɗi, dan ko ba a gaya mata ba, kammanin matar da ta gani da Khalil ta san mahaifiyarsa ce.
Tuni ta turawa Khalil saƙo kamar haka
"Please man, idan ban takuramaka ba, ka taimaka mini da dubu goma"
Da saƙon ya isa wayar Khalil, yayi mamaki, dan ko da abu mai kamar wasa, bata taɓa roƙonsa abin ficika ba, amma yau tana neman dubu goma
Bai yi tunanin komai ba, ya tura nata dubu talatin.
Mummy ta ƙarewa Hafsa kallo, dan ta gano wani aibun nata, saboda ta ji daɗin cin mutuncinta, amma ba taga alamar wani aibu ba, bayan na talauci.
"Ni ce uwar Khalil, na zo ne nan ne da mutanena, dan in sake ja miki kunne, muddin baki rabu da shi ba, yadda na saka aka watsar da wannan tsiyar da kuke kasawa ku dogar da shi, haka zan saka a rushe mini in da kuke zaune, saina tabattar da kun dauwama cikin tsiya. Wannan gayyar iskar da kike kasawa, da dudu kuɗinsa bai wuce kuɗin ruwan robar da Khalil yake sha a sati ba, da na sa aka watsar, kaɗan nayi miki, kin san waye Khalil kuwa? Kin san waye ubansa a ƙasar nan, kin masa asiri zaki mallake mini shi? To ahir ɗinki wallahi, kuma daga yau na saka almakashi na datse duk wata alaƙa dale tsakaninki da Khalil, saboda ba sa'an Aurenki bane, naji ya ce ke marainiya ce, sai ki jira idan ya buɗe orphanage Home, sai ki requesting ko zaki samu gurbi"
Hajiya Salma ta ce "Talaka kenan, akwai ladabin dole, ga yadda ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, irin wannan cinikin ne idan dare yayi suke tara maza su lamube su su basu kuɗi, banda haka ina wata awara zata riƙe mutu"
"Khalil ya biyani kuɗin asarar da akayi mini, kuma daga haka insha Allah in dai ni 'yar halak ce, bani ba Khalil har abada, in sha Allah na rabu da shi"
Hajiya Turai ta ce "Kar ma ki rabu da shi, kici ubanki ko ba dan Allah ba, ai karo da karo sai rago"
DOMIN SHIGA VIP GROUP KU TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR.
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Page37
Hafsa tabi bayan su Hajiya Turai da kallo, da mamakin irin tsanar da ta gani ƙarara a idon Mummy.
Jikinta a sanyaye tabi wurin da aka watsar mata da kaya da kallo, ga sauran mutane da suke tsaye a wurin, Mussaman majalisar mai shayin nan, da wanda suke jin haushinta bata kula su, da wanda take burgesu saboda kamewarta, wasu suka jajanta mata, abin takaicin shi ne yadda har su Hajiya Turai suka yi mata tijara suka gama baby wanda yayi yinƙurin dakatar da su ko basu haƙuri sai son jin ƙwaƙwaf.
Daga irin zage-zagen da suka yi ne, wasu suka gane cewa mahaifiyar Khalil ce da jama'arta.
A gaggauce Hafsa ta durƙusa, ta dinga tsince kayanta da aka baje su a wurin kamar abun banza, zuciyarta na wani irin raɗaɗi da zafi, ta dinga ƙoƙari ta danne hawayenta, mai shayi ya tayata tsince kayan, ya so saka baki, amma ganin su Hajiya Salma sun yi kama da manyan 'yan duniya ya sanya bai iya saka baki ba. Ya tsare mata abin hawa ta shiga, mai shayi ya ce "Ayi ta haƙuri Hafsa, haka rayuwa take"
Ita dai ba ta ce masa komai ba, sai da taga mai Napep ɗin nan ya ja baburin, ya bar wurin, sannan ta fashe da wani irin kuka, mai ban tausayi da ratsa zuciya.
"Yaushe zan samu sauƙin rayuwa ni Hafsa, daga wannan sai wannan, Astagfriullah" ta faɗa a hankali tana ƙanƙame jikinta, tana cigaba da raira kukanta, tana jin yadda zuciyarta tayi mata nauyi, shikenan Khalil ɗin da ta saka rai, ta fara samun afuwa a tare da shi, shima zai kauce, zata koma waccan duniyar da yayi ta ƙoƙarin fito da ita daga ciki, mai tarin damuwa da rashin gata.
Kan su kai gida, tuni idanunta sun yi mitsi mitsi, sun yi jawur kamar wadda aka sawa teargas, ta sauko ta sallami mai Napep, ta kwashi kayan da wasu suka yi buɗu- buɗu da ƙasa, ta shigo da su ta ajiye a tsakar gida.
Mama ta kalli kayan ta kalli Hafsa ta ce "Ke lafiya kuwa? Meye ya sameki wanan kayan ya aka yi suka yi kaca-kaca da ƙasa haka?"
Hafsa na ƙoƙarin dannewa, amma ta kasa kawai ta nufi ɗaki da sauri, tana zuwa ta faɗa kan katifar Mama, ta fashe da wani irin kuka, jikinta har rawa yake yi.
Mama ta biyo ta cikin tashin hankali, tana faɗin
"Hafsa ki gaya mini, meyafaru wannan wane irin kuka ne kike yi, Ki gaya mini menene" Mama tayia maganar cikin matsananciyar damuwa tana ƙoƙarin ɗago Hafsa.
Hafsa kasa magana tayi, kuma ta kasa yin shiru, nan da nan hankalin Mama ha ninka tashi, cikin rauni ta ce "Dan Allah ki gaya mini maiya faru, ko dai Najib ɗin ne dai?" Hafsa ta girgiza kai alamar a'a.
"To Hafsa ki gaya mini menene, har bugun zuciyata ya sauya wallahi, dan Allah ki mini bayani" tayi maganar hawaye na cika idanunta.
A birkice Hafsa ta tashi zaune, tana girgizawa Mama kai ta ce "Mama dan Allah kar kiyi kuka"
"To Hafsa ya zan yi, kin shigo kina wannan uban kukan, ga kayan sana'arki duk ƙasa, dole hankalina ya tashi"
Hafsa ta sunkuyar da kanta, wasu hawayen ma zubowa, ta saka hannunta ta share hawawnta, ta ɗan ɗago ta ce "Mama ina ga bani da sa'a a rayuwata"
"Subhanallah, kamar yaya, Meyasa kike faɗan haka?"
"Mama Khalil" ta faɗa tana sake fashewa da kuka.
Cike da zaƙuwa sa son jin ƙarshen zancen, Mama ta ce "Me Khalil ɗin yayi miki?"
Cikin kuka mai ƙuna zuciya, da dashewar murya, Hafsa ta ce "Mamansa ta zo ita da wasu mata inda nake sana'a, ta ce bani babu ɗanta, wai ni ba sa'ar aurensa ba ce ba, saboda ni talakace, suka ci mini mutunci a gaban mutane, suka zubar mini da kayan sana'ata. Ai kema Mama kin san ai ba dan kuɗinsa nake son sa ba ko?"
Mama tayi shiru, ranta ya ɓaci, idan Hafsa na cikin damuwa, tana iya haɗiyeta taƙi faɗa, amma tabbas tun